Showing 60001 words to 63000 words out of 88489 words

Chapter 21 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2057

saka Jabir da tambayoyi har sai da ta ji wane ne shi, ɗan gidan waye da sana'ar da yake yi. A nan ta gano ashe ma ɗan ƙanwar hakimin garinsu ne Lauri, wadda ke aure a cikin birnin.

A nan ta sanar da shi idan sun je ƙauyen shi ma ya tafi don ya gana da dangin mahaifin Bintoto. A cewarta gara ubanta ya sani da wuri ya tanadar mata gadon aure kafin lokaci ya ƙure. Da ƙyar ya samu ya ɗaga daga kan tabarmar da yake kai, saboda hirar Kandala babu aya babu waƙafi, hatta inda zai ajiye Bintoto sai da ta tambaye shi ɗaki nawa ne kuma ya fasalinsu yake.

Bayan ya dawo soron ya zauna, ya shiga goge gumin fuskarsa da Kandala ta saka shi haɗawa cikin ɗan lokaci. Saboda ko kaɗan ba ya son ta ƙure shi, a sanadin tambaye-tambayenta ta rusa masa tsarin da yake kai, gudun Bintoto ta boƙare masa bayan ya fara samun kanta cikin sauƙi.

Sai dai ita ma a cikin hirar tasu babu komai face tambayoyi da hirar yaushe zai kai ta Makka idan sun yi aure. Ya ce mata ta jira su ga lokacin ya zo komai za a bi shi daki-daki, amma ta kafe lalle ita sai ya faɗa mata bayan sun yi aure da kwana nawa za su wuce ƙasashen wajen da ya ce za su je yawon buɗe ido.

Dole Jabir ya gyara zama ya shiga zuba mata daɗin baki da cin alwashi iri-iri duk don ya ƙara farauto zuciyarta, sannan ya kwantar mata da hankali ta gano ba ƙaramar sa'a ta yi ba, tun da ta samu irin sa a matsayin wanda zai aure ta.

Misalin ƙarfe tara da rabi na dare Kandala ta leƙo tana cewa ya tafi gida kada dare ya yi masa a hanya. Abin da ya riƙo mata ya ba ta, sannan ya ciro dubu biyar ya ce ta ba su Kandala su sha ruwa a hanya. Ta rako shi har bakin ƙofar gidan cike da mamaki ta dinga wara ido tana faɗin,

"Ina motar da ka zo da ita?"

Sai da ya sosa kai sannan ya ce, "Faci ta yi na miƙa ta wurin mai gyara, saboda ba na son lokaci ya ƙure ban zo ba, shi ya sa na yi tattaki a ƙafa na ƙaraso don kawai na gan ki na ji sanyi."

"Wai Allah! Har na ji sanyi! Ba ka ji yadda na ji tsoro ba, kada a ce mutanen unguwar nan sun sace maka mota, ka san duka talakawa ne babu mai kuɗin kirki a cikin su. Ni wallahi yadda zan kwana a nan ma nake tunani. Na saba da kwanciya gidan masu kuɗi, haka kawai na kwana a nan zazzaɓi ya kama ni a banza."

Jabir yana ƙunshe dariyarsa ya yi mata sallama ganin Kandala ta leƙo tana kallon su. Alamun ta gaji da hirar tana son ya tafi Bintoto ta dawo cikin gida. Tana ɗaga masa hannu har ya yi nisa, sannan ta dawo tana kumbura fuska ganin Kandala a bakin gidan tsaye ta kasa tafiyar. Ta gefenta ta raɓa ta wuce tana faɗin,

"Shikenan sai a zo a saka wa mutane ido suna hira."

"Auren ma idan ba ki yi hankali ba da ni za ki je gidan na ga tsiyar da za ki tsinana, ga ɗakina ga na uwar mijinki. Saboda dole sai an saka miki ido a ga yadda za ki yi zaman auren idan kin iya."

Bintoto ta dinga rantsuwar babu inda Kandala za ta bi ta, idan ba gadi za take so ta yi mata a gidan auren ba, sai a ɗauke ta aiki. Hari dai shiru ta yi musu tana ta shirya kaya ba tare da ta bi ta kansu ba. Bintoto ma gajiya ta yi da surutun ta kwanta tana zuba hamma, kafin ka ce me barci ya yi awon gaba da ita bayan ta gama mitar kukan sauro yana damun ta. Kandala ta zo kwanciyar ita ma tana mitar Bintoto ta matse ta kafin ta koma faɗin,

"Ɗiyar Amadu dai an yi kwana kowa ya huta da jaraba."

Hari tana gyara kwanciyarta ta ce, "Inna 'yar nan tawa watarana sai kin nemi ganin ta da kuɗi ma ba ki samu ganin ta ba."

