Showing 69001 words to 72000 words out of 88489 words

Chapter 24 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2066

me ya faru da ke? Ki yi mana bayani."

Bintoto ta zame jikinta ta faɗi ƙasa tare da fashewa da wani sabon kuka tana kiran sunan Kandala da ƙara dunƙulewa ciki ƙasa. Hari da 'yan aikin Hajiya suka rirriƙe ta zuwa cikin gidan tana ta tirjiya alamun ba ta son shiga gidan suna shigar da ita ta ƙarfi.

Falo aka ajiye ta, Hajiya ta ce a kawo mata ruwa da abinci. Nan take aka cika mata gabanta da abinci har da su lemu kala-kala. Hakan ya sa duk yadda ta so nuna fushi da abincin dole ta haƙurƙure ta ja abincin tana ci tana kuka. Hari gefe ta ja tana kallon ta cike da takaici har ta gama cin abincin ta koma lasar hannu.



"Yanzu saboda Allah Bintoto ba za ki daina abubuwan da kike yi ba? Ƙiri-ƙiri kin ɗaga wa mutane hankali cikin dare kin hana kowa zama lafiya."

"Ai mutanen makarantar ne suka tsane ni. Kuma da zan shiga motar da ke kawo mu gida mai motar ya ce kada na shigar masa mota, idan na shiga sai ya ci ubana. Sannan kuma malamai suka yi ta duka na suna zagin Babana. Har da Kamdala ma wani malami mai ƙaton ciki sai da ya zaga. Kuma suka ce kada na sake zuwar musu makaranta tun da ni ba 'yar birni ba c...."

"Maƙaryaciyar banza! Shi malamin da kika yi wa rashin kunya har kika saka masa cinnaku a jiki har kin manta ba za ki faɗa waton? Wallahi ko ki daina halinki ko muguntarki ta zamo ajalinki baƙar munafuk...."

Zancen Aliyu kenan a lokacin da ya fito daga ɗakin Hajiya ya nufo falon, yana kai ƙarshen maganar ya kai mata shuri da ƙafa, kafin ya sauke mata dukan da ya yi niyyar kai wa ƙeyar kanta Hajiya ta dakatar da shi a fusace.

"Wai kai ba ka san a bi komai a hankali ba sai ka yi wa mutane hauka? A tunaninka hakan zai sa ta gyaru har ra daina abin da take yi?"

"Wallahi wannan yarinyar duka kawai ya dace da ita ba wata lallaɓawar da za a yi mata. Amma ni na tafi na bar ku da ita ku yi duk abin da kuka ga ya dace."

Ya fice yana maganar, jim kaɗan sai tashin motarsa aka jiyo alamun ya wuce ya bar su da ita. Shiru falon ya yi babu mai motsi sai Bintoto da ke rusar kuka. Sai da Hajiya ta ja numfashi sannan ta kira sunan da take kiran ta ta ce,

"Daina kukan, yanzu dai duk wata matsala ta zo ƙarshe. Tun da an gano ki kuma makarantar ma sun kore ki shikenan. Sai ki ci gaba da zaman gida tun da shi kike so ba abin da zai tallafi rayuwarki b...."

"A yi haƙuri Hajiya."

Hari ta tari zancenta ganin da gaske Bintoto ta gama ɓata mata rai. Hajiya ta yi wani murmushin takaici kafin ta ce, "Haƙuri ya ƙare Hari, ki tafi da ita gida, gudun wata matsala ta ƙara biyowa mu shiga tashin hankalin da ya fi wannan. Allah Ya gani na so rayuwarta ta inganta, amma hakan ba zai samu ba duk yadda na so kai zuciya nesa. Don yanzu da a ce ba a gan ta ba wane irin tashin hankali kike tsammanin za mu shiga? Kin san duk halin kakarta, komai za mu faɗa ba zai sa ta fahimce mu ba ballantana ta gano laifin na jikarta ne ba namu ba. Saboda haka ki je da ita gida, na fahimci Aliyu da abin da yake son na gane."

Jiki babu kuzari Hari ta shiga bai wa Hajiya haƙuri, sannan da godiya a kan ƙoƙarin da suka wajen ceto rayuwar Bintoto daga duhun ƙauyanci da rashin ɗa'a. Hajiya ta ce babu komai Allah Ya shirye ta, aka harhaɗa mata komatsanta suka bar gidan, misalin ƙarfe tara da rabi na dare.

Bintoto tana matsar ƙwalla suka isa unguwar su Hari. Ko da suka je suka tarar da Kandala tana zaune ta yi tagumi. Ganin Hari da Bintoto a lokacin gabanta ya ƙire ya faɗi, ta miƙe zumbur ta taryi gabansu ido tsakar ka ta ce,

"Wa nake gani kamar Bintoto?"

