Showing 39001 words to 42000 words out of 88489 words

Chapter 14 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2063

da turo baki, don ta san halinta sarai, abu ne mai wahala ta bari a yi abin arziƙi da ita ba tare da ta kawo wata matsala ba. Saboda ko a can ƙauyen ita ce ke hana ta zuwa makaranta a wasu lokutan, a cewarta boko karatun 'yan wuta ne, barin sa ya fi alheri idan mutum yana so ya gama da duniya lafiya. Makarantar zauren ma ba zuwa take yi ba, ko Mani ya faki idon Kandala ya kora ta gidan da bulala ba ta zuwa, yawonta kawai take yi a cikin garin ba ta nan ba ta can. Sai ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta koma gida, Kandala ta yi ta saka mata albarka da jin daɗin ta tafi Makaranta.

Hakan ya sa Bintoton gano shirun Kandala, musamman tagumin da ta rafka. Inna Hari ce ta yi hanzarin faɗin,

"Ai in dai karatu ne Inna ba za ta hana ki ba Bintoto. Rashin jin ki ne kawai ake gudu, ki je ki jawo wa mutane wata fitinar a can ana zaune lafiy..."

"Yo ai Inna na daina komai da nake yi, ki tambayi Maman Baby ga ta nan ki ji...don Allah ki faɗa musu gaskiya zan yi karatu ba zan koma yin rashin ji ba."

Ta ƙare maganar tana kallon Hamida idonta cike da ƙwalla. Hamida ta yi murmushi kawai don ita kanta ta san abu ne mawuyaci shiryuwar Bintoto a cikin ƙanƙanin lokaci. Amma tana ji a ranta kamar idan ta je makarantar, karatun ya fara kama jikinta za ta rage wani abu, ko kuma idan ta yi rashin mutuncin malamai suka horu ta a can, wataƙila za a samu ta rage halinta a huta da jarfa.

Wata gwauruwar ajiyar zuciya Kandala ta saki kafin ta kalli Hamida cikin sanyin jiki ta ce, "Ki yi haƙuri da abin da zan faɗa miki yanzu, saboda na fi kowa sanin wace ce Bintoto da ɗanyen aikinta, don ba na son garin neman gira a tsokale ido..."

"Ni dai Kandala gaskiya ki amince kawai, haka kawai ki ce za ki hana ni don kin ga Allah Ya sa zan zama 'yar gayu. To wallahi ni dai ko ba kya so tun da ina son karatun sai na yi."

Ta ƙare maganar tare da haɗe fuska cikin muryar kuka, ranta a ɓace ta miƙe tsaye tare da ɓare baki ta fasa wani uban kuka tamkar ƙaramar yarinya za ta bar wurin, Hari ta yi hanzarin riƙo hannunta cikin zafin nama ta zaunar da ita tana cewa.

"Ke fa matsalata da ke taɓara, idan kika bi a hankali ai za ta amince ne. Amma kina wannan shirmen yaushe za ta fahimci kin sauya halinki har ta bari ki yi Makarantar da kike so?"

Bintoto ta yi hanzarin share hawayen fuskarta tana kallon Kandala cikin fuskar tausayi tare da turo baki tana muimui. Kandala ta maka mata uwar harara sannan ta yi magana tana miƙewa tsaye ta ce,

"Nan da kika gan ta ko barci sai an yi da ƙyar take tashi, idan ba yanzu aka samu ta sauya halinta ba a sanadin zama gidan nan. Karatun ma ko a garinmu ba son sa take yi ba, sai Mani ya kora ta da bulala har zuwa makarantar sannan take zuwa. Don haka kada ki ɗora wa kanki wannan nauyin ki bar ta kawai ta ci gaba da aikin da ya kawo ta ana biyan ta kuɗinta duk wat..."

"Inna ki bar ta don Allah tun da tana so."

Hari ta yi maganar cikin sassauta murya, don ita ma a son ranta tana so a ce Bintoto ta samu karatun ko don ta goge ta zama 'yar birni kamar yadda take yi mata hasashen samun miji a birni, idan aka dace ta san ciwon kanta sannan ta zubar da shirmen da ke cikin ƙwaƙwalwarta.

Kandala ta nufi hanyar ficewa fuska babu yabo babu fallasa tana cewa, "Ku dai yi yadda kuke so, amma ku sani duk rigimar da ta ɗebo a tsakaninku ne babu ni a ciki ballantana ruwana."

"In sha Allahu ma babu abin da zai faru Inna, ki dai taya mu da addu'a."

Hari ta faɗa tana shafa kan Bintoto ta sake cewa,

"To 'yata, yanzu dai Inna ta amince, amma don Allah ki nutsu kada ki ba mu kunya kin ji?"

