Showing 66001 words to 69000 words out of 88489 words

Chapter 23 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2067

A nan suka zaunar da ita suna yi mata bayanin yadda tsarin Makarantar yake da wasu abubuwan da ba ta san kansu ba.

Amma hakan bai hana ta sake gwada musu halayenta ba. A wannan karon ma tana fahimtar babu kowa a wurin da take kama kunnen, prefects ɗin sun tafi ajijuwansu ana yi musu karatu, shi ma malamin ta hango kansa a duƙe alamun barci yake yi. Ta miƙe ta nufi inda ta hango ramin cinnaka da ke ta fitowa daga cikin ramin yana shawaginsa. Leda ta samo ta dinga tsintar cinnakun tana zubawa. Sai da ta tara mai yawa sannan ta nufi bayan ofishin malaman saiti da inda malamin yake zaune ya juya bayansa. Da dabara ta juye masa cinnakun ta saman wuyan rigarsa.

Cikin sauri ya motsa saboda ya ji alamun an taɓa shi ta bayan. Motsinsa ya sa wani cinnka ya gatsa masa cizo. Babu shiri ya zabura yana laluben inda ya ji cizon, kamar almara cinnakun suka dinga cizon shi ya ta ko'ina ya hau soshe-soshe. Bintoto da ke laɓe bayan tagar tana ɗaga kai tana hangen sa ta fito daga maɓuyar tana ƙyalƙyala dariya, ganin yadda yake ta tsalle yana faɗin,

"Subhanallah! Ohh my God!"

Cikin sauri ya cire rigar ya wurgar, sannan ya koma cire dogon wandonsa cikin ɗimaucewa ya wurgar yana faɗin,

"This is serious."

Kafin ka ce me, wasu malamai maza da ke cikin ofishin suka rufu a kansa da tambayar me yake faruwa, saboda mamakin ganin yadda ya birkice a lokaci ɗaya kamar wani sabon kamun hauka. Nan take aka saka shi cikin wani ƙaramin ɗakin ajiyar takardu, saboda gudun hankalin wasu malamai mata ko ɗalibai ya kai a kan abin da yake faruwa. Saboda ofishin malamai mata daban na mazan daban.

Muguwar dariyar da suka ji Bintoto tana yi a bakin ofishin abin ya yi matuƙar ba su mamaki kuma ya ɓata musu rai. Musamman da aka gano cinnaku ne suke cizon malamin, ganin nan take sun sakar masa ƙolallai kuma wurin ya yi ja kasancewarsa farin mutum.

Wani malami ya kamo Bintoto ya shigo da ita cikin ofishin, sai da ya durƙusar da ita tsakiyar malaman da barazana, sannan ya zare ido yana tambayar me ya kawo ta wurin.

A bayanin da ta yi masu suka gano ita ce ta haddasa wa malamin komai. Malamin ya fito daga ƙaramin ofishin yana muzurai saboda har lokacin bai daina jin zafin cizon cinnakun ba.

Ransa a ɓace ya yi musu bayanin duk abin da ya faru tsakaninsa da ita tun daga cikin ajinsu har zuwa nan ofishin. Bintoto ta hau zarar ido tana ranste-rantsen duk abin da malamin ya faɗa babu gaskiya ƙarya yake yi mata.

A nan suka shiga tattauna matsalarta ta rashin tarbiyya, a nan suka kai ƙarshen bai dace ta ci gaba da zama a cikin makarantar ba gudun ta ɓata musu sauran ɗalibai. Nan take aka kai zancen gaban shugaban makarantar. Bayan doguwar muhawara aka rubuta mata takardar dakatarwa, aka ce idan ta je gida ta bai wa Aliyu.

Sannan ba su bar ta iya haka ba, sai da suka saka ta horo kala-kala, ta sha kuka tare da roƙon a yafe mata amma babu wanda ya saurare ta. Kuma hakan bai hana ta yin aikin da aka saka ta ba, saboda taron da malaman suka yi mata tamkar za su cinye ta da rai. Ko da aka tashi makarantar ta yi tuɓus, tafiya ma da ƙyar ta dinga jan ƙafafuwanta tsabar wahalar da ta sha. Tana kallo Bus ɗin makarantar tasu ta tafi ba tare da ta bi ta kanta ba. Da ƙafa ta yi tattakin fita wajen makarantar tana ta tafiya amma ba ta san inda za ta je ba.

Tsabar kuka sai da idanuwanta suka kumbure, idan ta gaji da tafiya ta tsaya ta huta. Masu bi ta kai idan sun tambayi me take yi wa kuka ta yi banza da sh. Haka ta dinga yi tana ta kalle-kalle a titin tana tafiya, sai ta gaji ta zauna jim kaɗan ta miƙe ta ci gaba da tafiya. Haka ta dinga bin gefe-gefen titi har duhun magriba ya kawo jiki.



