Showing 24001 words to 27000 words out of 88489 words
Chapter 9 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
ta saka wa ranta masu gidan sun gama samun arziƙinsu tun a nan duniya sun cinye komai.
Ba ta ƙara shiga mamakin da ya tashi kashe ta ba sai da suka shiga falon gidan, a nan ne Kandala ta fara zarar ido yayin da Bintoto ke washe baki saboda farincikin ta tako arziƙi, suka zauna a ƙasan carpet d'in dake shimfiɗe tsakiyar kujerun. Kandala sai faman shafa carpet ɗin take yi tana taɓa jajayen leda seat ɗin da suka ƙara ƙawata falon, waɗanda raɓar ac ta sa suka ɗauki ni'imtaccen sanyi mai ratsa jiki. Sannan suka koma kallon Tv plasma da ke jingine jikin bangon falon tana aiki.
Kandala baki a buɗe take kallon Tv'n tana mamakin irin damben da ake ci a cikin tv kuma wai ba za a raba faɗan ba, hakan ya sa duk aka zo kai duka sai ta zabura tana faɗin,
"Mugun abu!"
Kafin ta koma faɗin,
"Wannan ƙarfi haka! Da alama dai ƙashi ɗaya ne da wannan mutumin, don Allah Hari duba mini ki gani wai mutum fiye da goma duk ya bai wa ƙasa ajiyar su. Ke kin san wannan daga ganin shi horon tuwon dawa ne."
Hari tana murmushi ta ce da ita,
"Ai shiri ne Inna, duk abin da kika gani ba gaskiya ba ne, shi ya sa ma..."
Babu shiri Kandala ta yi saurin faɗin,
"Wane shiri bayan kina ganin yadda yake fitar wa da mutane jini? duba..duba ki gani Har... Innalilahi wa inna ilaihirraji'un har da haƙori ya zubar don yana la'ananne.. kaiiiii! Subhanallah ya gama aiki wannan ai rashin imanin n...."
Sallamar wata dattijuwar mata ne ya sa suka kai kallonsu gare ta dukansu, bayan sun amsa mata ta zauna fuskarta ɗauke da murmushi ta dinga amsa gaisuwar da Harin ta fara yi mata, Kandala ma ta washe baki d dogon haƙorinta ya ƙara fitowa tana cewa,
"Hajiya sannu da fitowa, tun ɗazu muna nan muna kallon tanbaɗaɗɗen yaron can mai yi wa mutane dukan tsiya, kuma abin haushi kowa yana kallo babu mai iya rabawa."
Hajiyar sai da ta yi murmushi mai sauti sannan ta ɗauki remote ta rage muryar tv tana cey,
"Shiri ne kawai inna, amma ba da gaske dukan ake yi ba."
Kandala idonta a kan Tv ta ce,
"To kam wannan ai rashin daraja ne, wane shiri za a yi da dukan da za a fitar wa da mutane jini?"
Hari tana murmushi ta gyara zamanta sannan ta daƙile hirar cikin dabarar dafa kafaɗar Bintoto wadda ta yi nutsuwar dole tana kallo, idonta ƙurin ko ƙiftawa ba ta yi, ta ce da ita,
"'Yata ba ki gaishe da Hajiya ba."
Sai da ta a ɓata fuska cike da jin haushin Hari ta katse mata kallon, ganin sun haɗa ido da Hajiyar ta koma washe baki tana cewa,
"Sannu Hajiya!"
Hajiya ta faɗaɗa fuskarta da murmushi ta ce,
"Yawwa Umma Binta."
Bintoto ba ta ce komai ba ta mayar da kanta tana ci gaba da kallon, har da matsawa gaban tv gudun su Hari su dame ta. Hari tana 'yar dariya ta ce da Hajiyar,
"Ashe sunan tsohuwa ne da ita?"
Hajiyar tana murmushi ta amsa mata da cewa,
"Sunan ƙanwar mahaifiyata ne, kuma a hannunta na tashi har na yi aure shi ya sa duk inda na ji sunan ba na wasa ina girmama shi sosai gaskiya."
