Showing 6001 words to 9000 words out of 107295 words

Chapter 3 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1242

idan muna tare bana son mu rabu, saboda bana gajiya da kallon k'yak'yawan fuskar ki mai kawar min da duk wani b'acin rai, tare da dasamin farin ciki".

Lumshe ido tayi tana murmushi ba tare da ta ce komai ba, kalamun shi sun faranta mata rai mutuk'a, wannan yasa koda yaushe take sake jin wutar k'aunar shi na ruruwa a zuciyar ta.

Agogon hannun shi ya duba tare da maida kallon shi kanta, "lokaci yayi ya kamata ki koma gida, domin bana son ki kasance cikin matsala My love".

Murmushi tayi tana mik'ewa. "Ya kamata, ganin ka ya kan sani mantawa da komai".

Murmushi yayi, "ina aiki na dakyau kenan, abinda ya kamata kenan, dama tuntuni kika barni nake kid'a na da rawa na ni kad'ai".

Dariya suka yi tare da jerawa suna hiran su ta soyayya har zuwa inda yayi parking motan.

Sai da yabud'e mata ta shiga ya rufe, sannan ya zaga ya shiga tare da rufewa ya tayar suka kama hanya.

Nesa da gidan su Hunayda ya goga parking, inda sukayi sallama cikin jimamin za suyi kewan juna. Dubu biyar ya d'auka tare da mik'amata ta siya kati.

Karb'a tayi had'e da mai godiya ta fice a motan hannun ta rik'e da yar k'aramar ledar daya mata orde ice cream d'in da su choculate.

Da sallama ta shiga cikin gidan, Ammi dake tsakar gida ta amsa mata cikin sakin fuska.

"Ina Wuni Ammi!", Ta fad'a tare da d'an rusunawa.

Da fara'a ta amsa mata. Hunayda dake kitchen ne ta fito tana kad'e ruwan hanun ta da ta gama wanke-wanke kenan.

Had'a ido sukayi tare da sakar ma juna murmushi.

"Welcome!". Ta fad'a tana k'arasowa inda take.

"Yauwa! Wai yau lafiya bakije makaranta ba?".

Ta tambaya a lokacin da suka nufi k'ofar d'akin su.

"Lafiya!" Ta amsa. "Ammi ne taje anguwa, kuma bata dawo da wuri ba, babu key da za mu rufe gida shiyasa ba muje ba".

"Ok! Ai su Aisha suna tambaya na ke nace may be ko bakiji dad'i bane, toh dana duba ko zan hango Hajna itama ban ganta ba".

"Hakane, muna tare an barmu mu biyu a gida".

"Daga ina kike ne? irin wannan k'amshin naga sai k'yalli kike!". Ta fad'a cikin sigan zolaya.

"Uhumm! ke dai bari, daga Green park muke ni da rabin raina, yanzu ya sauke ni nan ya wuce".

"Wai ke Sahabat ba k'ya tsoron ranar da asirin ki zai tonu?".

"Hmmm!", ta sauke ajiyar zuciya, "ke dai bari , ai Allah ma ya kare amma da na boni da Ummi, kar ma Uncle Zakari yaji labari da kashina ya bushe".

Gyad'a kai tayi, "toh kinji ko, ina fad'a miki kiyi a hankali fa".

"Hunayda kin san fa so tunda kema kina yi, baza ki gane yanda nake ji akan zaiyad ba ina mugun son shi kin sani fa!".

"Hakane na san so, amma kuma ni ai duk samarin dazan yi da soyayyar da zamu d'ana duk a waya muke gama shi, sai idan ko mun had'u hanyar makaranta amma kinsan tsorona ma bazai barni inyi k'arya har in fice daga gida inbi saurayi wani gurin ba".

Ajiyar zuciya ta sauke, "toh kin gani ko ke da kike da freedom d'in rik'e wayan kenan, amma ni kina ganin yanda Ummi take da ra'ayin nan zata barni rik'e waya nan kusa kuwa? Kai da kamar wuya!. So kin gani da zan samu wannan daman nima bazan ringa satan hanya ina fita ba, idan ma zanyi toh bazai zama koda yaushe ba. Amma yanzu ko wayan zan amsa fa sai a b'oye da kuma dabara kamar wata b'arauniya".

"Toh ai sai kiyi hakuri zuwa lokacin da Ummi zata Amince miki".

"Ke dai mu bar zancen, barina tashi, sai mun had'u a WhatsApp anjima, yanzu ni zan wuce kafin a kira magrib".

Ta fad'a tare da mik'ewa tana gyara gyalen ta, a lokaci d'aya kuma ta mik'a mata ledan dake hannun ta, "Ga tsarabar ki, barina d'auki Chaculate ma Na'eef kafin in in shiga dashi duka gida a dasa min ayar tambaya".

