Showing 3001 words to 6000 words out of 107295 words

Chapter 2 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1243

Tashi tayi tare da fara k'ok'arin cire Uniform d'in jikin ta.

Da kulawa ta dube ta, "wai me yake damun ki ne Sahabat? Naga kin shigo gida yau a sanyaye?".

Ba tare da ta kalle ta ba ta cigaba da cire Uniform d'in.

"Babu komai Ummi, kawai kaina ke ciwo amma ya daina ma".

"Toh Allah ya sauwak'a!".

"Amin!" Ta amsa tare da sake duban ta.

"Idan kin canja kayan kije ki fara rage mana aiki a kitchen kafin su Surayya su k'araso sai su taya ki".

Girar sama da k'asa ta had'a jin abin da ta ke fad'a.

"Ummi ina fa son zuwa gidan su Hunayda ne in dubo ta, domin yau banga taje makaranta ba".

Wayan ta d'aga tare da dubawa taga 4:30 Pm.

"Toh shikenan, amma kar ki zauna, kinga dai nayi bak'uwa, sannan da ta tafi zanyi Typing ne so da kin duba ta ki dawo".

Dad'a zunb'uro baki tayi, ba tare da ta amsa ba.

Bayan ta tabi da harara tare da fara k'unk'uni. "haka kawai sai dai kizauna ke baza kiyi komai ba sai dai ki ta bamu Umarnin sai kace bayin ki! Ni wallahi na fara gajiya, haba! shikenan ke baza kiyi komai ba tun safe mutum ya tashi yayi ta bauta kenan kaman bawa. Ni wallahi gwara inyi aure na in tafi gidan miji inyi mai licence amma na gaji!".

Toh fa! kunji fa wata babban magana wai shin yima iyaye hidima bauta ne da ba lada?

Ina Sahabat, kije ga Mal.Jamil, na san zai miki cikaken bayanin kan hakkin iyaye kanki.

Bayan ta gama rage kayan jikin ta, fitowa tayi daga ita sai d'aurin k'irji da zani ta zo ta gitta su ba tare da ta kalle inda suke ba tayi wucewar ta kitchen, bucket ta d'auka tare da juye ruwan zafi dake wuta ta nufi band'aki dashi.

Bayan wucewar ta dukkan su dakatawa suka yi da hirar da suke, wanda duk akan littafi ne da kallo suka bita.

Hajiya Saudat ne tayi murmushi, "kai *Hibba!* mun kusa yin sirikai fa".

"Hmmm", tayi murmushi, "hajiya ni kaina girman yarinyar nan na bani mamaki kaman ana hura ta, duka-duka fa bata wuce shekara goma sha shida da d'an d'oriyar watanni ba, domin bata ma kai da rabi ba, amma kinga yanda ta zama wata uwar mata".

Dariya Hajiya Saudat tayi, "toh Allah dai ya basu mazaje na gari".

"Amin!", ta amsa.

Bayan ta fito daga wanka shiryawa tayi cikin riga da zani na atamfa, d'inkin zanin six pieces da rigan ta d'inkin Borno style, kayan su mata k'yau, a nutse ta zauna ta tsara k'walliyan ta tare da feshe jikin ta da turare, sannan ta d'auki mayafin ta da takalmi da suka dace da kayan nata ta sa. Wayan ta d'auka tare da soke ta k'ugun ta sannan ta fice.

A falo ta ja birki inda suke zaune har lokacin suna k'wasar fira, ranta gaba d'aya dama baya son Hajiya Saudat saboda yanda taga kaman ita take tunzura mahaifiyar nata take sata sauran aikace-aikacen gida.

"Ni zan wuce Ummi".

"Toh ki gaishe ta, kar ki zauna dan Allah Sahabat".

"Toh!", ta amsa in ta d'an dubi inda take zaune, "Umman Yusra sai anjima".

"Yauwa!", Ta amsa", "sai kin dawo Sahabat, a dinga kula dai da yan iskan samarin kan hanya. Allah ya kare a dawo lafiya!".

Amin ta amsa tare da ficewa tana sake jin haushin maganan nata, "Wai a ringa kula da yan iskan samarin kan hanya" Ce mata aka yi gurin su zanje ko kuwa?".

Haka tayi ta mitan ta dai ta ida fita daga gidan, a bakin k'ofa suka yi kicibis da su Surayya, da gudu Na'eef ya k'araso yayi mata Oyoyo, "Aunty Saha munje ajin ku muna ta jiran ki bak'ya nan, shine Aunty Surayya tace mu jira ki, shine muka zauna muna ta jiran ki amma bamu ganki ba".

