Showing 6001 words to 9000 words out of 88489 words

Chapter 3 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2051

kowane da adadin kuɗinsa sannan ta rufe mata da wata raga mai riƙon ruwa. Wadda aka jiƙe sharkaf da ruwa don kada goron ya sha iska ya yi saurin bushewa.

Ta yi ɗana da tiren goron tana tafe tana wasa da wani zare a hannunta hankalinta gabaɗaya ya ɗauku a kan wasar da take yi. Babu zato ta ci karo da wani saurayi suka yi kiciɓis, Cikin tsautsayi kafin ta kamo tiren goronta tuni ya yi sama ya dawo ƙasa ya kife, kafin ta ankara ya watse ɗaiɗaya a cikin ƙasa.

A zabure ta ɗaga kanta cikin fushi ta yi magana tana zaro ido.

"Kan uban nan! Ai na rantse da Allah sai ka biya shi! Cabɗijam haka kawai ka sa na yi ɓari don ba ka da imani?"

Ɗan saurayin ya duƙa cikin rawar jiki ya fara tsince mata goron ɗaya bayan ɗaya yana sakawa a cikin tire har ya tsince duka, sannan ya ɗauko ragar ya saka mata a cikin tiren ya miƙe fuska babu yabo babu fallasa ya isa gabanta ya tsaya yana 'yar dariya ya ce,

"Don Allah ki yi haƙuri wallahi ba da gangan na yi b.."

Wani kalar kallo ta yi masa, tare da ƙura masa ido ƙur ko ƙiftawa babu riƙe da ƙugunta tana girgizar jiki, sosai ta so saka shi dariya, amma dole ya ƙumshe dariyar da ta so kufce masa saboda gudun ya ƙara tunzura ta. Ya koma gyara goron a cikin tire kamar wanda aka saka sai ya mayar da shi yadda yake. Sai da ta gaji da hararar sannan ta ja baya tana ce masa,

"Ai na rantse da Allah kuɗin gorona za ka ba ni gabaɗaya, na riga na sayar maka! Don haka ka biya ni kawai ka juye goronka sauri nake yi. Amma ka sani guda ɗaya ba zan karɓa ba don ni na sayar maka da shi duka kawai ka ba ni kuɗina na koma gida."

Ganin idan ya biye ta za ta iya tara masa mutane, hakan ya saka shi tambayar ta kuɗin goron. Sai da ta karkace kai gefe sannan ta zaftaro kuɗin da ya saka shi zaro ido yana ƙare wa goron kallo, saboda ta ce atafau ita goronta na dubu ɗaya ne, bayan kwata-kwata goron ko ɗari biyar bai kai ba. Saboda wani ma gyaran tsutsa ne wanda bai wuce ashirin naira hamsin ba, amma saboda a zauna lafiya haka ya saka hannu a aljihu ya ciro ɗari biyu guda biyu huɗu ya miƙa mata. Sai da ta kalli kuɗin sannan ta maka masa harara tana ci gaba da girgizar jiki kamar wata babbar budurwa ta ce masa,

"Ai wallahi tun da ba tsohuwa nake ba ni ko ba zan karɓi tsofaffin kuɗi ba! Haka kawai don mugunta ga sababbi nan ina gani ka ba ni su, shi ne za ka haɗa ni da waɗanda kafin na je gida sun yage? To ni kuma wallahi ba zan karɓe su ba ahe!"

Ta ƙare maganar tare da murguɗa masa baki tare da juya kai gefe, ba ƙaramar dariya ta so ba shi ba, amman ya dake ya nuna mata ko kaɗan bai ji haushi ba. Ya mayar da kuɗin ya ɗauko mata sababbin da take so ya miƙa mata, jikinta yana rawa ta fisge kuɗin sannan ta sake cewa,

"Allah Ya taimake ka ka biya da sai na yi maka dukan billahillazi, kuma ina zan juye maka goron ni sauri nake yi?"

Sai da ya mayar da sauran kuɗin a aljihunsa sannan ya ce mata ta je duka ya ba ta.

Bintoto ta zaro ido waje cike da jin daɗi da mamaki a kan fuskarta ta ce,

"Da gaske?"

Yana murmushi ya ce, "Da gaske mana, amman da sharaɗin duk lokacin da na zo gidanku za ki fito mu yi hira."

Bintoto tana dariya baki a washe ta ce masa, "Ai idan har za ka ƙara ba ni irin waɗannan kuɗin sababbi dole zan fito kai ma ka sani, don haka ka zo kawai."

Ya juya yana 'yar dariya ya fara tafiya, ta bi shi da kallo kafin ta ɗaga murya tana cewa,



."Don Allah ta wace hanya za ka bi gobe?"

