Showing 54001 words to 57000 words out of 88489 words

Chapter 19 - SHAGALALLIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY Hadiza D Auta.docx

18 Dec 2025

2078

kuma wallahi duk abin da ya biyo bayan hakan babu ruwana. Ki san yadda za ki yi da su kun fi kusa, tun da ke kika ɗaure wa wannan shashashar ƙugu tana ci gaba da iskanci son ranta."

"Wallahi na ɗauka za ta gyaru mu samu lada."

"To ai ta gyarun har kin samu ladar."

Hamida naushin maganar ranta ya ƙara matuƙar ɓaci, har da guntuwar ƙwalla maƙale a cikin idonta tsabar jin takaici da haushin kunyata ta da Bintoto ta yi. Haka suka isa gidan su Hajiya kowanensu zuciya babu daɗi, suna shiga harabar gidan, Bintoto ta ɗaga kai tana so ta gano da gaske wurin 'yansandan ne ya kawo ta. Fahimtar gidan Hajiya ne ta yi hanzarin hararar ƙeyarsa a ranta tana faɗin,

'Yo idan gidan nan ne ai ni na ma fi son shi a kan baƙin gidansu. Ba su da aiki kullum sai masifa yen yen yen.'

Tun kafin motar ta gama daidaitawa ya isa inda ya yi niyyar tsayawa ta ɓalle murfi tana ƙoƙarin ficewa, a fusace ya zuro hannu ta baya ya kai wa kanta duka har sai da ta daki gefen motar yana faɗin,

"Ƙatuwar wawuya! Sai kin kashe kanki garin iskancinki mai lasisi."

Bintoto ta ƙame wuri ɗaya ta kasa gaba ta kasa baya, har ya fito daga motar ya ƙara kai wa kanta bugu ta kauce, bayan ya tura ta gaba yana cewa,

"Wannan shegen kan naki watarana sai na fasa shi idan ba ki yi hankali ba. Kai sai ka ce ƙaton mangwaro babu komai a ciki sai shirme da hauka. Dalla kwashi jakar tsommakaranki mu je ciki a yi ta ƙare da Hajiya, don wallahi kin gama zama gidana daga yau sai ƙauyenku."

Sai da ya saka ta gaba sannan suka rufa mata baya har cikin gidan bai daina sambatun faɗan da yake yi ba. Ai kuwa tana jefa ƙafarta cikin falon gidan ta fashe da kuka, Hajiya ta fara salati a ruɗe tana tambayar wa ya taɓa mata uwa, kuma me ke faruwa ta gan ta da jaka.

Aliyu zama ya yi babu jinkiri ya juye wa Hajiya duk abubuwan da take aikatawa, kafin Hamida ta ɗora da faɗar abubuwan da bai sani ba da wanda ya mance. Salati Hajiya ta dinga yi tana tafa hannu, musamman da ta ji labarin ta yi wa yarinyar mutane allura.

Shiru ta yi tsawon mintuna tana jimamin abin kafin ta kalli Bintoto ta ce,

"Mai sunan uwata me ya sa kika yi wannan shirmen? Yanzu idan ƙafar yarinyar mutane ta lalace ya za ki yi idan an kai ki hukuma? Kakarki tana fama da kanta ki jawo mata fitina, to gaskiya ko ni ba na goyon bayanki a nan. Ba ki kyauta ba, sannan kuma ba ki yi wa uwarɗakinki adalci ba. Tana ƙoƙarin ganin ta gyara ki amma ke kin hana wa kowa zaman lafiya a gidan da maƙota. To yanzu zan kira Hari na sanar da ita komai, su zo su tafi da ke tun da haka kike so sai ki koma gid...."

"Don Allah a yi mini haƙuri wallahi ba zan sake b..."

"Ke ɗin ce ba za ki sake ba? Ai ko kashe ki aka yi kika dawo duniya sai kin tafka tsiya."

Aliyu ya faɗa yana miƙewa tsaye cikin fushi ya ce, "Zo mu tafi Maman Baby."

Hamida ta miƙe da Baby a hannunta suna yi wa Hajiya sallama, kanta a kan waya tana ta ƙoƙarin nemo lambar Hari. Suka fice Bintoto ta raka bayansu da harara cikin haɗe rai ganin da gaske tafiya za su yi su bar ta. Sai a lokacin ta ji takaicin kanta da abin da ta aikata. Ganin da gaske shikenan ta rabu da gidan jin daɗi za a mayar da ita ƙauyensu ba tare da ta yi kuɗin da take buri ba. Asali ma babu wani mai kuɗin da ya gan ta ya ce yana son ta, talakan ma tun da ya zo sau ɗaya bai dawo ba.