Princess Dija.

35.

Kukan da ta fashe da shi, tare da rugawa da gudu ta isa inda take zaune ta faɗa jikinta ta ruƙunƙume; hakan ya tabbatar mata da lalle ita ce ba gizon da ta saba yi mata ne a ido ba. Cike da tsantsar mamaki ta bi Hari da kallo a cikin hasken ƙwan lantarkin da ya haska ɗakin, ganin jakar kayan Bintoto a hannunta tana ƙoƙarin kai ta ƙuryar ɗakin ta ajiye. Kandala ta bi ta da tambayar ina ta haɗu da Bintoton kuma har da jakar kayanta. Amma takaici bai bari Hari ta yi magana ba, zama kawai ta yi tare da yin tagumi tana sauke ajiyar zuciya.

"Wai Hari lafiyarki kuwa, ina ta yi miki magana kin yi banza da ni?"

"Ki yi haƙuri Inna, ban san ta yadda zan yi miki bayani ba ne, sannan ban san ta ina zan fara b..."

"Ki fara ta tsakiyar kaina Hari! Don alamunki ya nuna akwai wani mummunan abu da ya faru ga Bintoto, wanda har kike ƙoƙarin ɓoye min...to billahillazi duk abin da ya same ta ba zan yi wa kowa kawaici ba, kuma ban san kara ba ballantana na gwada ta a kan duk wanda ya cutar mini da Bintot..."

"Inna!"

Hari ta kira sunanta cikin wani yanayi na rashin daɗi da fargaba, ganin yadda ta fara yi mata saukalen maganganu tun kafin ta ji abin da ke faruwa. Tana shafa kan Bintoton ta shiga dudduba jikinta domin tabbatar da babu wani abin da ya same ta. Jin sunanta da Harin ta kira, hakan ya sa ta ɗaga kanta tana kallon ta cikin wani irin yanayi, kafin ta sassauta murya ta ce,

"Ba wata Inna sai gaskiya Hari. Ki sanar da ni kawai na ji me ya samu Bintoto kuma daga ina kika gan ta? Saboda tun da kika saka ƙafa kika fita ba ki sanar da ni inda za ki je ba nake cikin fargaba da tunanin a wane hali Bintoton take. Sannan zuwanki da ita a cikin daren nan ya nuna akwai wani mummunan abu da ya faru a can gidan aikin nata, shi ya sa ba kya son buɗe baki ki sanar da ni saboda an gama cin zalinta."

Shiru Hari ta yi na ɗan lokaci kafin ta sake sauke wata ajiyar zuciya ta magantu cikin yanayin damuwa da ɓacin ran da ya bayyana a kan fuskarta.

"Inna, kin fi ni sanin halin Bintoto da rashin jin da take aikatawa kala-kala tun a can ƙauye har zuwa nan. To a yanzun ma wani sabon abu ne ta sake yi, da ma can ko rikicin da aka yi har yaron Hajiya ya kore ta daga gidansa; ni ce na roƙi alfarmar a yi haƙuri Hajiya ta zauna da ita a gidanta, amma a bisa sharaɗin duk ta aikata wani abin da bai dace ba za su sallame ta. To a wannan lokacin ma ta sake gwada halinta, saboda ba ta dawo gida kamar yadda ta saba yi ba, asali ma har cikin daren nan babu inda ba a je neman ta ba, sai da ƙyar aka gano ta a bakin wani masallac...."

"Dakata Hari! Kai-tsaye ki fito ki sanar da ni ɓata ta yi. Kuma hakan ya faru ne a sanadin sakacin da suke yi wa riƙon nata. Don haka ni da ma can ba son zaman nata wani wuri nake yi ba. Dawo mini da ita da kika yi a nan ya fi mini farinciki da watarana a sanar da ni mutuwarta a hannun sakarkarun mutane marasa tsoron Allah. To ta Allah ba tasu ba, yadda duk suke son su ga ta wulaƙanta a duniya Allah ba zai bari a tozarta marainiyar Allah ba."

Sai da ta ja numfashi ta ɗan tsahirta da maganar kafin ta ɗora da cewa,

Gidansu kuma ko ba su kore ta ba ni da kaina zan je na taho da ita, don ba aljanna ake rabo a cikin gidan ba ballantana a ce rabon lahirarmu yana hannunsu. Hakan da suka aikata ya yi daidai, amma ki sani duk abin da ya samu Bintoto na assha wallahi ba zan ja bakina na yi shiru ba don kawai suna da kuɗi. Dole ne na yi fito na fito da su saboda babu uban da nake tsoro a cikin s...."