Dariya tayi tare da d'aukan hijab ta zura domin tayi mata rakiya.

Bayan ta ma Ammi sallama, suka fita tare domin ta mata rakiya.

******

Kaman ko yaushe bayan sallar isha'i, Abdulkareem ya nufi gidan shi kai tsaye, bayan ya saya ma yaranshi tsaraba kaman ko yaushe tare da mai d'akin nashi.

Da sallama ya shiga cikin gidan, da gudu Husna, yarinyar yar shekara hud'u da k'anin ta Abubakar da suke kira (Mussadiq )da ba zai wuce shekara biyu ba, suka nufo shi tare da kiran; "Abba Oyoyo Abba Oyoyo!".

Da murmushi ya shiga d'aga su d'aya bayan d'aya, yana dariya tare sumbatan su a goshi.

Bayan ya sauke su da d'an musu wasa ya. mik'a musu Bobo da Biscuit d'in da ya kawo musu, murna su ka shiga yi inda ya karb'a tare da fara k'ok'arin bud'e musu.

Duk abinda suke Salma na zaune tana karatun littafi a wayan ta, cikin kwalliyan ta na riga da wando na Pakistan, wanda rigan ya kai mata gwiwan ta, gyallen shi tayi d'auri da ta karkato dashi gaban goshin ta inda gefen kanta ya baiyana tare da fito da bak'i sutuk d'in gashin kanta daya sha gyrara yake ta k'yalli. Tunda ta juyo muryan shi taji ranta ya b'aci tuno daren su na jiya dashi, dan haka ta sake maida hankalin ta kan abinda take karantawa tare da yin kaman bata ma san da shigowan shi ba.

Duban su yayi yana murmushi. "toh kuzo muje d'akin ku ko, yan albarka!".

Ya fad'a tare da kama hannun su ya bud'e kofan d'akin tare da ganin shigan su kafin ya jawo musu k'ofan ya nufi inda take zaune, gaban shi na fad'uwa a lokaci d'aya kuma k'waliyar ta, ya mutuk'ar k'ayatar dashi tare da jin wani abu ya tsarga mishi.

Salma k'arshe ne wajen kaman ta komai kuma mace ne da duk namijin zai yi burin samun ta matsayin uwar y'ay'an shi, domin tana da ilimin ta na addini tare dana boko dai-dai gwargwado, tsafta, iya girki da kula da kanta wannan yasa idan ka kalle ta baza ka tab'a tunanin ma ta ajiye d'a d'aya ba.

Zama yayi a hannun kujeran da take zaune tare da sak'alo hannun shi saman kafad'un ta, a hankali ya furta; "My Salma, wani laifi nayi ne da ko kallo na ba a son ayi ballantana in samu tarb'a?".

Hannu ta tasa tare da cire nashi daga kafad'an ta. "Ban san ka shigo ba ai, Sannu da zuwa!".

Murmushin tak'aici yayi sannan zuciyar shi ta mishi zafi k'warai da yanda ta nuna mai, amma yayi kokarin danne zuciyar shi tare da had'iye abinda ya taso mishi.

"Yaya kuka wuni?".

"Lafiya lau". Ta amsa.

"Amma ina kike ajiye wayan ki yau? Na kira inji lafiyar ku tunda ke baki neman kiji na isa lafiya ba, amma baki d'aga ba kuma baki yi ko flashing ba".

Yatsina fuska tayi,

"tunda kaji shiru ai muna cikin k'oshin lafiya".

K'aramar ajiyar zuciya ya sauke ba tare da yace komai ba, ya kalle ta, "A taimaka min da abinci, domin yau sai naci in iya watsa ruwa, rabona da abinci tun break fast".

Dad'a d'aure fuska tayi, "ni ban dafa abinci ba, su Mussadiq ma indomie na dafa musu, kai kuma na san baka son ta shi yasa ban dafa da kai ba".

Da mamaki ya kalle ta.

"Amma me yasa baki dafa ba bayan ak'wai komai a gidan?".

"Bana jin dad'in jikina ne!". Ta bashi amsa tana shan k'amshi.

"Amma kuma yanzu kika ce min kuna lafiya".

"Uhumm!".

Ta fad'a tare da mik'ewa, "nifa gaskiya Abban Husna na fara gajiya da k'wak'wanka da bin diddigi, haba, tunda ka shigo sai tuhumana kake kaman wacce tama sarki k'arya!

Haba! ka barni inji da abinda da yake damuna mana!".

Ta k'arasa fad'a tare da shigewa cikin d'akin su Husna ta barshi zaune a gurin, baki bud'e.

Mamaki ne fal ranshi. Wai me yake faruwa ne haka?

Zugi ne wannan ko yin kanta? Ko kuwa Aljanu ne suka shafeta?

Amma yau Salma ce take treating d'in shi haka?!

