Showing 12001 words to 15000 words out of 88489 words

Chapter 5 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2056

Bintoto ta maka mata harara tana cewa,

"Ke dallah ki shigo mu je mu nuna masa gidan! Kin ga sauri yake yi kada mu ɓata masa lokaci."

Jamila ta fara ja da baya tana girgiza kai alamun tsoro, cike da jin haushin ta Bintoton ta sake magana a harzuƙe,

"Idan fa ba za ki shigo ba mu tafiya za mu yi wallahi!"

Cikin ɗari-ɗari Jamila ta shiga motar da ƙyar jikinta yana rawa saboda ita ma ba ta iya shiga motar ba, mutumin ya fito ya rufe musu ƙofa sannan ya koma mazauninsa ya tayar da motar, har ya yi gaba Bintoto ta yi saurin cewa,

"Ba ta nan ake bi ba! Juya baya akwai hanya mai sauƙi ta can inda ka fito."

Mutumin cikin aminta da zancenta ya yi ribas ya koma baya har suka ɓulle hanyar, cike da jin daɗi Bintoto ta sake nuna masa wata hanya tana cewa,

"Yawwa bi ta nan!"

Mutumin ya bi inda ta ce, suna tafe tana nuna masa hanyoyin da zai bi kamar haka;

"Miƙe wannan hanyar, yawwa sha kwana, miƙe sha waccan kwanar, ƙara miƙewa sha kwanar, yawwa bi ta nan..."

Haka ta dinga yi masa kwatance Jamila tana kallon ta cike da mamaki da fargaba har aka kai su kasuwa, cikin sauri Bintoto ta kama abin buɗewa cike da sa'a tana jawo shi ta buɗe ƙofar, jikinta yana rawa ta fito cikin sauri tana ƙumshe dariya ta kalli Jamila da ke zaune duk ta gama tsurewa ta ce da ita,

"To ai sai ki fito Malama!"

Ta fito da ƙyar sannan Bintoto ta rufe masa ƙofarsa da karfin gaske har sai da ya kai kallonsa a kan murfin. Sannan ta zo ta gefensa tana ƙumshe dariya ta ce,

"Yawwa mun gode Alhaji! Allah ya saka da alheri."



Mutumin ya zaro ido cike da mamaki Bintoto ta dafe tiren goronta da ke kanta ta manna da gudu. Jamila kam sororo ta yi tana fargaban abin da zai yi musu ta kasa motsawa daga inda take tsaye, sai da Bintoto ta waigo cikin gudun tana cewa,

"Wallahi ki zo mu je idan ya yanke miki kai babu ruwana."

Jin haka ya sa Jamila bin bayanta da gudu ita ma, yana ta kiran su amma ina ko waigo shi ba su yi ba. Sai ma ƙara ƙaimin gudun da suke yi suna ƙoƙarin shigewa cikin mutane. Bintoto tana gudu tana dariya har suka ɓace masa cikin dandazon mutanen da suka zo cin kasuwar.

Mutumin ya bi mutanen da ke kasuwar da kallo cike da tsabar mamakin da suka ba shi, babu shiri ya fashe da dariya shi ma saboda ko kaɗan bai yi tunanin za su iya yi masa wayo, hakan ya sa bai ji haushi ba. Asali ma shirmensu nasu nishaɗi ya saka shi, yana ta dariya har ya samu wani a cikin filin kasuwar ya tambaye shi ta inda zai bi ya isa gidan hakimin garin.

Mutumin ya yi masa nuni da hannu a kan ya koma cikin garin duk wanda ya tambaya zai kai shi gidan, ya yi masa godiya tare da ciro kuɗi ya yi masa alheri, sannan ya buga motarsa ya koma cikin garin.

Bintoto kam bayan sun daina gudun suka shiga sauke numfashin wahala, wata rumfa suka zauna suna dariya. Jamila tana nishi ta ce,

"Wallahi ke muguwa ce Bintoto, yanzu don mugunta kika hana mu nuna masa gidan kika saka shi ya yi wannan wahalar a banza?"

Bintoto dafe da cikinta tana dariya ta ce, "To ba mun sha lotonmu ba? Haka kawai sai mu bar banza ta wuce mu? Da fa yanzu ba mu isa zuwa kasuwar nan ba."

Jamila tana ci gaba da dariya ta ce,

"Kin san Allah; ban taɓa shiga mota ba sai yau, ashe haka ake ji idan an shiga wani shuuuuuu kamar ana tafiya cikin iska?"