Bintoto ta ɗaga kai, tare da miƙewa cikin yin wani tsallen murna ta haye bayan Kandala, sannan ta ruƙunƙume ta tana ihun faɗin,

"Ina mugun son ki Kandalata."

Hari da Hamida suka saka dariya, ganin tana ƙoƙarin kayar da Kandalar garin farinciki, ita kuma ba ta yi ƙasa a gwiwa ba wurin sakar mata duka a saman ƙeyar kanta ba, tana faɗin ta sake ta.

A nan aka sake bin zancen karatun nata a tsanake, bayan Hamida ta nemi alfarmar su zauna su ci abinci kafin su tafi. Ta yi musu jagora har zuwa ɗakin Bintoto sannan ta kai musu abincin a can suka baje. Bintoto a jikin Kandala suna cin abincin, tare da kalolin santi iri-iri a wurin Kandala suna yi mata dariya, saboda bakinta dagaje-dagaje da maiƙon jar miyar tana faɗin,

"Uh'umh! Yanzu Bintoto haka kike cin wannan daɗi kullum safiya ta Allah?"

Bintoto ta washe bakinta tana lasar hannunta, ba tare da ta ce komai ba. "Ai dole ki mini boren ba za ki bar wannan gidan arziƙi ba...wai Hari ko za ki tambayar mini matar gidan mu ji idan akwai wurin zamana ni ma su ɗan sakaya ni cikin gidan don Allah?"

Zancen Kandala kenan tana jinjina kai bayan ta gama gwaiguyar ƙashi tana faɗin,

"Duniya da daɗi Allah mai iko."

Hari ta yi hanzarin rufe bakinta tsabar wata kalar dariya da ta so kufce mata, sai da ta haɗiye tsokar miyar da ke bakinta tana tauna sannan ta ce,

"Ai ke Inna ire-iren waɗannan gidajen babu masaukin tsofaffi a cikinsa. Amma ki yi addu'a idan 'yata ta samu miji sai a yi miki ɗaki a can gidanta ki taya ta zaman auren..."

"A'a gaskiya Inna, ni dai ta yi zamanta wurin ki kawai, kada ta je ta dinga ɓata mini gida da yawun goro."

Dundu Kandala ta sakar mata a tsakiyar baya har sai da ta gantsara, ta kifa kanta saman tsintsiyar hannunta tana gunguni bayan ta sandare tana aika wa Kandalar wani malalacin kallo. Ƙwafa ta yi a lokacin da Inna Hari ta ce,

"Inna wannan dundun ai zai iya huda mata baya mu shiga uku."

"Gara kawai bayan ya hude tun da ba ta san ciwona ba Hari. Ni ce kawai a wahale koyaushe ina goyon rashin mutuncinta, amma ita ko kaɗan ba ta san darajata ba ballantana na sa ran za ta jiƙaina idan ta yi hankali."

"Ki yi haƙuri Inna ƙurciya ce kawai ke damun ta, idan ta yi hanakalin ai da kanta za ta gano inda duniya ta nausa gaba ta dawo kyautata miki. Don rabon Makka ta farko ke ce da kujerar idan muna da rayuwa."

Kandala ta yi mere tana dungure wa Bintoto kai ta ce, "Uhum, wannan da kika gani idan ta ƙara wanke dauɗarta da ruwan birni cewa za ta yi ma ba ta san ni b..."

Dawowar Hamida cikin ɗakin ya sa suka yi gum tare da jefar da zancen halin Bintotob aka kama wani zance daban, amma fuskar Kandala ko kaɗan babu annuri, alamun Bintoto ta gama ɓata mata rai.

Hamida ta yi musu sha tara ta arziƙi suna ta godiya, ita ma tana godiyar tsarabar da suka kawo mata. Ta bai wa Kandala sabuwar atamfa, sannan da rakiya har bakin ƙofar gida, saboda Hamida ta fahimci kukan da Kandala take yi duk da a fakaice take share ƙwallar tana baje fuska da murmushin yaƙe. Jikin Hari ya yi sanyi ƙalau, a kan fahimtar shirmen Bintoto ne ya ɓata mata rai har take hawayen, saboda ɗan zaman da ta yi da ita wuri ɗaya ta karanci mugun ƙulafucinta a kan jikar tata, bayan zallar tsagwaron son da ta ɗora mata tamkar ba ta da kowa sai ita kaɗai a cikin duniya.

Da dabara ta ja Hamida gefe, bayan Kandala ta yi gaba ta bar su a baya tace da ita, don Allah ta ƙara haƙuri da halin Bintoton, kuma ta lurar da ita muhimmancin Kakarta da yadda take ƙaunar cigaban rayuwarta. Saboda a tarbiyyar da Kandalar ta yi mata babu cusa tausayi a kan ɗawainiyar da take yi da ita tun tana ƙarama har girmanta. A komai ganin take yi ita dole a yi mata, babu zancen taimakon ta za a yi ko kuma alfarma ce za a yi mata. Shi ya sa ko kaɗan ba ta jin komai don ta ɓata wa wani ko ita kanta Kandalar. Saboda a rayuwarta ba ta san muhimmancin kowa ba ballantana ta san girman mutum ko ta mutumta mutane.

