Showing 1 words to 3000 words out of 107295 words
Chapter 1 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
Compiled By Golden Pen Writer's Association.
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene One_
~*Page 1*~
A kwance take, sanye cikin English wears na riga da skirt ja da rantsin fari a jikin shi, kayan sun amshi yanayin jikin ta kasancewan ta ba mai jiki sosai ba, sannan sun zauna ɗas a jikin ta tare da baiyana k'uruciyan ta. *HUNAYDA* Kenan, ƴar matashiyar da baza ta gaza shekara goma sha bak'wai ba (17years).
Farin earpiece ne a kunnen ta, a lokaci ɗaya kuma hankalin ta na kan wayan ta k'irar Tecno Camon 12. Kana kallon ta zaka fahimci hankalin ta gaba ɗaya na kan wayan ne, domin ko k'ifta idon ta bata yi, jifa-jifa takan yi murmushi, a lokaci ɗaya kuma takan lumshe idon ta tare da runtse su na ƴan wasu dak'ik'u sannan ta buɗe tare da sake mai da hankalin ta kan screen ɗin wayan.
Daga kitchen Hajiya Hauwa ce mahaifiyar ta, wanda suke kira da *Ammi*, take ta k'ok'arin haɗa musu abincin dare, inda yar autan nata *Hajna* da baza ta wuce shekara goma ba (10years) take taya ta wasu aiyukan.
Ganin aiyukan suna neman kwaɓe mata, yasa ta ɗaga murya tare da fara kiran sunan ta.
"*Hunayda!* *Hunayda!!* *Hunayda!!!*"
Amma babu alaman motsin mutum ballantana tasa ran anji kiran har a amsa mata. Maida kallon ta kan Hajna da take k'ok'arin gyara kayan miya tayi, a sanyaye ta kira sunan ta;
"Hajna!".
"Na'am Ammi".
Ta amsa tare da dakatawa daga abin da take.
"Je ki duba min Aunty ki, ko tana banɗaki ne".
"Tohm!".
Ta amsa tare da tsame hannun ta, ta nufi ɗakin da sallama, ta tura k'ofan ta shiga, inda ta same ta kwance ruf da ciki, ta kafe idon ta akan waya. Ganin bata san da shigowan ta ba yasa ta k'arasawa tare da ɗan girgiza ta, a lokaci ɗaya kuma take sanar da ita sak'on Ammi na kiranta.
Cikin jin haushin katse ta da tayi ga karatun littafin da take ta watsa mata harara.
"Sai kije ai ina zuwa, kin sake baki kina kallo na, ko baki taɓa gani na bane?!".
"Um um".
Ta amsa tana ficewa daga ɗakin cikin rashin jin daɗin canjawan ɗabi'un ƴar uwar tata, domin da sam bata ko mata tsawa bare k'yaranta. A sanyaye ta k'arasa madafan inda ta sanar da Ammi wai tana zuwa.
Kallon ta take tare da yin nazarin sauyawan ta.
"Dama idon ta biyu?".
Ta jefo mata tambaya.
"Eh". Ta amsa. "Toh me take yi, duk wannan ihun kiran ta da nake?".
"Wayan tane dai na gani a hunnun ta, sai earpiece dake kunnen ta".
"Shikenan, je ki kwashe kayan gugan da Magaji ya kawo ki jera min a wardrobe, idan tazo ta k'arasa markaɗen".
"Toh Ammi".
Ta faɗa cike da ladabi tare da shigewa cikin hanzarin domin aiwatar da umarnin mahaifiyar nata.
A can ɗaki kuwa Hunayda sai da ta k'washe tsawon mintuna biyar sannan ta ajiye wayan tare da fitowa cikin rashin walwala.
"Gani Ammi".
Ta faɗa a dai-dai lokacin da ta k'arasa k'ofan kitchen ɗin.
Kallo ɗaya ta mata taji ranta bai mata daɗi ba, domin waƴannan sabbin ɗabi'un da take gani tattare da ita sun fara isan ta, wanda tana iya k'ok'arin ta amma ta rasa gane kanta da inda ta dosa.
Cikin takaici ta dube ta.