"Inna! Don Allah ki san me kike faɗa, idan hankali ya gushe hankali yake nemo shi. Bintoto da kika gani duk abin da ya faru ita ce ta jawo komai. Lokacin da ba a gan ta ba Hajiya har kuka sai da ta yi saboda tashin hankal...."

"Ai dole ta shiga tashin hankali Hari, don ɗan mutum ba tamkar kiyashe ba ne. A ce tun safe har dare ba a ga yarinya ba kuma a ja baki a yi shiru ni ba za a iya faɗa mini na sani ba? Sannan idan sun damu da ita ai ba za ta ɓace ba, don tun da take hannuna ba ta taɓa wuni guda ba a san inda ta shiga b...."

"Daga makaranta fa ta wuce yawonta ba ta dawo gidan ba kamar yadda ya saba, saboda kawai ta yi wa malami laifi an hora ta, shi ne ta zaɓi ɗaga wa kowa hankali ta hanyar ƙin bin motar da ke kai dawo da ita gida. Bayan ita ta saka wa malami cinnaku a cikin riga suka yi ta cizon sa, a sanadin haka shugaban makarantar ya ba ta takardar sallama daga makarant...."

"Sallama? To ai tun da ba takardar barin duniya aka miƙa mata ba da sauƙi." Kandala ta faɗa tana juya kai tare da kwance ƙullin goron da ke haɓar zanenta ta gutsura. Tana ƙoƙarin mayar da goron ta ƙulle Bintoto ta fara sharar ƙwalla tana cewa,

"Wallahi Kandala haɗuwa suka yi daga malaman har 'yan makarantar suna ta duka na da buloli. Sannan suka saka ni shara da wankin bayi har da kamun kunne sai da na y.... yiiiii!"

Ta ƙare maganar cikin muryar kuka, kafin ta fasa wani sabon kuka mai sautin da ya ƙara tunzura Kandala. Cikin fusata ta ce,

"To to! Yanzu na ji yadda kan zancen yake, wato a makarantar ma sun dake ki? To ai da ma can su gidan aikin naki su suka ji za su iya saka ki makarantar, don babu wanda ya roƙe su. Kuma saboda kawai kin saka wa malami cinnaku za a taru a dake ki? Sai ka ce wadda ta ɗauko kunamu ko macizai ta saka masa a rigar, ai wannan zalunci ne da cin amana, don hakan da suka yi miki ba zai hana cinnaka yi wa malamin wani cizon ba, haka kawai a yanke miki irin wann ɗanyen hukuncin? To wallahi ba zan bar zancen nan ya tafi a banza ba! Sai na je da kaina har makarantar na rama miki duk rashin imanin da suka gwada a kank..."

"To ai ni ban san ta inda ake bi a je makarantar ba. Sannan malamin makarantar mugu ne kamar ɗan Hajiya. Kada ki je don yana iya sa 'yansanda su kama mu a banza."

Bintoto ta faɗa tana ɓata fuska ta tashi daga kan cinyar Kandalar tana goge hawaye. Wani kalar kallo Kandala ta bi ta da shi a lalace kafin Bintoton ta gyara zamanta ta sake cewa,

"Ni babu abin da ya fi ɓata mini rai kamar yadda shi ɗan gidan Hajiyar ya yi ta zagi na, bayan dukan da ya yi mini a cikin motarsa da gabanta da muka zo gidan. Kuma na rantse da Allah ba zan taɓa yafe musu ba dukan su tun da ni ba baiwar gidan uban kowa ba ce a faɗin duniya."

Tsaye Kandala ta nemi miƙewa jikinta yana rawa tana faɗin, "Ai wallahi ba zan bar zancen nan ya tafi a iska ba, dole ne na nuna musu ba su daki banza b...."

"Ki zauna ni dai, ina za ki je a cikin daren nan? Ni fa na faɗa miki babu yadda za a yi na gane inda Makarantar take."

Bintoto ta tambaye ta tana ɗaga kai daga zaunen tana kallon ta saboda ba ta son ta je ko'ina a daidai lokacin, Kandala tana gyara ɗaurin zaninta tana faɗin,

"Gidan tsohuwar banzar Hajiyar zan tafiya. Ai ba baiwa na kai ta yi musu aikatau ba, ke ma kina da gatanki."

"Inna!" Hari ta kira sunanta saboda jin abin da take shirin yi ganin ta ja mayafinta tana ƙoƙarin saka takalmi a ƙofara ɗaki.

"Ke ƙyale ni Hari! Don wallahi ko na je ban gane gidan ba idan na dawo sai na bi dare ina yi musu muguwar addu'a."

