Showing 15001 words to 18000 words out of 88489 words

Chapter 6 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2060

da Allah na ci ko kaɗan ne, shi ne kuma don ba ta da imani ta yi mini sharri. Bayan ita ma ai na gan ta tana cin dambun a kan hanya tun kafin ni na ci."

Kandalar ta ƙura mata kallo tana nazarin maganar sannan ta wurga mata wata jar harara ta ce,

"Kin san Allah Bintoto ki kiyaye ni kada ki janyo na lakaɗa miki mugun dukan da zan karya ƙafarki da shegen hannun da kika ci dambun da shi. Don wannan guntun bakin naki mai kama da bakin kajin Kulu; ya tabbatar mini da cewa ƙwace dambun kika yi ta ƙarfi kika ci ba roƙon ki ta yi ba."

Bintoto ta zaro ido waje a ruɗe tana cewa,

"La'ilaha illallahu kai Kandala! To idan har da gaske ƙwace na yi mata a ce kwarankwatsa dubu ta faɗo mini a ka. Amma wallahi Allah ita ce ta ce da ni na zo na ci, idan kuma kin zaci ƙarya nake yi a kira Dijen yanzu a gabanki ki tambaye ta ki ji idan ba ta faɗi gaskiya ba."

Kandala ta yi kanta a zafafafe ba tare da Bintoton ta tantance ba ta ji ta fisgo ta da ƙarfi. Ihu ta saka tana tirjiya amma sai da ta kai ta gaban kwanon ta dangwarar da ita, tare da kai mata wata muguwar faka a ƙeyar kai. Ta faɗi ƙasa daɓas tana ci gaba da rantse-rantsen Dijen ce ta ce ta ci ita ba ƙwace ta yi mata ba, Kandala ta ɗauko kwanon ta ajiye saman cinyarta cikin ƙunar zuciya ta ɗaga wata fanteka da ke kusa da ita sama tana cewa,

"Kafin na lissafa uku ki cinye shi tas ko kuma wallahi ki janyo na ƙara ɓalle miki gotaccen hannunki yanzun nan ba tare da na tantance b...baƙar kwaɗayayyiya!"

Bintoto ta zumɓuro baki tana muimui alamun ba ta son cin dambun, kafin Kandala ta shammace ta ta kai wa bakin faka, babu shiri ta fasa ƙara dafe da bakin tana faɗin,

"Wayyo bakina!"

Kandala ta ƙara kai mata wani dundu a tsakiyar baya ranta a ɓace tana cewa,

"Za ki cinye dambun ko sai na yi miki ɗure? Don billahillazi ba zan yi kunya biyu ba, dole ne ki cinye shi tas, ni kuma na ji daɗin kai Hajo ƙara wurin Dagaci. Don da raina da lafiyata ba zan taɓa bari ki rasa maƙogwaro b...za ki ci ko sai na dinga kwakkwaɗa miki fantekar nan..?"

Bintoton ta janyo kwanon tana kwarantun faɗin,

"Innalilahi Kandala! Ni kam ko haƙora ɗaya babu a bakina duk kin zubar da su garin dukan bakin. Don Allah ni dai ki yi haƙuri wallahi na ƙoshi dubi cikin..."

Ta ƙare maganar tana turo cikin yayin da Kandala ta kai mata wani mugun mangari da fantekar a kai kafin ta sake cewa,

"Ƙundun ubanki Bintoto! Na ce da ke ƙundun ubanki malfar Amadun Jaririya! Za ki cinye ki ba ni kwanon ko kuwa sai kin jawo maƙogwaron naki ya toshe a banza?"

Bintoto ta fara kai loma tana matsar ƙwallah cike da jin zafin zagin da ta yi wa Babanta ta haɗa har da kakarta Jaririya, waton mahaifiyar Amadun. Kandala ta samo dogon kare ta tsaya kanta har sai da ta cinye dambun ta sha ruwa, sannan ta lafta mata karen a baya cikin masifa da ɗaga murya ta sakw cewa,

"To Hajo an ci dambun ki ki sa a toshe mata numfashi ma ba iya maƙogwaro ba. Sannan ke kuma wallahi kika kuskura na ji ko kallon jikanyarta kin sake yi sai na canza miki fuska, kuma ki sani kwanan nan zan mayar da ke wurin Amadu tun da kin fara lalacewa ki je can Jaririya ta ɗora daga inda na tsaya, ke kullum ba za ki bar mutum ya huta ba sai kin janyo abin da zai dame shi. Idan ban da Allah ya yi ni mai taurin ƙashi da na zuciya da tuni kin sa hawan jini ya kama ni."