"Sai ka ce abin kirki kuka haifa, wannan sokuwa har wani son ganin ta zan yi? Ni fa mamakin wannan yaron da ke son ta ma nake yi. Ko me ya gani a jikinta da zai wuce matan duniya ya ce sai ita kaɗai yake so?"

Hari tana zuba hamma ta ce, "Shan koko ɗaukar rai Inna."

Daga haka suka yi shiru kowa ya koma nazari kafin barci ya kwashe su duka. Asubar farin suka farka suka yi sallah, sai da suka karya sannan suka yi shiri. Ƙarfe takwas na safe a cikin tasha ta yi musu, a cewar Kandala su tafi da wuri tun kafin munafukan garinsu su fito shan iska.

"Su Mani ana can gindin bishiya, wataƙila ma babu abin da ya sauya."

Kandala ta faɗa tana juye baki gefe, saboda takaicin ya zama ragon ƙarfi da ya ji. Da ƙarfinsa amma ya lalace gindin bishiyoyi yana gulma da sa ido, bayan ga aikin ƙarfi kala-kala wanda zai nemo kuɗin da zai rufa wa kansa asiri da matarsa.

"Da a ce Kulu ba juya ba ce, da tuni asirin Mani ya tonu."

Kandala ta yi maganar cikin ƙunar rai, saboda takaicin Mani ko tuna shi ta yi sai ta ji haushi. Hari da Bintoto babu wanda ya bi ta kan zancenta, saboga gyangyaɗin da suke yi, daga ita har su barcin suka sha har aka isa garin, ba tare da sun sani ba. Alamun rage gudu da saukar motar ya sa suka farka, ɗan dako ya ɗaukar musu kayansu zuwa gida, don a kan hanya suka rabu da Hari ita ma ta nufi nasu ɓangare.

Tun daga nesa da yara suka hango Bintoto da Kandala suka fara ihun murnar ga su nan, nan take gari ya ɗauka Kandala da Bintotonta sun dawo daga birni. Cikin ɗan lokaci gidansu ya cika da mutane ana ta yi musu barka da zuwa. Bintoto kam tun a kan hanya ta fara rabon minti da biskit, yara suka biyo ta buuu a baya suna ta tsalle.

Kandala kuma ta baje saman tabarma har da buɗe ƙafafuwanta a bakin ɗakinta, sai wasar baki take yi ana ta shigowa yi musu barka da zuwa. Kulu ma duk da ta san watan tashin hankalinta ne ya dawo, amma hakan bai hana ta jin daɗin ganin su ba.

Mamaki fal ran Kandala ganin alamun ciki a tattare da Kulu. Hakan ya sa duk ta motsa sai ta kai kallonta gare ta, don tana so ta tabbatar shin cikin ne ko kuwa jin daɗin an bar mata gidan ita kaɗai ne ya sa ta sauya. Babbar ɗiyar Kandala da 'ya'yanta suka garzayo ana ta murnar dawowarsu.

Mani yana tsaka da hira cikin abokansa ya ji labarin zuwan su Kandala. Baki har kunne ya isa cikin gidan abokansa suna zolayar shi da cewa, ya tashi ga rumbun hatsinsa can ta dawo. Sai dai hango Kandala cikin bisashenta tana ta faɗa ya ji ƙirjinsa ya buga. Don bayan mutane sun rage ta nufi wurin da take kiyon, ganin kamar babu uwar garken akuyarta. Jikinta yana ɓari ta shiga ƙwala wa Kulu kira, ta iso wurin cikin faɗuwar gaba ta rusuna tana faɗin,

"Inna ga ni."

Wani kallo ta yi mata mai ɗauke da tuhuma kafin ta ce, "Ina kuka kai mini uwar garkena?"

Kulu ta shiga sosa jiki da kai tana ƙoƙarin magana amma ta koma in'ina, alamun ba ta son cewa komai. Sai da ta buga mata tsawa haɗe da zagi cikin ɗaga murya sannan ta ce,

"Ai...ai...Inna lokacin da kina can ciwo na y..."

"Ciwo kika yi ni na ɗora miki ciwon?"

Kulu ta shiga girgiza kai kafin ta samu bakin faɗin, "Sh...shi ne da aka kai ni asibiti sai likita ya ce sai an yi mini hoto ga ciki. Da muka dawo babu kuɗin Mani ya ɗauki uwar garken ya sayar aka yi mini magan...."

"Na rantse da Allah! Na rantse da kabarin kakana Buba Shagirbi sai kun biya ni akuyata daga ke har shi Manin! Yanzu don ba ku da imani shi ne za ku rasa akuyar da za ku sayarwa sai uwar garken...? Shin ke gidanku babu akuyoyin ne ko ba kina da kaji ba? A kan me za a ɗaukar mini akuya a sayar ba tare da na sani b...."

