Showing 87001 words to 88489 words out of 88489 words

Chapter 30 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2062

da miji da haƙuri da duk abin da ta gani, ta ji ta yi kamar ba ta ji ba, idan ta gani ma ta yi kamar ba ga komai ba. Saboda zaman lafiya da neman albarkar auren.

Ita dai kallon su kawai take yi, duk da sosai faɗan da suka yi mata na raina manya ya shige ta. Kuma ta ci burin gyara halinta don Allah ba don tana son zaman auren ba. Haka suka tafi suka bar ta tana gungunin cewa ita ma tana tafe da an kwana biyu don ba za ta iya rayuwa a gidan ba.

Da ma can ko ƙawayenta da aka zo da su ba a bar kowa ba, duk da sun so tsayawa su yi sayen baki kamar yadda aka saba yi a al'adance. Ƙanwar Amadu ta ce babu wanda za a bari gidan, tun da ba gari ɗaya ba ne ballantana idan dare ya yi su nemi gidajensu. Amma a haka sai da abokan Jabir suka ba su kuɗin sallamarsu kamar yadda shi ya buƙata, saboda ya san Bintoto ba za ta ce a yi musu wani abin kirki ba.

Haka suka Hari suka koma ƙauyen kowa yana faɗar albarkacin bakinsa, dangane halayen Bintoton da yadda suke jin fargaba da tsoron ta'adin da za ta yi idan ta samu dama. Duk da Hari ta ja Jabir gefe ta ja kunnensa a kan ko da wasa kada ya bari ta raina shi, sannan ya tirsasa ta yin abu matuƙar shi yana so. Sannan kada ya ɗaga mata ƙafar da za ta dinga jayayya da shi gudun ta kunya ta shi a idon mutane.

Ta ɓangarensa kuma, har dare ya yi bai daina tunanin huɗubar Inna Harin ba. Saboda shi kansa ya san aiki ne ja a gabansa zama da Bintoto a wuri ɗaya. Amma dole ya ƙarfafa kansa a matsayin shi ne mijin, saboda fita kunyar masu ganin wautarsa na auren ƙaramar yarinya. Duk da shi ɗin ma ba wani babba ba ne, don duka shekarunsa a duniya ashirin da bakwai ne, amma abokansa da yawa sun tsani auren ƙwaila, kuma sun nuna masa wani lokaci rainon ma wahala ne, gara yarinyar da ta gama girma a gaban iyayenta. Musamman ma ita tashin ƙauye, wadda ba ta san komai ba sai rayuwarsu ta ƙauyanci.

Shi kam ya ce shan koko ɗaukar rai, ya ji ya gani idan ba Bintoto ba sai rijiya. Dole suka bar shi da kayansa saboda ganin shi ne mai yi su 'yan Allah Ya sanya alheri ne.

***

Bintoto tana zaune ita kaɗai cikin ƙuryar ɗakinta da tagumi don ta kasa kwantawa, misalin ƙarfe tara da rabi na dare Jabir ya shigo ɗakin da ledodinsa ya ajiye a bakin gadon. Bakinsa har kunne ya dinga yi mata wani kallo kafin ya isa ya zauna kusa da ita yana cewa,

"Amarya ba kya laifi ko kin kashe ɗan masu gida."

Ba ta ɗaga kai ta kalle shi ba, kamar yadda ba ta motsa daga zaunen da take ba. Hannunsa ya kai ya nemi jawo ta jikinsa, ta zabura babu shiri tana kallon shi bayan ta buge masa hannun ta ce,

"Na shige su! Mene ne haka kuma?"

Guntun gemunsa ya shafa kafin ya yi mata wani kallo ƙasa-ƙasa da ido yana sake cewa, "Mijinki ne Fatima. Buɗe idonki da kyau ki gan ni yau ranar farinciki ce gare mu duka."

Wani kallo ta yi masa mai ɗauke da harara kafin ta ce, "Ni tun ranar da na gano kai talaka ne na daina son ka. Sannan don mugunta kai da su Kandala kuka haɗa kai kuka yi mini aure ba tare da na sani ba. Alhajin ma da ya so ya aure ni Kandala ta kore shi har da fasa masa gilashin mota. Don haka ni ba matarka ba ce, kuma kada ka sake taɓa mini hannu ko wutar hawuya ta cinye naman jikinka."

Shiru ya yi na ɗan lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Muhimmancin miji a wurin matarsa ya wuce haka Fatima Don komai na yi da ke lada zan samu, hannunki ma idan na riƙa lada akwai ladar da Allah zai ba ni, ballantana na yi kwanciyar aure da ke kin samu rabo."