Bayan Hajiya ta gama waya da Hari ta ce da 'yan aikinta su kawo wa Bintoto abinci. Tana ci tana gunguni saboda duk abin da Hajiya ta tattauna da Hari tana ji.

Don Hari ta so ko ita Hajiyar ta riƙe ta idan akwai abin da za ta dinga yi mata ko da wanke-wanke ne. Amma Hajiya ta nuna ita sam ba za ta iya zama da ita ba gudun ta jawo mata wata fitinar kamar yadda ta yi wa su Hamida.

Marece sakaliya Hari ta iso gidan ita kaɗai, saboda ba ta faɗa wa Kandala abin da ke faruwa ba, don ko da Hajiyar ta kira ba ta nan tana wurin aikinta. Da niyyar sai idan ta dawo ta sanar da ita duk abin da ya faru, Bontoto tana ganin Harin ta fashe da kuka tana faɗin,

"Wallahi Inna na yi alƙawarin duk abin da nake yi zan daina. Don Allah ki ce ta matsa wa ɗanta na koma gidans...."

"A'a kam ba kya son zama gidan, da kina so da ba ki yi wa 'yar mutane allura b....ni sake ni!"

Ta ƙare maganar cikin ɗaga murya saboda jin haushin an kore ta a lokacin da take son ganin ta shiryu. Hari ta saka Hajiya gaba da magiya tare da ban haƙuri har ta samu ta shawo kanta, a kan Bintoto za ta zauna gidan, amma a bisa sharaɗin duk ranar da ta yi musu rashin hankali a bakin aikinta. Hari ta aminta da sharaɗin, sannan ta ja Bintoto bayan ɗakunan gidan ta dinga zuba mata faɗa, har da ranƙwashi da jan kunne kala-kala, sai da ta tabbatar ta yi laushi sannan ta ja hannunta suka koma ciki. Inda a gaban Harin Bintoto ta ƙara bai wa Hajiya haƙuri tare da ɗaukar alƙawarin ba za ta sake kwatanta laifin da take yi ba.

A nan Hari ta yi sallama da su ta tafi, Bintoto kuma aka ce ta kai jakar kayanta ɗakin 'yan aikin gidan. Bayan tafiyar Harin ma Hajiya gaba ta saka ta tana ta yi mata faɗa a kan ta bar abubuwan da take yi. Sannan makarantar da aka ce an saka ta za ta ci gaba da zuwa. Tun da an kashe kuɗi ba za a bari su bi iska ba. Bintoto ta yi mata alƙawarin za ta tsaya ta yi karatu.

Daga haka Hajiya ta sauko daga fushin da take yi da ita. Don da ma can takaicin abin da ta ji ta aikata ne ya sa ta nemi rabuwa da mai sunan uwarta, wadda ba ta haɗa ta da kowa a duniya ba. Safiyar Litinin Bintoto ta yi shirin makaranta tun da asuba, ko da bakwai ta yi kowa ya gan ta da shirinta har da jakar makarantarta a baya. Hajiya ta sa direbanta ya kai ta har makarantar, sannan aka yi mata bayanin idan an tashi ta jira Bus ɗin makarantar za ta kawo ta har bakin titin unguwar sai ta ƙaraso. Idan ma ba za ta gane ba za a sa wani ya tsaya wurin da an sauke ta a nuna mata hanyar dawowa gida.

Cikin zumuɗi ta tafi, saboda farin cikin an kai ta cikin motar masu kuɗi. Ko da aka sauke ta tana wani bouncing da hurar hanci don a gano da gaske ita ɗiyar masu kuɗi ce. Kai-tsaye wurin assembly ta nufa, inda ta ga ɗalibai suna ta zuwa suna layi, kasancewar ba ta san kan komai ba ta shige layin da take ra'ayi. Sai dai tana shiga ake ture ta a ce ba layin ajinsu ba ne. Kafin ka ce me a gaban wurin ta yi kokawa da mutum ya kai uku, a ƙarshe wata prefect ta hango ta ta saka ta duƙawa. Ganin ta kamar girmansu guda ta ƙi yin abin da ta ce ta yi, yarinyar ta ɗaga bulala tana zabga wa ƙafafuwan Bintoto. Ita ma ta taƙarƙare ta cakumo hijabinta tana ƙoƙarin kai mata naushi.

Yan'uwanta prefects suka taru a kan Bintoto suna ta jibga, da wani malami ya gan su ya tambayi dalili suka sanar da shi. Da bayanin da Bintoton ta yi masa ne ya gano ba ta san komai a kan tsarin Makarantar ba. Shi ne ya yi mata bayanin komai, sannan ya ba su haƙuri suka ƙyale ta. Amma sun ci alwashin duk ta sake shiga gonarsu sai sun sauya mata fuska.