"Inna cik...ciki ne gare ta, Inna shi ya sa na biya kuɗi likita ya duba ta aka ceto lafiyarta. Kuma wallahi Inna akuyar ma ta kwana biyu ba ta da lafiya, gudun ta faɗi ta mutu a yi biyu babu na nemo Ɗan Alhaji muka daidait...."

Zancen Mani kenan cikin rawar jiki da tashin hankali, don da ma ya shirya wa zuwan ranar, saboda ya sani muddin ta yi ido biyu da dabbobin ba ta hango uwar garken ba akwai matsala. Kafin ta katse shi cikin fusata tamkar za ta kai masa duka ta ce,

"Dole ku daidaita! Lalle dole ku samu daidaito da Ɗan Alhaji a kan akuyata! Tun da ni ce na yi gohon yi wa Kulu cikin. To billahillazi ka kwana da shirin sai ka biya ni akuyata daga kai har ita, ko kuma kolo ya gan ku a cikin faɗin garin nan. Don ficikata ba za ta yi ciwon kai a kan hidimarka ko ta Kulun ba. Ciki kuma idan dare ya yi ka ƙara yi mata wani yau sai ta haɗa biyu, ɗaya a gabanta ɗaya a bayanta, tun da ka tanadi kuɗin abin yankawa da icen yi mata ruwan zafi."

Haƙuri ya shiga ba ta tare da yayarsa da mutanen da ke shigowa yi mata sannu da zuwa. Amma hakan bai hana ta ci gaba da faɗanta ba, sannan ta sanar da shi duk abin da ta tara Bintoto za ta kashewa. Idan ma ya kwana da tunanin yi wa Kulu ciki don ta yi suna ya yaudari kansa.

Takaicinsu shi da Kulun ya sa ba ta kwana ba sai da ta nemo mai sayen dabbobin duka aka yi cinaki. Babu jinkirin komai ya bayar da rabin kuɗi ya ce idan safiya ta waye zai kawo rabi. Da kuɗinta ƙulle a ƙugu ta kwana, zuciyarta cike da saƙe-saƙen yadda za ta sayar da gonarta a sirrance ba tare da Mani ya sani ba. Saboda ko damuna ta kama sai dai ta bayar da ita sufuri idan ba ita ce za ta yi noman ba, amma shi ba ya iya yin komai sai zaman kashe wando a cikin gari.

Saboda ya saba da lalaci auren ma ita ce ta yi masa, hakan ya sa ya yi tsammanin za ta ci gaba da ɗaukar ɗawainiyarsa kamar yadda ta saba.

Tun da safe ta bayar aka sayo mata kaji masu kyau ta shiga aiki Bintoto da sauran jikokinta suna taya ta. A cewarta kada iyayen Jabir su zo neman auren Bintoto Amadu ya kasa yi musu fitar kunya. Da kanta tare da taimakon maƙota aka dafa shinkafa da miya. Bayan ta yi wa Kulu kashedin kada saka mata hannu tun da tofe-tofen yawu take yi. Bintoto ta dinga yi mata gwalo tana dariya ta ce,

"Yelumm! Wata ta ji haushi an hana ta aiki saboda ƙazanta."

Kulu ba ta kula ta ba, gefe ta ja tana kallon mutane ana ta hada-hada, jefi-jefi tana ta tofar da yawun da ko kaɗan ba ta iya haɗa su ballantana su wuce cikin maƙoshinta. Da ma can aikin ƙarfin hali ne ta so yi, saboda ƙarnin naman kajin da aka yanke gabaɗaya ya hana ta jin daɗin zuciyarta. Sai da ta shige bayi ta yi amai sannan hankalinta ya kwanta.

Bintoto kam sai rawar kai take yi tana ta faɗa wa mutane ta kusa aure kuma mijinta mai kuɗi ne, har da Makka zai kai ta. Jamila da sauran ƙawayenta suka cika gidan suna ta kallon ta cike da burgewa, uwa-uba ƙaryar da take ta sharara musu ba ƙaramin sha'awar zuwa birnin ta cusa musu ba.

Musamman da Inna Hari ta zo gidan ta sa Bintoto ta yi wanka ta saka sabuwar atamfarta cikin kayan da Hamida ta kai aka ɗinka mata. Ta yi kyau sosai ga sabon kitson da ke kanta ya ƙara fito da fuskarta. Inna Harin ta ce ta saka mayafi mahaɗin atamfar sai ta fi kyau, fiye da hijabin da ta dunkuma ta ɓoye gayun. Ga sabuwar sarƙa da ɗan kunne sun yi mata ɗas tamkar ba ita ba.