Kallon mamaki ta dinga yi masa kafin ta ce, "Shi auren ma har da wata kwanciyarsa ake yi? To ni ban iya kwanciyar ba, rabon ma da ka faɗa ba na so na samu a bar ni a haka, iya cutar da kuka yi mini ta kawo ni wannan unguwar ma ya is..."

Rungumo ta ya yi gabaɗaya a jikinsa, babu shiri ta ture shi ta miƙe tsaye jikinta yana rawa ta shiga nuna shi da hannu idonta a zare tana cewa,

"Wai ashe da ma kai ma ɗan iska ne ban sani ba?"

Fuskarsa ya haɗe wuri guda shi ma ya miƙe yana cire babbar rigarsa yana faɗin, "Idan ma ɗan iskan ne ni zan koya miki yadda ake yi mu iskance tare. Ga kaza da doya da ƙwai nan na sayo mu ci idan muka yi sallah."

Zancensa na ƙarshe ya hana ta ficewa daga ɗakin kamar yadda ta yi niyya. Don batun iskancin da ya ce zai koya mata ya ba ta tsoro matuƙa, amma kazar da ya faɗa da doyar sun saka ta jin wani sanyi a zuciya. Tana laɓe jikin ƙofar ƙuryar tana satar kallon ledodin ya shige bayi, cikin sauri ta rarumo leda ɗaya ta buɗe, jikinta yana rawa ganin banza ta samu ta fara yago cinyar kaza ta kai bakinta. Ko da ya fito daga bayin ya hango ta tsaye tana ƙoƙarin taune ƙashin cinyar. Dariya ya so yi, amma ya basar yana faɗin,

"Ki shiga ki yi arwala ki zo mu yi sallah."

Tana lasar hannunta ta ce, "Ai sai ka jira na cinye ledata sai mu yi sallar."

"Ledarki kuma?"

"E." Ta amsa masa tana murguɗa baki.

"Ai ledodin duka namu gabaɗaya kuma tare za mu ci. Ki ajiye idan muka gama sallah sai mu ci."

Tana hararar shi ta ajiye ledar ta nufi bayin tana gunguni saboda jin haushin ya hana ta cinye kazar, don salon rowa kuma wai har da shi ba ita kaɗai ba.

Ta yi arwalar tana ɓata fuska ta fito, hijabi ya miƙa mata ta karɓa ta saka. Suka yi sallar daban-daban, bayan kuma ya yi mata bayanin tare da za su yi duk abin da ta ga ya yi ita ma ta yi. Amma ita kaɗai ta yi tata a ranta tana faɗin,

'Ku ji mutum, sai ka ce wani liman a masallaci. Ai wallahi ba zan bi ka ba don ko kiran sallah ban ji ka yi ba, amma don don girma haka kawai ni zan bi shi.'

Addu'a ya shiga yi musu tare da fatar zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Amma har ya shafa ita ba ta shafa ba, sai da ya juyo yana kallon ta sannan ta shafa tana haɗe fuska ta miƙe. Hijabin ta cire ta faɗa kan gadon ta kwanta tana rufe ido.

Jim ya yi na ɗan lokaci kafin ya nemo plate a kitchen cikin kayanta ya zube musu doyar da ƙwan, sannan ya shiga ɓalle kazar da ta fara ci yana ɗorawa saman doyar.

Saman gadon ya ɗora plate ɗin bayan yana kai doyar bakinsa yana faɗin, "Ki taso mu ci ko na cinye kayana."

Zumbur ta zabura cikin fushi ta zaune tana kallon Plate ɗin tana kumbura fuska ta ce,

"Raba ka ba ni nawa ban yarda da cin zalin ba."

"Ai tare za mu ci. Idan kina so na bar miki duka kuma sai idan kin yarda mu kwana a kan gado ɗaya."

Girman gadon ta kalla kafin ta ce, "To kada ka kuskura zuwa kusa da ni a cikin barci. Idan ka yarda ba za ka matso inda nake ba ni ma na yarda."

"To shikenan, ga shi ki cinye duka bari na je na yi wanka na dawo."

Cike da jin daɗi ta ja plate ta dinga ci tana rawa da kai har da 'yar waƙarta alamun tana cikin farinciki. Ko da ya fito daga wankan ya tarar da har ta cinye ta juya kwanciyarta. Murmushin mugunta ya yi bayan ya sauke plate ɗin daga kan gadon ya ajiye ƙasa yana goge ruwan jikinsa.

Princess Dija.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login