Showing 72001 words to 75000 words out of 88489 words

Chapter 25 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2074

ƙi bari ta karɓa, ta lashe maiƙon ƙosan da ya kama hannunta garin ƙwatar ledar, sannan ta fara kai masa duka. Nan take kokawa ta kacame a tsakaninsu, kasancewar shi ma akwai shi da ƙarfin hali ya dage kare kansa. Amma hakan bai hana ta samun sa'ar kama ledar ta yi ta mammatse ƙosan ba, ganin abin da take yi ne ya saka shi sakar mata ledar ta yi ta mutsuttsukar ƙosan har ta wargaje shi kamar dambu, sannan ta jefar da ledar a ƙasa tana faɗin,

"Gobe idan na ce ka zo ka yi mini gardama."

Ɓacin ran da ya gama kai shi wuya ya saka shi ɗaukar duwatsuna ya dinga jefa mata yana kuka ita kuma tana ta tsallen kaucewa, ko da mutane suka ankara da su har wata sabuwar kokawa ta sake sarƙewa a tsakaninsu. Aka shiga tsakaninsu aka raba damben, bayan yaron ya samu sa'ar yage mata fuska da akaifunsa, wani gefe har ya yi jini.

Kukan da yaron yake ta yi ana rarrashin sa ya sa Kandala fitowa daga gidan, don da ma can hankalinta bai kwanta ba ganin Bintoto ta fita gidan. Hango ta a tsakiyar mutane ya sa ta isa wurin da sasaarfa tana faɗin,

"Lafiya aka zagaye ki haka, me faru?"

A nan take wani matashi ya yi mata bayanin da yaron ya yi musu yana kuka. Bintoto tana riƙe ƙugu ta ce,

"Ai ba ƙosan na ci ba. Ga abin shi nan a ƙasa ya tafi da kayansa. Da ma sai da na ce ya zo cikin lumana amma ya ƙi zuwa har sai da muka yi faɗa."

"To laifin me ya yi miki da za ki kira shi?"

"Aikensa zan yi kuma ya ƙi zuwa shi ne muka yi faɗa."

Daga lafuzanta aka gano ita ce ba ta da gaskiya, mutane suka shiga faɗar maganganu a kan duk abin da ya faru ita ta haddasa komai, duba da bayanin da yaron ya yi. A fusace Kandala ta fisgo hannunta tana faɗin,

"Wuce mu je tun kafin dafin bakin mutane ya kama ki wani abu ya same ki. Saboda mayu sun yi yawa a gari ba a gane su a fuska."

Haushin maganar da ta faɗa ta sa kowa ya hau bakinsa. Ita ma ta shiga mayar musu da raddi, inda ta nuna ƙarara tana goyon bayan Bintoto kuma ba ta ga laifinta ba a kan abin da ta yi wa yaron. Don hatta ƙosan da ke cikin ledar sai da aka buɗe aka ga yadda ta yamutse shi. Kuɗi wani bawan Allah ya ciro ya bai wa yaron ya ce ya je ya sayo wani ƙosan. Shi ya tafi da wanda Bintoto ta hautsine da niyyar raba rigimar ganin yadda Kandala ta hau bakinta, ana ta musayar yawu tsakaninta da masu zafin zuciyar da suka kasa shanye gugar zanar da ta yi musu.

Yaron ya bar wurin yana goge hawaye ya nufi wurin sayar da ƙosan. Sai dai ko da ya je babu ƙosai ya ƙare har wasu suna nema.

"Wallahi idan ba ki rage masifa da jawo mini abin magana ba sai na yi miki dukan kawo wuƙa a cikin gidan nan, baƙar almura!"

Zancen Kandala kenan bayan ta shigar da Bintoto cikin ɗaki tana dungure mata kai. Ganin yadda yaron ya yage mata fuska tana ta yarfa hannu a kan zafin da wuraren suke yi mata.

Sosai Kandala ta ji zafin faɗan da ta jawo mata tun da safe har aka ji mata raunin, bayan takaicin da ta kwana da shi a kan abin da su Hajiya suka yi mata. Tana cikin yi mata faɗan ita kuma tana ƙoƙarin kare kanta da faɗin yaron ne ya ja ta, a daidai lokacin suka jiyo muryar wata mata a sama tana ta rafka sallama a tsakar gidan.

Tare suka fita cikin sauri suna rige-rigen ganin wace ce. Ganin matar da yaron da Bintoto ta gama faɗa da shi; Kandala ta gano dalilin zuwan ta gyara tsayuwarta. Tana haɗe rai ta amsa sallamar alamun duk abin da ta zo da shi za ta same shi.

