Showing 18001 words to 21000 words out of 88489 words

Chapter 7 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2054

gidan, ta ɗauki lokaci tana cin kukanta, tare da iƙirarin sai ta je birni ta auri mai kuɗin da zai kai ta Makka.

Bayan kwana biyu labari ya watsu a cikin gari Kandala da Bintoto za su je birni aikatau, wasu da yawa sun zo har gida suna nuna wa Kandala ta yi zamanta ta bar Bintoto kawai ta je, amma ta kafe kai-da-fata a kan sam ba za ta zauna ba ƙafarta ƙafar Bintotonta.

Kulu kam murna cikin ranta kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don daɗi, Mani ne kawai mai baƙincikin tafiyar da takaicin rashin da zai yi, don da ma ita ce gatansa, idan ta tafi bai san yadda zai yi da hidimar gida da sauran matsalolin yau da gobe na rayuwa ba, shi ya sa ya yi ta magiya a kan kada ta je ta bar Bintoto kawai su tafi, amma ganin babu fuska ya daina kushe tafiyar ya koma neman abin da zai samu a wurinta kafin ta tafi.

Bintoto kam bankwana ta dinga yi da ƙawayenta, tana sanar da su mai kuɗi za ta aura idan ta je birni wanda zai kai ta Makka. Jamila kuwa alƙawari ta yi mata a kan cewa duk ranar da ta yi kuɗi ita za ta dinga yi mata aikatau a gidanta. Jamila tana dariyar haukar ta da sambatun da take yi na shirme ta ce da Bintoton,

"Ke a tunaninki don kin je birni aikatau sai ki yi kuɗi har ki je Makka? Lalle ma, to ai ko su Karime da Habbobo da suka tafi babu abin da suka samo. Kuma har suka gama aikatau suka dawo gida ba su samu miji a birni a nan garin aka yi musu aure. Don haka ke ma...."

"Yi mini shiru da baƙin bakinki!"

Bintoto ta kai wa Jamila wani kalar naushi a saman bakinta, wanda ya saka ta dakatar da maganar ba tare da ta shirya ba. Tare da yi mata wani mugun kallo kafin ta ce,

"Sannu mai baƙin baki! To ta Allah ba taki ba ce ai, na san baƙin cikin tafiyar kike ji shi ya sa kike yi mini muguwar fata. To ko kina so ko ba kya so sai na auri miji ɗan birni kuma a gaban idonki zai kai ni Makka. Kuma na rantse da Allah kina kallo zan yi rabon kayan Makka, sai na bai wa kowa a garin nan amma ke na hana mik...kuma daga yau ko gani na kika yi kika yi mini magana sai na darje miki baƙin bakinki mai shegen wari."

Tana gama faɗar hakan ta bar wurin bayan ta buga mata tsaki har da zuba mata yawu a jiki, tare da toshe hanci alamun warinta take ji. Jamila kam dafe bakin nata ta yi, wanda take jin zogin naushin da Bintoton ta yi mata har lokacin, sai ƙoƙarin shafa shi take yi saboda jinin da ke fita tana gogewa da gefen ɗanƙwalinta, yayin da take ta tofar da yawunta jinin yana fita. Saboda Bintoto ta fasa mata leɓe, sannan haƙorinta ma jini suke yi.

"Allah Ya isana wallahi. Baƙar muguwa kuma ba za ki taɓa auren ɗan birnin b..."

Jamila ta faɗa tana kallon bayan Bintoton, ganin ta juyo a fusace ta bar wurin da gudu, Bintoto ta rufa mata baya tana faɗin,

"Wallahi ki ma tsaya don ko gaban Innarki kika je sai na ci malfar ubank..."

Tsoro ya hana Jamila tsayawa, ta nufi gidansu da gudu tana kiran sunan Innarta. Bintoto ma ta afka babu shayi ta nemi jawo Jamila a bayan Innarta da tana ƙoƙarin kai mata duka. Innar Jamila ta samu riƙe hannuwan Bintoto gam tana faɗa, hakan ya bai wa Jamila damar faɗawa ɗakinsu ta datse ƙofa. Haushi ya sa Bintoto yin cikin Innar Jamila da nufin su yi kokawa tana haki tana faɗin,

"Ai sai mu yi faɗan da ke tun da kin saye mata faɗan...." Tana maganar ta zura ƙafa ta shure garin da ta gani a cikin ƙwarya, daidai lokacin da Habu ya shigo gidan cike da mamaki, saboda ganin abin da ke faruwa kamar almara, Bintoto da kokawa da Innarsu. Ita ma kamar mai tsoron ta hannuwanta kawai ta dinga riƙewa amma ko duka ɗaya ba ta yi mata ba.

