Showing 30001 words to 33000 words out of 88489 words
Chapter 11 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx
a kansa fuskarta cike da tambayar abin da ya faru, tun kafin ta isa inda yake ta tsaya. Babu zato ita ma ta jefa ƙafarta saman sauran ayabar santsinta ya ja ta ta tafi luu, sai dai kafin ta faɗi ya tallafo ta tana salati ya miƙar da ita gefe ransa a ɓace, tana ƙoƙarin yin magana ya riga ta da cewa,
"Mahaukaciyar yarinyar can nake so ki fito mini da ita a inda ta ɓoye!"
Hamida ta waiga hanyar ƙofar ɗakin Bintoton tana cewa, "Tana ɗakinta bari na kira t..."
Ƙarar wayarsa ta katse masa maganar da ya yi niyyar yi, cikin sauri ta bar wurin yana magana. Babu jimawa ya yi sallama da mai kiran nasa wanda ya yi daidai da fitowar Hamida daga ɗakin Bintoton. Sai dai tun kafin ta ƙaraso ya bar wurin cikin sauri yana cewa,
"Ki haɗa mini jakata kafin na dawo wata tafiyar gaggawa ce ta kama n.."
Yana maganar yana tafiya har ya fice da sassarfa bai bi ta kan Bintoto ba, ballantana ya zaƙulo ta daga maɓoyar ya yi mata kalar hukuncin da zuciyarsa ta gama yankewa a kanta. Cikin sanyin jiki Hamida ta ɗauke ɓawon ta jefa kwandon shara, sannan ta nemo mopper ta goge wurin jikinta yana rawa ta rufe firij ɗin ta faɗa ɗakinsa da ɗan gudunta, cike da fargaban kada ya dawo ba ta gama aikin da ya saka ta ba.
Bintoto da ke bayan firij ɗin zafinsa ya gama ɗumama jikinta har ta yi gumi tsabar dunƙular da ta yi. Ganin babu kowa ta fito cikin sauri ta ƙara buɗe firij ɗin ta zura kanta ta zuƙo numfashi. Kukan Baby da ta ji ya sa ta yi hanzarin katse ayaba biyu, ta ɗauki lemu ɗaya da apple ta rungume a jikinta, kafin ta rufe firij ɗin da ƙafa ta bar wurin jikinta yana rawa ta koma ɗakinta. Zaman dirsham ta yi tana 'yan waƙe-waƙenta ta fara cire fatar lemu tana faɗin,
"Su dai har da lemunsu na 'yangayu ne. Ji fatarsa babu ƙarfi har jira take yi na jawo ta biyo ni."
Da santi kala-kala ta cinye ayabar har apple sannan ta koma lasar baki a ranta tana faɗin,
'Ko dai na koma na ƙaro wai!'
Zumbur ta miƙe cikin sauri ta fice ɗakin ta leƙo kanta tare da yin ƙasake domin ta tabbatar daga ina take jin sautin kukan Baby. Kamar haɗin baki ta jiyo muryar Maigidan da sautin Hamida suna magana a cikin falo. Baki ta turo tare da aika wa cikin falon harara sannan ta ja guntun tsaki ta koma ɗakint tana dube-dube, a ranta tana faɗin,
"Wannan gida kamar a aljanna wallahi. Ni da ma an bar ni gidan nan har sai na mutu a jingine gawata jikin wancan abin mai sanyi, ina so ya yi ta hura mini iska mai daɗi."
Da ire-iren waɗannan tunane-tunanen nata na shirme ta faɗa toilet. Cike da karambani ta kunna shower kamar yadda ta ga Hamida ta yi. Sai ta fara yin tsalle sannan ta shige tsakiyar ruwan suka yi ta sauka a kanta tana rawa da waƙa kala-kala tana juyi. Ta kwashi tsawon minti talatin a cikin ruwan har sai da muryarta ta fara shaƙewa ta shiga tari babu ƙaƙƙautawa. Sannan ta kashe shower cikin sauri ta fito da kayanta a jiƙe ta haye katifa ta dunƙule wuri ɗaya tana rawar sanyi.
