Showing 36001 words to 39000 words out of 88489 words

Chapter 13 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2073

ladaftu da kyau Hamida ta rufe ƙofar gate, sai da ta ga Bintoton ta galabaita bayan ta gama firgita da karen sannan aka kama mata shi yana ta haushi da ƙoƙarin cafko ta.

Ƙasa ta faɗi tana birgima Hamida tana yi mata faɗa a kan rashin mutuncin da ta aikata wa mai rake, tana ƙara sautin gunjin kukanta da rantsuwar ba za ta sake ba, tsabar tashin hankalin da karen ya saka ta gabaɗaya ta zauce da ban haƙurin da sai da ya dinga saka mutanen da ke bakin ƙofar gidan dariyar dole.

Sannan ta ja ta suka fita har gaban mai raken ta ce ta ba shi haƙuri. Jikinta yana rawa ta duƙa har ƙasa idonta yana tsiyayar ruwan hawaye ta shiga haɗa hannu tana roƙon don Allah ya yi haƙuri ya yafe mata ba za ta sake ba.

Maigadin da gayya ya sake sakin karen ya yi kanta afujajan, a firgice ta zubura tana ihun wayyo uwarta kamar walƙiya ta faɗa gidan a sukwane tana kururuwa, cikin kiɗimewa ta ci tuntuɓe ta faɗi karen ya yi kanta yana ƙoƙarin cizon ta. Yanayin yadda take sambatun tsoro ta bai wa mutane tausayi, aka riƙe karen ta miƙe da jan jiki ta samu maɓoya.

Hamida ta sake bai wa mai raken haƙuri, sannan ta yi wa maigadin godiya ta ja motarta zuwa cikin gidan. Zuciyarta a sake ta buɗe ƙofar ta shige, tare da cin alwashin duk ta sake jawo mata rigima ta gama zaman gidan kenan don ta gaji da tsarabobin rashin jin ta da kullum sababbi suke zama.

Wunin ranar Bintoto sukuku ta yi shi, don bayan firgicin kare yanayin fuskar Hamida ma ya saka ta shiga taitayinta, saboda ruwan faɗan da ta juye a kanta kamar za ta rufe ta da duka. Sannan ta tsorata sosai da kalamanta a kan duk ta sake yin abin ya ɓata mata rai sai ta kawo karen har cikin gidan a cikin ɗakinta ta rufe ta da shi, sai ya gama cinye naman jikinta tass za ta buɗe ta.

Wannan barazanar ta yi matuƙar tasirin ladaftar da ita, don har takatsantsa ta shiga yi a komai na gidan gudun kada ta kuskure a sa karen ya kashe ta a banza. Amma ta ci alwashin duk ta sake ganin mai raken sai ta rama abin da ya jawo aka yi mata a sanadinsa.

Wasa-wasa Bintoto sai da ta kwashe kwana uku a nutse ba tare da ta yi laifi ba har zuwa ranar da maigidan zai dawo daga tafiya. Kuma a ranar Kandala ta yi wa gidan tsinke zuwa ganin ta a kan haƙurinta ya ƙare, kuma ta gama kawaicin da take yi wa Hajiya. Saboda tun daga ranar da suka rabu take uzzura wa Hari da zancen son zuwa ganin Bintoto, duk da an kai ta wurin aikin ta ga gidan babu wata matsala, amma hankalinta gabaɗaya yana kan Bintoto, a duk wani motsinta sai tuna ta tare da zancen zucin ko me take yi a daidai lokacin?

Aikinta ma da Hari ta samo mata, hidimarsa bai sa ta manta da Bintoto ba. Saboda wanke-wanke take yi wa wata Hajiya mai waina, sannan da miƙa abinci da kwashe kwanonin da aka ci abincin idan an kammala. A can take wuni sai dare ya yi ta dawo gidan Hari ta kwanta, ba ta rasa ci da sha ba, amma hankalinta ya ƙi kwanciya saboda rashin ganin Bintoto.

Ranar da aka kwana uku ba su tare; ta saka Jaeri gaba a kan sai ta kai ta gidan aikin ta ga halin da take ciki. Domin a cewarta ko barci rabi da rabi take yi saboda mafarkin da take yi da ita kowane dare. Hajiya da kanta ta ba ta haƙuri a wayar Hari, tare da yi mata alƙawarin idan ta cika sati har gida za ta turo direbansu ya ɗauke ta ya kai ta gidan su Hamida ta gano Bintoton. Hakan ta kasance kuwa, domin ranar tana zuwa tun da asuba ta shirya, ko wurin aikin nata uzuri ta bayar kamar wadda idan ta je a can za ta kwana.