Lokacin da aka gama assembly aka shiga aji, a nan ma sai da ta yi faɗa da wata da ke yi mata dariya tana cewa babba cikin 'yan yara. Hakan ya sa ko da ta shiga ajinsu kowa ba ta yi wa magana ba. Su ma saboda an hana su tsokanarta babu wanda ya bi ta kanta. Sai da aka tashi break ta ga yadda kowa yake fito da abinci, sannan ita ma ta fito da kular da Hajiya ta saka mata a kwando.

Tana yauƙi take cin dankalin turawan da ya sha jar suya har da wainar ƙwai gefe. Tas ta cinye ta sha ruwa, kuma babu wanda ta yi wa bisimillah. Amma ita idonta yana kan abincin yaran mutane tana dogon wuya. Idan aka taya mata jiki yana rawa take zuwa ta jefa hannu, ko da mai abinci za ta ankara har ta tashi da komai ta bar yara da mamaki. Haka ta dinga yi kujera-kujera tana leƙen me suke ci. Wasu su ba ta wasu kuma su hana ta, ranta fes tana shafa cikinta ta tabbatar da ba ƙaramin ƙoshi ta yi da abincin yaran mutane ba.

Lokacin da aka tashi Bus ta ajiye ta bakin titin su Hajiya. tana tsaka da wara ido ta hango ɗan saurayinta mai jiran dawowarta tsawon lokaci. Tana ƙoƙarin bin wata hanya ta ji magana a bayanta ana faɗin,

"Kada ki je ki ɓata, zo na nuna miki gidan."

Da mamaki ta bi shi da kallo kafin ta ce,

"Amma dai kai aljani ne ba mutum ba."

Yana 'yar dariya ya ce, "Me ya sa na tashi daga mutum na koma aljani?"

"Saboda ban san wa ke faɗa maka inda nake ba sai dai na gan ka kawai."

"To daina mamaki, tun jiya da kika yi laifi aka dawo da ke nan unguwar na biyo ki na ga gidan."

"Kammmm!"

Ta faɗa tare da riƙe ƙugu ta dakata daga tafiyar da take yi. Tsabar mamaki da jin haushin wai har ya san ta yi laifi an koro ta. Hakan ya sa ta haɗe fuska tana nuna shi da hannu ta ce,

"Wai ba na ce kada ka sake yi mini magana ba? Sau nawa zan faɗa maka ban san ka ba? Kai idan ma na san ka ni ba na son talaka yana yi mini magana, haka kawai mutum ya goga mini warin talauci a banza ya sa tsiya ta shafe ni ina cikin arziƙina."

Murmushi a kan fuskarsa ya ce, "Yanzu dai ban da wani laifi a wurin ki sai zamana talaka?"

"E, ka je ka yi kuɗi kamar yadda na yi ka gani idan ban dinga kula ka ba."

"Haka kika ce?"

"E, haka na faɗa ka je ka yi kuɗin ka gani. A duniyar nan me ake yi da talauci? Ai tsananina da shi kallo daga nesa ina yi masa bye-bye."

"Zance ya ƙare, idan na yi kuɗi za ki aure ni?"

Sai da ta yi masa kallon sama da ƙasa sannan ta ce, "In dai kana da kuɗi ko ba na son ka zan aure ka. Amma fa sai idan kana ba ni kuɗin ina sakawa cikin asusuna zan tabbatar da kai mai kuɗi ne."

"To, ga gidan can ki ƙarasa, in sha Allahu daga gobe zan fara zama mai kuɗi."

Ya juya cikin wani yanayi a kan fuskarsa, ita ma ta yi gaba tana hura hanci ta ce, "To ai ka yi kuɗin mu gani tun da kuɗin banza ne."

Ta tafi tana dariya, har da waigawa tana kallon bayansa tana ci gaba da dariya ta ce, "Baƙin aljani, da haka zan kore ka kada ka shafa mini tsiya a banza."

Ba giri-girin ba dai....😃

Princess Dija.

30.

Da wani kalar nishaɗi ta shiga gidan, don tun daga nesa ta gane gidan ne, ta shige tana waige-waige tana cewa,

"Bari dai na ƙara kallon unguwar da kyau kada na ɓace watarana. Ba don wancan mayen ba da yau na ɓace a cikin birnin nan 'yan yankan kai su sha jinina a banza. Tun da Hajiya ta yi mini ƙarya ba ta turo kowa da zai nuna mini hanyar ba."