Dariya tayi, "toh Na'eef Gani nan yanzu ka ganni. Yau ban jira ku ba nayi tafiya ta, yanzu kaje gida ka cire Uniform, Surayya tayi ma wanka ak'wai ruwa a wuta", ta fad'a tare da kallon inda take tsaye.

"Barina je anguwa in dawo Sis".

"Toh Aunty sai kin dawo, amma ina zaki irin wannan k'waliyya haka? Kinga yanda kikayi k'yau kuwa!".

Dariya tayi, "toh na gode, idan na dawo k'yaji. Me zan siyo ma?".

Ta tambaye shi.

"Chaculate!", ya amsa yana tsalle.

"Toh shikenan zan kawo ma".

Da gudu ya shige cikin gida, inda Surayya take biye da shi.

"Hibba! dole fa mu tashi tsaye da yima yaran nan addu'a Allah ya shiga tsakanin su da wayannan samarin zamanin masu rud'in yara su lalata musu rayuwar". Cewar hajiya Saudat

"Ke dai bari k'awata, ni shi yasa nake takatsan-tsan da duk wani motsin Sahabat, saboda Allah ya mata diri da garab'an jiki. Kinga wannan yasa fa ko waya bazan yarda ta rik'e ba gaskiya, ni ina tunani ma sai taje gidan auren ta, saboda wannan waya.....", ta d'aga wayan ta tana jujjuyawa.

"....Illan shi yafi amfanin shi yawa. Domin duk abin da kake nema zaka samu cikin shi, idan alkhairi ne zaka samu ko akasin shi".

Ajiyar zuciya hajiya Saudat ta sauke. "Amma yanzu ke kina ganin hajiya hanata rike waya shine mafita? Ni inaga fa ba shi bane mafita. Domin yaran nan da kike ganin idan har suka tasa ma ka hana su rik'ewa sai kiga sunje samarin sun sai musu kuma suna rik'ewa a b'oye ba tare da kin sani ba. So kinga ba daga nan take ba fatan kawai Allah ya shirya mana zuri'a, amma ni rayuwar nan ma tsoro take bani , domin kinga Mallam Usman mak'wafcin mu nan yar shi Saliha haka saurayin ya sai mata waya sama da shekara ba tare da sanin iyayen ba, toh haka dai har mahaifin ya fahimta, k'arshe kar kiga tijaran da ya mata ya karb'i wayan nan amma abin mamaki yarinyar nan ba ayi wata ba saurayin nan ya sake sai mata wani, ta cigaba da rik'ewa ba tare da sanin iyayen nata ba. Ke ni yaran nan har tsoro suke bani".

"Toh Allah ya k'yauta. Hakan kam yana faruwa sosai, Allah dai ya kare mana zuri'a".

"Amin!", ta amsa.

"Kin san fa hajiya duk wani burina da tunanina yana kan Sahabat, cikin yaran nan gaba d'aya nafi jin ta a rai na. Bani da buri da ya wuce in ganta cikin farin ciki...".

Shigowan su Na'eef ne yasa su dakatawa daga maganan da suke.

******

Duk wani aikin da Ammi ta bata Ulumarnin yi kafin ta dawo haka tayi shi na ganin dama ko ince ko oho, dan haka cikin k'ank'anin lokaci ta gama tare da tattare kayan data b'ata ta zuba su gun wanke-wanke, share kitchen d'in tayi sama-sama ta rage wutan abincin dake wuta tare da lek'awa d'akin Ammi. Hajna ce a falo tana k'ok'arin sa turaren wuta a d'an k'aramin k'yak'yawan kasko.

Harara ta b'alla mata, "ni zan shiga wanka, ki duba abinci dake wuta idan yayi ki sauke".

"Toh", ta amsa cikin rashin jin dad'in abinda yar uwar nata take mata, domin ita har bata so Ammi ta aike ta kiran ta domin idan har ta tadda ta da wayan ta a hannun ta, ta Isar mata da sak'on toh wuni zata yi k'yarar ta da mata tsawa.

*******

Bayan fitowan ta daga gida taku kad'an tayi ta ja ta tsaya daga gefe tare da fitowa da wayan ta k'irar tecno Spark 4, yan latse-latse tayi tare da karawa a kunne.