"yanzu Hunayda Fisabilillah kina k'wance a ɗaki tun safe baki da wani aiki sai latse-latse a waya! Tunda Abban ku ya sai miki wayan nan kika haɗu da Sahabat kuka ɗinke, ɗabi'un ki sun canja gaba ɗaya! Idan tazo baku da aiki sai ku kulle kanku a ɗaki kuna labaran Social Media, mussaman WhatsApp da Littatafan Hausa, ni ban san irin wannan zamani naku ba Hunayda! Idan karance-karancen littattafai ne ai nayi shi, kuma ban daina ba har sai da na haife ki hidiman raino ya sani watsi da karatun littafi, wanda har abada bazan iya biyan wayannan marubuta ba, domin sun taka rawar gani sosai a cikin rayuwa ta, na koyi darasi masu tarin yawa wanda iyayena basu koyar dani ba, kama daga yanda zan k'yautata ma miji na tare da sauke duk wani hakkin shi daya rataya a wuyana, zamantakewa na da mak'ota, tsakani na da dangin miji na, yanda zan k'yauta ta ma iyayena domin samun kyakkyawan k'arshe, da ma sauran abubuwan da dama na rayuwa!".
Daɗa zunɓuro bakin ta tayi, tunda ta fara magana inda gaba ɗaya sauraron ta take amma hankalin ta yana can kan wayan ta da ta bari.
"Ki shige ki ɗauki kayan miyan can ki ida gyara su, sannan ki markaɗe su. Idan kin gama ki asa bisa wuta sannan ki fidda kayan salad ki fara yanka su. Bari na watsa ruwa ina zuwa".
Bata jira cewar ta ba ta fice daga kitchenɗ'in tare da nufan ɗakin ta. Tana tsaye a kofar kitchen ɗ'iin cikin jin haushi da bakin cikin aikin da mahaifiyarta ta bata umarni.
K'aramar tsaki taja.
"Ni shikenan a gidan nan bani da ƴancin kaina!? Sai dai inyi ta bauta, Abba ya kawo ƴan aiki amma kin ce a'a, tsakani da Allah Ammi sai kace bakya sona, ba dama kiga na zauna hakanan sai kin k'irk'iri wani aikin da zaki nemo ki lik'a min!".
Mita ta cigaba da yi tana aikin cikin jin haushi tare da yin komai cikin rashin nutsuwa, yanda taga dama ba tare da nutsuwa ba.
*******
A cikin aji a yayin da malami yake cikin karatun Qur'ani mai girma, inda duk ɗalibai sun maida hankalin su kan sauraron malamin da kallon yanda bakin shi yake motsawa, domin suma su samu daman mai-maita abinda ya faɗa dai-dai ba tare da kuskure ba. A lokacin kuma Sahabat da take zaune a bencin baya hanun ta rik'e da Qur'ani Izu sittin, wayanta ne rik'e a hannun ta. Ta cikin Qur'anin inda baza'a iya hango shi ba, hankalin ta na ga wayan ta da sam ba ta iya jiyo duk wani abinda yake faruwa cikin ajin, duk da kuwa yanda sauran ɗalibai yan uwan ta suke ɗaga murya wajen bitan karatun da malamin nasu yake biya musu da zazzak'an muryar shi cikin suratul Maryam.
Gaba ɗaya littafin ya tafi da duk wani imaninta, a lokaci ɗaya kuma tana imagining abinda take karantawa da ita yake faruwa, wajen da ko a yaushe yake ainihin ɗaukan hankalinta tare da tafiya da imanin ta a littafin, sosai take jin daɗin yanda daren nasu na jaruman littafin ya birge ta, tsawon awa uku yana kan amaryan shi sannan ya samu nutsuwa, inda ya dakata ba dan ya gaji ba sai don tausayinta da yaji ganin tayi laushi. A dai-dai lokacin kuma ta runtse idonta, nan take taji wani abu na fita daga k'asan ta.
Runtse ido tayi tana jin wani irin daɗi a lokaci ɗaya kuma cikin ta ya fara murɗeta.
Kashe wayan tayi tare da k'wantar da kanta saman benci, idonta a runtse, gaba d'aya tsikar jikin ta a tashe yake.