Bintoto kam baya ta ja, ta bar Kandala ta yi gaba tare da tsayuwa gaban matar suna fuskantar juna ido cikin ido suka dinga yi wa juna kallon hadarin kaji. Kafin matar ta gyara tsayuwarta tana cewa,

"Ƙara na zo kawo miki a kan yarinyar da ta daki Khalifa."

"To idan kin gama sai ki duba fuskarta da ya so fincike mata idanuwa."

Kandala ta yi maganar tana kallon gefe, haushi ya sa matar ta fara magana cikin ɗaga murya ta ce, "Saboda kawai ya ƙi nuna mata ƙosan da ya sayo mana; shi ne fa ta dake shi kuma ta wargaje ƙosan sai da wani ya biya kuɗi, ga shi an je sayen wani ƙosan ba a samu ba, kuma shi kawai ake jira idan sun ci su je makaranta. Yanzu ga shi sun yi latti kuma Babansu bai jira ya yi masa bayanin komai ba ya kama shi ya dake shi, a kan jinkirin da ya yi na dawow..."

"Ni na sa ya yi jinkirin har aka dake shi? Ko kuma ni na ce ya ƙi samo ƙosan? To ba zan yi mata magana ba! Ki je ki yi duk abin da za ki yi tun da ke ma yaron naki ba za ki iya nuna masa girman na gaba da shi b...kuma ba ki ga abin da ya aikata mata a fuska ba!"

Wani kallo matar ta yi wa Kandala cike da mamaki kafin ta fara girgiza kai da jiki tana bubbuga ƙafa ƙasa tana huci ta ce,

"To tun da 'yar haka ce; wallahi, na rantse da Allah idan ta sake taɓa shi hukuma ce za ta raba mu da ku a cikin unguwar nan! Don na gano kawaicin da na so yi a kan Hari ba zai taɓa yiyuwa ba! Sannan na fahimci duk abin da kike nufi, kamar yadda aka sanar da ni ko laifin yarinyar ma ba ki gani ba. To ni babu ruwana da tsufan mutum tun da ba ya son gaskiya, matuƙar aka sake shiga gonata wallahi sai na ɗauki mataki a kanki da ita yarinyar duka!"

Tana gama faɗar maganar ta juya riƙe da hannun yaron za su fice. Kandala ta bi bayansu tana faɗin, "Idan kika kai mu hukumar ki ce su rufe mu ɗan makullin ya ɓace! Ko kuma ki ce su kashe mu tun da rayuwarmu tana hannuns....!"

"Wallahi idan ta kawo iskanci ki dake ta Kandala."

Wani mugun kallo Kandala ta yi Bintoton a kan jin furucinta. A fusace ta yi kanta tana faɗin, "Na dake ta ko ke na ci ubanki? Ai babu wanda ya jawo mini ɓacin ran face ke! Kina ji har da faɗin ba za ta yi wa Hari kawaici ba, to don malfar ubanta ta dawo ta yi duk rashin mutuncin da ta ga dama. Wallahi idan ba ki yi hankali ba a yau ɗin nan sai na kai ki Maidala kin koma hannun Amadu. Shikenan ni babu ranar da zan huta don na haifi uwarki? To ki shiga hankalinki na fara gajiya aure ma zan yi miki na huta da jarfa irin taki. Sai ki je can gidan mijin ki ƙarasa iskancin da ya yi saura. Bari Hari ta zo ta kira mini Jabirun a yi mai yiyuw...."

"Wallahi shi kam ba Jabiru ne sunansa ba. Haka kawai ki ce masa Jabiru sai ka ce talaka wanda bai da gida da mota! Hu'um lalle m...."

Takalmin da ta raruma ta wurga mata a kai ya sa ta yi hanzarin ficewa gidan cikin azama tana gunguni. Kandala ta kai zaune babu shiri tana goge hawayen da take ƙoƙarin dannewa suna ƙin ba ta haɗin kai.

Princess Dija.✍️

36.

Wunin ranar gabaɗaya bai yi wa Kandala da Bintoto daɗi ba. Sai da dare Hari ta dawo, a nan Bintoto ta fara kai mata ƙarar Kandala, kafin ita ma Kandalar ta yi mata bayanin duk abin da ya faru.

Hari shiru kawai ta yi tana nazari kafin ta ce, "Inna, wannan dalilin ya sa ban ji daɗin da Bintoto ta bar gidan su Hajiya ba. Saboda zamanta a can zai gyara wasu matsalolin da ake fama da su kanta. Musamman sallah da zuwa makaranta, don na fahimci ko sallah Bintoto buga ta kawai take yi babu sani a kanta. Sannan makaranta, idan tana zuwa yau da gobe tana kama wasu abubuwa su amfani rayuwarta."

