Showing 81001 words to 84000 words out of 88489 words

Chapter 28 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2065

titin makarantar ta tsaya tana neman abin hawa. Kwatsam sai ga Alhaji mai mota ya durfafo bakin titin, ya tsaya saiti da ita yana murmushi bayan ya zuge gilashin ya ce ta shigo su tafi.

Babu shiri ta washe baki tsabar farin ciki da jin daɗi ta yi hanzarin buɗe motar ta shige. Ya ja suka tafi yana cewa da ita,

"Amaryar mai kuɗi. Yaushe kika ga ya dace a saka ranar auren namu?"

Ta yi hanzarin rufe fuskarta da tafin hannayenta tana leƙensa ta kussuwar 'yan yatsunta tana dariya. Alhajin yana dariyar shi ma sannan ya ce,

"Ina so idan muka je gidan ki haɗa ni da wani a gidanku za mu yi magana."

Cike da farin ciki ta ce, "Inna Hari kake so na kira maka ko Kandala?"

Yana kallon titi ya ce, "Babu wani namiji a gidan naku?"

"Mu kaɗai ne a gidan, saboda gidan Inna Hari ne muka zo ni da Kandala. Amma Kawu Mani yana can garinmu da Babana."

"Na gane, danginku suna ƙauye zama kawai kuke yi a nan garin, haka ne?"

Ta ɗaga masa kai tana 'yar dariya ta ce, "Amma fa ni Na fi son zama garin nan saboda 'yan gayu ne. A can garinmu kuma 'yan ƙauye ne ko Makka ba sa zuwa. Ai kai za ka kai ni Makka idan ka aure ni ko?"

"Makka da Umrah duka zan kai ki idan kina so. Har da wasu ƙasashen ma za mu je yaw...."

"Hu'um! Haka Jabir ya faɗa amma daga baya na gano ashe talaka ne bai da kuɗi. Allah Ya sa kai ma ba ƙarya ce kake yi mini ba."

Ta yi maganar tana gyara zamanta tare da haɗe fuska tana murguɗar baki. Jim ya yi kafin ya yi magana saboda rashin jin daɗin abin da ta furta ya ce,

"Ƙarya kuma?"

"E, ita ya yi mini, ba ka ga lefen da ya kawo mini ba kayan ma kala biyar ne, kuma abin haushi har da bireziya da wando ya saka mini. Sai ka ce an faɗa masa cewa ni 'yar iska ce kamar sa."

"Lefe?"

"E."

"Kina nufin an kawo miki lefe?"

Tana murguɗa masa baki ta ce, "Amma ai ba na son auren. Ni kai nake so na aura shi bai da kuɗi talaka ne."

Shiru kawai ya yi mata ba tare da ya ce komai ba, saboda ya shiga nazarin yin abin da ya dace. Hakan ya sa ya ji ya dace ya ga wata a cikin mata biyun da ta kira sunansu. Bai sake cewa da ita komai ba har suka isa ƙofar gidan, kai-tsaye ya ce ta shiga ta kira masa Kandala ko Hari. Ta fita da gudu ta faɗa gidan, mintuna a tsakani ta fito da gudu ta koma cikin motar ta zauna tana haki.

"Bari na fita kafin su zo. Ke ma ki fit...."

Zancen Alhajin ya katse saboda kiran sunan Bintoto da Kandala ta yi dafe da ƙirji a cikin tashin hankali ta gefenta.

Daga ita har Alhajin suka kai kallonsu gare ta babu shiri. Kafin Kandala ta riƙe abin buɗe motar tana ƙoƙarin buɗewa da niyyar ta jawo Bintoto ta fito da ita ta ƙarfi. Bintoto ta murɗa abin buɗewar ta ciki da karfi ta turo ƙofar har sai da ta ƙwale wa Kandala kai. Ihu da salatin da ta yi ya sa Bintoto saurin kai hannunta ga goshin nata tana shafawa cike da fargaba ta dinga faɗin,

"Wayyo Allah yi haƙuri. Ke ce ba ki janye ba har na ƙwale ki."

A fusace Kandala ta kai mata dundu a baya kafin ta cakumo hijabinta tana jan ta tana faɗin, "Yau sai kin faɗa mini uban me mai motar nan ya aikata da ke a cikin motar."

Haka ta dinga jan Bintoto tana tafiya tan tirjiya tare da faɗin, "Wallahi ni aurensa zan yi yana da kuɗi kuma ya amince zai aure ni."