A daidai lokacin kuma Mallam Jamil idon shi ya kai kanta.
"Wacece a k'wance ana karatu?!".
Bata d'ago ba har sai da abokiyar zaman ta a bencin takai hannu ta taɓa ta.
A sanyaye ta ɗago da kai tare da zuba idanunta kan Mal. Jamil.
"Yaya ana karatu kika kwanta? Ko baki jin daɗi ne?".
Sauran ɗaliban ajin kuwa duk sun bar abinda suke tare da zubo mata ido. Idon ta sun kaɗa sunyi ja, cikin daskararriyar muryanta ta amsa.
"Eh Mal. Cikina ne ke min ciwo".
"Subhannallah!".
Ya faɗa cike da tausayawa. "Allah ya baki lafiya. Sai kije Office ki karɓi magani ko?".
"Toh". Ta faɗa inda ta sake komar da kanta kan bencin. Bayan sun sake biya mai yaji karatun ya musu sallama ya fita. Dama shine last period, dan haka yana fita ɗalibai suka fara fita suna kama hanyar gida, ita ma haka ta fito cikin rashin walwala ta nufi gida ba tare da ta jira k'annen nata ba.
Tun kan ta k'arasa shiga ta jiyo dariyar mahaifiyar nata da shewa ita da Aminiyar ta Hajiya Saudat.
"Kai Aminiya ta, ai ina faɗa miki wallahi littafin nan yayi wuta, kinyi mutuk'ar k'ok'ari, gaba ɗaya kar kiga yanda duk group ɗin da kika shiga na WhatsApp littafin ake nema, kai baki taɓa rubuta littafin da ya samu masoya kaman wannan ba tawan!".
Jin Abin da suke faɗa yasa ta dakatawa tare da sake sauraron su.
"Ai ni kaina abin na bani mamaki, k'awata, kinsan jiya na amsa waya sama da mutum goma duk akan page ɗin jiya suna yabawa tare da jinjina min.
Kai ban taɓa tunanin littafin *NI DA SHI* zai samu ɗunbin wannan masoyan ba. Sharhi dana gani har ban iya karatan su ba, ke ban faɗa miki ba, akwai wacce ta ce in tura mata account namba na banda katin waya dana samu".
"Kai! Toh ai dole k'awata, ai kin tafi da imanin mu ne gaba ɗaya, ni kaina banda Abban Yusra na kusa ai ban san yanda zan k'are ba".
Dariya suka sake bushewa dashi tare da tafawa.
A dai-dai lokacin kuma da Sahabat ta kasa ɗaga k'afan ta jin maganganun da yake fitowa daga bakin mahaifiyar nata. Dama itace Marubuciyar *NI DA SHI*? toh me yasa bata amfani da asalin sunan ta a matsayin marubuciyar da duk wanda ya santa zai gane ta dashi? Cikin k'arfin hali ta k'arasa shiga ɗakin da Sallama cikin sanyi jiki.
Dakatawa sukyi da dariyar da suke tare da maida kallon su kanta a tare.
"A'a, yan makaranta!".
Hajiya Saudat ta faɗa tana murmushi.
"Ina wuni?".
Ta faɗa cikin rashin walwala.
"Lafiya". Ta amsa tana k'ara faɗaɗa fara'arta.
"Ina wuni Ummi?".
"Lafiya lau". Ta amsa da fara'a. "Ina kika baro su Na'eef da Suraiyyan?".
"Suna baya suna zuwa".
Ta faɗa tare da shigewa cikin ɗaki. Da kallo suka bita inda suka sake mai da hankalin su kan firar su, sai dai sun rage murya saboda kar ta jiyo su.
Jakan makarantarta ta ajiy ta faɗa kan gado tare da kai hannu ta k'asan maran ta. Lumshe idon ta tayi tare da cigaba da motsa hanun ta. Ba tafi minti biyar ba ta samu nasarar gamsar da kanta. Samun nutsuwar da tayi yasa ta dawowa cikin haiyacin ta, nan take taji takaicin kanta tare da jin wani bak'in cikin abinda ta aikata.