Jikinsa yana rawa ya katso bulalar dalbejiyar da ke tsakiyar gidan, idanuwansa a rufe ya dinga zabga wa Bintoto tana tsalle da ihun kiran sunan Kandala. Innarsu tana hana shi dukan ta amma bai ji ba, sai da ya zane ta raɗam sannan ya jefar da bulalar. Cikin masifa ya dinga faɗin,

"Idan ke ba za ki iya da ita ni zan iya, a kan me za ta zo har cikin gidanmu ta yi masa iskanc...?"

"Halin Kandala na sani Habu, a kan Bintoto komai tana iya yi a garin nan, ga shi ka yi mata irin wannan dukan ban san da wane idon zan kalle ta ba."

Ta yi maganar tana kama hannun Bintoto tare da ƙoƙarin miƙar da ita tsaye tana komawa, saboda ta daku sosai ko tsayuwa ba ta iya yi, amma hakan bai sa ta yi kuka ba.

"Duk abin da zai faru ya faru! Kokawa fa na ga tana yi da ke, wallahi ko gobe ta sake zuwa cikin gidan nan ta yi mana rashin mutunci sai na ci ubanta. Kandala ta daɗe ba ta tsire ni ba."

Yana gama faɗar maganar ya fice gidan, Jamila da Innar su suka yi cirko-cirko suna kallon Bintoto da ke kwance cikin ƙasa tana tofar da yawu. Saboda ganin yadda jikinta ya yi ruɗu-ruɗu da shatin bulala. Da ƙyar Innar Jamila ta miƙar da ita tsaye tare da yafa mayafinta ta riƙe ta zuwa gida. Da niyyar ta ba Kangala haƙuri saboda sanin Habu ya taro musu faɗan da ba su iyawa. Hakan ya sa ta ga gara kawai ta saduda tun da wuri kafin abin ya rincaɓe.





A yo agaji da tuwon ƙasa.😅

Princess Dija ✍️

*SHAGALALLIYA!*

*HADIZA D/AUTA*

₦500, 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim. Shaidar biya 08022014771.



*LAMBA SHA BIYU.*

Tun a soron gidan Kandala Bintoto ta ƙwace daga riƙon da Innar Jamila ta yi mata, tare da duƙawa ƙasa ta damƙo ƙasa ta watsa musu a ido daga ita har Jamila. Ganin ta fasa ƙara Innarta kuma ta buga salati tana laluben bango, ita ma ta faɗi ƙasa tare da yage baki ta fasa wata uwar ƙara tana faɗin.

"Wayyo ni Allah wayyo ni kaina! Kandala! Kandala kina ina za a kashe ni?"

Sai ga Kandala ta faɗo soron kamar an jefo ta, zane yana kwancewa tana ƙoƙarin ɗaura shi, ɗankwali a hannunta ta isa inda Bintoton take ta kwatsa ihu iya ƙarfinta, jikinta yana rawa ta rungumo ta tana faɗin,

" Innahu min Sulaiman...ke..ke tsaya ki faɗa mini ke da wa?"

Kafin Bintoton ta rage kukan ta yi magana kamar yadda Kandalar ta buƙata; Innar Jamila da ta gama mutsuttsukar idanuwanta har sun yi ja, ta matso kusa da Kandala cikin marairaita tana faɗin,

"Haƙuri kawai za ki yi Kandala. Saboda duk abin da ya faru ita ce ta jawo. Amma dai don Allah da girman Manzon Raham....!

"Dakata Asabe! Daina zagaye-zagaye ki faɗa mini gaskiya me kika yi mata take irin wannan kukan tamkar wadda aka ɗora wa wuƙa a wuya?"

Cike da fargaba Innar Jamila ta karkace kai tana faɗin, "Wallahi billahillazi babu abin da na yi mata kin ji rantse irin rantsuwar ɗan Musulm...."

"Wallahi karya take yi Kandala! Ita da Jamila da Habu suka taru a kaina suna ta duka da buloli...dubi jikina ma ki ga shaida."

Ta ƙare maganar ta cire rigarta ta jefar tana nuna mata kalolin shatin da Habu ya yi mata, Kandala ta shiga salati tana tafa hannuwa idonta a kan Innar Jamila don ta kasa furta komai tsabar mamaki. Don ita kanta Asaben mamakin Bontoto ya sa ta shiga rabon ido tare da faɗin,

"Na rantse da Allah ƙarya kike yi Bintoto ni ko sau ɗaya ban sake ki ba, Jamila ma haka."

"Idan ƙarya nake yi ai ga shaida a jikin....Kandala wallahi idan kika ƙyale su ban yafe miki ba, saboda har da Baban Jamila aka dake ni. Ita ma Innarsu ta dake ni, Habu ma ya dake ni har da zagi na yana cewa ko ɗanbuzu ya dawo duniya sai ya dake shi ballantana ni ɗiyar Amadun Jaririy...."