Tana maganar tana turo baki, yayin da Kandala ta dage sai ta saka ta gidan ta ƙarfi. Ganin ba za ta iya da ita ba ya sa ta rarumo wani ƙaton dutse ta yi kan motar Alhajin ta sauke a gilashinsa na gaba. Ji kake fassss ta rugurgutse masa kaya, sannan ta koma borin faɗin,

"Sai na yi shari'a da kai matuƙar ka ɓata mini rayuwar Bintoto. Baƙin mugu azzalumi mai furfurar 'yan iska! Irin ku ne ke ɓata yaran mutane! Yarinya da aure a kanta amma kake bibiyar ta? Munafuki ɗan iska mai ruwan la'anannu! Uban me za ka yi da ita idan ba so kake yi ka cuce mu a banza ba? An yi mata auren ma ba za ka bar ɗaukar a mota ba sai ka yi mana shaiɗanci da baƙar manufar da kake bin mu da ita! Wallahi Allah Ya saka mana a kan duk abin da ka aikata sai mun yi shari'a da kai a gaban Allah. Don haƙƙin aure ba zai bar ka ka huta ba har abada tsinannen Allah da Ma'aiki."



Haka Kandala ta dinga yarfa masa miyagun maganganu tana kuka har ya bai wa motarsa wuta ya juya. Ta bi shi da ruwan duwatsu tana jifar sa kamar wata mahaukaciya har sai da aka riƙe ta.

Nan take mutane suka taru a kanta suna ba ta haƙuri tana ta kuka Hari tana rarrashin ta da maganganun kwantar da hankali suka shige gida. Turus suka yi suna kallon Bintoto, wadda haushin abin da Kandala ta yi wa Alhajin ya sa ta ji gara kawai ta bar musu gidan ta tafiyarta ta huta da halinta.

"Ina za ki je da jakar kaya haka?"

Bintoto tana gunguni ta ce, "Wurin Babana zan koma garinmu. Na gaji da halin Kandala ba zan iya zama da ita ba."

Princess Dija

39.

Hari ta sandare wuri ɗaya tsabar takaici da rasa abin yi, dangane rashin hankalin da Bintoton take shirin aikatawa.

Cikin muryar kuka Kandala ta zagaye su ita da Bintoton ta shige ɗakin Hari tana faɗin, "Ai sai mu tafi tare a yi bikinki a kai ki ɗakin mijinki haka ma ya fi mini alheri."

Hari ta yi saurin karɓe jakar da ke hannun Bintoto ta ja hannunta zuwa cikin ɗakin ranta a ɓace. Zaunar da ita ta yi saman gado sannan ita ma ta zauna bayan ta mayar da jakar inda ta ɗauko ta. Daidai lokacin da Kandala ta gama lalubo wasu kuɗi a inda ta ɓoye su tana ƙoƙarin kwance mugun ƙullin da ta yi wa kuɗin tana cewa,

"Hari, kira Jabiru ki ce masa ya shirya za a kai masa amaryarsa a cikin kwanan nan. Sannan ki karɓo kayan da muka saya a wurin masu shago. Waɗanda kika kai ajiya ma ki karɓo su duka a je a yi mata jeren ɗaki. Da ma sai da na faɗa miki, gara a miƙa masa ita tun lokacin da aka ɗaura musu auren kowa ya huta da mugun halinta. Amma kika ce a jira shi bai gama nasa shirin ba, to ni dai na shirya kai masa ita sai ya ƙarasa shirin tana can gidan nasa."

Hari ta yi shiru ba ta tare da ta ce da ita komai ba, sannan ba ta iya motsawa daga zaman da take yi ba. Har Kandalar ta gama kwance ƙullin ta shiga lissafin kuɗin tana goge hawaye da gefen hannunta tana cewa,

"Abin da ya dace kenan tun da har ta iya haɗa kaya ta ce za ta bar gida ta koma gidan ubanta. Da ta faɗa mugun hannu gara a kai ta gidan mijin kawai a wuce wurin."

Shiru ɗakin ya yi kafin Bintoto ta gyara zamanta tana cewa, "Wai wane aure ne ake zancen an ɗaura? Kuma ni ce ake nufin za a kai gidan miji?"

Wani kallo Hari ta yi mata kafin ta ce, "Aure dai da kika sani ana yi tsakanin mace da namiji shi aka yi miki da Jabir. Kuma tun da kika san salon ki bar gida gara a kai masa ke kawai, da ki je ki faɗa baƙin hannu abin ya zo ya dame mu gabaɗay...."

"To ni yaushe ma aka yi mini auren ban sani ba? Ni fa na faɗa muku ba zan auri talaka ba mai kuɗi nake so."