Bintoto ta bi ta da wani kallo hawaye yana zuba a kan fuskarta tana zunɓuro baki tana gunguni. Kandala ta kwaɗa mata wata uwar tsawa ta ce,

"Za ki tashi daga nan ko sai na taushe ki?"

Bintoto ta miƙe tana gunguni ta yi cikin ɗakinsu, Kandala kuwa juyawar da za ta yi caraf suka haɗa ido da Kulu, wadda ke tsaye ta sha jinin jikinta tana kallon su cike da jin daɗi tana ƙumshe dariya, babu shiri ta yi saurin haɗiye dariyar da take yi ta bar wajen da sassarfa ta faɗa ɗakinta. A harzuƙe Kandala ta ɗaga murya tana cewa,

"To mazuga maƙwangama masu zuwa lahira da allon makaɗi! Kin ji daɗi ko? Sai ki zuba ruwa ƙasa ki sha baƙar munafuka, don zalunci ba za ki ce a yi haƙuri ba sai dai ki laɓe kina ta dariya! To ki sani tun da har kika ƙi ba ni haƙuri na yi ta dukan ta kina kallo; wallahi sai Allah ya isar mata a kanki, don da a ce kin zo kin ba ni haƙuri da yanzu ban yi mata abin da na yi mata ba. Ke kam Kulu zama da ke ma bai da wata rana ko kaɗan. Mani ya kwaso jangwam ya ajiye mana a cikin gida..."

Haka ta dinga sauke haushin ta a kan Kulu tana zabga faɗa kamar ta ci babu, Kulu kam ta lafe a cikin ɗakinta tana ƙyalƙyala dariya, saboda faɗan rashin dalilin da Kandala take yi a banza a wofi ya sa ko kaɗan ba ta ji zafin maganganun da take wurga mata ba.

Wunin ranar zir haka suka cinye shi daga Kandalar har Bintoto babu wata walwala, da dare ya yi ma ko kwanciyar da suke yi a gado ɗaya Bintoto ƙin hawa gadon ta yi, ta yi kwanciyarta ƙasa ita ma Kandalar ta ƙyale ta.

Sai da tsakiyar dare da Bintoton ta ga barcin Kandala ya yi ƙarfi tana ta minshari sannan ta lallaɓa ta kwanta bayanta, saboda sabo da kwanciya bayanta ya sa ta kasa yin barcin kirki tun da ta farka, ta yi ta juye-juyenta tana gunguni saboda har lokacin ba ta daina jin haushin ta ba. Amma tana kwanciya bayanta kafin ka ce me har barci ya yi awon gaba da ita, sai da Kandalar ta tashi fitsari ta gan ta a bayanta ƙafarta saman jikinta ɗaram. A ranta ta ce, 'Ba kin ce ba kya ji ba! Gobe ma ki sake 'yar malfar uba.'

Da dabara ta sauke ƙafar a hankali sannan ta miƙe ta fice ɗakin. Da safe ma Bintoto da fushi ta tashi don da ta ci alwashin sai ta rama dukan da ta yi mata a kan Dije, a cewarta tun da ta jawo aka buge ta a banza ita ma sai ta ji a jikinta, haushin hakan ya sa ko karin safe ba ta ci ba.

Tana zaune cikin rana tana shan hantsi da gunguni a bakinta suka jiyo sallamar Hari, cikin sauri ta miƙe ta nufi wurinta tana ihun murnar ganin ta, ita ma Harin cike da jin daɗi ta rungume ta a jikinta tana faɗin,

"Oyoyo ɗiyata."

Bintoto ta ruƙunƙume ta har zuwa wurin Kandala da ke ta faman wasar baki tana ce wa Hari marhaban lale da zuwa.

Jikinta yana rawa ta shinfiɗa mata tabarma ta zauna, Bintoto maƙale a jikinta suka fara gaisawa da Kandala a tsanake, sannan ta kalli Bintoto da ke wasa da gefen gyalenta tana cewa,

"Ƴata kwana biyu ya jikin naki? Ina can ina tunanin halin da na bar ki. Hannun ya warke ko?"

Bintoto ta turo baki cikin muryar shagwaɓa ta ce, "Bayan jiya Kandala ta yi ta duka na saura kaɗan ta ƙara karya mini hannu..."

Hari ta rufe baki tana ƙumshe dariya ta ce mata,

"To me kika yi aka dake ki?"

Bintoto ta share hawayenta da ya jiƙa mata fuska ta ce,

"Wai cewa ta yi na ci dambu bayan ni ko cin shi ma ban yi ba, ga shi yau ko abin karin safe ma ƙin ba ni ta yi cikina sai kuka yake yi."

