Showing 33001 words to 36000 words out of 88489 words

Chapter 12 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2068

haushi ta dungure mata kai da kalolin ƙoso, a cikin fushi ta fara balbala mata ruwan faɗa a ranta tana jin kamar ta rufe ta da duka ko za ta rage jin haushin ta . Bintoto kam barin wurin ta yi tana zagin ta a zuciya da gungunin tare da cin alwashin sai ta rama ƙoson da ta yi mata a kan Baby.

Princess Dija ✍️

20.

Kwana ta yi tana kumbura fuska, don ko abincin dare da Hamida ta dafa ta kawo mata har cikin ɗaki ƙin ci ta yi. A nan ta bar shi ko wanka sai da ta tsayu a kanta ta yi shi, tana gunguni ta yi barci rabi da rabi da juye-juye saboda kewar kwanciya a bayan Kandala. Sai tsakar dare da yunwa ta tayar da ita dole ta ci abincin tana zagin Hamida da mijinta, a cewarta;

"A farko na zaci ita matar tana da kirki, amma ashe duk halinsu ɗaya, to ni kuma duk sai kun san ɗiya ce ni ba shegiya ba, don ba zan zura ido na bar ku ku cuce ni a banza ba."

Da ire-iren waɗannan zantukan a bakinta ta sake komawa barci. Da safe ma ta ƙi fita daga ɗakin, ko sallar da Hamida ta tayar da ita ce mata ta yi ta yi. Bayan da man can ba ta damu da yin sallar ba. Tsakaninta da sallah asuba ko magriba, idi, ko sallar Juma'a idan sun tafi masallaci da Kandala. Amma sauran duka shan ruwan tsuntsaye take yi musu.

Lokacin da Hamida ta shirya zuwa wurin aiki ta ƙwala mata kira, saboda ba ta son zuwa ɗakin nata gudun ta ga abin da zai ɓata mata rai, shi ya sa ta tsaya daga inda take tsaye a cikin falon rungume da Baby tana bubbuga bayanta don ta samu ta yi barci. Amma sarai tana jin ta ta yi shiru kamar ba ta san tana yi ba. Sai da ta gaji da kiran nata ganin za ta ɓata mata lokaci ta yi latti, ta leƙo ɗakin tana cewa,

"Wai ke Fatima ba kya ji ina kiran ki ne?"

Bintoto ta turo baki sannan ta ce, "To ai ni Bintoto nake ba Fatima sunana ba."

Sakato Hamida ta yi tana kallon ta babu shiri dariya ta suɓuce mata ganin yadda take kallon sama da tagumi ko ƙiftawa ba ta yi.

"To Fatima ni dai a haka nake son kiran ki ba wani Bintoto ba, yau Juma'a ba zan jima ba zan dawo gida. Saboda haka na so bar miki Baby amma halinki ba zai bari na bar ta ba, tun da ina nan ma kika yi mata cizo ballantana kin ga ba na cikin gida.."

"Ai ko jiya wasa muke yi ni da ita shi ne ta yi kuka. Kuma ni ma ta cije ni amma na yi haƙuri na yafe mata."

Bintoto ta faɗa tana rungume hannuwanta a ƙirji tana kumbura fuska. Hamida ta yi 'yar dariya tana cewa, "Wasa ake yi da cizo har shatin haƙori ya fito? Umm.. ni dai kada ki ɓata mini lokaci tashi mu je yau ba zan bar ki cikin gidan nan ba. Abin karinki ma yana can saman baranda a harabar gidan na ajiye miki. A can za ki zauna sai na dawo, kuma kika fita cikin gidan kare yana cikin unguwar nan zai iya cije ki kuma babu ruwan kowa."

Bintoto ta fito daga ɗakin tana hararar Hamida da gefen ido, saboda gaba ta saka ta har suka fice cikin gidan. Tana matsar ƙwalla a ranta tana cewa,

'Ai ni ko wallahi duk bala'i ba zan bar gidan nan ba.'

Wurin da ta nuna mata ta zauna tare da dunƙule fuskarta cikin cibiyoyinta har Hamida ta buɗe gate ta fice da motarta, sannan ta sake rufe gate ɗin tare da leƙo kanta ta ƙaramar ƙofa tana jaddada mata kada ta fita gidan, saboda kare yana yawo cikin unguwar zai iya cije ta.

Ko kallon ƙofar da take tsaye ba ta yi ba har ta ja motarta ta wuce asibiti. A hakan ma ta ja lokaci a ƙame wuri ɗaya ba tare da ta motsa ba. Tsabar takaici da haushin wulaƙancin da take ganin Hamida ta yi mata a kan 'yarta.