Kafin ka ce me zazzafan zazzaɓi ya rufe ta ruf ta shiga kakkarwa, ita kaɗai a saman katifar tana juyi dafe da kanta da ke masifar ciwo tana kiran sunan Kandala a kan don Allah ta zo kanta cirewa zai yi.
Hamida kuwa, kukan da Baby take yi ya hana ta saurin shirya wa maigidan nata jakar tafiya, dokarsa ta Bintoto ba za ta sake ɗaukar ta ba ta katange mata son kai ta wurinta. Da dabara ta ba ta kayan wasa bayan ta haɗa mata madarar NAN da ake ba ta tana wasa da fidar. Cikin sa'a ko da ya dawo ta gama komai, tare suka fito da shi a falo yana ja mata kunne a kan sai ta saka ido sosai ga Bintoto. Gudun ta jawo musu wata musibar da za ta dame su tun da ta ji ta ga gani za ta iya zama da ita a yadda take. Dalilin da ya sa Bintoton ta ji tashin muryarsu a falo kenan kafin ya bar gidan.
Daga rakiyarsa ta nufo ɗakin Bintoto a lokacin ta ji motsin saukar ruwa toilet zuciyarta ta saƙa mata wanka take yi. Hakan ya sa ta koma hidimar baby bayan ta kwashe ɓawon ayaba da lemun da ta sha ta watsar a tsakar ɗakin, sannan ta faɗa kitchen tana yi musu girkin dare.
Misalin ƙarfe bakwai da rabi na dare Hamida ta shigo ɗakin ɗauke da plate ɗin abincinta, kuma da niyyar ta ji idan ta yi sallah. Saboda shirun da ta ji ba ta fito ba har lokacin, tunaninta ya ba ta barci ta yi bayan ta fito daga wankan. Sai dai halin da ta gan ta a ciki hankalinta ya tashi sosai, jikinta yana rawa ta ajiye plate ɗin ta yi kanta.
"Fatima, Fatima!"
Sunanta ta shiga kira ganin fuskarta har ta sauya idanuwanta sun yi ja bayan tarin da take yi har da atishaya. Ɗago ta ta yi cikin rawar jiki hucin zafin jikinta ya dake ta bakinta yana rawa ta ce,
"Ya salam! Daman ba ki da lafiya kuma shi ne ba ki sanar da ni ba?"
Bintoto ta ƙara langaɓe mata tare da fashewa da kuka tana kiran,
"Kandala, wayyo don Allah ki..kira mini Kandalat...wayyo kaina Kandala ki zo...zan..zan mu..t...."
Ta ƙare maganar jikinta yana ciccira. Hamida ta fice ɗakin cikin sauri ta haɗa mata allurori da dabara ta tsikara mata ɗaya tana ihu da kururuwa ta yi mata sauran ɗayar da ƙyar.
Sannan ta taimaka mata ta cire kayan jikinta ta sauya wasu, ta kai ta falo ta kwanta a kan doguwar kujera ganin ta jiƙe katifar gadon, ta yi mata rufa da bargo ruf. Kafin ta koma ɗakin ta saki fanka saboda katifar ta yi saurin bushewa. Kayanta kuma ta jefa cikin injinin wanki zuciyarta cike da tausayin Bintoton da halin da take ciki.
Princess Dija ✍️
19.
Tsakiyar dare Bintoto ta farka da wata mahaukaciyar yunwa, jikinta yana rawa ta nufi firij saboda mafarkin tana cin ayaba ta gama yi. Kanta tsaye ta fiddo ƙundun ayabar ta fara yago ta ɗaya bayan ɗaya tana ci, don a take ta ci fiye da ƙwara goma. Sannan ta koma kan apple da lemun kwali idan ta gutsura ta zuƙi ruwan lemun. Sai da ta ji cikinta zai fashe sannan ta tsaya tana nishi tare da shafa cikin tana faɗin,
"Wai Allahna! Ni kam har daɗi ya yi mini yawa!"