A can gidan su Hajiya kuma ganin ƙarfe shida da rabi ta buga har lokacin ba ta dawo ba; ta tayar da direbanta ta ce ya tafi makarantar ya dubo ta. Ko da ya tafi maigadi ya tabbatar masa da cewa lalle babu kowa a cikin makaranta tun da yamma kowa ya watse.

Aka kira shugaban makarantar ya sanar da direban Hajiya duk abin da ya faru, har da takardar sallamar da aka ba ta ta kai wa Aliyu duk ya sanar da shi.

Hankalin Hajiya ya tashi matuƙa a lokacin da direban ya kira ta a waya ya yi mata bayani, ta ce da shi kada ya dawo gida sai da Bintoto, ya shiga neman ta a titunan garin ko Allah zai sa a gan ta. Sannan ta kira Aliyu a waya ta sanar da shi komai da ya faru, yana ƙoƙarin zille wa zancen shi ma ta matsa masa dole sai ya fita neman ta, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magriba kowa yana ta haramar arwala.

Wasa-wssa har ƙarfe tara na dare ba a gano inda Bintoto ta shiga ba, hankalin Hajiya a tashe ta kira Hari tana tambayar ba ta je gidan ba? Hari ta koma gefe cikin sassauta murya gabanta yana bugawa, ta sanar da ita ko mai kama da ita ba su gani a cikin gidan ba

Gudun Kandala ta jiyo abin da ke faruwa ta tara mata jama'a ta shiga uku. Don abu ne wanda ta tabbatar muddin ta ji labarin Bintoto ta ɓata sai ta tayar da hankulan mutanen unguwar gabaɗaya sun san halin da ake ciki, tsabar masifa da ruɗun da za ta shiga a kan ɓacewar Bintoto.

Ku fito mu bazama neman matar Jabir.🏃🏻‍♀️

Princess Dija.

34.

Bintoto kam tsabar tafiyar da ta sha da jigata; tafiya ma ta kai da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta. Babu shiri ta ja ta tsaya wurin wata mai soya doya da ƙosai. Ta yi tsaye a gaban kaskon suyar ƙosan tana ta kallon matar tare da ƙura wa ƙosan ido. Tun matar ba ta ankara da ita ba har ta fara yi mata faɗa tana kora ta, a kan ta bar wurin ganin ta sanye da kayan makaranta. Bintoto sarauniyar kwaɗayi sai da ta yi gaba sannan ta dawo da gudu wurin matar ganin wani ya tsaya zai saya yana miƙa kuɗi.

"Don Allah don girman Ubangiji ka saya mini ko kaɗan ne yunwa nake ji."

Ta yi wa mutumin magana a marairaice tana shafa cikinta. Matar tana aika mata harara ta ce da mutumin, "Wannan bakar yarinya idan ba ta ci kosan nan ba za ta iya mutuwa, tun ɗazu take tsayuwa tamkar ta faɗo mini a ka."

Mutumin ya ce a ba ta ƙosai da doya na ɗari biyu. Haka matar ta wurga mata ƙwarori a leda ta jefa mata. Ta duƙa cikin sauri ta ɗauka tana aika wa matar harara ta ce,

"Ai tun da na rantse sai na ci shi ko ba kya so."

"Mayyar banza! Ki je ki yi ta ci."

Matar ta faɗa tana ci gaba da sallamar mutane Bintoto ta yi gaba tana zagin ta ƙasa-ƙasa tana cin ƙosan. Sai da ta yi nisa da ita ta ɗaga murya tana cewa,

"Mai ƙosai!"

Tana waigowa ta yi mata daƙuwa ta zura da gudu dafe da jakar makarantarta da ke goye a bayanta, sannan kwandon abincinta a hannu. Kai kawai mai ƙosan ta girgiza cike da takaicin wasu iyayen da suke ɓata yaransu, ta yadda yaran ba sa shayin nuna rashin tarbiyyar a ko'ina saboda ba a nuna musu sun yi kuskure a lokacin da ya dace. Sai bayan sun girma a dawo ganin laifin yaran bayan dama ce aka ba su tun suna ƙananu.

Bintoto kam ta ci tafiya sosai kafin ta samu bakin wani masallaci ta kwanta, tana sauke numfashin wahala tana kuka, bayan ta kwankwaɗi ruwan randar masallacin kofi biyu tana nishi. A daidai lokacin ladanin masallacin ya ƙaraso wurin yana ta sauri zai je ya yi kiran sallah.

Hango ta a wurin jikinta da kayan makaranta, ya yi hanzarin isa inda take yana faɗin,

"Ke! Me kike yi a nan wurin?"