"Idan kika je gidan nasa za ku yi kuɗin tare idan Allah Ya haɗa arziƙinku wuri ɗay...."

"Wallahi ni ko na je gidansa idan na ga bai da kyawu dawowa zan yi."

Zabura Hari ta yi tana nuna ta da hannu cikin ɓacin rai ta ce. "Wai ke wace irin ɗiya ce ana taro ki kina ƙara botsarewa! Shikenan ke ba ki san kin yi kuskure ba ballantana yanzu ki gano laifinki ki bai wa Inna haƙuri? Ana gabas kina yamma tsabar kin raina mutane! To ki shiga hankalinki tun kafin ki kai ni bango na yi miki mugun dukan da sai an rasa gane kamannink...."

Hari!"

Kandala ta kira sunanta da ƙarfi saboda ganin yadda ta tunzura za ta iya yin abin da ta furta. Cikin sauri Hari ta ce,

"Inna ki bar ni da ita yau na nuna mata ni ma na iya tijara tun da ba ta gane kowane yare sai na ɗaga murya! A kan me za a bar ta tana gwara kanmu ta inda ta ga dama? Gaskiya ni kam haƙurina ya kusa ƙarewa, don haka ki yi shiru ki bar ni da ita Allah ma ya sani kin yi iya ƙoƙarinki a kanta. Yaushe za a zuba mata ido ana tausar ta ana nuna mata hanya amma a ce sai abin da ta ga dama take yi?"

"Haƙurin dai za mu ƙara yi da ita Hari. Saboda na fahimci tun farko ita Allah bai yi ta kamar sauran mutane b...."

"Ba haka ba ne Inna, wallahi tun farko don ba a nuna mata ta yi kuskure shi ya sa rashin hankalinta yake ƙara yin gaba. Amma da a ce an tanƙwara ta tun tana ƙarama da yanzu ba a dinga shan wahalarta da yawa har haka b...."

"Dakata Hari!" Kandala ta faɗa tana mayar da kuɗin inda ta ɗauko su bayan ta sake ƙulle su tamau tana cewa,

"Kada dai a ce da ni kike waɗannan maganganun naki duka. Saboda ni ce na ƙi tanƙwara ta tun tana ƙarama ba ita ce ta ƙi tanƙwara kanta ba. Idan ma don muna zaune cikin gidanki ne kika gaji da mu kika koma faɗa mini magana a fakaice; to kin yi haƙuri tafiya za mu yi mu bar miki gidan gobe-goben nan, gara ki sani ni ma na gaji da zaman da nake yi a garin nan. Saboda ga shi da aurenta Alhazawa suna ƙoƙarin ɓata mata rayuwa a banza garin son abin duniya da shegen kwaɗayi irin nata."

"To ni dai Allah Ya san komai Inna, tun da ba ki son a yi wa Bintoto faɗa na bar ki da ita ki yi duk abin da kika ga ya fi. In sha Allahu daga yau ba zan ƙara shisshigin saka kaina cikin sha'aninku ba. Na karɓi ƙaddarar rashin haihuwar da Allah Ya ɗora mini na yarda da Habi ta haifi Bintoton ba ni ba. Kuma in sha Allahu ni ma aure zan yi a cikin wata mai kamawa, idan da rabon na haihu zan haihu. Da ma saboda ku na ƙi amincewa da zancen auren, amma tun da haka ta faru babu komai kowa ya yi abin da ya ga zai fisshe shi."

Tana gama maganar ta fice ta bar musu ɗakin. Aikace-aikace ta tsiro a tsakar gidan cikin zafin nama, saboda ranta ya gama ɓaci da halin Kandala da na Bintoton duka. Kuma ta saka wa zuciyarta ko ba su bar gidan a goben ba kamar yadda Kandalar ta faɗa, ita za ta yi aurenta kurkusa ta huta da ajiyar su cikin gida suna caza mata kai a banza.

Sororo Kandala ta yi naɗe da hannuwa tana kallon bakin ƙofa, saboda tun da ta bi Hari da kallo lokacin da za ta fita daga ɗakin; ba ta ɗauke idonta wurin ba tsabar mamaki da wani sabon imanin da ya shige ta nan take. Musamman zancen rashin haihuwar da ta yi, da auren da ta faɗa za ta yi saboda su ta ƙi amincewa.