Cike da jin dadi Kandala ta washe baki ta ce,
"Ai suna ne mai daraja tun asali, saboda ɗiyar Ma'aikin Allah guda ce babu tamkar ta a duniya."
Hajiya tana murmushi ta ce,
"Haka ne tabbas Allah ya ba mu albarkacin masu daraja!"
Dukansu suka ce amin, kafin Hari ta ɗan muskuta sannan ta ce,
"To Hajiya ga Inna Kandala nan ita ce kakarta, mai sunan tsohuwar kuma ita ce wadda kika ce na samo miki."
Hajiyar ta kai kallon ta ga Bintoto sannan ta yi 'yar dariya ta ce,
"Ta yi sosai, duk da cewa ina ganin kamar za ta yi ƙanƙanta da raino, don na fahimci da wuya idan za ta mayar da hankali a kan abin da ake so ta y...."
Kandala ta yi caraf da zancen tana cewa,
"Za ta iya kuwa! Don tana son yara sosai ko a garinmu tana ɗaukar 'ya'yan maƙota, kuma da ƙyar ake karɓar su hannunta idan ta goya su har barci suke yi a bayanta."
Hajiyar ta yi murmushi sannan ta ce,
"To ya yi babu damuwa, bari direba ya zo ya kai ta gidan da za ta yi aikin, an yi sa'a ma yau matar gidan tana gida ba ta fita wurin aikin ba."
Kandala ta yi saurin haɗiye wasu yawu muƙut sannan ta ce,
"Amma da ni za a je na ga gidan duk lokacin da na tashi ganin ta sai na je, duk da na so a ce ni ma akwai aikin da zan yi a can sai mu zauna tare da ita, ko kuma a bar mu nan gidan ni da ita mu yi wani aikin kamar sai ya fi da a kai ta wani gida daban."
Hajiyar ta yi 'yar dariyar manya saboda ta gano ba ta son rabuwa da ita ne kawai, cikin murmushi ta ce da ita,
"Ki yi haƙuri Inna, ai can ɗin ma gida ne za ta je saboda matar yaron gidan nan ne za ta yi wa aikin."
Kandala ta yi shiru kawai ba don ta so ba, haka aka tsadance kuɗin aikin kowa ya amince. Hajiyar ta miƙe tana kiran wata 'yar aikinta, jikinta yana rawa ta rusuna ta gaishe da su Hari kafin ta mayar da hankali a kan Hajiyar. Kai-tsaye ta ce ta je da su wurin direban gidan ya kai su gidan Hamida.
Sannan ta wuce ciki bayan ta ce su jira ta, mintuna a tsakani ta dawo da wata leda da kuɗi a hannunta ta miƙa wa Hari suka yi sallama. Hari ta ɗaga Bintoto sama tare da jan hannunta gudun ta tsaya magana ta kunyata su a gaban Hajiya. Don ƙaramin aikinta ne ta ce ba za ta je ba sai ta gama kallo. Har suka fita falon Bintoto ba ta daina waigen Tv ba, duk da jan da Hari take yi wa hannunta, don ta san muddin aka biye ta ba fitar za ta yi ba.
Da sauran kallo. Yanzu ma aka fara.
Domin ci gaba da karanta littafin Shagalalliya ku biya kuɗinku ku more karatunku mai cike da zallar nishaɗi.
*Princess Dija✍🏼*
* SHAGALALLIYA!*
*NA HADIZA D AUTA*
1 kacal, 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya ta wannan lambar 08022014771.
*LAMBA SHA BIYAR.*
A wannan karon sun shiga motar lafiya ba tare da ƙauyanci ba, amman wajen rufe ƙofar sai da aka rufe wa Kandala tana rufe ido tare da janye fuskarta gudun tsautsayi ya sa garin rufewa a buge mata fuska.