Wacce take tarairaiyan shi tare da nuna mai dukkan kulawa tare da soyayya, yau ita ce take mai irin haka, to me ya mata?

Tambayan da ya tsaya mai a rai kenan! Wanda dashi ya wuni.

Duk ciwon da take fa bata tab'a barin shi yaci abinci a waje, haka zata daure ta shiga kitchen ta dafa mishi.

Ya d'auki tsawon wasu mintuna agurin yana ta tunani, kafin yayi dauriyan tashi ya shiga bed room d'in su.

Yana jiyo muryanta gurin su Husna suna karatu.

Wannan ya sake tabbatar mishi lallai dashi take wannan fushin.

Toh laifin me na mata haka da baza ta fito ta fad'a min ba?

Rage kayan jikin shi yayi ya fad'a toilet domin ya watsa ruwa, jikin shi a sanyaye.

~_From The Everlasting Golden Pen đź–Š of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~

© *2020*


_~We Love U All~_❤
🙆🏻🤷🏻‍♀ *_MENENE RIBA TA ❓_* 🤷🏻‍♀🙆🏻

© *2020*

🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

*~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~*

*~We are bearier's of so golden pen~*đź–Š

*~We write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our penđź–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*

♣ _Scene Two_

~*Page 4*~

Sahabat na fita daga gidan su Hunayda ta tari mai machine ya kai ta layin su, dan ta isa gida da wuri, kasancewar ba wani nisa sosai, yasa suka isa cikin ƙanƙanin lokaci, tana sauka ana kiran sallar maqrib.

Da sallama É—auke a bakinta ta isa É—an madaidaicin gidan na su, ba kowa a tsakar gidan, hakan yasa ta shiga falon kai tsaye.

"Sahabat ina kika tsaya, ban gayamiki ki dawo da wuri ba, ki É—aura girki?!".

Ummi ta faÉ—a, wacce take zaune akan kujerar dake falon, wayarta na hannun ta tana latsawa ,da alama har Hajiya Saudat tabar gidan bata tashi daga gurin ba.

Turo baki Saha tayi tana ƙara jin haushin mahaifiyar tata.

"Ba inda na tsaya, da naje na tadda Hunayda bata jin daÉ—i ne shi ne na tsaya".

Tayi maganar cike da jin haushi da tsoro, bata yadda sun haɗa ido ba dan kar ta gane ƙarya tayi mata.

"Ayyah Allah ya bata lafiya, to sai ki je kiyi sallah ki É—aura muku abinda zaku ci".

Fuuu! ta wuce É—akin su, ba tare da ta ce komai ba, dan tsabar haushin Ummin da take ji.

"Shikenan mutum komai sai yayi, duk inda naje sai an jira na dawo, ke kenan latsala waya, baki iya yin aikin komai ni na fara gajiya! Ni ce wannan, ni ce wancan! haba! mutum an maida shi jakin dole", a ranta tayi maganar cike da jin haushi.

Tana shiga É—akin Na'eeb ya rugu ya rungume ta,"Oyoyoo! Aunty Sahabat kin dawo, ina chocolate É—i na?"

Cikin fushi ta ce,"Na dawo!". Ta miƙa mishi, bai bi ta kanta ba ya fita yana murna da jin daɗi.

Suraiyya ma tai mata sannu da zuwa, "Aunty Sahabat ina da assignment".

"ki ƙyale ni da wani Assignment, da wanne zanji!?".

Cikin faÉ—a- faÉ—a tayi maganar, ganin yadda tayi maganar ba daÉ—i yasa ta sassauta murya.

"Suraiyya ki bari sai gobe da safe, kin ga yanzun zan É—aura mana abinda zamu ci, kuma idan na gama da abinda zanyi".

"Ba komai Aunty Saha,muje na tayaki wani abun".

"Yawwa!"

Bayan ta idar da sallah ta fito zuwa kicin É—in, har lokacin Ummi na gurin tana ta faman latsa waya, basu ce mata uffan ba, suna ta aikace-aikacen su amma tamkar bata san suna gidan ba.

********************

*Wanene Zaiyad*

Zaiyad Kabir Safana shi ne cikakken sunan Zaiyad, mahaifin shi Kabir Safana haifaffan É—an jahar kaduna ne, dan kasuwa ne wanda yayi fice a jahar kaduna.

Tun zaiyad na ƙarami mahaifiyar shi ta rasu, wanan dalilin yasa Alhaji Kabir Safana ya ɗau son duniya ya ɗaurawa Zaiyad, baya ganin laifin shi ko kaɗan, yana sakar mishi kuɗi yayi yadda yake so ba mai taɓa shi.

Zaiyad ba wani mai kyau ba ne irin na azo a gani, sai dai ba laifi yana da nashi irin kyaun, shi ba baƙi ba sanan kuma ba fari ba, amma kuma ɗan gaye ne.