Vibration ɗin wayanta ne yasa ta saurin tashi ta jawo jakan, inda ta ciro shi da sauri tare da nufan can k'uryan ɗaki ta amsa kiran. Filo ta ɗauka tare da cusa kanta ciki a lokacin ɗaya kuma ta rage muryan ta saboda kar su jiyo ta.
********
Cikin kulawa ya dube ta tare da k'wantar da murya.
"Tun jiya da dare nake ta binki, Salma ki faɗa min abin da yake damun ki amma kin k'i, sai amsa min kike da ba komai, kar ki manta fa duk duniya baki da wanda ya kaini, a matsayina na mijinki kuma uban ƴaƴan ki, bana jin ak'wai abin da yayi saura daza mu ɓoye a tsakanin mu".
Dad'a had'a girar sama da k'asa tayi tare da ture bakin ta tana kumburi.
"Ni nace maka ba komai. Ba komai, idan ak'wai ai zan faɗa maka, kaina ne kawai ke min ciwo, amma tun jiya ka dame ni da magana ɗaya, please ka barni haka inji da ɗaya mana!".
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke ganin yanda take mishi magana gaba ɗaya kaman ba Salman shi ba, mai tausasa murya da kwantar da kai a duk lokacin daza ta mai magana.
"Shikenan".
Ya faɗa cikin sanyi jiki. "Ni zan fita".
"Sai ka dawo". Ta faɗa ba tare da ta dubi inda yake ba.
Girgiza kai yayi cikin sanyi jiki ya fice daga gidan cike da jimamin canji daya gani tattare da matarshi. Bayan addu'ar fita daga gida da yayi, ya fice tare da buɗe madaidaiciyar motan shi k'irar 206 fara sol! Tasha wanki sai k'yalli take.
Tuk'i yakeyi, amma zuciyar shi sam ba daɗi. Istighfari ya cigaba da maimaitawa a laɓɓenshi har ya isa masana'an tashi. Domin Yana mutuk'ar son matar shi, baya son abin da zai kawo wata ɓaraka cikin zamantakewan su, dan haka gaba ɗaya hankalinshi a tashe tun jiya, amma yayi juyin duniyan nan ta faɗa mishi matsalar amma tak'i.
Bayan fitan shi tsaki taja tare da hararar bayan shi. "Namiji har namiji amma baka iya awa biyu da mace kuna mu'amalan aurataya! ?. Ni wallahi hakuri na ya k'are kwata-kwata da komai da komai kagama daɗewa baka wuce 30-40 minutes! Dubi littafin *GIMBIYA TA* dana karanta jiya a WhatsApp, da *ZAZZAFA* dana karanta a Wattpad yanda suke yin dogon zango da matayen su, har fiye da awa huɗu zuwa awa biyar suna mu'amala amma banda ni, haba wallahi da sake!"
.
Haka tayi ta sambatu ita kaɗai kamar sabuwar kamu.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._
*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:*
"Allah Almighty has said:
'The son of Adam denied Me and he had no right to do so. And he reviled Me and he had no right to do so. As for his denying Me, it is his saying: 'He will not remake me as He made me at first' (1) - and the initial creation [of him] is no easier for Me than remaking him. As for his reviling Me, it is his saying: 'Allah has taken to Himself a son,' while I am the One, the Everlasting Refuge. I begot not nor was I begotten, and there is none comparable to Me.'"
(1) i.e., bring me back to life after death.
[Bukhari (also by an-Nasa'i).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ تَعَالَى: كَذَّبَنِي ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، وَشَتَمَنِي وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: لَنْ يُعِيدَنِي كَمَا بَدَأَنِي، وَلَيْسَ أَوَّلُ الْخَلْقِ بِأَهْوَنَ عَلَيَّ مِنْ إِعَادَتِهِ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّايَ فَقَوْلُهُ: اتَّخَذَ اللَّهُ وَلَدًا، وَأَنَا الْأَحَدُ الصَّمَدُ، لَمْ أَلِدْ وَلَمْ أُولَدْ، وَلَمْ يَكُنْ لِي كُفُوًا أَحَدٌ رواه البخاري (وكذلك النسائي)
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene One_
~*Page 2*~
Motsin da taji alaman za a shigo ya sata sauri datse wayan tare da b'oye ta cikin rigar ta.