"Hello Dear", ta fad'a bayan an d'aga wayan ta d'ayan b'angaren aka amsa.

"Hi Sweedy! Har kin fito ne?".

"Eh na fito!".

"Good! Gani nan k'arasowa ki jirani".

"Toh", ta fad'a tare da katse wayan. Tafiya ta fara yi cikin takun ta mai d'aukan hankali.

Cikin mintunan da basu gaza biyar ba ta iso inda suka saba had'uwa, tsayuwar ta yayi dai-dai da Goga Parking d'in shi, batayi k'asa a gwiwa ba ta k'arasa jikin motan inda ya bud'e mata k'ofa, mazaunin gaba ta shiga tare da rufe k'ofan ya k'ara ma mota giya suka hau hanya.

Kaman ko yaushe gurin shak'atawa suka nufa.

*******

Bayan Ammi ta fito daga wanka ta shirya cikin doguwar rigar ta na wani jan material, kayan sun amshe ta kasancewan ta farar fata, sun kuma b'oye k'uruciyar ta domin daga ido baza ka ce tana da ya kaman Hajna bama ballantana Hunayda.

Kitchen ta nufa da hanzari jin abinci na k'auri. Da sauri ta k'arasa tare da murd'e switch d'in gas ya mutu, bud'e tukunyar tayi tare da duba dahuwar abincin gashinan a ido ba sai ta tab'a ba bai dahu ba amma babu ruwa cikin tukunyan sai k'onewa da ya fara yi.

Ranta ne taji ya b'aci amma ta danne tare da fara duba Yankan kayan salad d'in data sata.

"Subhannallah!", Ta fad'a ganin irin yanda ta yanka mata. Wai me yake damun Hunayda ne? Me take Nufi ne?

Tambayoyin da suka cika mata zuciyan ta kenan, domin wasu irin yankan da tayi fato-fato da sai ka d'auka fad'a akayi da ganyen.

A fusace ta nufi d'akin ta tare da tura k'ofa ta shiga.

A tsaye ta same ta daga ita sai towel alaman ta fito daga wanka, tana zaune gaban dressing mirror wayan ta na hannun ta.

Jin Yanda aka turo k'ofan ya sata saurin mik'ewa game da ajiye wayan.

"Me yake damun ki ne haka Hunayda?! Ina hankalin ki yake ne?! Ko dan na tursasaki kinyi aiki baki yi niyya bane yasa zakiyi yanda kike so, wanda ko Hajna baza tayi wannan b'arnar ba!?".

D'an Sosa k'eya tayi tare da sunar da kai k'asa.

"Ammi me nayi?".

Domin ita har ranta bata ga laifin data yi ba, sai dai tasan tayi aikin cikin gaggawa.

"Au!, me kikayi kike tambaya na?".

"Yanzu ace dafa farar shinkafa yau ya gagare ki, baza ki iya tsayar da ruwan da zai wadace shi ya dahu ba?".

Dahm! K'irjin ta ya buga domin sai Yanzu ta tuna fa bayan ta tafasa ta tsane ta mai da tukunya ta aza a wuta ba tare da tasa ruwa a ciki ko kad'an ba.

"Ammi dan Allah kiyi hakuri wallahi na manta ne dana tafasa na tsane na mayar tukunyan bansa ruwa ba".

Takaici ne ya kama ta jin abinda ta fad'a. Wanda gaba d'aya ma ta rasa abinda zata ce mata sai wani kallo da take watsa mata.

"Su kuma kayan salad d'in fa? Kin manta suma baki yanka ba ko?".

"Um'um!".

Ta fad'a tana sunkuyar da kanta domin tsoron Ammi ne ya kamata, ganin b'acin rai kwance a fuskan ta wanda ita baza ta iya tuna sanda taga fushi har haka daga gare ta ba.

"Shikenan!", ta fad'a cikin tak'aici, "Idan abu da kike me k'yau ne, ki cigaba Hunayda, Allah ya gani ina iya k'ok'arina kanki, kuma wannan abu tun ba yau ba kin saba yin su kuma ba tare da wani matsala ba, amma saboda kina aikin daya fi nawa lada na d'ago ki yasa kimin yanda kike so ko?!".

Girgiza kai tayi idon ta ya ciciko da k'walla;

"Ba haka bane Ammi, dan Allah kiyi hakuri kar kiyi fushi dani, Insha Allahu bazan sake ba na tuba".

Ta k'arasa maganan ta had'e hannun ta guri guda.