Sai da ta gaji da kallon wuri guda sannan ta yi ƙwafa tare da kai kallon ta ga kofin shayin da Hamida ta ajiye mata, sannan da baƙar ledar da ta ƙulle mata biredi da masar ƙwai. Cikin rawar jiki ta yi wurin tare da jawo ledar yawunta yana katsewa ta buɗe ta fara kai wa bakinta tana hararar kofin shayin tana faɗin,

"Mara mutunci sai na shanye ka duka ba zan rage komai ba, tun da ba ni na ce a ba ni ba."

Sai da ta cinye biredin da ƙwan, ta zuƙe shayin har da lashe kofin tas da zura harshenta cikin kofin tana lasar inda duk ta samu harshen nata ya kai, kafin ta kalli ƙofar shiga gidan ta ja tsaki tsabar haushin Hamida ta hana ta yin abin da ta ci burin yi a ranar. A fusace ta wurgar da kofin a tsakiyar gidan tare da bin shi da gudu ta shiga kai masa harbi da ƙafa tana buga shi kamar ƙwallo. Haka ta mayar da shi abin wasa ta yi ta buga kofin da ƙafa tana bin shi da gudu tana ihun yeeee ta cinye.

Ita kaɗai a cikin gidan tana ta hauka har ta gaji don kanta ta buɗe gidan, ta fita tana leƙen inda ta hango karen ya fito a ranar da ta fara ganin shi. Kamar an jefo wani mai rake a layin gidan ta hango shi tafe da baron rakensa mai kyau kuma mai tsafta, ta shiga tsallen jin daɗi tare da shan gabansa cikin sauri tun kafin ya isa inda take, bakinta yana rawa ta fara faɗin,

"Gara da Allah Ya kawo ka, yanzu nake so na tuƙa mota na tafi wurin sayen ta, ashe da na yi gajen haƙuri tun ga shi ka zo har ƙofar gidanmu."

Shi ma yana murmushin jin daɗin maganarta, ya fara tattaɓa raken yana faɗin, "Allah Sarki, ai haka abin yake."

Sai da ta gyara tsayuwarta tana kallon raken, a ranta tana jin kamar ta zari ɗaya ta ruga da gudu, amma ta yi dauriya tana haɗiyar yawu ta ce,

"Raken ɗari biyar za ka ba ni."

Tana gama maganar ta haɗe fuska kamar gaske ita mai kuɗin ce, har da riƙe ƙugu bayan ya zaɓo mata wata ƙatuwa ta ce,

"Ƙare fere mini ita da kyau don ba na son ƙazanta."

Ya ja wuƙa har da 'yar waƙarsa yana gyaran raken ya miƙa mata tare da yayyafa wa rakensa ruwa ya buɗe murya yana faɗin,

"Gaaaa rakeeees!"

Bintoto ta kafa wa raken haƙora ta datso ruwan yana bin gefen bakinta tana wani lumshe ido ta ce,

"Umm Ummm! Wai Allah wagga rake da daɗi take...ƙaro mini wata irin ta guda biyu mu gani nawa kuɗin suka kama."

Cike da jin daɗin yabon raken da ta yi ya ƙara zaɓo mata biyu masu kyau yana faɗin,

"Ai wannan raken tawa ba a wurin kowa za a samu irin ta ba. Shi ya sa duk wanda ya saya sai ya nemi ya ƙara..."

Haka ya yi ta zuba yana sake gyaran raken kamar yadda ya yi mata a farko. Bakinta cike da tokar raken tana tauna ruwan yana ratsa tsakiyar kwanyarta ta ce,

"Ai ni ma a rayuwata ban taɓa shan raken da ta yi daɗin wannan ba....amma wai don Allah a ina ake dafa ta ne a cikin garin nan?"

Dariya mai raken ya yi har da ƙyaƙyatawa, tsabar farincikin ta fara santi a kan rakensa, kafin ya sake cewa,

"Sha ki ƙara kenan...ba ni kuɗin na wuce don yau da alama ko ɗaya ba zan koma da ita gida ba."

Bintoto ta karɓi raken guda biyu bayan wadda ke hannunta tana sha ta juya kamar ba za ta ce da shi koma iba. Shi ma ya biyo ta yana faɗin,

"Ko dai wata za a ƙara miki ne?"

Ta waigo idonta a kan fuskarsa ta nuna masa gidan su Hamida da raken hannunta tana cewa,

"Ka ga wancan gidan?"

Mai raken ya jinjina kai alamar ya gani, cike da gadara ta datsi raken tana taunawa ta ce,

"Gidanmu ne, mu je can na ɗauko maka kuɗinka idan ban ƙoshi da waɗannan ba sai ka ƙara mini."