Shi yasa Zaiyad ya taso cikin rashin jin magana da sangarci, sai yadda yake so, sai abinda yake so.

Gaba ɗayan unguwar Rimi daga kan layin Isa Gaita harda sauran layikan, ba wanda bai san waye Zaiyad ba gurin ɓata yaran mutane, baya shaye-shaye sosai amma ta fannin ɓata yaran mutane ko ince yaudara dan sai da yarda mace, ya ƙware sosai ta fannin yaudara, duk wayau mace sai dai bai kwallafawa ranshi ita ba, cikin salon shi zai sa mace ta amince da shi, yadda bata isa takai ƙarar shi ba.

Ranar da ya haɗu da Saha a central market, taci ado kasancewarta mai son ado ce, da shigar ƙananan gaya ko atamfa ce ɗamaman ɗinki ake mata, da soyayya ya isa gareta, bai sha wata wahala gurin shawo kan ta ba, wanda har zuwa yanzun bai baiyana mata manufar shi ba, kullum nuna mata yake yi shi kamili ne.

Wanan kenan akan Zaiyad Kabir Safana.

Zaiyad ne kwance akan doguwar gujerar da ke falon, idan ka ganshi zaka ɗauka bacci yake yi, amma a zahiri lamo kawai yayi.Kwakwalwar shi ke ƙara nuna mishi hoton yadda dirin Sahabat yake, lips ɗin ta yadda take sarrafasu idan tana magana shi yafi ɗaukar hankalin shi.

Ɗan tsaki yayi iya leɓan shi haɗe da cizon leɓan, sanan ya ce cikin raguwar muryar shi mai cike da kasala.

" Da sannu!! zaki shigo hannu yarinya, ban taɓa daɗewa da mace ba tare da na cin ma burina ba irin ki, amma na kusa cin ma haƙa."

********************

Bayan fitar Sahabat Hunayda ta É—auko tsarabar da ta kawo mata, kiran Hajna ta fara.

"Hajna! zo ki amsa".

Ammi, wacce ke zaune a gurin ta kalle Hunayda cikin kulawa ta ce, "Hunayda ina kika samu chocolate haka da yawa?".

"Ammi, Saha ce ta kawo min".

"Ita ina ta samu, na gansu da yawa".

Shiru Hunayda tayi na ɗan dakiƙu kafin ta ce, "Ban sani ba, amma siyowa tayi".

"To ku kula dai Hunayda,rayuwar yanzun ta zama abinda ta zama sai kun kula".

Cikin sanyin murya ta ce,"To Ammi."


Hajna ta zo cike da jin daÉ—i ta amsa tana sha, kallon yanayin Ć´ar uwarta ta ya sauya yasa ta ce mata, "Aunty Hunayda kin tuno lokacin da Abba ke kawo mana irin wannan, ki min wayau ki shanye?".

Dariya suka yi dukan su harda Ammi.
Suna nan zaune aka kira sallah suka tashi suka yi, bayan duk sun idar suka ƙarasa yin aikin su sannan suka zauna a falon jiran mahaifin su.

Da sallama ya shigo É—akin, cikin jin daÉ—i da farinciki suka amsa mishi.

"Sannu da zuwa Abba". Hunayda da Hajna suka faÉ—a a tare, Hajna ta amshi ledar dake hannun shi.

Cikin sakin fuska da nuna kulawa ya ce, "Yawwa ya kuka wuni?".

"Lafiya lau Abba".

Ammi dake gefe zuciyarta cike da farin ciki tayi mishi sannu da zuwa.

"Ya gidan Ammin Hajna?".

"Lafiya lau ya aiki?"

"Alhmdllh! sai godiya".

Sannan suka zauna suka dan taɓa fira cikin so da ƙaunar juna, sannan su Hunayda suka yi musu sallama suka tafi ɗakin su.

*Wacece Hunayda?*

Maryam shi ne ainihin sunan Ammi mahaifiyar Hunayda Ć´ar kaduna ce,a unguwar badikko.Hamza shi ne ainihin sunan Abbah,wanda shi ma É—an kadunan ne unguwar hayin É—an mani.

Maryam cikin so da ƙauna ta taso gurin iyayenta, su biyu mahaifin su ya haifa, yayan ta Ibrahim sai ita, mahaifin Hamza(Abba) abokin mahaifin Maryam ne(Ammi), tamkar ƴan uwa haka suke, dan abotar su tun yarinyata, sai kuma gashi yaran su sun fara soyayya a tsakanin su,dukkan su wa wani bako suka yiba kandy kowanan su yayi,dan ƴan kasuwa ne iyayen na su, atamfofi suke saidawa a kasuwa.

Maryam tana da tarbiyyarta wacce ta samu daga iyayenta, sai da ta kammala aji uku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login