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi tsabar sanyin da jikinta ya yi a lokaci ɗaya. Don nan take ta ji rashin daɗin fushin Harin da ɓacin ran da ta gani kwance a kan fuskarta, cikin raunanniyar murya mai ɗauke da nadama ta ce,

"Ikon Allah! Ashe Hari kina son mu har haka da yawa ban sani ba? Ni kam da kin faɗa mini wannan maganar tun kafin yanzu ai da tuni kin yi aurenki kin gama. Ina ni ina hana ki yin sunnar Ma'aiki? Ai ko yankan namanmu ake yi a garinmu gara mu koma mu bar ki ke ma ki sarara a cikin gidanki."

Hari ta yi banza ba ta ce mata komai ba, ganin Kandala tana ta jimamin abin tare da maimaita maganar da ta yi mata bayanin barin gidan ta yi aurenta. Hakan ya sa daga can tsakar gidan ta ɗaga murya tana ce mata,

"Idan ma lokacin auren ya yi ai ba a nan zan zauna ba Inna. Ya ce gidana daban zan zauna ba tare da sauran matansa ba."

"To shi wannan gidan sai ki yi ya ya da shi? Ko sayarwa za ki yi?"

"Idan kina da ra'ayin ci gaba da zama garin nan za ki iya zamanki, don ba sayar da shi zan yi ba. Idan kuma ba kya son zaman shikenan sai na zuba 'yan haya su dinga biya na kuɗi duk shekara."

"Allahu Akbar Hari. Ubangiji Allah Ya yi miki albarka. Ban san da wane baki zan nemi yafiyar ki a kan ɓacin ran da na saka ki ba. Ni kaina ban san wane irin hali ne da ni ba, idan na ji ana yi wa Bintoto faɗa sai na ji kamar ana yankan naman jikina. Don Allah ki yi haƙuri da halinmu daga ni har ita Hari. Don yanzu na tabbatar ko ni ce na durƙusa na haife ki iya biyayyar da alherin da za ki yi mini kenan. Wataƙila ma ko Habin ba za ta iya yi mini irin ladabin da kike yi mini b...."

"Za ta yi fiye da haka ma Inna."

Hari ta yi saurin faɗin hakan saboda ganin kukan da Kandala take yi, wanda da ma can a kusa ruwan hawayen nata yake jira kawai take yi a kira shi ya ƙaraso. Daga haka komai ya wuce tamkar babu abin da ya faru. A nan suka shiga tsara yadda za a yi taron bikin Bintoto da zuwa yi mata jere.

Ita dai shiru kawai ta yi musu ba tare da ta ce da su komai ba. Ta jawo littafinta na makaranta tana ta bitar karatun da aka yi mata aka ce ta haddace. Saboda fushin Hari da faɗan da ta yi mata ya shige ta sosai kuma ya kama jikinta. Don koyaushe cikin rarrashin ta take ba ta taɓa ɗaga mata murya ba sai a ranar.

Zuwan Jabir ya sa Hari ƙwala mata kira, a lokacin ta gama sallar magriba ko tashi ba ta yi a kan sallayar ba, saboda tun da rana ya kira Hari a ruɗe yana tambayar ta ta dawo gida. Bayan ta sanar da shi lalle ta dawo sannan ta ce ya zo tana son ganin shi.

Ana gama magriba ya zo, bayan sun tattauna da Harin a kan maganar bikin da tsayar da ranar bikin ta kira masa ita suka gaisa. Duk da ba wata doguwar hira suka yi ba, ganin ba ta son yi masa magana shi ma ya shafa wa kansa lafiya. Saboda ya tambaye ta ya aka yi ba ta jira shi ya kawo ta gida ba. Ta yi banza da shi ba tare da ta ce masa komai ba, jiki babu kuzari ya yi sallama da su a kan zai dawo wurin Hari su ƙarƙare magana ko bayan sun tafi ne.

Tun da sassafe Kandala ta bai wa Hari kuɗin sayen wasu kayan da suka rage ba a saya ba. Sannan ta ce ta raba alawa da dabino ga mutanenta saboda idan an gama shagali a can ƙauyen a nan za su dawo a gama harhaɗa komai, sannan a kai Bintoto daga nan gidan nata zuwa gidan mijinta. Hakan ya sa suka bar Hari da komai suka nufi ƙauyen.

Suna zuwa Kandala ta iske dangin Amadu ta sanar da su bikin Bintoto ya tashi, ba tare da dogon bayani ba ta ce mijinta ne ya nemi a yi komai a gama yana buƙatar matarsa.

Kasancewar sun bar mata wuƙa da nama a kan hidimar Bintoto da duk abin da ya shafe ta; ba su ja zancen da tsawo ba suka ce Allah Ya sanya alheri. Da ma can sun haɗa abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login