Bintoto ta yi banza da shi kamar ba ta ji ba har ya isa kanta yana muzurai ya sake cewa,

"Lafiyarki kuwa? Ko ba kya jin me nake faɗa?"

A nan ma ta yi masa banza, don ko kallon sa ba ta yi ba har lokacin, sai sharar hawaye take yi tana ajiyar zuciya. Fahimtar ba ta da niyyar magana ga lokacin sallah yana ta gudu har wasu sun fara zuwa. Ya yi hanzarin barin wurin ya shiga Masallacin ya yi kiran sallar. Ko da ya fito ya ga mutane har sun fara zagaye Bintoto suna yi mata makamancin tambayoyin da ya yi mata, amma su ma babu wanda ta ce da komai. Hakan ya sa ya yi zargin ko kurma ce wataƙila ba ta ji kuma ba ta magana.

Nan take ya hau yi mata maganar kurame, bayan wasu sun riƙa ta an tayar da ita zaune tana ƙara langaɓewa.

Ɗaga kanta ta yi tana ƙare wa mutanen da suka zagaye ta kallo ɗaya bayan ɗaya. Kafin ta fashe da wani kalar kuka mara sauti tana faɗin,

"Wayyo Kandala ki zo za a kashe ni!"

Maganar da ta yi suka gano ba kurma ba ce, a nan aka rufu kanta da tambayar ina ne gidansu, waye mahaifinta a garin kuma a wace unguwa take.

Sai dai kasancewar ba ta san sunan unguwannin garin ba, ballantana ta faɗi sunan wata unguwa ko ta su Hajiya; zarar ido kawai ta dinga yi kafin ta koma yi musu misalin yanayin gidan su Hajiya da bayyana abubuwan da ke cikin unguwar tasu. Amma ko kaɗan hakan bai sa sun gano unguwar da take ƙoƙarin kwatantawa ba. Don tun da yamma mutane suka dinga tambayar inda ta fito da unguwar da take. Kasancewar ba ta riƙe komai a kanta ya sa ta kasa furta sunan unguwar su Hajiya kamar yadda ta ji Hari tana faɗa.

Ganin an tayar da sallah kuma masu son taimakon ta za ta ɓata musu lokaci; suka bar ta a nan suka shige masallaci. Sai da aka gama liman ya yi sanarwar an tsinci wata yarinya a bakin masallacin, da kalar uniform ɗin da ke jikinta.



A nan take wani bawan Allah ya ce ya san makarantar yana da lambar shugaban makarantar, ɗaga waya ya kira shugaban makarantar. Inda ya yi masa bayanin an ga ɗalibar makarantarsu, kuma alamu ya nuna ɓata ta yi ba ta san inda za ta je ba. Cikin tashin hankali da murnar samun labarinta; ya ce a riƙe masa ita yanzu zai ƙaraso. Saboda tun da ya ji labarin ba ta koma gida ba yake cikin fargaba, gudun wani abu ya same ta a ce su ne sila.

Jikinsa yana rawa ya kira Aliyu ya sanar da shi an gan ta, tare da yi masa kwatancen masallacin da aka faɗa masa don su haɗa ƙarfi su je tare. Aliyu ya nufi inda aka faɗa masa kai-tsaye yana tsaki, tsabar gajiya da gundura da yawon neman ta, wanda Hajiya ta saka shi yi ba don yana so ba. Motarsa kawai ya juya cikin mugun gudu ya isa wurin, da jagorancin wayar da yake yi da shugaban makarantar da ke yi masa kwatance har ya isa. A gefen masallacin ya yi parking, ya fito ransa a ɓace ya isa inda ya ga mutane sun yi cincirindo.

.

Da sassarfa ya isa inda take zauna ta haɗa kai da gwiwa tana kuka. Hango shugaban makarantar a cikin tawagar mutanen ya sa ya yi wurin sa yana miƙa masa hannu suka gaisa. Kafin ya koma kallon Bintoto ya fara faɗin,

"Shashasha! Wato a nan kika ɓoye, gabaɗaya kin ɗaga wa mutane hankali, kin sa an hana ni zama lafiya. Tun kafin magrib nake ta bulayin neman ki, amma don rashin mutunci kin zo nan kin zauna, tamkar wadda ba ta san kowa a garin b...."

"Yanzu dai a yi haƙuri, tun da an gan ta sai a bi ta a hankali har a samo kanta a ji dalilin da ya hana ta komowa gida."

Zancen wani dattijo kenan saboda ganin yadda Aliyun yake yi tamkar ya rufe ta da duka. A fusace ya ce,

"Babu wani dalili illa na rashin mutuncin da ta saba yi."