Hamida ta yi wa Hari alƙawarin ɗora Bintoto a hanyoyi masu kyau, sannan ta ƙudurta haƙuri da ita ko don ta tallafi rayuwarta ta samu lada.

Haka suka rabu jiki babu kuzari kowa da abin da yake saƙa wa ransa. Bintoto ma da ke cikin giyar rashin sanin ciwon kai kewar rabuwa da Kandala ya saka ta zubar da hawaye.



Bayan sun tafi ta shige ɗakinta tana ta kuka, zuciyarta cike da son zuwa gidan Inna Hari ta kwana, a gefe ɗaya kuma cike da ɗokin karatun da za a saka ta. Tana ta wassafa yadda za ta saka uniform da kurin da za ta yi a matsayinta na ɗiyar mai kuɗi idan ta je.

Hamida kuwa, takaicin rashin dawowar maigidanta ya sa ta manta shaf da zuwa ɗakin Bintoto ta ga halin da take ciki, har ta shige barci. Saboda ya kira ta a waya yana sanar da ita ba zai samu dawowa ba.

Da ma ɗabi'arta ce rufe gida ko da rana balle duhun dare ya kutso kai. Don haka Bintoto ta kwana a falo TV a kunne tana kallon Wrestling har ita ma barcin ya yi awon gaba da ita. Sai da Hamida ta ji hayaniya tsakiyar dare ta fito a tsorace. Saboda nannauyan barcin da ya ɗebe ta ba ta farka ba sai da kukan Baby ya tayar da ita.

Da hannu a ka ta isa gaban Tv ta kashe ƙirjinta yana bugawa, sannan ta zare komai da ke jone ranta a jagule ta gyara mata kwanciya tare da rufa mata bargo da ke yashe ƙasa, wanda ta yi guzurinsa daga ɗakinta zuwa falon, don kawai ta ji daɗin kallo a lokacin da ta shige cikin bargon, ranta fes ta baje ɗaiɗaya a kan doguwar kujera. Bayan ta gama ciny tsarabar da Kandala ta kawo mata, kayan fruit ɗin da ta yanka a faranti ma tana kallo tana tsinta da cokali mai yatsu tana sha tana yanga. A ranta tana jin kanta wata hamshaƙiya ganin yadda take yin abin da take so babu mai kyarar ta.

Asubar farin Hamida ta tayar da ita sallah, tana gunguni ta ja bargonta zuwa ɗaki ta datse ƙofa. Saboda ba ta son Hamida ta sake takura mata bayan ba ta gama yin barcin ba. Maimakon ta yi sallah sai ta koma kan gado ta duƙunƙune, wani sabon barci ya kwashe ta sai ƙarfe bakwai da minti ashirin ta farka. Shi ma a sanadin dukan ƙofar ɗakin da Hamida ta yi ta yi ranta a ɓace. Saboda ta yi ƙwanƙwasa ƙofar cikin arziƙi har ta gaji ta fara masifa, tare da kiran sunanta a fusace.

Zumbur ta zabura cikin tashin hankali ta faɗa bayi, saɓanin buɗe ƙofar da ya dace ta fara yi ko don ta daina kiran sunanta a sama. A gurguje ta yi wankan sannan ta fito ta buɗe ɗakin, daidai lokacin da Hamidar ta dawo cikin shirin fita aiki, fararen kayanta na asibiti a jiki don ta bar wurin ta je ta shirya ganin ta ƙi buɗewa. Ranta a ɓace ta fara balbale ta da faɗa tamkar ta rufe ta da duka, don tsabar haushi ba ta san lokacin da ta dungure mata kai ba tana faɗin,

"Wai ke ba za ki sauya halinki ba ko? Kalli yadda kika bar ɗakin tun kwanukan abincin jiya da baƙi suka ci kin kasa kwashewa. Sannan kin yi wa falo kaca-kaca da ledodin biskit da na minti, kuma kin sha fruits kin bar farantin sai da na ɗauke miki. To buɗe kunnuwanki da kyau ki ji na gaji da halinki, ko ki gyara ko ki bar gidan nan a yau ɗin nan! Ba za ki saka ni hawan jini ba tun ina yarinyata, haka kawai kafin na haifi yaran da za su saka ni ciwon kai ke ki haifar mini da wani ciwo. Wai tsabar kin raina mutane hatta Tv a buɗe kika bari ta kwana tana aiki. To idan kika bari maigidan nan ya dawo ba ki sauya ba ke ma kin sani ba zai zauna da ke a haka b...."