Bintoto ta sake fashewa da wata arniyar dariyar sannan ta ce,

"Allah ya so ni ni kam na taɓa shiga sau ɗaya wannan ne na biyu, ai yasin da ban san ta yadda zan buɗe motar ba, da shikenan ƙaryarmu ta ƙare don wallahi tsaf zai iya tafiya da mu garinsu, ya kai mu a yanka mu da ranmu su sha daɗinsu."

Jamila ta miƙe tsaye tana faɗin, "Ni dai ta shi mu je kada ya zo ya same mu a nan mu shiga uku."

Bintoto ta miƙe tana cigaba da dariya ta ce, "Ke kam Jamila wallahi baƙar matsoraciya ce ke, shi ya sa ba koyaushe nake son fita da ke talla ba."

Jamila ta yi banza ba ita, har suka ci kasuwar suka siyar da komai ba su daina dariyar abin da suka aikata ba.

.

1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lambar; 08022014771.

D/AUTA Ce✍🏻

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA TARA.*

Bayan sun gama cin kasuwar, a kan hanya Bintoto ta ja wa Jamila kunne cikin tsiwa ta ce mata,

"Saura kuma idan muka koma gida ki faɗi abin da muka yi asirinmu ya tonu."

Talatu tana dariya ta ce, "Ba zan faɗi ba ai, kada na sha duka a banza wajen Habu, ko daman can neman abin da zan yi kawai yake yi don ya dake ni koyaushe."

Bintoto ta yi mata wani kallo a lalace sannan ta fara magana tana jifar ta da harara ta ce,

"To ke sai ki zauna kina kallo ƙato ya yi ta jibgar ki? Ai na rantse da Allah da ni ce ke tsaf zan sha fili da shi mu daki juna. Ke ko kin tsaya tsoro yana cin zalinki a banza..uhumm!"

Jamila ta zaro ido waje tana cewa,

"Rufa mini asiri Bintoto! Yayan nawa zan daka? Cabɗijam! Ai da kuwa a ranar sai ya somar da ni idan ya riƙa ni."

Bintoto ta murguɗa mata baki tana marmaɗi da ido tana cewa,

"Eh, shi fa! To ubanki ne da ba za ki rama ba? Ni wallahi kin ga Kulu idan ta dake ni ramawa nake yi, ke ko Kawu Manin ne ya dake ni wani zubin cizon shi nake yi ballantana ke da Habu yake yayanki, ai ba haifar ki ya yi ba."

Jamila ta riƙe baki da tagumi tana jinjina maganar Bintoton kafa j ta sake cewa,

"Cabɗijam! Ai ranar da duk na gwada ramawa na san har karya ni sai ya yi wallahi, yanzun ma fa sai Inna ta saka baki yake ƙyale ni idan ya yi zuciya..hu'ummm! Lalle! To Ni kin ga tafiyata tun kafin wani ya ji hirarmu a faɗa masa na shiga uku."

Kai-tsaye ta saki hanyar da suke bi ta yi ratsen wata hanyar da za ta kai ta gidansu. Tafiya take yi amma a cikin zuciyarta tana ta jinjina irin dukan kawo wuƙar da za a yi mata a duk ranar d ta yi kuskuren rama dukan da Habu yake yi mata. Saboda Babansu ya ba shi damar hukunta duk wanda ya yi laifi a cikin gidan, har Innarsu wani lokaci yana hana ta abu kuma ya sa ta yi, saboda ko kaɗan ba ta tsayuwa inda Allah Ya ajiye ta, ba ta da aiki sai yawon gidaje da an yi an ce. Shi ya sa wani lokaci har gida ake zuwa turkar ta, don ma Habun yana namijin ƙoƙarin kare mata martaba a duk lokacin da aka zo gidan da ƙudurin cin zarafinta.

Bintoto kam da harara ta bi Jamila cikin jin haushi ta ce,

"Ni ma idan ban da ƙaddara ai ke ba tsarata ba ce ballantana har na yi abota da ke, don watarana ma idan na yi kuɗi ku ne masu goge mini silifas a lokacin da na dawo daga Makka."

Haka ta yi ta mitar zancenta tana tafiya tana surutai tamkar da wani take labari, da abin ya yi mata daɗi ma ajiye tiren goron ta yi tana wata kalar tafiya cikin yauƙi har da sagale hannu irin na 'yangayu, tana yatsine fuska riƙe da ƙugu ta ce,

"Ke kawo mini abinci ki je ki ɗebo mini ruwa na sha, ke kuma zo ki yi muni fifita zafi nake ji. Yawwa ke kuma zo lunda mini hancin..."