Tun da suka shiga unguwar su Hamidar kallon su ya koma sama, saboda ganin dogayen gidaje masu benaye hawa-hawa gwanin burgewa. Domin kafatanin unguwar ta masu kuɗi ce sai tsilla-tsilla da za a kira masu dama-dama, amma unguwar ta yi fice da sunan manyan masu kuɗi waɗanda suka ci suka ƙoshi. Domin ko a tsarin gidajen za a fahimci sai wane da wane ne a cikin ta.
Har bakin ƙofar gidan aka ajiye su suka fito Kandala da Bintoton suna ƙara ware idanuwa suna ta kallo, don ko Hari da ta goge da zama cikin 'yan birni ba ta ɗauke idanuwanta daga kallon gidan ba. 'Yar aikin Hajiya ta yi musu jagora har cikin gidan zuwa wani ƙaton falo irin na alfarma, ƙamshin da ya mamaye hancinsu ya sa dukansu suka ja numfashi. Saboda falon ya tsaru ta ko'ina ƙalƙal tamkar ba a rayuwa a cikin sa, bayan sun zazzauna ƙasa 'yar aikin Hajiya ta yi ciki ta bar su, mintuna a tsakani suka fara jin kukan ƙaramar yarinya yana doso falon.
Sai ga wata matashiyar mace mai kimanin shekara ashirin da biyar ta fito saɓe da 'yarta a kafaɗa tana girgiza ta saboda azabbaen kukan da take yi, tare da 'yar aikin suka ƙaraso falon fuskarta a washe ta zauna tana gaishe su, Bintoto ta bi ta da kallo cike da burgewa saboda ganin ta fes da ita waton 'yar gayun gaske, sannan ga ta ma sha Allah babu makusa, duk da cewa ba ta cika manyan kyau ba amma babu muni a fuskarta. Bugu da ƙari gayunta ya sa ta zama wata kalar tauraruwa a idanuwan su Bintoto.
Hamida tana ci gaba da girgizar 'yarta ta ce da su,
"Yanzu Hajiya take sanar da ni za ku zo!"
Hari ta gyara zamanta ta ce,
"E, Haka ne."
Sannan ta kalli Bintoto ta sake cewa,
"Ga wadda za ta taimaka miki da rainon yarinyar, duk da cewa kin sani amma yana da kyau a ƙara yi miki bayani...yawwa Bintoto je ki karɓi 'yar taku ki gani don na san za ta daina kukan idan ta gano ke ce kika ɗauke ta."
Ta ƙare maganar tare da kallon Bintoton tana dariya cike da umarni a kallonta, Bintoto ta miƙe cikin zumuɗi ta karɓe yarinyar ta ɗora ta a bayanta da nufin goya ta, sai ga yarinya tana shirin faɗowa saboda zilliyar da take yi. Hakan ya jawo hantar Hari da Kandala kaɗawa, saboda tsoron ta kayar da ɗiyar mutane su shiga uku, amma cikin sa'a ta goya ta sannan ta kalli Hamidar ta ce,
"Ɗauko zani na saka sai goyon ya fi daɗi."
Hamida tana dariya ta miƙe cike da jin daɗi ta yi ciki mintuna a tsakani ta fito da zanin ta miƙa wa Bintoto. Bakinta a washe ta karɓa ta goye yarinyar tsantsan sannan ta fara bubbuga duwawunta tana yawo, kamar almara yarinya ta yi shiru saboda ta ji daɗin goyon,kuma daman shi take buƙata ba ta samu ba. Don Hamida ba ta son goya ta, sai kullum tana saɓe a kafaɗa shi ya sa wani lokaci take damun ta da rigima, musamman idan tana jin barci.