Bakinsa a washe ya ce, "Ranki ya daɗe ko dai bahon za ki juye mini gabaɗaya na huta da yawo? Don ire-iren ku manya na san wannan ƙaramin aiki ne a wurin k...."

"Ai da jiya ka zo bayan wannan ma idan na juye sai ka koma gida ka ƙaro mini wata. Saboda akwai kuɗi masu yawa da Babana ya ba ni kafin ya yi tafiya, kuma a jiyan duka na rabar da su. Masu aikina ma ba su samu ba sai yau zan sake raba musu kuɗin....mu je ƙofar gidan ka jira ni na ɗauko maka kuɗinka ka san masu kuɗi komai suke so saya suke yi yadda suka ga dama."

Mai rake ya ƙura mata kallo zuciyarsa cike da wasi-wasi a kan zancenta, saboda ganin yanayin ta ko kaɗan ba ta yi masa kama da ɗiyan masu kuɗi ba. Duba da kayan jikinta da takalmin ƙafarta tsohon sani gare shi tun a ƙauyensu. Saboda har sun yi mata kaɗan tsabar ajiyar da Kandala ke yi wa takalmin gudun ta lalata su da wuri. Sannan ga ɗaurin ɗankwalin da ke kanta kamar an kifa kwando, da ɗan kunnen da ke kunnenta na tsofaffi waɗanda ake rabo a yayin bikin aure masu suna tsiyarku dangi. Waɗannan abubuwan sun saka shi tunanin kamar abin da ta faɗa babu gaskiya. Amma saboda ya ga iya gudun ruwanta ya bi ta yana faɗin,

"Ki ce kawai na dawo gobe ko za a dace na shiga cikin 'yan aikin naki a raba da ni?"

"E fa, ka dawo kawai idan za ka iya, ai mu masu kuɗi komai muka yi daidai ne...ƙaro raken ɗaya ka haɗa mini kan kuɗin."

Sai da ya tsaya kallon ta, saboda zancenta ya gama fallasa masa ba ɗiyar kowa ba ce duk su ne shi da ita mutanen ƙauye. Sannan ya zaro raken ɗaya ya miƙa mata tare da haɗe fuska ya ce,

"Kuɗinki sun kama dubu biyu. Je ki ɗauko mini na wuce kada ki ɓata mini lokaci."

Bintoto ta karɓa tana wurga masa harara tare da turo baki ta ce,

"Ni dai ba ni, idan kuma ganin kake yi kamar ba zan iya biya ba ka riƙe kayanka. Daman ku talakawa ba ku iya cin arziƙi ba. Ana so a yi maka taimako amma kana ƙoƙarin yi wa kanka asara....mitssss!"

Ta ƙare maganar tare da jan tsaki ta yi cikin gidan a fusace kamar za ta tashi sama. Tana shiga ta rufe ƙofar tare da kiciniyar danna sakata jikinta yana rawa tsabar tsoron kada ya biyo ta cikin gidan ya ga inda ta ɓoye, ga shi babu kowa ballantana a tare mata rigimar.

Uban tsalle ta daka bayan ta datse ƙofar gidan da sakata ta leƙa gefen kusufar gate ɗin tana kallon shi cikin haɗe fuska ta ce,

"Malam ka yi haƙuri ka tafi sai gobe zan biya ka kuɗin yau babu ko ficika a hannuna."

Princess Dija ✍️

21.

Baki a sake ya bi gefen fuskarta da kallo, kafin ya ƙaraso jikin gate ɗin gidan ya nuna ta da hannu ya ce,

"Nan da kika gan ni wallahi na fi ki tashanci. Ko ki fito ki ba ni kuɗina ko na diro ta katanga na ci miki uba! Don a kan rakena ban ƙi na yi miki yankan rago ba matuƙar kika ce za ki nuna mini iskancinmu na karkar..."

"Ai ba cewa na yi ba zan biya ba ko! Cewa na yi ka jira zuwa gobe, idan kuma ba za ka bari ba to ka jira matar gidan ta dawo sai ta biya mini. Ai Allah ma ya sa ni ba matsiyaciya nake ba, ballantana ka nuna mini warin talauci a kan raken da ma ba ta da wani daɗi don an taimaka maka an saya."

Imanin da ya gama kama shi a kan batutuwanta masu kashe jiki da zallar tsagwaron takaici, tsaye kawai ya yi yana kallon ƙwayar idonta da ke leƙensa ɗauke da hararar bayan murguɗar bakin da take yi masa har da guntayen tsakinta mai sautin,

'tsutt tsutt.'

"A tunaninki iri na za ki yi wa wayo?"