"Shikenan!", ta fad'a tare da jin tausayin ta, kuma a lokaci d'aya zuciyar ta yake sanar da ita dole ta mata uzuri ta kuma ringa nusar da ita a hankali, saboda ba d'abi'an ta bane, da tana k'ok'arin yi mata komai cikin tsari da nutsuwa koda bata sata ba, zata mata duk abinda ya kamata.

"Ki ringa kula Hunayda, Dan Allah na rok'e ki, kinga ke mace ne gidan wani zaki je, idan baki nutsu kin koyi duk wayannan abubuwan ba idan kika je naki gidan wa zai miki?

Kiyi k'ok'arin yin amfani da abinda kika karanta da wanda ake fad'akar da ku a makaranta koda yaushe, saboda watarana idan da rai da safiya ke ma uwace kuma na tabbata baza ki so yarki ta miki abinda kike yi min yanzu ba, baza ki tab'a son haka ba kuma nima bana miki fata. Dan haka ki k'ara kula, domin idan kayi dai-dai zaka ga sakamakon ka, idan kayi ba dai-dai ba ma zaka gani.

So ki kula sosai kuma kar ki maida hankalin ki kan abinda ba zai amfane ki ba".

Jikin tane yayi sanyi da nasihar mahaifiyar nata. A sanyaye ta furta; "Insha Allahu Ammi zan kula, na gode".

"Yauwa maza ki sa kaya ki fito, wannan b'arnar da kikayi mu gani ko za a iya gyarawa".

"Toh!", Ta amsa tare da fara kintsawa a sanyaye, domin maganganun mahaifiyar nata ya shige ta, kuma tabbas ta gamsu, gaskiya take fad'a mata sai dai fatan Allah ya miki Albarka, "ki dauki abinda yake mai amfani cikin littatafan da kika karantawa masu amfani, sannan kiyi watsi da marasa amfani, domin ko wani littafi babu inda bazai miki nuni da nashi darasin ba sai dai idan anyi shi ne domin nishad'i ba ilimintarwa ko fad'akarwa ba". Amma ita sam bata jin zata iya daina karanta littafi.



~_From The Everlasting Golden Pen ๐Ÿ–Š of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~

ยฉ *2020*


_~We Love U All~_โค
๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคท


*_MENENE RIBA TA โ“_*

๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†

ยฉ *2020*

๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

~*WRITTEN BY*~ โ„ข _Golden Pen Writers Association_

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._

~*DAGA ALQALUMAN*~๐Ÿ‘‡๐Ÿป.....โœ

โ™ฆ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

โ™ฆ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

โ™ฆ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

โ™ฆ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ฦ˜AREENATEEY.*

โ™ฆ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

โ™ฆ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

On the authority of Zayd ibn Khalid al-Juhaniyy (may Allah be pleased with him), who said:

The Messenger of Allah (may the blessings and peace of Allah be upon him) led the morning prayer for us at al-Hudaybiyah following rainfall during the night. When the Prophet (may the blessings and peace of Allah be upon him) finished, he faced the people and said to them: "Do you know what your Lord has said?" They said: "Allah and his Messenger know best." He said: "'This morning one of my servants became a believer in Me and one a disbeliever. As for him who said: 'We have been given rain by virtue of Allah and His mercy,' that one is a believer in Me, a disbeliever in the stars (2); and as for him who said: 'We have been given rain by such-and-such a star,' that one is a disbeliever in Me, a believer in the stars.'"

(2) The pre-Islamic Arabs believed that rain was brought about by the movement of stars. This Hadith draws attention to the fact that whatever be the direct cause of such natural phenomena as rain, it is Allah the Almighty who is the Disposer of all things.

[Bukhari (also by Malik and an-Nasa'i).]