Tana tafiya tana maganganu har ta shige cikin gidan, kamar almara ta hango Kandala da Hari cikin falon suna hira da Hajiya. Wani uban tsalle ta daka tare da ihun kiran sunan Kandala ta yi kanta ta faɗa a sukwane, tsabar jin daɗin ganin su. Baki har kunne ta dinga matso fatar kumatun Kandala tana faɗin,

"Kandala kun zo gidan amma ko ku ce mini ga ku nan na yi sauri."

Hajiya ta taryi zancen tana cewa, "Ai duka laifin nawa ne uwata, shaf na manta da zancen saka wani ya taro ki. Yanzun nan muke maganar ma, ina da niyyar na tura wani ya zo da ke sai ga ki kin dawo. Amma tun da kin gane hanyar ai shikenan gobe ba sai wani ya yi miki jagora ba."

Bintoto ta ɓata fuska tana wasa da gefen hijabinta tana cewa, "Bayan har na tashi ɓacewa."

Gabaɗaya suka saka dariya. Kandala sai kallon Bintoto take yi tana jin daɗi a ranta. Ganin yadda ta sauya a lokaci ɗaya wani girma ya taso mata na ban mamaki. Ga haske da ta yi jikinta ya mulmule alamun zaman birnin ya karɓe ta. Da ma can ba ta da muni idan aka cire baƙin da Allah ya yi wa fatarta fenti da shi. Amma kuma baƙin mai kyau ga kyakkyawar ƙira irin ta ɗiya mata. Matsalarta ɗaya shirme da wautar da suka yi wa kanta yawa kuma suka zarta shekarun haihuwarta a duniya.

Hajiya ta ce ta tashi ta cire kayan makarantar ta ci abinci ta dawo. Ta miƙe ba don ranta ya so ba tana waigen Kandala tana dariyar jin daɗi har ta shige. Suka bi ta da dariya ganin yadda take yi alamun ba ƙaramin farinciki take ciki ba, saboda ganin ba zatan da ta yi musu kamar almara. Don tun ƙarfe huɗu suke gidan, sun zo bai wa su Hajiyar haƙuri a kan abubuwan da ta aikata.

Saboda Kandala ba ƙaramar kaɗuwa ta yi ba a lokacin da Hari ta rattaba mata duk abin da ya faru. Har ta fara faɗin a dawo mata da Bintoto su koma ƙauyensu tun da zaman birnin bai karɓe su ba. Faɗa ta dinga yi sosai a kan don me su Hamida za su kori Bintoto a gidansu, ba tare da sun yi mata uzuri har sai ta sake ba. Da ƙyar Hari ta fahimtar da ita illa da haɗarin da ke cikin yi wa yarinyar mutane allura ba tare da ta san ƙa'ida da dokokinta ba. A nan Kandala ta shiga tsoro da fargaban kada ƙafar yarinyar mutane ta samu matsala a haɗa su da hukuma, kamar yadda Hari ta tsorotar da ita ganin duk laifukan Bintoto da ta lissafa ba su sa ta gano ta yi kuskure ko wani babban laifi ba.

Bintoto bayan ta cire kayan da abincin ta dawo falon ta zauna saman cinyar Kandala kamar wata 'yar yarinya tana cin abincin, har sai da ta ture ta tana faɗin,

"Saukar mini ƙafa ja'ira! Tun da ba ki jin tausayin tumurmusa ni kamar kin samu jaka."

"Daga ma kin samu na zauna saman ƙasusuwa, cinyar taki ma da ko naman kirki babu."

Dundu Kandala ta sakar mata a baya tare da aika mata daƙuwa tana faɗin, "Rodi ne kika hau ba ƙashi ba, 'yar rainin hankali. Shegen son jiki ko mage albarka."

Ta daina cin abincin tana kumbura fuska tare da ƙamewa wuri ɗaya alamun ta yi fushi. Hajiya ce ta yi saurin faɗin, "Yi haƙuri uwata, ai nan gaba kaɗan 'ya'yanki ne za su hau cinyar har su yi mata fitsari a jiki."

Babu shiri Bintoto ta ƙyalƙyale da dariya tana faɗin, "Wallahi har kashi sai na sa an yi mata a cikin baki."

Gabaɗaya suka saka dariya, daga haka ta saki jikinta tana cin abincin suna ta hira. Har ƙarfe shida da rabi ta buga Hari ta ce su tafi gida kada magriba ta yi musu a hanya.

Bintoto ta riƙe hannun Kandala tana matsar ƙwalla a kan cewa ita sai ta bi su. Hajiya da Hari suka dinga ba ta haƙuri a kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login