Ya ƙare maganar da nuna kansa saboda ta gama ba shi mamakin duniya gabaɗaya. Ba ta yi aune na, kafin ta ba shi amsa ta ji dutsin da ya wurgo mata a kussuwar da take leƙensa cikin ƙunar zuciyap, aka dace ya daki gate ɗin bayan ta ja baya, a ƙufuke ta zuro hannunta tana yi masa daƙuwa tana faɗin,

"Wallahi ban yafe maka b..."

Cafkar da ya so kawo wa hannun nata ya sa ta yi wani ihu tare da janye hannun tana faɗin,

"Kuma ba za a biya raken ba ka yi duk abin da kake so, talakan banza mai warin talauci."

Daga haka ta koma saman barandar da ta sha shayi ta yi zaman dirsham tana ta gatsar rake tana waƙoƙi tare da aika wa ƙofar harara. Daga inda take tana jiyo sautinsa yana ta zage-zage da kai wa gate ɗin duka haɗi da shuri da ƙafa, tsabar haushin da ta tura masa.

Bintoto kam raken ta shanye tas tana ci gaba da waƙe-waƙenta, ta tara tokar raken a gabanta tana lasar baki. A nan ta baje tana hamma saboda barcin da ya cika mata ido tana sambatun daɗin raken ina, a ranta tana faɗin ina ma zai ɗan ƙara mata idan ta samu kuɗi ta biya shi.

Mai rake kam saboda ta kai shi bango, cikin ɗan lokaci ya tara mata tsirarun mutanen da ke wucewa ta ƙofar gidan. Har wani ya so biyan kuɗin amma mai rake ya kafe a kan ko an biya shi sai ya yi mata dukan kawo wuƙa, tun da ta yi masa rainin wayon da bai taɓa cin karo da shi ba tun da ya fara sana'arsa .

Ana cikin rigimar Hamida ta dawo daga aiki. Tun da ta shiga layin nasu ta ji gabanta yana faɗuwa dam-dam. Saboda hango mutane a ƙofar gidan ya tuna mata da Bintoto da ta bari ita kaɗai babu kowa. Hankalinta a tashe ta isa ƙofar gidan ta yi parking, jikinta yana rawa ta fito tana tambayar abin da ya faru.

Wani maigadin maƙocinsu ne ya yi mata bayanin abin da mai raken ya sanar da shi. Hannunta a ƙirji ta sauke ajiyar zuciya saboda tunaninta ya faɗa a kan wani mugun abu ne ya samu Bintoton. Babu jinkiri ta fito da kuɗi a jaka ta miƙa wa mai raken, zuciyarta a cunkushe ta isa ƙofar gidan ta bubbuga kafin ta leƙa ta hango ta kwance ta juya wa gate ɗin baya. Ranta a ɓace ta shiga ƙwala mata kira amma har ta gaji Bintoto ba ta san tana yi ba, saboda wani mugun nannauyan barci ne ya kafce ta mai haɗe da mafarkai.

Tsabar haushin da ta bai wa Hamida ya sa ta kalli maigadin maƙocinsu ta ce,

"Baba ina Black?"

Kai-tsaye ya sanar da ita barci yake yi, fuskarta a haɗe ta ce ya kawo mata shi don shi ne kaɗai zai yi maganin rashin mutuncin Bintoto. Daga jin haka kowa ya yi sakato yana kallon ta, mai raken ma gyara tsayuwarsa ya yi don ya ƙi tafiya duk da ta biya shi kuɗin rakensa. Cikin ɗan lokaci Maigadin ya jawo shi yana ƙugi suka tsaya a ƙofar gidan. Da dabara ya saka shi wartsakewa har ya koma zuba haushi babu ƙaƙƙautawa.

Haushin karen ya yi nasarar tayar da Bintoto daga kafurin barcin da take yi. Zumbur ta miƙe da ihu ta shiga wara ido tana neman inda yake. Domin a tsammaninta ya shigo gidan yana so ya kamo ta ya cije ta.

A daidai lokacin ne ta ji muryar Hamida da ke bakin gate tana kiran sunanta. Cikin sauri ta isa bakin gate ɗin da nufin buɗe mata amma haushin karen ya sa ta tsaya hannunta a ka tana faɗin,

"Don Allah ki kori karen kada na buɗe ya cije ni."

Ran Hamida a ɓace ta ce, "Malama ki buɗe babu abin da zai yi miki!"

Da ƙyar ta buɗe gate ɗin tare da zubawa da gudu, Hamida kuma tun kafin ta shiga ta tura karen ya bi ta aguje tana kururuwa da ihun wayyo a taimake ta suka shiga zagayen gidan ita da shi. Saboda kawai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login