Ƙorafinta ya sa Hari shiri tun kafin motar da za ta kai su ta zo. Kasancewar sun yi shawarar saya wa Hamida kuka, daddawa da kayan yaji, kuma an saya har Kandala ta ƙulle tamau tare da kayan zaƙin da take saya tana ajiye wa Bintoton. Da dabara Hari ta ja tafiyar zuwa ƙarfe goma da rabi na safiya, saboda ƙagarar da Kandala ta yi waje ta koma tana jiran zuwan motar da Hajiya ta ce za ta kai su gidan aikin Bintoton.

Ƙarfe sha ɗaya a kan hanya ta buga musu, duk da gudun da direban yake yi amma Kandala ganin take yi ko kaɗan motar ba ta sauri. Kasancewar Hamida ta san da zuwan nasu hannu kawai ta saka a asibitinsu ta dawo gida. Kuma ta yi hakan musamman saboda dawowar Baban Baby da zuwan su Kandalar.

Amma ko da wasa ba ta sanar da Bintioto ba, don ta daina hira da ita a gidan gudun ta sake sakar mata fuska ta jawo mata wata fitinar da ta fi wadda take aikatawa. Sai dai ta saka ta yin wanka da shiri a cikin kayanta da fitar mata, waɗanda suka yi mata kaɗan kuma take da niyyar kyautarwa. Don sanadin haihuwar Baby wasu kayan nata da yawa sun matse ta, tsabar gayunta tun tana budurwa ɗinki ma daidai jikinta ake ɗinkawa, kuma ba su jimawa a hannunta matuƙar ta yi sababbi sai ta rage yawan kayanta. Wannan dalilin ya sa ta haɗa wa Bintoto kala biyar a cikin kayanta ta miƙa mata, tare da umarnin ta saka ɗaya daga cikin kayan a ranar, sannan kuma ta fito falo ta zauna za su yi baƙi.

Bintoto a gaban madubin ɗakinta bayan ta gama wankan ta shirya tsaf da ita har da goga madarar turaren da Hamida ta saya mata, ta shiga juyi a gaban madubin bakinta a washe tana ta kallon kanta tana zuba shirmen surutan da ta saba koyaushe. Kiran da ta ji Hamida ta yi mata ne ya sa ta ɓata fuska, tana gunguni da bubbuga ƙafa ƙasa tsabar jin haushin ta katse mata abin da take yi, don kalolin tafiyar take yi a gaban madubin tana yauƙi tare da sambatunta na dogon burin da take yi koyaushe.

Princess Dija ✍️

22.

Ta fito ɗakin tana haɗa fuskada gunguni, amma tun da ta ƙyalla ido ta hango su Kandala a cikin falon bakinta bai sake rufuwa ba, tsabar jin daɗi da mamakin ba zatar da suka yi mata. Don wani uban tsalle ta daka tare ihun kiran sunayensu ta yi wurin Kandala aguje ta faɗa jikinta. Ita ma Kandala tsabar daɗi da farincikin ganin ta ba ta san lokacin da ta fashe da wani kalar kuka ba. Saboda a take murnar ganin ta ta koma kukan daɗi, sai da su Hari suka yi ta ba ta baki sannan ta share hawayenta idonta a kan fuskar Bintoto ta shiga shafa kanta tana cewa,

"Bintoto me kike ci kika zama 'yar gayu haka a lokaci ɗaya ni kika bar ni da kewarki?"

Ta ƙare maganar tana share sabon hawayen da ke bin fuskarta, saboda kukan da take ƙoƙarin dannewa amma hawayen ya kasa tsayawa a cikin idonta. Bintoto ta turo baki ranta a jagule ganin kukan da Kandalar ke yi, amma hakan bai hana ta magana cikin tsiwa ba.

"Ni dai Kandala ki daina kukan nan kada ki jawo Anti ta ji tausayin ki ta ce ki tafi da ni gida sun fasa riƙo na...bayan kuma aikin da aka kawo ni don shi ma maigidan ya ce ba ya s..."

Kallon da Hamida ta yi saurin wurga mata ya sa ta kawar da kai tana kumbura fuska tare da sake cewa,

"Ai gaskiya ce dole a faɗa, don kin san da yana gidan nan ba zai bari na zauna da ku ba sai ya ce a mayar da ni...."

Murmushi kawai Hamida ta yi kafin ta ce,

"Ai babu ruwansa Fatima, don ko jiya da muka yi waya sai da ya ce ina kike kin daina rashin ji? Saboda da ma can rashin jin naki ne ba ya so, ba wai zamanki a gidan ne damuwarsa ba. Amma yanzu tun da kin rage jawo mana rigima lafiya lau za ki zauna da shi a cikin gidan nan..."