Babu shiri ya waigo cike da mamaki ya jefo mata tambayar "Lafiya?"

Tana wasar baki ta ce, "So nake yi ka sake zubar da goron, ai na san za ka saya ko?"

Bakinsa ya dafe saboda dariyar da ta suɓuce masa, amma a haka ya ba ta amsa da cewa,

"Ki biyo ta nan za mu sake wani karon kamar yau. Amman fa a goben ko kin zubar da goronki ba zan biya ko ficika ba."

Bintoto ta murguɗa masa baki da hararar gefen ido ta ce,

"To na ji, shi kenan ta fi kawai."

Ya juya yana dariyar shirmenta, saboda sai da ta sake ɗaga murya ta jefo masa tambayar, "Amma dai kai ba ɗan garin nan ba ne ko?"

Ba tare da ya juyo ba ya ce mata "E, baƙunta na zo."

Ta bi bayansa da harara sannan ta ɗora tirenta a kai tana haɗa kuɗin wuri ɗaya tana cewa ,

"Ai dai na yi maka wayo, kuma duk ka kuskura muka sake haɗuwa gobe ma sai ka zubar, kuma dole sai ka sayi goron ka bayar da kuɗin sababbi. Baƙin mugu kana da kuɗi da yawa a aljhunka amma ka ce ba za ka biya ba don kada na ƙaru da kai. Hu'umm! ai yasin ba ka isa ba ma duk muka sake haɗuwa dole ma sai ka sake saya tun da wawa ne kai ba ka da wani wayo."

Haka ta yi ta sambatunta ita kaɗai kamar a gabansa take yi, sannan ta je wani gida ta wanke goron ta sake jera shi a tire yadda yake tun farko, sannan ta yi wurin tallar a ranta tana cewa,

_"Ina ma na samu wani hamagon da zai sake zubar da goron ya biya ni. Yasin da gangan zan kifa wa mutum tiren na ƙwale masa kai kuma ya biya ni kuɗin gorona."_

Ku ci gaba da biyo ni don wannan duka shimfiɗa ce a cikin littafin SHAGALALLIYA😊 1k ne kuɗin, za ku same shi a Telegram ba tare da kun yi jira ba. A WhatsApp ma ga mai buƙata PC saboda gudun hayaniya zai iya zuwa mu yi tsada. 1230094555 Access Bank Hadiza D Auta. Lambar waya don turo shaidar biya ko wani ƙarin bayani: 08022014771.

Akafta.

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D. AUTA*

*LAMBA SHIDA.*

Ko da ta tafi tallar ko rabin goron ba ta sayar ba ta dawo gida, saboda ganin ana faɗa ta kasa ta tsare, har sai da aka gama faɗan kaf aka watse, tana ɗauke da tiren goronta a kai tana dariyar jin daɗi da mugunta. Cikin nishaɗi ta nufi gida tana ƙyalƙyala dariya a duk lokacin da ta tuno yadda aka ɗauki Innar Jamila sama aka kayar, sannan aka turmushe kanta cikin ƙasa tana tusoshin wahala.

Da dariya ta faɗa gidan ba tare da ta yi sallama ba, babu shiri dariyar ta tsaya mata cak a sanadin hango kajin Kulu a ƙofar ɗakin Kandala, suna ta caccakar wani abu a cikin kwano. Wanda ba ta raba ɗaya biyu a kan cewa nata ne aka ajiye mata, amma tsabar sun samu sake sukae yin watanda yadda suke so. Haushi ya sa ta yi mugun tsalle tare da kai musu shuri da ƙafa a cikin a rashin sa'a, babu zato sai ga tangal ta faɗi ƙasa warwas riƙe da tiren goronta gam-gam gudun ya zube, amman hakan bai hana goron yin tsalle ya watse ƙasa ba, cikin tsananin takaici ta yi magana a ƙufule tana cewa,

"Kan Uba! Ai wallahi yau sai kun san kun ci mini garin kwaki!"

Tiren ta fara ajiyewa sannan ta miƙe tsaye, cikin zafin nama ta damƙo mafefecin Kandala ta yi cikinsu da duka idonta rufe, a nan ta ci nasarar buge wani ɗan kaza ya faɗi yana shure-shuren mutuwa. Hakan ya yi dai dai da fitowar Kulu daga ɗakinta za ta ajiye kwanon da ta gama cin abinci, aguje ta saki kwanon ta yi kan ɗan kazarta da ke gangar mutuwa tana faɗin,

"Na shiga uku! Me kika yi masa Bintoto?"