ุนูŽู†ู’ ุฒูŽูŠู’ุฏู ุจู’ู†ู ุฎูŽุงู„ูุฏู ุงู„ู’ุฌูู‡ูŽู†ููŠู‘ูุŒ ุฑูŽุถููŠูŽ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู†ู’ู‡ู ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุตูŽู„ู‘ูŽู‰ ู„ูŽู†ูŽุง ุฑูŽุณููˆู„ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุตูŽู„ู‘ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ูŽ ุตูŽู„ูŽุงุฉูŽ ุงู„ุตู‘ูุจู’ุญู ุจูุงู„ู’ุญูุฏูŽูŠู’ุจููŠูŽุฉูุŒ ุนูŽู„ูŽู‰ ุฅูุซู’ุฑู ุณูŽู…ูŽุงุกู ูƒูŽุงู†ูŽุชู’ ู…ูู†ู’ ุงู„ู„ู‘ูŽูŠู’ู„ูŽุฉูุŒ ููŽู„ูŽู…ู‘ูŽุง ุงู†ู’ุตูŽุฑูŽููŽ ุงู„ู†ู‘ูŽุจููŠู‘ู ุตูŽู„ู‘ูŽู‰ ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ุนูŽู„ูŽูŠู’ู‡ู ูˆูŽุณูŽู„ู‘ูŽู…ูŽ ุฃูŽู‚ู’ุจูŽู„ูŽ ุนูŽู„ูŽู‰ ุงู„ู†ู‘ูŽุงุณูุŒ ููŽู‚ูŽุงู„ูŽ ู„ูŽู‡ูู…ู’: ู‡ูŽู„ู’ ุชูŽุฏู’ุฑููˆู†ูŽ ู…ูŽุงุฐูŽุง ู‚ูŽุงู„ูŽ ุฑูŽุจู‘ููƒูู…ู’ุŸ ู‚ูŽุงู„ููˆุง: ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุฑูŽุณููˆู„ูู‡ู ุฃูŽุนู’ู„ูŽู…ูุŒ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ุฃูŽุตู’ุจูŽุญูŽ ู…ูู†ู’ ุนูุจูŽุงุฏููŠ ู…ูุคู’ู…ูู†ูŒ ุจููŠ ูˆูŽูƒูŽุงููุฑูŒุŒ ููŽุฃูŽู…ู‘ูŽุง ู…ูŽู†ู’ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ู…ูุทูุฑู’ู†ูŽุง ุจูููŽุถู’ู„ู ุงู„ู„ู‘ูŽู‡ู ูˆูŽุฑูŽุญู’ู…ูŽุชูู‡ูุŒ ููŽุฐูŽู„ููƒูŽ ู…ูุคู’ู…ูู†ูŒ ุจููŠุŒ ูƒูŽุงููุฑูŒ ุจูุงู„ู’ูƒูŽูˆู’ูƒูŽุจูุŒ ูˆูŽุฃูŽู…ู‘ูŽุง ู…ูŽู†ู’ ู‚ูŽุงู„ูŽ: ู…ูุทูุฑู’ู†ูŽุง ุจูู†ูŽูˆู’ุกู ูƒูŽุฐูŽุง ูˆูŽูƒูŽุฐูŽุงุŒ ููŽุฐูŽู„ููƒูŽ ูƒูŽุงููุฑูŒ ุจููŠุŒ ู…ูุคู’ู…ูู†ูŒ ุจูุงู„ู’ูƒูŽูˆู’ูƒูŽุจู
ุฑูˆุงู‡ ุงู„ุจุฎุงุฑูŠ (ูˆูƒุฐู„ูƒ ู…ุงู„ูƒ ูˆุงู„ู†ุณุงุฆูŠ)

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*

โ™ฃ _Scene One_

~*Page 3*~

A zaune suke a wasu fararen kujeru, gefen su ruwa ne da d'aid'aikun jama'a suke d'an giftawa, a dai-dai wannan yammacin da iska mai dad'in gaske yake kad'awa cikin nutsuwa da saukar da yanayi farin ciki ga duk wanda ya shak'e ta, duk wanda ka gani gurin da yar budurwan shi gefe ko matar shi. Ice cream ne gaban su da sauran tarkacen kayan ciye-ciye.

Zaiyad saurayi ne mai ji da tashe tare da ji da kanshi, d'an shekaru 25 a duniya, yana zaune ne cikin shigar sa ta k'ananun kaya na riga da wando, wanda duka kayan sun kasance farare sol, kayan sun karbe shi sosai, takalmi da agogon shi duk farare ne, sai bak'in glass d'in daya sa a idon shi, wanda ya dace da yanayin fuskar shi.

D'aukan ice cream d'in yayi a cokali tare da nufan bakin ta dashi yana murmushi.

Bata yi k'asa a gwiwa ba ta bud'e bakin ta ya zuba mata ciki, lumshe idon ta tayi tare da motsa d'an k'aramin bakin ta, ta fara tsotse wa.

Haka suka cigaba da ba ma junan su cikin kwanciyar hankali suna murmushi.

Sun dauki tsawon lokacin kafin suka gama, kallon ta yayi yana murmushi.

"My Saha,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login