Hari ta kalli Kandala tana 'yar dariya ta ce,

"Inna me 'yata ta yi aka dake ta kuma ba aka hana mata abincin safe?"

Kandala cike da jin haushi ta miƙe ta buɗa wani kwano ta ce,

"Kin ga ɗumamen tuwonta da aka ba ta ta ƙi ci tun da safe. Har hura na ce ta je ta sha idan ba ta son tuwon amma ta yi banza da ni. To don bindin jakin Amadu ki je duk inda za ki faɗa na hana abincin tun da Amadun Jaririya ya ba ni ki ce kada ya sake ba ni gobe."

A masifance ta zauna tana hararar Bintoton ta sake cewa,

"Ai wannan 'yar taki da kike gani wallahi baƙin halinta ya fara saka ni tunanin kai ta gidan ubanta, don na gaji da jawo mini maganar da take yi. Ni kenan kullum raba faɗa da bayar da haƙuri bayan ni kaina ba ta bar ni na huta ba."

Hari ta yi shiru tana nazari na ɗan lokaci sannan ta kalli Kandalar ta ce,

"Ki yi haƙuri Inna, kin san kowane yaro da kalar ƙurciyarsa, saboda haka idan har kin amince ni zan je da Bintu birni ta zauna a hannuna, idan kuma Allah ya kawo wurin aiki nagari sai na kai ta ta zauna ko babu komai tana rage miki waɗannan abubuwan da take aikatawa, amma dai ke ya kika gani?"

To fa! Anya Kandala za ta iya rabuwa da Bintoto kuwa?🤭😅

Akafta😊

*PRINCESS DIJA✍🏻*.

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D/AUTA*

*1k kacal kuɗin littafin, 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya 08022014771.*



*LAMBA SHA ƊAYA.*

Ido Kandala ta zaro tare da dafe ƙirji tana cewa,

"Aika..me...?"

Cikin sanyi jiki Hari ta ce,

"Aikatau Inna, amma kuma idan kin ga da matsala sai ta yi zamanta a hannuna kawai."

Kandala cikin rashin kuzari ta ce,

"Ke ma kin san ba zan iya rabuwa da Bintoto ba, amma idan har za a haɗa da ni a wurin aikatau ɗin sai mu je ni da ita, kin ga shikenan ba za mu daina ganin juna ba idan muna tare."

Hari ta ƙumshe dariyarta sannan ta ce, "To ai ke Inna duk in da za a kaita a can za ta zauna tare da su, kuma idan aka ce da ke za ta iya yiyuwa ma su ce sun fasa, don haka idan har kin gamsu da ba zan cutar da Bintoto ba; to ki amince ta zauna a hannuna, da sharaɗin idan ta samu aikin za ta je ta wuni wurin aikin ta dawo wurina ta kwanta. Amma ke ya kika gani yanzu?"

Nan take cikin Kandala ya shiga murɗawa saboda tashin hankali da faɗuwar da gabanta yake yi. Jikinta yana rawa ta miƙe ta ja buta aguje ta yi bayi, Bintoto ta bi ta da kallo toshe da baki tana dariya har sai da ta shige, sannan ta tashi daga kwancen da take a kan cinyar Hari ta zo daidai kunnenta ta yi mata raɗar cewa,

"Don Allah ki sace ni kawai mu yi tafiyarmu, don wallahi Kandala ba za ta amince ta bari na yi tafiyar nan cikin daɗin rai ba."

Inna Hari ta janyo hannunta ta riƙe gam sannan ta ce,

"Waton ke har murna kike yi za ki tafi ki bar ta ko?"

Bintoton ta turo baki tana cewa,

"Ni fa mai kuɗi nake son na aura a can birnin ya kai ni Makka."

Hari ta rufe baki tana dariya ta ce,

"Ashe Bintu har yanzu ba ki daina wannan shirmen naki ba?"

Bintoto ta lafe a jikinta tana cewa,

"Haƙorin Kandala ma ina so na sa a cire shi idan na yi kuɗi a saka mata na ƙarfe."

Hari tana dariyar shirmen Bintoton Kandala ta fito daga bayin riƙe da ƙugu tana haki kamar wadda ta sha gudu ta dawo mazauninta ta zauna, sannan ta kalli Hari ƙwalla cike da idonta ta ce,

"Ni dai Hari da an bar zancen nan Allah ya gani da na fi farin ciki, saboda ina hangen kamar Babanta ma ba zai amince da wannan tafiyar b..."

Bintoton ta yi saurin faɗin,

"Ke dai Kandala sai idan ke ce kawai ba ki so na je, amma ina ruwan Babana da wannan tafiyar shi da ko damuwa ba ya yi da gani na? Sai dai idan baƙinciki kike so ki yi mini kada na samu wanda zai kai ni Makka don kin ga ina son zuwa."