Haka ta yi ta hauka ita kaɗai sai da ta hango wani dattijo tafe a kan hanyar sannan ta ɗauki tiren ta ɗora a kai tana tafiya tana cewa,

"Ai na rantse duk na yi kuɗi sai nasa an yi mini wanka, don babu abin da zan sake yi sai dai na yi zaunena a yi ta mini komai. Haka kawai zan bari na yi wasa da dama ta! Bayan a garin nan namu kaf babu wanda ya fi ni son na zama Hajiya matar Alhaji."

Tana gaf da shigewa gidansu ta hango wata yarinya ɗauke da kwano a kanta, murya ta ɗaga tana kiran sunanta tare da bai wa yarinyar umarnin ta zo. Cikin haɗe fuska ta waiga saboda ta gama gane muryarta tana gunguni ta ce,

"Aike na a ka yi fa!"

Bintoto ta galla mata harara tare da riƙe ƙugu ta sake cewa,

"To wani abu na ce zan yi miki? Cewa fa kawai na yi ki zo."

Yarinyar ta kafe a kan ba za ta je ba sauri take yi, Bintoto ta tako cikin fushi da taƙama har inda yarinyar take tsaye tana ta gunguni. Fuskarta a haɗe ta cewa yarinyar,

"Ni dai buɗa mu gani mene ne a cikin kwanon? "

Yarinyar ta yi mata wani kallon uku kwabo tare da ja baya tana cewa,

"To dambu ne, kuma aike na aka yi na kai wa Inna tsohuwa."

Bintoto ta ɗaga kai kasancewar ta fi yarinyar tsawo ta buɗa murfin kwanon duk da yunƙurin hana ta gani da ta yi, ƙamshin manƙuli da dambun ya sha ya sa ta yi saurin haɗiye yawu muƙut riƙe da murfin ta leƙa fuskar yarinyar cikin sassauta murya ta ce,

"Don Allah Dije kin bari na yi loma uku?"

Yarinyar ta girgiza kai alamun a'a, Bintoto ta ɓata fuskata cike da jin haushi ta ce,

"To biyu fa?"

A nan ma yarinyar ta turo baki ta ce,

"Aike na fa aka yi ba nawa ba ne."

Bintoto ta marairece fuska ta ce,

"To loma ɗaya kacal! Na san dai ita ba za ki hana ni ba ko?"

Yarinyar cikin ƙosawa ta yi saurin cewa,

"To ni dai kada ki yi babbar loma kada a gane an taɓa."

Bintoto ta washe baki cike da jin daɗi ta jefa hannunta a cikin kwanon da ke saman kan yarinyar, tsabar mugunta ta kwaso dambu cike fam da hannunta har da tozo, cikin sauri ta kai bakinta tana runtse ido. Da ƙyar ta samu ta haɗiye shi, idanuwanta har da ja suka yi garin haɗiyar yawun da zai wuce mata da shi a wuya, maimakon ta mayar da murfin ta rufe salun-alun; sai ta koma ɗebo wata arniyar lomar da ta kwashe fiye da rabin dambun tana faɗin,

"Sai dai ki yi haƙuri don wallahi ni kam ba zan tsaya iya loma ɗaya ba."

Ganin ta'asar da ta aikata yarinyar ta fara mita a kan don Allah ta rage kada a ce ita ce ta cinye shi a hanya. Amma hakan bai hana Bintoto auna dambun a bakinta ba, sannan ta rufe mata murfin ta yi ƙoƙarin yin magana tana cewa,

"Ni dai yi sauri ki tafi kada wani ya gani a ce na cuce k...."

Tsautsayi ya sa dambun ya sarƙe ta, nan take ta fara tari babu ƙaƙƙautawa saboda ya shaƙe mata wuya sosai, yayin da wani ya shige ta hancinta.

Ihu ta fasa tana zarar ido tare da jefar da tiren tallar goro ta faɗi ƙasa tana murƙususu cikin ƙasa, sannan tana ci gaba da tari riƙe da wuyanta cikin fitar hayyaci, yarinyar tana kallon ta tana murguɗa baki da gunguni ta ce,

"Allah ya ƙara miki baƙar muguwa."

Ta bar ta a nan tana ta mulmula a cikin ƙasa, tari kawai take yi tare da neman agajin ruwan da za ta sha amma babu kowa a wurin. Sai da ta gama jigatuwa tana gaf da shiɗewa sannan maƙociyarsu Duduwa ta fito daga gidansu, kamar almara ta hango ta kwance a ƙasa tana wani irin tari da nishi tamkar numfashinta zai fita, da sauri ta ƙaraso wurinta tana salati, cikin firgici da mugun tsoron da ya shige ta, ta tallabo ta suka yi wurin Kandala tana ƙwala mata kira cikin gigicewa.