Tana zuwa ɗan kazar yana daina motsi alamun ya mutu, cikin ɓacin rai ta ɗago fuskarta a cure ta ce mata,

"Wallahi ki ji tsoron Allah! Don idan kina zaton ni kike yi wa to kanki kike ɗaukar wa kaya, saboda duk zaluncin da kika yi musu ranar lahira sai Allah ya fitar da haƙƙinsu a kanki."

Ta ƙare maganar cikin matsanancin ɓacin rai da mugun jin haushin ta a ranta, don a yadda ta ji a lokacin idan ban da ta san taɓa ta zai jawo mata wani ɓacin ran da yafi mutuwar ɗan kazar; da ta saki jiki ta jibge ta iya son ranta. Amma dole ta ƙyale ta ta juya ta bar wajen cikin ƙunar rai saboda babu halin ɗaukar mataki. Bintoto kam kallo ta bi bayanta da shi tana murguɗa baki cikin tsiwa ta ce,

"Wa ya ce su je su ci mini garin kwaki? Ke yanzu ba ga shi kin ci naki ba har kin fito da kwano! Amma ni kike tura wa kaji su cinye nawa don baƙar mugunta da zalunc..to wallahi ko gobe suka taɓa mini abinci sai na lakaɗa musu ɗan banzan dukan da ya fi wannan!"

Kulu dai ƙanzil ba ta ce mata ba, ganin hakan ya sa Bintoton barin wajen tana harare-harare ta fara kwashe goron da ya zube, sannan ta kai tiren ta ajiye ta zauna tana gungunin faɗin,

"Ai na rantse da Allah ni ba zan ci garin kwakin nan ba, sai dai idan sayo wani zan yi na sha da sikari...haka kawai su je su ci kashi su dawo su saka mini baki a gari kuma ni na zo na ci? Tab! Lalle ma tun da an mayar da ni wawuya so dole na ci, uhum!"

Bayan ta gama surutan nata ta miƙe kamar wata kububuwa tana kumbure-kumburen fuska ta fice gidan. Wani garin ta siyo a cikin kuɗin goron da aka biya ta, har da sikari da ƙuliƙuli ta shigo gidan da 'yar waƙarta alamun jin daɗi. Ƙirjinta ya buga dam babu shiri ta yi turus saboda hango Kandala zaune saman tabarma a bakin ɗakinta, ta buɗe ƙafafuwa tana lissafin kuɗi. Cikin sauri ta ƙarasa tana faɗin,

"Kandala ina kika samo waɗannan kuɗaɗen haka?"

Kandala tana ta lissafinta ba ta tanka mata ba har sai da ta gama sannan ta ɗaga kai ta ce mata,

"Wurin Mandiya na je na karɓo kuɗin adashena, kin ga yanzu sai na je na sayo miki turmin atamfarki ta sallah a kai miki ɗinki, sauran kuɗin kuma zan ƙaro miki kwanoni na adana saboda aurenki, don kina samun miji zan aurar da ke na huta da halinki, saboda a kullum burina bai wuce na ga an kai ki ɗakin mijinki ba ke ma ki yi aure kamar yadda kowa yake yi."

Bintoto ta ɓata fuska tare da kwanciya kan cinyarta cikin sanyin jiki tana cewa,

"Ni dai Kandala wallahi ba na son aure yanzu, sai na tara kuɗin zuwa Saudiyya. Saboda ke ma kin sani mazan garin nan babu wanda zai iya kai ni Makka, ko ke ba ki so na je aikin hajji na sayo miki ɗankwali mai walƙiya?"

Kandala ta dungure mata kai daga kwancen cike da jin haushi ta ce,

"To sannu ɗanwake ka fi ubanka! Baƙin lissafin naki kenan da kika saba, idan ba ɗora wa kai wahala ba a garin nan namu duka mutum nawa ne suka aikin Hajji? Da har kike wannan dogon burin da ko'ina ba zai je da ke ba, ko an ce miki zuwa Makka wasa ne da har za ki je da kuɗin sata?"

Bintoto ta yi saurin tashi zaune tare da turo baki tana kallon ta ta ce,

"Sata kuma! Ni nake yin satar?"

"Ƙwarai ko!"

Kandala ta faɗa tana gutsura goro tare da kawar da kanta gefe, cikin muryar kuka Bintoto ta ce, "Wallahi Allah ni idan ban da sau ɗaya ban taɓa ɗaukar miki kuɗi ba, kuma Allah ma ya sani idan ba sau guda ba ne wutar saƙara da lazza ta ƙona ni!"

Kandala ta yi mata wani kallo tare da dungure mata kai sannan ta ce,

"Wai ke halan kin ɗauka ba na jin ki idan ina barci kina lalubar gefen zanina inda nake ƙulle kuɗina? To ina ganin ki idan kin ga zan tashi ki yi sauri ki saki, don haka kar nake kallon ki kada ki zaci kwanan gaske nake yi idona biyu yarinya."