"To ya za mu yi? Tun da aikin gama ya gama. A yi mata aure kawai kowa ya huta."

Hari ta ƙura wa Bintoto kallo tsawon mintuna kafin ta ce, "Aure a wannan lokacin da take ciki zai iya kawo wata damuwa. Ganin yadda ko a gida fama ake yi da ita ballantana ta yi aure."

"Idan shi mijin zai taimake ta ai zai fi mu ba ta kulawa. Ko babu komai zai ajiye ta wuri ɗaya babu fita, sannan idan ya so na ga wasu matan aure suna zuwa makaranta a nan birni, sai a saka ta can ta dinga jin wa'azi ko za a samu ta gyara wasu kurakurai."

Ajiyar zuciya Hari ta sauke mai ƙarfi kafin ta ce, "To, babu damuwa, bari idan mijin ya zo sai mu yi magana da shi mu ji yadda za a yi. Amma ni a son raina karatu na fi ra'ayin ta yi saɓanin auren da ake son yi mata a wannan lokacin. Don kwata-kwata ko shekara sha huɗu ba ta ƙarasa ba, kuma auren wuri ko a ilmance an faɗa yana da matsala, musamman a wajen haihuwa a nan yaran mata suke samun yoyon fitsari."

"Laaha'ilaha illalLah! Yoyon fitsari kike yi wa Bintoto fata Hari? Ashe da ma ba kya ƙaunar ta ban sani ba? Cabɗijam! Gara da Allah Ya toni asirinki kika faɗa da bakinki har na ji. To wallahi laƙada ja'akum ki ga yoyon fitsari a kanki ba dai a kan Bintoto b... innalillahi! Lalle Hari ban san ba ki ƙaunar mu tsakani da Allah ba sai a yau. Ikon Allah!"

"Ke ma kin sani Inna tsakani da Allah nake zaune da ku. Sannan ban taɓa yi wa Bintoto wani kallon da ya wuce 'yar da na haifa da cikina ba. To me ma zai sa na yi mata muguwar fatar da ni ma abin zai dame ni idan har wani abu ya same ta?"

"Babu abin da zai same ta sai alheri, tun da ke kin manta lokacin da aka yi miki auren ko girman ta ba ki kai b...."

"To Inna ai kin ga har yanzu ban haihu ba. Ita kuma muna fatar mu ga nata iri a duniya"

"Allah Ya nufe mu da gani Hari. Kin ji abin da za ki faɗa ba ki zauna ki lanƙwashe ƙafafuwa kina yi wa 'yarki baƙin jaye-jaye ba. Allah dai Ya taimake mu mu samu ta sauya rayuwarta ko don gaba."

"Amin Inna."

Daga haka hirar ta tsaya Hari ta miƙe cikin ɓacin rai ta fara dafa musu taliya. Saboda rashin zamanta a gidan ya sa Kandala da Bintoto cin garin kwaki da rana, da daren ma fura Kandala ta sayo ta dama musu. A cewarta ba za ta iya girki da gawayin da Hari take dafa musu abinci ba. Kada ta je garin girkin zaninta ya taɓo gawayin ya kama da wuta ta ƙone a banza.

Misalin ƙarfe bakwai na dare Jabir ya zo, saboda ya tafi gidan su Hajiya direban gidan ya sanar da shi duk abin da Bintoton ta aikata, wanda ya yi sanadin da Hajiya ta dawo musu da ita. Ransa babu daɗi ya fara gaishe da su Hari, ya yi musu jajen abin da ya faru sannan ya koma soron gidan Bintoto ta kai kujerun zama suka zauna.

Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya ce da ita, "Za ki koma wata makarantar, amma ta matan aure ce zan saka ki."

Bintoto ta turo baki tana cewa, "To ai ni ban yi auren ba."

"Farawa za ki yi, da mun yi auren sai ki ci gaba. Saboda ba na son a sake kai ki wata makarantar da za ki yi rashin ji a dake ki a banza. Amma ita wannan malamai ba sa duka, sanann kuma 'yan makarantar suna da hankali ba a bari ki yi abin da zai sa a ce kin yi ba daidai ba."

Shiru ta yi masa tana kallon saman rufin soron, har sai da ya gaji da bayanin ta gyara zamanta tana cewa,

"Da mun yi aure da kwana nawa za mu je Makka?"