"To, ki yi haƙuri ki dawo ki zauna don Allah Inna. Abin nan fa duk bai kai yadda kike kallon sa ba. Aiki dai ne sun ce ba sa so shikenan zance ya ƙare, kuma idan kin fahimci Bintoto da kyau duk abubuwan da ta faɗa an yi mata babu wanda yake gaskiya, ita ce ta tsara abin ta da kanta. Don ga shi ta nuna ba ta so ki tafi, saboda ta san ba ta da gaskiya. Kuma wallahi a yadda Bintoto ta ɓata wa Hajiya rai ɗanta yana iya sa 'yansanda su kama ki su kulle idan kika je yi wa mahaifiyarsa maganganu. Kuma kin ga mu za mu shiga uku, 'yan kuɗin da muke ƙoƙarin tarawa a yi hidimar auren Bintoton su ƙare a wurin 'yansanda."

"Yi mini shiru Hari! Ko lahira za a kai ni ba zan bari a cutar da rayuwar Bintoto ba ina kallo ba!"

Da ƙyar da dabara Hari ta shawo kan Kandala ta dawo cikin ɗakin ta zauna tana haki da ajiyar zuciya, tamkar wadda ta sha gudu tsabar fitinar da ke ranta da faɗar maganganun da duk suka fito daga bakinta. A ƙoƙarinta na son sauke fushin da ke ranta, haka ta yi ta zagin Hajiya, Aliyu da malaman makaranta tare da duk wanda Bintoto ta ce ya dake ta. Tsinuwa kuwa sun sha ta fi cikon kwando. Daren ranar haka Kandala ta cinye rabin sa tana masifa tare da gutsurar goro jefi-jefi tana Allah-wadai da masu kuɗin garin duka. Don tun tana yi Hari tana sauraron ta tana ba ta haƙuri, har ta yi barci ta bar ta tsakiyar shimfiɗarta tana ta mita, Bintoto kam sai faman zuba minshari take yi hankalinta a kwance tana ɗora mata ƙafafuwa duk inda ta ga dama.

Washegari ko wurin aikinta ƙin zuwa ta yi. Ko da Hajiya mai abinci ta kira Hari tana tambayar lafiya ba ta zo ba, cewa ta yi a ce mata zazzaɓi mai zafi ne ya kafce ta, cikin jimami ta yi mata addu'ar samun sauƙi suka yi sallama. Bayan sun karya a gaggauce Hari ta yi wanka ta bar su gidan, saboda ta gaji da mitar Kandala wadda tun asubar farin tana farkawa da zancen ta tashi a bakinta.

Ganin ta fice ta bar musu gidan su kaɗai, Bintoto ta fito ƙofar gida ta zauna tana kallon mutanen da ke ta wucewa. Sannan a gefe ɗaya tana ƙare wa gidanen unguwar kallo tana yatsine-yatsinen fuska tana tsaki. A ranta tana ta faɗin,

'Baƙar unguwa, gabaɗaya talauci ya yi musu mugun kamu. Duk gidajensu tsofaffi babu mai gida sabo, ni yaushe zan iya zama a nan duk ruwan kwatami sun cika musu hanyoyi, mutum yana kallo amai yana shirin zuwa, uhumm Allah Ya ba su kuɗi su huta da warin talauci. Ni dai Allah Ya sa na fita daban, don na samu miji mai kuɗi wanda zai kai ni ƙasar waje mu yi yawo idan na dawo Makka.'

Can ta hango wani yaro yana ta sauri riƙe da leda a hannunsa, tana kallon sa har ya zo daidai ƙofar gidan zai wuce. Cikin sauri ta miƙe tana faɗin,

"Kai zo nan!"

Yaron ya yi mata wani kallo kafin ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya ce da ita komai ba. A ƙufule ta sha gabansa tana faɗin,

"Don ubanka kana ji ina magana za ka yi mini banza?"

Hannu ya nuna mata yana faɗin, "Ki bari da ni."

Ta buge hannun cikin sauri tana faɗin, "An ƙi a bari da kai, mu ga ledar mene ne a ciki?"

Yana kallon ledar ya ce, "Ƙosai ne na sayo. Ko akwai kuɗinki a ciki na ba ki kasonki?"

"Kan uba! Ni za ka yi wa habaici?"

"Ai ba habaici ba ne baƙar magana ce."

Ya amsa mata kansa a tsaye alamun shi ma jan wuya ne.

"To wallahi yau sai na ga uban da zai hana na dake k..."

Ta cakumo gaban rigarsa tare da ƙoƙarin ƙwace ledar da hannu ɗaya, shi ma yana ƙoƙarin hana ta ta hanyar buge hannun nata da ƙafa. Haushin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login