Bintoto ta yi tsuru-tsuru da ido sannan ta ce, "Yanzu dai kina nufin ɓarauniya ce ni ko?"

Ta ƙare maganar cikin kuka, Kandala ta jawo ta jikinta cikin sigar rarrashi tana faɗin,

"Ke kam me ya sa ba ki san wasa ba? To wasa nake yi miki ai, don ni ban taɓa kama ki kina kwance ƙullin kuɗina ba ko sau ɗaya ma. Don ke ma kin sani a garin nan kaf babu wanda ya isa ya kira ki da ɓarauniya na ƙyale shi ballantana ni na faɗi hakan.. share hawayenki Allah ma ya kiyaye wannan rana."

Bintoto ta janye jikinta daga nata ta miƙe tana kumbura hanci ta jiƙo garin ta yi nesa da Kandala ta zauna tana sha tana zunburar baki alamun ta yi fushi.

Kandala kam har cikin ranta ba ta ji dad'in yadda ta ɓata mata rai ba, shi ya sa ta koma faɗin,

"Ina kuɗin gorona da kika sayar?"

Bintoto ta cire ɗankwalinta inda ta ƙulle kuɗin ta ciro su duka ta ajiye gefenta ba tare da ta ce komi ba ta ci gaba da shan garin kwakin, Kandala ta miƙe ta zo ta ɗauki kuɗin tana lissafawa, ganin ɗari shida sababbi kar ta zaro ido waje tana cewa,

"Ko kin sake komawa tallar bayan wadda na ɗora miki a farko?"

Bintoto ta yi mata kallon gefen ido sannan ta ce,

"Sauran kuɗina ne, ki cire kuɗinki da nake sata a ciki ki bani saura zan saka a asusuna."

Kandala ta zauna kusa da ita tana wasar baki ta ce,

"Daɗina da ke saurin ƙufula, yanzu wannan ɗan abin har ya kai ki yi ta fushi da ni Bintoto? To kwantar da hankalinki daga yanzu kullum na yi sallah zan yi miki addu'ar Allah ya ba ki miji mai kuɗin da zai kai ki Makka ki yi aikin hajji."

Babu shiri Bintoto ta yi saurin washe baki saboda jin daɗin maganar ta ce, "Ai ko wallahi da sai na sa an bugo miki akwatin zinari ki dinga saka tufafinki ki daina saka su cikin fanteka. Saboda ɓeraye su bar shiga suna yi miki kashi a cikin kaya."

Kandala ta yi dariya sannan ta ce "Ni dai ki bar akwatin zinarin, haƙorin azurfa nake so ki sayo mini na saka wa haƙorin nan nawa, kin ga ni ma sai na zamo Hajiya Kandala kamar ke."

Bintoto ta fashe da dariya har da riƙe ciki sannan ta ce,

"To ai ke Kandala haƙorinki irin na giwaye ne, ta ya za a samu haƙorin Makkar da zai yi masa daidai a duniyar nan?"

Kandala ta kai mata dundu a baya ta goce tana dariya ta ce, "Ke dai ki yi ta addu'ar idan na auri miji mai kuɗi na sa a cire shi a saka miki na ƙarfe wanda idan kin so za ki iya cirewa ki ci abinci da shi kamar cokali."

Kandala ta miƙe tana dariya ta ce,

"Bari dai na je na ɓoye kuɗina tun kafin Mani ya zo ya gan su ya saka ransa a banza, ga shi kuma ba ba shi zan yi ba tunda har ya nuna matarsa ta fi mu ni da ke, don haka idan dai Kulu ce ga ta nan ga shi, saboda ko kajinta aka bar shi da su sun ishe shi wahala, ballantana mugun halinta na zalunci da munafurci."

Bintoto ta kai cokalin gari a bakinta, wanda sai da ta ciko shi fam har ya yi tozo, sannan ta haɗiye da ƙyar tana cewa,

"Ai Kandala da ma kin ce ta mayar da su gidansu mu huta da su, kin ga ma garin da kika bar mini ko? To ko da na dawo duk sun ci rabi sun shige cikin kwanon suna ta wawaso."

Kandala ta yi ƙwafa cikin ƙarin jin haushi ta ce, "Sai ba ita ba! kaɗan daga cikin aikinta kenan baƙar muguwa, ai da kin karya 'yanbanza ma a huta."

Bintoto ta yi saurin faɗin, "Ai wallahi sai da na kashe mata ɗan kaza ɗaya yau, don ko gobe ma suka sake ci mini abinci ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login