Mintuna a tsakani yarinya ta shiga sauke numfashi da ajiyar zuciya tsabar jin daɗin goyon da kukan da tasha, hakan ya faranta wa kowa rai saboda ganin Bintoton ta fara sanin kan aikinta. Hari ta bai wa Hamida haƙuri a kan zaman da za ta yi da Bintoton, sannan ta ƙara nuna mata cewa yarinya ce sai ana yi ana nuna mata hanya idan ta yi laifi. Hamida ta ɗauki amanar Bintoto da kyau saboda jin daɗin kulawar da ta fara yi wa 'yarta cike da burin faranta mata ita ma. Da haka ta yi musu alheri suka yi sallama da ita ta rako su har bakin gate, Kandala tana share ƙwalla ganin Bintoto tana yi mata bye-bye, cike da farincikin za ta zauna gidan 'yan gayu ita ma ta zama mai kuɗi.
Hari da 'yar aikin duka suka shiga mota amman Kandala tsaye take jikin motar tana kuka, ganin hakan ya sa Bintoto ta zo wurinta tare da yi mata raɗa a kunne tana cewa,
"Kin ga gidan masu kuɗi ne ni ma kuɗin zan yi na kai ki makka Kandala, don haka ki yi haƙuri ki tafi don ALLAH tun kafin ki jawo matar ta ce ta fasa son aikin na shiga uku."
Kandala ta dungure mata kai cike da takaici ta juya tana ƙoƙarin shiga motar tana kuka, Bintoto ta turo baki cike da jin haushi ta sake cewa,
"Ni dai don Allah ki daina kukan nan Kandala sai ka ce an ce da mun rabu mutuwa zan yi? "
Takaici ya ƙara rufe Kandala ta yi banza da ita tana ci gaba da goge ruwan hawayenta, Bintoto ta rufe mata ƙofar bayan ta shige cikin gidan tana wasar baki ta ce,
"Sai watarana Kandalata! Inna sai kun ƙara zuwa gani na..."
Hari tana ɗaga mata hannu direban ya ja motar suka tafi, hakan ya janyo Kandala ta fashe da wani sabon kuka mai sauti iya ƙarfinta tana faɗin,
"Wayyo kaina shikenan an raba ni da Bintoto!"
Hari tana ba ta haƙuri suka kama titi, Bintoto kam hankalinta a kasance ta bi Hamida suka koma cikin gidan goye da yarinyar, wadda har lokacin ba ta daina ajiyar zuciya a cikin barcin ba, bayan sun koma falon ta kalli Hamidar tana cewa,
"Wannan abin naki shi baya magana ne? Na ga a can gidan da muka fito nasu har dambacewa ake yi muna ta shan kallo."
Bayaninta ya sa Hamida ta fahimci abin take nufi da zancen, tana 'yar dariya ta nufi Tv ta kunna mata tashar Arewa 24, sannan ta juyo tana cewa da ita,
"Zo mu je ki ga masaukin ki sannan ki dawo ki ci gaba da kallon."
Idon Bintoto a kan Tv ta ce,
"Laaa! Ashe har da Hausa abun yana yi na ji kamar ita ce ake yi fa! Don Allah bar ni na gani kar kafin mu dawo su ɗauke maganarsu."
Hamida ta ɗauki remote ta ƙara volume kawai sannan ta zauna tana dariyar shirmenta don ta fahimci tana da abubuwan ban dariya da yawa, saboda muryar kaɗan take fita, amma don ta ji daɗin kallon kawai ta ƙara mata. Kamar haɗin baki aka fara waƙar makullin zuciya, daɗin waƙar ya sa Bintoto ta fara cashewa a gaban Tv tana kwaikwayon yadda ta ga masu rawar suna yi. Hamida sai faman cin dariya take yi saboda yadda take ta wata malƙwasar jiki tana karya wuya. Da shauƙin waƙar ya ɗebe ta ta murɗe ƙafafuwa garin koyon rawar Zee pretty inda take harba ƙafa ɗaya baya, kawai sai ga Bintoto ta yi bayan duka ta faɗi babu shiri ta taushe yarinya, kafin kace me yarinya ta tsala ihun kuka na tashin hankali. A zabure Hamida ta yi kansu ta karɓe yarinyar ranta a ɓace ta fara duba jikinta tana shafa kanta, don gefen teburin tsakiyar falon da suka faɗa kansa ya buge mata kai. Wanda cikin ɗan lokaci wurin ya haye ya yi ƙaton ƙololo, ga jikin yaro ba taushi da kuma tsautsayi ya afka tun a tashin farko.