Abokanta sai jan ta suke yi kowa yana so ya yi magana da ita. A ƙarshe wulaƙancin da ta yi musu ya sa suka ja gefe suna kallon ta. Saboda ture Jamila ta yi da ke kusa da ita tana faɗin,

"Ke dalla matsa can, wallahi duk warin talauci kuke yi. Dube ku don Allah gabaɗaya ma ko wanka ba ku yi ba. Ni yaushe zan iya zama cikin ku ku shafa mini ƙazanta saurayina ya zo da motarsa ya ji ina warin dauɗa. Yawwa bari na faɗa muku tun yanzu, idan ya zo kada wadda ta je wurin sa, don ko kin je ni zan faɗa masa ban ma san ku ba."

Haushin maganganun da ta faɗa musu ya sa suka bar gidan suna gulmar ta. Yayin da suka yi dandali a ƙofar gidan suna zancen yadda ta koma 'yar birni daga zuwanta har ta samu miji mai mota. A nan suka yi shawarar su ma za su roƙi Hari ta tafi da su birnin ta samo musu maza masu kuɗi, kamar yadda ta samo wa Bintoto miji mai mota.

Princess Dija.

32.

Da misalin ƙarfe uku na rana Jabir da iyayensa suka dira gidan hakimi. A can aka gama tantance yadda za a tafi gidan Amadu Baban Bintoto. Don tun kafin zuwansu Kandala ta tafi da kanta ta sanar da shi abin da yake faruwa. Hakan ya sa ko da iyayen Jabir da wakilan hakimin suka isa: sun tarar da tabarma an shimfiɗa musu. Sannan da yayu da ƙannen Amadu waɗanda suka karɓi zancen auren hannu biyu. A nan aka yanka sadaki dubu ɗari Jabir ya biya lakadan. Sannan da kuɗin gaisuwar iyaye ana ta addu'a da sam-barka. Musamman ganin motar da ya zo da ita matan garin sai leƙe suke yi ana ta faɗin Bintoto ta yi goshi, kuma ta taki arziƙi daga zuwa birni aikatau ta dawo da miji mai kuɗi.

Bayan sun bar gidan su Amadun suka nufi gidan Kandala, a can aka yi musu babbar tarba ta musamman. Don ɗakin Kandala aka jera masu kwanonin abincin da ruwa mai sanyi har da zoɓo. Jabir da abokinsa tare da iyayensa biyu maza suka saki jiki suka narki abincin iya cikinsu. Naman kajin ma babu abin da suka bari sai ƙasusuwa tsabar garɗin naman da daɗin miyar Kandala mai wadatacciyar daddawa.

Lokacin da suka gama aka bar Jabir shi kaɗai sannan aka kira Bintoto su gaisa kafin su wuce. Bintoto ta shigo kanta tsaye idonta a kan kwanonin abincin, zuciyarta cike da ɗokin idan sun fita ta hau kan naman kafin a riga ta.

Hango ƙasusuwa a saman murfin kwanon miyar ne ya sa ta shiga satar kallon kwanonin tana dogon wuya, don gabaɗaya hankalinta yana can ba shi take sauraron abin da yake faɗa ba. Fahimtar inda hankalinta yake, Jabir ya yi 'yar dariya yana cewa,

"Gaskiya miyar nan taku ta yi ɗan banzan daɗi. Wataƙila ma ke ce kika yi girkin shi ya sa na ji daɗinsa sosai."

Bintoto ta shiga hararar kwanon miyar tana turo baki ta ce, "Ai ni ba abin da na iya. Duk abin da ka gani Kandala ce ta yi tare da Inna Maimuna."

Baki a sake Jabir ya dinga kallon ta yana ƙoƙarin goge maiƙon bakinsa da hankacif ya ce, "Gaskiya ki koya kafin mu yi aure. Idan ba so kike yi mu fasa zuwa ƙasashen wajen ba mu zauna garin nan Kandala ta dinga ba mu abinci b...."

Wani kallo ta yi masa kafin ta taɓe baki tana cewa, "Hu'um! Ni kam ba zan zauna a garin nan ba sai dai idan kai kaɗai za ka zauna. Yanzun nan ma fa har na gaji da garin, na matsu mu tafi warin talakawa ya fara damu na."

Dariya ta so suɓuce masa, amma dole ya matse ta a bakinsa ya miƙe yana gyara zaman babbar rigarsa ya ce,

"Mu za mu wuce sai kun zo, don na san ku ma ba za ku jima a nan b..."

"Ai gobe-goben nan za mu wuce. Idan ma ba su tashi tafiya ba ni kam na gaji komawata zan yi."

Tana maganar yana saka takalminsa suka fita tsakar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login