"Don Allah Anti ki yi haƙur..."

"Yi mini shiru shashasha! Shin kin yi sallah?"

Bintoto ta shiga rabon ido alamun rashin gaskiya tana sosa kai ta ce, "A'a, amma ni dai na..na yi wallahi tun cikin dare da kika tayar da n.."

"Ba ki yi sallah ba!"

Hamida ta yi maganar kai-tsaye ranta a jagule tare da riƙe ƙugu tana wurga mata wani mugun kallo ta sake cewa,

"To sai kin bar gidan nan! Kuma karatun ma an fasa saka ki, don babu yadda za a yi na zauna da wadda ba ta yin sallah a cikin gidana. Oya haɗo kayanki na wuce da ke inda aka kawo mana ke...ba zan iya ba gaskiy..."

A miliyan ta kai ƙasa riƙe da ƙafafuwanta tana magiyar faɗin, "Don Allah...don Manzo Sallallahu alaihi wasallama Anti ki gafarce ni.... wallahi na tuba daga yau ba zan sake b..."

Princess Dija ✍️

24.

"Yi mini shiru!"

Ta katsa mata tsawa, Bintoto ta sha jinin jikinta riƙe da towel ɗin da ke kanta tana kyarmar jiki. Umarni Hamida ta ba ta a kan ta tashi ta yi sallah, kuma minti uku kacal ta ba ta ta gama komai ta same ta a falo.



Ta fice cikin sauri saboda ƙarar wayarta da ke tashi alamun ana kiran ta. Bintoto ta miƙe cikin rawar jiki ta doddosa sallah faka-faka don ba ta san me ake faɗa a cikin sallar ba, daga cikin kayan da ta ba ta ta saka kala ɗaya. A gurguje ta fice hijabi a hannunta har tana cin tuntuɓe ta isa falon ido tsakiyar ka tana haki, tamkar wadda ta sha gudu.

Tsaye take a kan Hamida har ta gama wayar sannan ta yi saurin durƙusawa ƙasa tana faɗin,

"Ina kwana Anti?"

Hamida ta yi mata wani kallo kamar ta yi dariya amma ta basar tare da ɗauke kallonta a kanta ta ce,

"Kin sa na yi latti, da na so kai ki makarantar da za ki fara zuwa a yi miki 'yantabiyu. Amma kin ja wa kanki sai gobe idan kin yi sammakon yin sallah kin shirya cikin lokaci. Don haka yanzu mu je na ajiye ki gidan su Hajiya, idan na dawo aiki zan biya na ɗauko ku don Baby ma a can zan barin ta. Kuma saura rashin jin da kika yi jiya ki gwada yi musu a can, kin ga shikenan kin hutar da ni yi musu bayanin yadda halinki yake da yadda za mu rabu da ke salun alun."

Tana maganar tana tafiya da 'yarta a kafaɗa ta fice falon zuwa farfajiyar gidan da jakarta a ɗaya kafaɗar. Jiki babu kuzari Bintoto take bin bayanta har bakin mota, sai da ta yi magana sannan ta rufe ƙaramar ƙofar shiga falon gidan ta miƙa mata makullin. Ta shige motar cike da jin daɗi a ranta, amma fuskarta babu annuri, saboda hararar Hamida da take yi ta gefen ido. Har suka kai gidan su Hajiyar idonta a kan sitiyarin motar da Hamida take juyawa cike da ƙwarewa, a ranta tana jin watarana sai ta fita yawo da motar Hamida a garin, tun da ta gano jujjuya hannu kawai ake yi da sitiyarin tuƙin babu wuya.

Baby tana ta gwarancin ta a kusa da ita amma ko kaɗan ba ta bi ta kanta ba, sai da ta jawo ta a lokacin da Hamida ta tsayar da motar ƙofar gidan sannan ta ɗauke ta tana faɗin,

"Yi shiru, zan saya miki goriba."

Hakan ya sa Hamida ta bar ta da ita, ta shige cikin gidan da sasaarfa tana faɗin, "Ki biyo ni da ita ki miƙa ta wurin Hajiya."

Ta yi gaba ta bar su a baya, Bintoto ta rage tafiya sai da ta ga ta gama gaisawa da miagadin gidan sannan ta bi bayanta, a ranta tana faɗin,

'A kan 'yarki zan rama duk cin zalin da kika sa kare ya yi mini. Kuma ma don rainin hankali sai da kika yi niyyar kai ni makaranta a yau kika fasa. To wallahi sai na fanshe komai a kanta.'

Tana tafe tana zancen zucinta har ta shiga wani ɗan soron da ke kai mutum cikin gidan, a cikin famfas ta nutsa akaifarta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login