Har an fara wasar ashe😲😂
*Princess Dija ce✍🏼*
SHAGALLIYA
16.
Ganin ƙololon da ke kan yarinyar ya sa Bintoto tsurewa ta shiga zarar ido bayan ta ɗora hannu aka tana cizon yatsa. Hamida ta shiga murza wurin daidai lokacin da suka jiyo gunjin mota alamun maigidan ne ya dawo. A zabure ta miƙe jikinta yana rawa ta yi ɗakinta da sasssarfa, ganin wurin har ya fashe jini ya fito. A nan ta bar Bintoto tsaye tamkar an dasa ta tsabar sanyin da jikinta ya yi, amma hakan bai hana ta sake bin wata waƙar da aka saki ba, har da gwada yadda ake yin rawar tamkar ba ta aikata komai ba.
Yana shigowa falon ya yi ido biyu da Bintoto a tsaye tana wara hannuwa har da juyi bakinta yana muimui saboda bin waƙar da take yi. Cike da mamaki ya zagaya ta bayan kujeru ya shigo cikin falon, bayan ya gama kallon ta tsawon mintuna riƙe da ƙugu ko ƙiftawa ba ya yi. Ganin ta gan shi har sun haɗa ido amma ba ta daina rawar ba, ballantana ya samu arziƙin gaisuwa ko ta nutsu. A harzuƙe ya bi gefenta tamkar ya kai mata duka ya kashe socket ɗin sannan ya ciire wayoyin yana kumbura ya nufi wurin Hamida, saboda jiyo sautin kukan yarinyar yana tashi babu ƙaƙƙautawa.
Ransa a ɓace ya faɗa ɗakin idonsa a kan yarinyar da Hamida ke ƙoƙarin goge mata jinin da tissue, takaicin jin kukan da yarinyar take ta tsalawa ya ƙara ƙona masa rai. Hakan ya sa ya rufe ta da faɗan da ya saba ta inda yake shiga ba a nan yake fita ba. Domin tun kafin ya ji dalilin kukan ya fisge yarinyar daga hannunta yana nanacin ya gaji da sakacin da take yi wa rainon yarinyar. Cike da fargaba ta fara magana cikin sanyin muryarta da tunanin za ta fita idan ta sanar da shi gaskiya.
"Don Allah ka yi haƙur...wallahi tsautsayi ne kawai ya jawo ta ƙwale da table ɗin falo, amma dukanmu ba mu san hakan za ta faruwa b.."
"Dukanku ke da wa?"
Sai da ta haɗiye yawun firgicin da take ciki sannan ta ce, "Ni da wadda ta ƙwale ta ba da gangan b.."
Wani mugun kallon da ya wurga mata fuskarsa a cure ya sa ta haɗiye sauran maganar da ke cikin bakinta. Fuskarsa a cure ya saɓa yarinyar a kafaɗa sannan ya nuna ta da ɗan yatsa cike da gargaɗi ya yi magana cikin kaushinn murya ya ce,
"Ta bar gidan nan kafin na dawo! idan kuma na tarar da ita hatta ke sai na nuna miki asalin wane ne ni!"
Yana gama maganar ya fice daga ɗakin, ransa a ɓace ya fice gidan ko kallon inda Bintoton take bai yi ba ballantana ya bi ta kan kumburin da take yi saboda jin haushin kashe kallon da ya yi, sannan da mugun kallon da take wurga masa riƙe da ƙugunta tun a lokacin da ya fito har zuwa fitarsa cikin falon.
Shiru ya ratsa tsakani bayan fitarsa gidan, daga Hamida har Bintoto babu wanda ya yi motsin kirki. Sautin kiran da aka yi wa Hamida ya ja hankalin Bintoto zuwa inda wayar take, cikin sauri ta isa wurin cike da farin ciki ta rarumi wayar