"La'ilaha illallahu yau na ga bala'i ganin idona! Yanzu abin na Habu ya wuce dukan ki har ya kai kan ubana ɗanbuzu? To billahillazi yau ni ko su a garin nan! Sai na ga wanda ya ɗaure musu ƙugun haɗuwa su dake ki sannan har a zagar mini mafari."

Kandala tana ƙoƙarin miƙewa tsaye Innar Jamila ta yi wuff ta fice soron gidan tana jan hannun Jamila da ke bakin ƙofar gidan tana hawaye, don ƙasar da Bintoto ta watsa musu ta ƙi fita cikin idonta. Kandala kam tana miƙewa cikin gida ta nufa tana zazzaga masifa da zagin tushen Asabe da mijinta da 'ya'yanta tare da tsine musu albarka kala-kala. Hannun Bontoto ta ja bayan ta ba ta zane ta rufe jikinta suka fice gidan tamkar ta tashi sama.

Kulu ta bi su har bakin soron gidan cikin jimami, duk da wani gefen zuciyarta cike yake da jin daɗin an hora Bintoto. Bayan ta tabbatar sun tafi ta koma dariyar ƙeta ita kaɗai cikin gida tana yi tana buga ƙafa har da 'yar rawa alamun duniyar ta yi mata daɗi. Da ma can ta matsu su tafi birni su bar mata gidan ta sarara.

Kandala kam ba ta zame ko'ina ba sai 'yansandan garinsu suke zama. Don a cewarta ko wurin hakima ba za ta tsaya gudun a ce za a sasanta su ji bulus. Tiryan-tiryan Kandala ta yi wa 'yansandan bayanin cin zarafin da aka yi wa Bintoto. Ita ma da aka zo tambayar ta babu ko ɗar ta ce da 'yansandan Habu ya taɓa neman ya lalata ta, don ta ƙi amincewa ne ya ce duk ya kama ta sai halaka ta. Shi ne tana zuwa gidansu suka rufe ta da duka.

Sannan Kandala ta saka ta ɗage zanin da ta rufa mata tana nuna musu shatin bulolin da ke jikinta. Cikin ko-in-kula Bintoto ta zare zanen duka ta ajiye duk da 'yan ƙidan dangin da suka fara tsiro a jikinta. Ganin wani ɗansanda yana kallon ta ne ta yi hanzarin ɗaukar zanen ta rufa tana aika masa harara. Kafin ta zura kai daidai saiti da kunnen Kandala ta ce,

"Kin ga wani ɗansanda can yana kallon ƙirjina."

"To mene ne abin kallo a ƙirjin naki? Duk matan duniya ba su ishe su kallo ba sai k...?"

Bintoto ta yi hanzarin rufe mata baki don ba ta so ta buɗe zancen a fili ba. Jami'an ma ba su bi ta kan faɗan nata ba, sai haƙuri suka dinga ba ta cikin sigar wasa har ta sauko aka haɗa ta da wani ɗansandan da zai je ya zo da Habu, Jamila da iyayensu.

Zungui-zungui ɗansanda ya saka su Kandala a gaba har ƙofar gidan su Jamila, mutane suka dinga mamakin me gaminsu da 'yansanda. Cikin sa'a Habu zai shiga gidan, Bintoto ta yi tsalle tana nuna shi tana faɗin,

"Ga shi nan mugu, shi ne ya dake ni."

Caraf ɗansanda ya damƙe shi yana faɗin, "Ina sauran mutanen gidan?"

Sai da Habu ya yi masa wani kallo sannan ya ce, "Suna ciki."

"Inna, shiga ciki ki ce su fito."

Ɗansandan ya faɗa yana aika wa Habu wata muguwar harara. Habu ya shiga gyara zaman wuyan rigarsa yana cewa, "Ai ni na dake ta, mu tafi kawai ba sai an kira kowa b...."

"Wallahi ƙarya yake yi! Har da Babansu ya dake ni."

Bontoto ta yi hanzarin faɗa tana nuna shi da hannu tare da murguɗa masa baki da gungunin faɗin, "Allah Ya isa mugun banza."

Kandala kuwa tuni ta faɗa gidan tana kiran, "Asaben tana ina? Fito mu je, yau sai an fitar mana haƙƙinmu ni da Bontoto. Gobe ko wani kika ga ya buɗe baki zai furta sunan Ɗanbuzu za ki hana ballantana a zage shi gabanki. Idan ban da cin zalin irin naku Bontoto guda nawa ce da har za ku yi mata taron dangi ku dake ta. Don tsabar abin kunya wai har da Alin kanwa. To, yau duk sai kun gane ba kanwar lasa nake ba."