Ta miƙe dafe da ƙugu ta rufe firij ɗin ta bar kwalayen da ta shanye da ɓawon ayabar duka a wurin, sannan ta koma kan kujerar ta kwanta zuciyarta cike da tunanin kwaɗon garin kwakin Kandala da take ci a garinsu, sannan da irin daɗin da ta sha zuwanta gidan a cikin 'yan kwanaki. A ranta ta ce,
'Kandala sai dai ki yi haƙuri ki bar musu ni kawai, don wallahi ko za a kashe ni ba zan koma wurinki ba. Haka kawai ki yi mini asarar daɗin da nake sh....'
'Ƙululuuu..'
Cikinta ya yi wani ƙugi a lokaci ɗaya ya shiga murɗawa, aguje ta watsar da bargon a nan falon ta ruga da gudu zuwa ɗakinta, a haka ta faɗa toilet jikinta yana rawa ta haye saman masan gabaɗaya da ƙafafuwanta ta yi tsugunno a inda ake zama da ɗuwawu. Ta shiga kwararo zawo 'ziiiiii' tana rintse ido tare da nishi tana runtse ido, har ta samu juye rabin cikinta sannan ta sauko da dabara tana toshe hanci ganin aika-aikar da ta tafka. Domin gabaɗaya ta ɓata kwalbar har inda ake jingina baya.
Jikinta yana rawa ta kunna shower ta tara ɗuwawunta ta wanke kashin sannan ya miƙe ta yi wa ruwan hanya da hannunta suka koma kallon masan suna sauka samansa da niyyar wanke kashin ya wuce.
Caraf ta hango inda Hamida ta taɓa ruwa suka zo ta yi wurin ta danna makunnin ruwan sai ga ruwa yana ta fitowa har da tozo ya wuce da kashin gabaɗaya. Amma ta ƙi saki ta koma wasa da makunnin ruwan cike da nishaɗi idan ta kunna ta kashe, haka ta dinga yi sai da ta gaji don kanta ta fice ta haye katifa, tare da buɗe ƙafa ɗaya-ɗaya ta baje tana sauke numfashi har barci ya sake yib awon gaba da ita.
Da asuba da ƙyar Hamida ta tayar da ita barci tana gama harigidon sallar da ba ta san komai a kanta ba ta koma ta baje tana ta barci. Ko da Hamida ta gama shirin zuwa aiki ta shigo ɗakin tana sauri ta ce mata ta je kitchen abincinta yana can ta ci. Kuma kada ta je ko'ina babu jimawa za ta dawo, cike da jin daɗi Bintoto ta sauko gadon tana cewa,
"Ki bar mini yarinyar to sai mu zauna kafin ki dawo."
Hamida ta so hakan amma babu yadda ta iya dole ta zaɓi zuwa da ita a kan ta bar ta wani abu ya faru maigidan ya ga laifinta. Duk da tana sauri sai da ta nuna mata yadda za ta wanke bakinta da brush da makilin. Sannan ta fice gidan zuriyarta cike da fargaban kada ta yi mata muguwar ɓarnar da abin zai dame ta. Saboda ta ga aika-aikar da ta yi wa ayaba bayan ta sake yi wa wuri kaca-kaca sai da ta gyara. Amma ta ci burin idan ta dawo za su yi zama na musamman domin hana ta yin abin da zai jiƙa mata aiki ta bar ta da gyara.