"Ba zan kai ki ko'ina ba sai kin daina rashin ji, kuma sai kin iya karatun boko da na Islamiyya. Saboda a can Makka kowa da Larabci yake magana, ƙasashen waje kuma inda za mu je shaƙatawa mu huta su kuma da Turanci suke yin magana. Don haka ba za mu je ana yi miki tambayar kalar abincin da kike so ki ci ba ki san komai ba. Haka kawai ki sa na ji kunya kuma su ma su fasa ba ki abincin yunwa ta lalata miki hanji."

"To idan haka ne ai ka saka ni makarantar ka gani idan ban yi karatun ba. Da ma can ni ce nake ƙin tsayawa na gane karatun, amma yanzu zan dinga kallon malamin duk abin da ya faɗa sai na haddace kuma na yi rubutu a littafaina."

Wani farinciki ya kama Jabir, fuskarsa a sake ya dinga zuba mata daɗin baki da kalolin alƙawurran jin daɗi da sharholiyar da za su yi idan suka yi aure, amma sharaɗin shi ne sai ta tsaya ta yi karatu kuma ta gane abubuwan da ake koyarwa."

Ita ma ta yi masa alƙawarin tsayuwar daka ga karatun har sai ta iya Turanci da Larabci. Kafin ta tafi sai da ya ga Hari ya sanar da ita ƙudurinsa, saboda makarantar ta yaƙi da jahilci ce, wadda matan aure da zawarawa suke yi idan ba su samu damar karatun a lokacin ƙurciya ba. Hari ta ji daɗi sosai ta dinga saka masa albarka tana godiya. Ya ce in sha Allahu a cikin kwana biyu zuwa uku yake son ya kammala mata komai ta fara zuwa. Saboda shi ma bai gama gyaran inda za su zauna ba. Kafin ya gama ta samu abin da ta samu a makarantar, don idan sun yi auren ma zai bar ta ta ci gaba har ta samu takardar Sakandare.

"Amma fa inda matsalar take ita Bintoto ba ta da takardu Firamare, ta ya ya za ta shiga Sakandare babu shaidar ta gama Firamare?"

Sai da ya yi jim kafin ya ce, "Zan ga yadda za a yi. Idan ma ba a samu na saye ba sai a sa ta zana jarabawar a wannan shekara wata makaranta."

"To Allah Ya shige mana gaba, kai ma ya saka maka da alheri a kan wannan gudunmawar da za ka yi wa rayuwarta."

***

Kamar yadda Jabir ya shirya haka ta kasance, shiga nan fita nan miƙa kuɗi can bayar a nan, da haka ya samu alfarmar aka bai wa Bintoto takardun Firamare. Sannan ya koma yi mata cuku-cukun samun makarantar koyon yaƙi da jahilcin. Cikin sa'a ya samu ya yi mata registration, sannan ya ɗinka mata uniform masu ɗauke da riga da wando da dogon hijabi har ƙasa, wasu ma har da liƙaf idan suna ra'ayi.

Kandala garin godiya har da kuka ta yi masa tsabar jin daɗin Bintoto ta samu wanda yake son cigabanta. Jabir kam ko godiyar ma ba ya so, saboda tun a ranar da ya fara ganin Bintoto shirmenta da komai nata yake burge shi. Hakan ya sa duk da ya san halayenta ba sa turba mai kyau; amma bai ji a ransa zai iya fasa aurenta ba. Saboda yana so ya gyara mata rayuwa ko babu komai zai yi jihadi.

Bintoto ta fara zuwa makaranta, kuma cikin nasara duk wani rashin jin da take yi a can ba ta yi ba. Saboda manyan mata ne kowa sabgar gabanta take yi. Babu mai damuwa da ita idan ba wani abu aka ga ta yi ba daidai ba a koya mata. Sallah ma a can ta fara sanin yadda ake yin ta, tsakanin raka'o'inta da abin da ake karantawa a cikin gaɓoɓin sallar. Ta ɗauki sati biyu ana koya mata yadda ake yin sallah kafin ta riƙe a kanta.

Sannan malamai da wasu manyan matan da ke bibiyar sha'anin karatun da duk ake koya mata, suna tsoratar da ita sosai a kan hukuncin wanda ba ya cika sallah. Da wannan dabarar Bintoto ta fara cika sallolinta, amma a hakan ma watarana haɗawa take yi, sallar wuni ɗaya ta yi su a lokaci ɗaya. A cewarta ai wahala ce a ce sai an jira lokaci ya yi kafin a yi sallar. Duk ranar da ba a zuwa makaranta tun asuba take gama sallolinta ta huta. Ba ta faɗa wa kowa sai Kandala a cikin kunne take cewa,

"Kandala na haɗa sallata ta yau duka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login