Haka ta dinga maganganu har suka fice ƙofar daga ita har Asaben da Jamila. Inda suka tarar da ƙofar gidan ya cika ana ta tambayar abin da ya faru. Babu kunya Bontoto ta dinga faɗa wa mutane Habu ne ya so lalata ta.

Haka suka rankaya zuwa wurin da 'yansandan suke tsayuwa a bakin titin garinsu. Tare da mutanen da suka rako su duk da korar da ake yi musu sai da wasu suka rufa musu baya. Sai da suka sake jin ba'asin Kandala da na Bintoto sannan suka ji na Habu da na Innar Jamila da Jamila. A nan suka fahimci Bontoto ba ta da gaskiya, kuma maganganun da ta faɗa duka sun saɓa abin da su Habu suka faɗa.

Shugaban 'yansandan da ke wurin ya yi musu sulhu, tare da yi wa Habu faɗa sosai bayan ya sa an yi masa buloli kamar yadda ya saki ƙwanji ya yi wa Bintoto. Saboda ya tabbatar musu da lalle shi ne ya dake ta, kuma shi kaɗai ba tare da kowa ba. Bugu da ƙari mahaifinsu ma ba ya garin, ya tafi birni kai kanwa kamar yadda ta zamo sana'arsa.

Amma hakan bai hana su caji naira dubu huɗu daga hannun Habu ba, don ita ma Kandala sai da ta miƙa musu dubu ɗaya tun a farkon zuwanta don su ji daɗin yi mata abin da take so. A haka suka dawo gida bayan an saka Habu ya bai wa Kandala da Bintoto haƙuri, tare da kashedin duk ya sake shiga sabgarta sai sun rufe shi gidan yarin birni.

Sai dai ko kaɗan hukuncin da suka yi bai yi wa Kangala daɗi ba, don a son ranta a rufe su duka har Alin kanwa idan ya dawo garin. Innar Jamila kan tun a kan hanya ta yi wa Jamila kashedin ta raba abotarta da Bintoto. Kuma idan ta sake jin an gan su tare sai na lahira ya fi ta jin daɗi.

Habu kam komai bai ce da kowa ba, har ya shige gida ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa. Saboda takaicin mari da tsinka jakar da aka yi masa bayan da gaskiyarsa. Sannan ya ci alwashin muddin Bontoto ta sake shiga gonarsa sai ya kusan kashe ta. Sai dai ya bar garin, amma ba zai lamunci iskancin kowa ba.

Kandala ma suna zuwa gidan ta ɗora ruwan zafi ta dinga gasa wa Bintoto jikinta tana ihun zafi ta yi a hankali. Haka mutane suka dinga zuwa yi wa Kandala jaje a kan abin da ya faru, don labari ya karaɗe ko'ina ana ta yamaɗiɗin Habu ya nemi Bintoto da lalata. Don ta ƙi amincewa ya lakaɗa mata mugun duka, shi ne dalilin da ya sa Kandala ta kira musu 'yansanda. Ana yi musu jajen a rai Bintoto tana faɗin,

'Baƙin mugu, ga shi nan ya ja wa kansa na ɓata masa suna a gari. Don ni ba Jamila ba ce ballantana na bari ya dake ni a banza.'

****

Bayan kwana biyar da faruwar rigimar Hari ta diro garin, cikin nasara ta sanar da Kandala ita ma an samu wurin aikinta, Kandala murna har tsakiyar kai. Nan take ta bar wa Kulu kula da akuyoyi da tumakin da take kiyo, tare da abin da kuɗin abin da za su ci kafin ta yi maramarin gida ta waiwayo wa garin. Sannan ta ɗauki ƙullin kayanta a kai na Bintoto a hannu suka rankaya bayan sun yi sallama da mutanen gari ana ta Allah Ya kiyaye.

Tafe suke a cikin motar da za ta kai su cikin babban birni, Bintoto da Kandala sai sharar barci suke yi har da minshari, irin minsharin da ya hana sauran mutanen da ke cikin motar sakewa, yayin da wasu ke tsaki masu earpiece kuma suka dinga maƙalawa a kunnuwansu. Saboda ƙarar minsharin da Kandala ke yi har da wani ƙugi, kuma tana dire shi za a ji ta sake jan wani numfashin sosai sannan ta sauke shi tare da wata haniniya mai kama da kukan doki, inda ƙarar sautinsa yake ta faɗin,

"Hiiiiiiii! Huhhhuhh!"

Kafin ta canza style ɗin minsharin ya koma faɗin, "Taaashii! Taaaashiii!"

Dole kallo da hankalin mutanen da ke cikin motar ya dawo kanta, domin wasu har da miƙewa tsaye suna leƙen fuskarta yadda yawun barcin ke biyo dogon haƙorinta mai tsini yana sauka saman zanin da ta yafa, har zuwa fuskar Bintoto da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login