Garin wanke baki sai da Bintoto ta yi wa makilin rabi, gabaɗaya ta gurje dasashinta ya fashe yana ta jini tsabar darza da bakin ya sha. Ba ta fahimci ta yi wauta ba sai da ta zo cin dafaffiyar indomie ta sha tarugu, tana kai wa bakinta loma ɗaya ta yi hanzarin dafe kai tare da zaro ido ta kwarma kuwa, a zabure ta miƙe cikin tashin hankali ta shiga zagayen falon dafe da kanta tana faɗin,
"Wayyo! Wayyo na boni bakina!"
Ta ɗauki lokaci yajin bai saki bakin ba, duk kwaɗayinta ruwan gora ta koma sha masu sanyi tana kurkure baki tana zubar da ruwan a inda duk ranta ya yi mata daɗi a cikin falon. Babu zato ta taka ƙafarta saman ruwan, santsin tayis ya ja ta ta faɗi ƙasa har kanta ya ƙwale, bakinta a yage ta fasa wata uwar ƙara dafe da kan ta fice falon da gudu tana waige, saboda ta gama tsorata don zuciyarta ta ba ta aljanu ne suka fisge mata ƙafa ta sha ƙasa.
Harabar gidan ta shiga shawagi tana leƙe-leƙe kasancewar babu maigadi a gidan saboda tsattsauran hali irin na maigidan. Domin kusan kowa a gidansu tsoron shi ake ji, Hajiyarsa kaɗai take taka masa birki ya bi ko da ba ya so. Amma ƙannensa ko gidan ba sa zuwa saboda masifar faɗansa da ba ya jiran sai an taɓa shi.
Bintoto kam garin leƙe-leƙenta ta hango wani filin shaƙatawa da ƙarfen lilo mai mazauni guda biyu. Cike da tsantsar farinciki ta isa wurin da gudu ta haye abin zaman bakinta a washe ta shiga wulwula kanta bayan ta riƙe igiyar lilon tana rufe ido idan ta yi gaba ta dawo baya.
Da abin ya yi mata daɗi ta yi dabarar hawa ta miƙe tsaye, a bisa gangancin da ta yi ƙafarta ɗaya ta zame, babu zato ta faɗo bakinta ya daki abin zaman ta fasa uwar ƙara saboda ta datse harshenta da haƙori jini ya ɓalle nan take.
Dafe da bakinta tana kuka da matsar ƙwalla ta shiga zubar da yawun jinin tana kai wa abin lilon harbi da ƙafa tare yi masa daƙuwa tana zagin sa. Sai da ta gaji don kanta ta bar wurin tana haɗiye yawu da ƙyar saboda gefen harshen nata da ya buge har ya kumbure.
Falo ta koma tana ƙoƙarin haɗa kallo amma ta kasa, duk da ta jona komai daidai amma ba ta iya kunna Tv ba. Haka ta yi ta wasa da remote idan ta latsa ta koma wayar ƙarya tana yatsina fuska da wata tafiya a tsakiyar falon. A ranta tana ji ina ma a ce gidanta ne kuma komai na gidan nata ne.
Haka ta kwashe tsawon awanni tana shiririta har zuwa lokacin da Hamida ta dawo ta tarar da ita tana sharar barci a ƙasan carpet bakinta a hangame yawu yana bin gefen bakin. Saboda ta yi maganin yunwar da ta addabe ta da kwalin hollandia mai sanyi. Kuma ta koma ma'ajiyar kayan shayi ta ci biredi ta kwaɓa madara da milo ta lashe. Bakinta dagaje da danƙon madara da milo, tana ta nishi saboda zogin da harshen yake yi mata har lokacin.
Hamida tsaye ta yi a kanta, zuciyarta a cunkushe saboda ganin yadda ta yi wa falon ɗaiɗaya kamar ba a taɓa gyara shi ba. Komai a watse bayan dauɗar da tayis ɗin ya yi wurare da dama sanadin ruwan da ta yi ta zubarwa, kuma ta dinga bi ta kai da ƙafafuwanta. Saboda ko yawon da ta yi cikin gidan duka babu takalmi a ƙafarta. Nan take ran Hamida ya ɓaci babu zato ta kai wa Bintoto harbi da ƙafa cikin fushi tare da faɗin,
"Tashi ƙazamar banza!"