'Babu wani kare shi da za ki yi Anti, don kawai kin ga idon su Kandala. Bayan ke ma kin koyi muguntarsa kina yi mini.. yawwa Kandala, Wallahi ki yi mata magana kare take sakar mini ya yi ta cin naman jikina...dubi hannuna ki gani saura kaɗan ya sake fama mini gociyar da Kulu ta yi mini."

Ta ƙare maganar tare da wurga wa Hamida wata kalar harara bayan ta ƙara shigewa jikin Kandalar ta lafe tamkar wata ƙaramar yarinya 'yar goye. Cike da jin kunya Hamida ta yi hanzarin faɗin,

"Idan ba kya rashin ji me zai sa a haɗa ki da karen t..."

"Amma kuma fisabilillahi idan maganar Allah ake yi me zai sa a haɗa ɗan mutum da kare? To a gaskiya idan har irin wannan horon kuke yi mata don kun ga ba ta jin magana gara kawai a bar aikin tun da ba dole ba ne..ashe ba banza ba nake ta mafarki da ita tana kiran sunana!."

Zancen Kandala kenan, ranta a matuƙar ɓace saboda jin kalamin Bintoto da amsar da Hamida ta bayar. Saboda kai-tsaye ta ji aikin ya fita ranta don zuciyarta ta ba ta zalunci kawai suke yi wa Bintoton ganin an kawo musu baiwa tana yi musu aikatau. Amma fahimtar da Hari ta yi wa Bintoton za ta samu tarbiyya idan zamanta ya yi tsawo a gidan, hakan ya sa ta katse Kandala daga boren da ta fara yi gudun ta ɓata lamarin aiki ya koma mata baya, idan har aka rashin sa'a zaman ya rushe za a wargaza 'yar nutsuwar da ta fara nuna kanta a cikin rikitattun halayen Bintoton.

"Haba Inna, ke ma fa kin san halin 'yar tawa ba ta barin bakin mutum zama kurum matuƙar tana ga wuri. Kuma shi karen ba wai an yi ne don ya cije ta ba, tsoratarwa ce kawai don a samu ta rage abubuwan da take y.."

"Daina yi wa zancen nan kwaskwarima Hari, ko ba ki ji abin da ita uwar ɗakin tata ta faɗa ba? To ba don ba a son Bintoto aka kawo ta aikatau birni kare ya ci naman jikinta ba. Tun da ba baiwa ba ce gara kawai a haƙura da aikin a samo mata wani gidan da ba za a dinga firgita ta da cizon kare ba. Don irin wannan tsaf za a saka mata ciwon hauka garin ladaftarwa ta zauce a saka ni cikin masifa... don haka baiwar Allah don Allah idan kin san ba za ki riƙe mini Bintoto amanar Allah ba ki biya ta kuɗin ranakun da ta yi a gidanki kina tsoratar da ita mu tafi mu bar miki gidanki, tun da aikin ba na dole ba n..."

Zancen Kandala ya katse saboda jin furucin da ke fita daga bakin Bintoton. Domin kuwa zumbur ta tashi daga jikinta ta tsaya ƙyam a gabanta riƙe da ƙugu tana faɗin,

"Ai na rantse da Allah babu inda zan je sai dai ki yi haƙuri ki bar musu ni! Hu'umm lalle ma Kandala, to irin abincin da take ba ni ko Inna Hari ga ta nan ba za ta iya saya da kuɗinta ta ci shi ba, ko na yi ƙarya Inna?"

Ta ƙare maganar tare da nuna Hari da ɗan yatsa, kafin ta sake magana bayan ta murguɗa baki, ganin Harin ba ta ce komai ba ta ce,

"Don haka babu inda zan je ni kam. A bar ni a nan, rashin jin ma da ba ta so ina yi mata na daina...Anti ki faɗa musu don Allah kwana nawa rabon da na yi miki laifi a gidan nan? Ko raken da na sha kika biya kuɗin ai ban sake yi miki irin haka ba ko?"

Hamida ido da baki a sake take kallon ta tsabar dariya da mamakin halin Bintoton na rashin shayin duk abin da ya zo bakinta, bayan ta gama jin haushin furutan Kandalar da suka sa ta gano ita ce tushen matsalar Bintoto, don zuciyarta ta gama tabbatar mata ita ce tsanin duk wata taɓarar da Bintoton take yi, saboda babu tsawatarwa a cikin riƙon da take yi mata kuma ba ta so kowa ya taya ta gyaran tarbiyyarta, sannan ta fahimci tunanin Kandala ya tafi a kan rashin so ne ke sa a yi wa Bintoto horo, saboda ita kaɗai ce mai ƙaunar ta a duniya, kuma ba ta son abin da zai ɓata mata rai.