Saboda ta tsorata da yanayin da ta gan ta, cikin sauri ta ajiye ta tsakiyar gidan ta ɗebo ruwa da gudu tamkar ta kifa ta kai wa bakinta, da sauri Bintoton ta fara zuƙar ruwan iya ƙarfinta, yayin da ruwan da sauran dambun da bai wuce ba suka haɗu suka sake sarƙe ta har zuwa cikin ƙwaƙwalwar kanta da hancinta. Babu shiri ta faɗi kwance riƙe da hanci da kai tana kwarara ihu da ɗan sauran ƙarfin da ya rage a jikinta.

"Wayyo zan mutu! Hancina! Kandala hancina!"

Kandala ta ƙara ruɗewa ta ja ta a jikinta ta fara hura mata maɗiga, sannan ta koma bubbuga mata baya a haukace, Bintoto kam sai ihu take yi tare da rirriƙe wuyan Kandalar saboda azaba. Sai da ƙyar ta ji abin ya lafa mata, sannan ta daina kururuwa bayan ta tara wa kanta mutane. Waɗanda ba ta san da su a kanta ba sai da ta fara dawowa cikin hayyacinta, a nan aka shiga jajanta wa Kandala tare da addu'ar Allah Ya tsare gaba.

Amma tsabar shaƙiyanci irin nata, bayan kowa ya watse ta dawo dariyar Kandala saboda ganin yadda ta nemi haukacewa don kawai ta sarƙe. Cike da jin haushin firgicin da ta saka ta a banza, ta dungure mata kai tare da tashi daga zaman 'yan borin da ta yi, bayan ta kakkaɓe ƙasar da Bintoton ta yi mata wanka da ita a lokacin da take turmuje-turmuje a cikin ƙasa.

"Wai Allah! Yau na ciyo wa kaina wahala, amman fa wallahi dambun da daɗi Kandala."

.

Ta yi maganar tana kallon bayanta, babu shiri ta waigo cikin faɗa ta yi magana cike da ƙunar rai ta ce,

"Dambun mutane kika ci ashe? To Wallahi duk kika jawo mini rigima yau sai kin ci duka a cikin gidan nan."

Bintoto tana dariya ta sake cewa,

"Raina ne ya biya da shi Kandala, shi ya sa na ɗan ci kaɗan, amma fa cikina ya cika kamar na ƙoshi da na sha ruwan nan yanzu."

Kandala ta buɗa baki za ta yi magana kenan suka ji muryar Inna tsohuwa kakar Dije, surfa bala'i take yi tun a soron gidan har ta shigo cikin gidan, Bintoto ta miƙe jikinta yana rawa ta yi bayinsu da gudu, Inna tsohuwar kuma kasancewarta 'yar bala'i tana ƙarasowa gaban Kandala ta dangwarar da kwanon dambun, a masifance ta fara magana tana haɗa numfashi ta ce,

"Ga dambun nan na kawo mata ta ƙarasa cinyewa! Amma ku sani sai ta san ta ci shi yau! Don daga nan idan na fita wurin Malam Mainasara zan je a ja mata yasin mai wuta, gobe ko an ce ta sake tare Dije ta taɓa abincina wallahi ba za ta iya ba. Domin kuwa gabaɗaya sai na sa an shafe mata maƙogwaro ta yadda ko ruwa ba za ta iya haɗiyewa ba ballantana ta ci abinci."

Tana gama faɗar hakan ta wuce fuuuuu ta bar gidan, Kandala ta bi kwanon dambun da kallo ko motsi ta kasa yi, saboda takaici ya daskare ta wuri ɗaya tamkar icen da aka gama dasawa.

1K ne kuɗin littafin. 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lambar; 08022014771.

D. AUTA✍🏻

*SHAGALALLIYA*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA GOMA.*

Ranta a ɓace ta waigo ta kalle ta fuska a haɗe ta ce,

"To ai sai ki zo ga dambun nan an kawo miki ki ƙasara cinyewa, tun da kin zama mayya! Ke har kullum nasiha nake yi miki amma Allah bai sa kika koyi kawar da kai da danganar Musulunci ba? Ke kenan ba za ki ga abu ki bar shi yadda kika gan shi ba sai kin yi shigar sharu ba shan...ki zo na ce!"

Ta ƙarasa maganar a ƙufule cikin fusata, Bintoto ta baro jikin katangar bayin da take laɓe cikin ɗar ɗar ta isa gaban Kandala cikin marairece fuska fiki-fiki da ido ta ce,

"Wallahi Allah Kandala ita ta ce na zo na ci ina tafiyata ni ban ma san da ita ba, amma ta kira ni. Kuma sai da na ce mata ba zan ci ba, ba zan ci b...ta yi ta roƙo na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login