Shugaban makarantar ya karɓe zancen da bayanin abin da ta aikata wa malaminsu wanda ya sa aka hora ta, sannan suka ba ta takardar sallama, inda ya ƙara da cewa,

"Mu ma fa wannan yarinyar ta so ta goga mana laifin da zai ɓata mana sunan makaranta. Sa'a ɗaya ta ci da take sanye da kayan makarantar da babu yadda za a yi a gane daga inda ta fito. Saboda tambayar duniya an yi mata amma ba ta ce da kowa komai ba, sai sunan Kandala da take ta kira, sannan ta ƙi bayanin da za a gano inda take da unguwarsu ballantana a kai ta gida sai da aka kira ni a waya na z...."

"Ai wannan yarinyar da kuka gani ba ƙaramar hatsabibiya ba ce! Duk abin da take aikatawa da gangan take y...za ki tashi mu tafi ko sai na tattake ki a nan wurin?"

Aliyu ya faɗa yana ƙoƙarin kai mata duka ana rirriƙe shi. Bintoto ta miƙe tana ciccika alamun ta gama yin zuciya, ta nufi motarsa jiri yana ɗibar ta. Tsabar yunwa ta gama cinye cikinta, don rabonta da abinci tun ƙosai da doyar da ta ci. Su ɗin ma ta dai ci ne kawai, amma tayar da kwaɗayi kawai ta yi, saboda ta saba mugun ci, irin wanda sai ta ji za ta yi amai sannan take haƙura.

A cikin motar ma haɗa kai da gwiwa ta yi tana ta shesshekar kuka da ajiyar zuciya. Har ya gama godiya ga mutanen da suka jajanta abin, sannan ya shigo motar yana faɗa ya fisgi motar tamkar zai tashi sama ya kama titi.

Sai da ya gaji da kukanta sannan ya buga mata tsawa ta yi masa shiru ko ya tsayar da motar ya yi mata dukan kawo wuƙa. Dole ta ja bakinta ta yi shiru ganin da gaske zai iya aikata mata abin da ya faɗa, duba da yadda yake a fusace.

Yawan kiran da Hajiya take yi masa yana ƙin ɗagawa, a ƙarshe ya ɗaga cikin muryar mai ɗauke da fushi ya ce mata ga shi nan zuwa gidan ya an gan ta.

Hajiya ta kai zaune babu shiri dafe da kanta tana faɗin, "Alhamdulillah Allah na gode wa Allah."

Hari da ke zaune gaban Hajiyar tana sharar ƙwalla ta yi hanzarin ɗaga kai saboda jin labarin an gan ta. Fuskarta a sake cike da murna ita ma ta ɗaga hannu tana godiya ga Allah.

Don tsabar firgici ba ta san lokacin da ta kawo gidan su Hajiya ba. Ko Kandala ba ta san fitarta cikin gidan ba. Saboda tsoron abin ya yi ƙamarin da dole babu yadda za a yi sai an sanar da ita abin da yake faruwa. Kuma ba ta san da wane kalar yare za ta bayyana mata laifin na Bintoto ne ba na kowa ba. Don Hajiya ta yi mata duk bayanin da ta samu a kan abin da ya faru makaranta.

Ko da Aliyu ya iso gabaɗaya mutanen gidan suna ƙofar gidan ana jiran su.

Saboda Hajiya ta ɗaga wa kowa hankali a gidan, har masallatai aka dinga zuwa ana kai sanarwa, bayan wurin hakiman unguwanni da zummar ko an kai ta can, ko kuma idan an samu wani labarin da ya danganci ɓatan wasu a sanar da ita.

Aliyu ya yi parking motar ya fice a fusace yana cewa, "Wallahi Hajiya idan ba ki rabu da yarinyar nan ba sai ta jawo miki fitinar da ta fi wannan! Ki kore ta kawai ta bar gidan nan kawai kowa ya hut..."

"Yi mini shiru Aliyu! Da ɓatan ta za mu ji ko da surutanka? Ba ka ce an gan ta ba, ina take?"

Aliyu da ya juya yana kallon motarsa ya ce, "Tana jin ki ai ba ta ga damar fitowa ba n...."

Yana maganar ya yi cikin gidan cike da jin haushin Bintoton. Hajiya da Hari tare da sauran masu aikin gidan suka isa inda motar tasa suna kiran sunanta. Ganin ta a dunƙule wuri ɗaya ko motsi ba ta yi Hari ta jawo ta cikin wani sabon fargaba tana kiran sunanta cikin ɗaga murya.

"Bintoto! Bintoto me ya same ki?"

Luu ta yi ta faɗa jikin Hari idanuwanta a rufe tana mashalo. Salati Hajiya ta saka tana kuka ta dinga taɓa Bintoto tana kiran,

"Mai sunan uwata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login