Shirun da Hamida ta yi ya bai wa Hari damar kallon Kandala da ta kafe Bintoto da ido baki a sake tsabar mamakin da ta ba ta.

"Kin dai ji da kunnenki Inna, har raken mutane ta sha ta bar baiwar Allah da biyan kuɗi! To da a ce baiwar Allahr nan tana cutar da Bintoto babu abin da zai sa ta ce ba za ta bar gidanta ba. Amma saboda jin daɗin zaman da take yi da su; ki dube ta da kyau ki ga yadda ta fara sauyawa a cikin sati ɗaya kacal! Don Allah kalli ko kayan jikinta ki gani Inna ai ba da su ta zo gidan nan ba, don ko ba a faɗa ba kyautatawa ce ta jawo ta yi mata wannan alherin. Don haka ki bar zancen barin aikin a nan inda kika yi shi tun kafin zancen ya yi tsawo, saboda jikina yana ba ni zamanta a gidan nan alheri ne kuma ta sanadinsa za ta samu nutsuwar da muke fata, kuma duk abin da kika san tana yi wanda ba kya so za ta daina shi babu jimawa. Amma idan kin zaɓi ta bar aikin shikenan sai mu tafi da ita kawai, sai dai ba baki na yi mata ba, amma da wuya ta sake samun wani gidan aiki irin wannan matuƙar ta bar sh..."

"Wallahi babu inda zan je ni kam!"

Furucin Bintoto kenan tare da nufar ɗakinta da niyyar komawa ta rufe ƙofa, har sai sun tafi ta fito gudun Kandala ta raba ta da gidan jin daɗi a cewarta. Amma maganar da ta ji Kandalar ta yi cikin sanyin murya da sanyin jiki ya sa ta dawo bakinta a washe ta zauna kusa da ita tare da komawa jikinta ta lafe har da rufe ido tsabar jin daɗi. Domin ita ma Kandalar an yi sa'a ta hango abin da Hari take ƙoƙarin nuna mata kuma ta fahimci komai daga yanayin Bintoton.

"Ai shikenan ta ci gaba da zama Hari, da ma ni karen da ta faɗa ne ya ba ni tsoro. Kada garin horo a kuskure ya guntule mata ƙafa ko hannu, kin ga kuma ni bar mini ita za a yi babu wanda zai aure ta idan ta koma musaka."

Ba Hamida kaɗai zancen Kandala ya bai wa dariya ba har da Harin kanta, don sai da ta ƙumshe bakinta tsabar dariyar da ta zo mata babu shiri. Musamman da ta kai wa Bintoton faka a baya tana faɗin,

"Ni ɗaga ni uwar son jikin tsiya, ko kuma na haɗa ki da karen ya cinye dogon bakinki kowa ma ya huta da kalolin fitinarki."

Garin tashi zaune kanta ya daki haƙorin Kandalar ta yi hanzarin dafe wurin tana faɗin,

"Wayyo Kandala ki yi wa haƙorin giwarki magana kin ga ya cije ni a tsakiyar kai."

"Bantar ubanki! Mashi ne ya cake ki ba haƙori ba."

Hamida babu shiri ta fashe da dariya, a cikin dariyar ta ce, "Kai jama'a! Ashe a tsakaninku ma ana kaftawa."

Hari tana dariyar ita ma ta ce, "Ai in dai Inna da Bintoto suna wuri ko ba a so sai an yi dariya. Amma kuma a hakan babu mai shiga tsakaninsu, wanda ya shiga kuma kunya zai kwasa. Iyakacin mutum da su ido, don idan sun gama artabun sake ɗinkewa suke yi kamar ba su ba. Saboda haka ki yi haƙuri da duk abin ya faru, kuma mun yaba sosai da riƙonku Allah ya biya ku. Da yardar Allah ita ma watarana za ta yi hankali ta bar duk abin da take yi, ko babu komai bakin kowa zai sarara da bari-barin da ake faman yi da ita kullum ku ma za ku samu lada."

Da murmushi mai sauti a kan fuskar Hamida ta ce, "Allah ya ƙara mana haƙurin zama da juriya gabaɗaya...ammmm..sai batu na gaba a kan ita Bintoton; da ma mun yi magana da maigidan a kan ya dace a saka ta makaranta. Amma sai kun amince idan kuna da ra'ayi sannan za a yi komai.."



sabon kafce🏃🏽‍♀️

Princess Dija ✍️

23.

"Ni dai ina so, ko da su ba su amince ba."

Zancen Bintoton kenan tana kallon Kandala tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login