A zabure ta tashi tana waige-waige da murza idanuwa tana kallon Hamida fuskarta a kumbure ta ce,
"Me na yi miki kuma da za ki dake ni? Ko ba ki ga kwana nake yi ba?"
Hamida ta sunkuya ta ajiye Baby da ke ƙoƙarin kuka fuskarta a cure ta ce,
"Fice mini daga nan baƙar ƙazama kin wani hargitsa mini falo tamkar kafin na fita ban gyara shi ba. Ji..ji..yadda har ruwa kika zubar mini a cikin falo! To wallahi idan kika sake da kaina zan kore ki cikin gidan nan domin ba za ki saka mini ciwon zuciya ba."
Tana masifar faɗan tana gyaran falon Bintoto tana zaune idonta a kanta amma ko motsin kirki ba ta yi ba. Maimakon ta ba ta haƙuri ta koma aika mata harara idan ta juya baya. Sai da ta ga Baby tana ƙoƙarin sauka daga kan kujerar ta miƙe cikin sauri ta ɗauke ta. Kallon ta kawai Hamida ta yi tare da jan tsaki, saboda ta gama ɓata mata rai don ta tsani ƙazanta da ƙazamai. Sannan ga ta da ƙyanƙyami a komai nata sai ta nutsu da tsaftarsa take amfani da shi.
Sai dai dariyar da Baby take ƙyalƙyalawa a kan wasar da Bintoto take yi mata sosai ta rage mata zafin da ta cusa mata. Saboda hatta plate ɗin da ta zuba mata abin kari yana saman kujera ajiye ta ci kaɗan ta bar saura saboda bakin ya ƙi ba ta haɗin kai, ga kuma harshen da ta datse. Cike da jin daɗin ganin Baby ta saki jiki da ita ta ce,
"Ki bi a hankali kada ki sake yi mata rauni ki jawo mini shiga uku."
Bintoto ta ƙara riƙe ta gam tana yi mata wasa, a bisa gwaji ta fara saka mata hannu a baki tana janyewa da sauri tare da ɓoye hannun a jikinta Baby tana ɓangalar dariya. Da gangan ta sake saka mata yatsanta daidai lokacin da Hamida ta ja jakarta da ke kan kujera ta yi ɗaki. Saboda gajiyar da ta kwaso da aikin da ta yi daga dawowa ko zama ba ta yi ba, sosai take jin ƙyamar jikinta tana da buƙatar wankan gaggawa.
Baby tana dariya ta gatsa wa Bintoto cizo da ƙarfi har da runtse ido, Bintoto ta yi hanzarin faɗin,
"Wash Allah!"
Kafin ta koma yarfa hannun tare da wurga mata daƙuwa tana aika mata harara. Sai da ta ɗaga kanta ta hango Hamida ta shige ɗaki sannan ta jawo hannun Baby ta gatsa mata cizon da ya sa ta zabura tare da ƙwalla ƙara a lokaci ɗaya.
'Ni ma na rama ki ji inda da daɗi.'
Abin da ta faɗa kenan tana ƙwafa, ganin Hamida ta fito a firgice ya sa ta yi hanzarin ɗaukar ta tana jijjiga ta kamar gaske.
Da sauri ta karɓe ta tana tambayar abin da ta yi mata. Bintoto ta shiga rantsuwar ba ta yi mata komai ba idan kuma ta zaci ƙarya take yi ta tambayi Babyn ta ji. Ido kawai ta shiga zare mata tare da cure fuska saboda ganin shatin cizo a hannun Babyn. Don haƙorin Bintoton sun fito raɗau a kan fatarta wanda ko ba a faɗa ta tabbatar da cizon ta ne ta yi.
Cike da jin