Kandala ta bi ta da kallo riƙe da haɓa ranta a ɓace ta ce,

"Da ina baƙinciki da ke tun a ranar da kika yi sanadin mutuwar Habi zan murƙushe ki sai kin daina numfashi, don haka tun da ma kika yi wannan maganar babu inda za ki je! Makkah kuma ki hau buzu ki tashi sama rauhanai su kai ki ki tabbata a can idan kina so ba damuwata ba ce."

Ta miƙe cike da jin haushi ta shige ɗakinta, Hari ta kalli Bintoton cikin sanyin jiki ta ce,

"Me ya sa kika ce mata haka? To bari ki ji ni na ma fasa tafiyar da ke, kuma daga yau ban sake zuwa ganin ki tun da ba ki jin magana."

Hari ta miƙe da niyyar tafiya, Bintoto ta yi saurin riƙe mata hannu cikin hawaye ta ce,

"Don Allah ki yi haƙuri Inna, daga yau na daina ba zan sake ba kin ji? Ai kin haƙura ko?"

Hari ta janye hannunta tana cewa,

"To sake ni na je na bai wa Inna haƙuri."

Bintoto ta sake ta tana share ƙwalla, Hari ta yi cikin ɗakin da sallamarta a baki, da murya ƙasa Kandala ta amsa mata saboda kukan da take yi, jikin Hari ya yi sanyi ƙalau ta zauna bakin gado zuciyarta cike da tunanin janye ƙudurinta a huta, saboda hango idanuwan Kandala da suka rine nan take zuwa ja, tsabar takaicin Bintoto da baƙin cikin da take ciki na rabuwa da ita. Hari ta fara magana cikin tattausan lafazi ta ce mata,

"Don Allah Inna ki yi haƙuri, kin san shirmen Bintoton ta iya yiyuwa ma ita ba ta san ma'anar abin da ta faɗa miki ba, don haka don Allah ki yafe mata, sannan kuma idan hankalinki bai kwanta da tafiyar ba sai a fasa kawai. Amma Inna inda kin daure kin amince da tafiyar za ki ga amfaninta a gaba, ko babu komai za ta nutsu ta rage wannan rashin jin da take yi koyaushe."

Kandala ta saka gefen zaninta ta share hawaye sannan ta ce,

"Ni dai gaskiya da a za a samo mana wurin aikatau ɗin ni da ita da na fi jin daɗin wannan tafiyar, amma wallahi ko kaɗan ba zan iya barin ta ta je birni ta zauna babu ni ba."

Hari ta ce, "To idan muka je tare Inna shi Mani da matarsa fa? Barin su za ki yi su kaɗai anan ki bi Bintoto?"

Kandala ta yi wani mere sannan ta ce, '"Tun da ba ni nake auren ta ba ai dole na bar ta na tafi Hari, idan ya ji yana iyawa ya kula da matarsa don na gaji da zaman ciyar da ita yana gindin bishiya yana shan iska koyaushe, saboda bai da wani aiki sai na zaman kashe wando suna gulmar mutane."

Hari ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta ce, "To tun da haka ne in sha Allahu zan je na bincika na ji ko za a samu inda za ki rakuɓa ke ma ki yi aikin, amma ita yana da kyau yanzu idan na tashi tafiya na je da ita, idan aka yi katari daga zuwa aka samu gidan kirki sai na haɗa ta da su, ke kuma ko daga baya ne sai na zo mu tafi idan an samu naki wurin aikin."

Kandala ta marairece fuska tana cewa, "Da dai za ki taimaka da kin bari ni ma mun tafi tare a yanzun, kin ga sai na zauna a wurinki har a samu wurin aikin . Idan ma abin kashewa ne babu to ni ina da kuɗin da zan ba ki a haɗa mu ci abinci kafin a samu nawa aikin."

Hari kanta ya yi nauyi girim, domin ta rasa ta wace hanya za ta bi ta zille mata, ganin ba dama ya sa ta amince mata dole don babu yadda za ta yi, kai-tsaye ta ce su shirya dukansu, idan ta yi kwana biyu za ta dawo su tafi tare.

Da haka aka katse maganar sannan hankalin Kandala ya kwanta, amma Bintoto hannu ta ɗora a ka tana ihu da kururuwar wayyo Allah sai ta bi Hari, duk da an sanar da ita cewa za ta dawo su tafi amma ba ta yarda ba, ita dole da ita za ta tafi ƙafa-da-ƙafa.

Da ƙyar ta samu ta shawo kanta ta fice

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login