Showing 30001 words to 33000 words out of 107295 words

Chapter 11 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1269

yake yinshi, wanda ita kuma sai take kallon hakan a matsayin gazawa.

Haka dai sukayi wankan su suka gama, har yanzu Salma ta zuba ido taga ta inda Abdul zai fara mata, ta kai matuƙa iya geji, ta tuno da jarumn wani littafi, salon shi da iya aikin shi kaɗai ya isa yaja hankalin mace ta so shi.

Saidai saɓanin yanda Salma ta zata, ko bayan da sukayi addu'a suka kwanta, baya Abdul ya juya mata, baccin shi ya shiga kwasa haiƙan, ya gaji ne sosai, yau kanshi ya ɗauki chaji, aikin kamfani ba kowa bane zai iya aiwatar dashi, saboda ko naira ta ɓace sai an tuhume ka, gashi idan kamfani zata fidda kaya, dole ne kayi tsaye wajen ganin iya adadin kayan da aka fitar.

Juye juye Salma ta dinga yi, wani irin haushin Abdul take kuma ji, ji take kaman ta rufe shi da duka, ji da'allah yanda ya saki baki yana ta sakin numfashi, shi dai ta tabbata ba zai cenza ba kenan? Wai kodai sai ta zaunar dashi ne ta bashi Page ɗin ya karanta da kanshi zai gane yanda gwarazan maza suke tafiyar da matan su a kan shimfiɗa ne? In bashi ba ita ta taɓa ganin namiji mai juya ma mata baya? Ita ko a litattafai ji tayi ana cewa miji rungume matarshi yake suyi bacci,bayan sun gama harka har asuba, wata ma cewa ake da ƙirjin mijinta take matashi ko fillow,bayan sun kwashe tsawon awanni huɗu suna abu ɗaya kenan.

Hannu ta sanya ta fara bubbuga shi. "Abdul Abdul" cikin bacci ya jiyo ta, sai ya tashi zaune yana murtsike idanu, "Menene Salma?"

"Menene fa kake tambaya ta? Kasan dai dukkan mazan da suka amsa sunan su maza, suna cen suna biya ma matansu buƙata ko? Amman gashi kai kazo ka sheme man saman gado kana kwasar baccin ka" Ta faɗa tana mai Zumɓura baki gaba. Bai kula ba, saboda babu haske a ɗakin, saidai yanayin yanda yaji tayi maganar yasan an kusa komawa ruwa.

"Yi haƙuri Salma, na gaji ne sosai wallahi, ki bari bayan sallar asuba"

"Gaskiya a'a, kawai idan ba zakayi ba sai ka faɗa man, ɗan minti ashirin ɗin ma da kake yi gashi yanzu ka gagara"

Maganar tata kam ta bashi mamaki, anya Salman shi ce kuwa? Koda yake ai ba yanzu ne ta fara irin waɗannan abubuwan ba.

"Nidai wallahi na fara gajiya, gara in fito maka a mutum, wannan shine auren fa, idan har ba zaka iya ba, gara ka sauwaƙe mani inje in nemi daidai dani.."

"Subhanallah salma, kanki ɗaya kuwa?" yayi saurin faɗa, yana mai lalubo wayar shi ya kunna ya haske ta. Sai ta kauda fuska tana mai cewa "Ah to ai gaskiya ce"

Shiru ne ya biyo baya, yayin da zuciyar Abdul keta bugawa. Dole ne ya raba Salma da wayar nan, wayar na neman zame mashi bala'i, watau ta fara karance karance kenan irin wanda yake jin labari? Tana haɗuwa da ƙawayen banza, masu tura matan mutane zuwa ga halaka ko?"

Matsawa yayi sosai zuwa kanta. Yana mai tallafo kanta, " Ya Rab Salma, why? Haka kika fi so?" ya jefa mata tambaya.

Gyaɗa mashi kai tayi. Shima sai ya jinjina kai alamun to bari in maki yanda kike so, Amman ba zan kashe kaina ba.

Duk yanda Abdul yayi ƙoƙari yau ga Salma bata yaba ba, bata kuma gode ba, hasalima wancen Hisham ɗin take tunowa. Ana cikin haka ne taji Abdul ya zaren jikinshi daga gareta, ba yanda ta iya, ai sai ta saki kuka sosai, hankalin Abdul yayi mugun tashi, matsalar Salma na neman gagarar shi, ya zaiyi ne wai? Ga matsalar wajen aiki da yau da sukayi lissafi anyi shoi na wajen miliyoyi kuma shi ke da alhakin hakan.

Ga matsalar registration na ƙanen shi maƙudan kuɗi ake nema a hannun shi, wanda mahaifiyar shi ta ƙafe akan lallai sai shine zaiyi mashi, ga kuma matsalar cikin gida ta salma.

Dafe kai yayi sosai kanshi ke juya mashi, ya rasa yanda zaiyi. Miƙewa yayi ya shiga toilet. Yana fitowa bai kula Salma dake ta kukan ƙorafi ba, ita lallai baiyi mata yanda saura kema matan su ba.

Duvet ɗinshi kawai ya ɗauka, yana mai komawa falo, salma ta saba dawowa falo ta kwanta, yau sai ya kwammace ya bar mata ɗakin gabaki ɗaya. Ya fara gajiya sosai da matsaltsalun Salma, zuciyar shi na raya mashi abubuwa da dama, wanda baya san ya ɗauki shawara ko ɗaya daga cikin wanda zuciyar tashi ke bashi, domin yasan hakan ba zaiyi ma Salmar daɗi ba. Saidai ba yadda zaiyi, muddin bata gyara ba, shi kuwa dole ne ya nema ma kanshi mafita, ai yasan lafiyar ta lau, Tunda da ba haka take ba, balle yace ko tana cikin irin matan nan da basa gajiya da ɗa namiji.

Da kyar ya samu bacci ɓarawo ya ɗauke shi, itama Salmar kwanciya tayi tana mai zuzzunɓura baki da ƙunƙuni, ta sare da lamarin Abdul, bata ji idan ya cika cikakken ɗa namiji kyaun da haibar a fili ce, Amman idan aka je other Room fa saidai a hankali, dole ne ta fidda kunya ta tambayi ƙawayen nata, ko kuma tabi marubuciyar *ambaliya* domin taji idan akwai wani siriri da zata bada, wanda itama zata samu irin Abdul ya dinga mata irin yanda Hisham kema matarshi.


*****'

Kaman yanda Ammin tata tace mata, yau tun da safe ta shiga kitchen ta toya masu doya da kwai ɗinɗa Ammin tata tace mata, sai ta haɗa masu shayi mai kyau.

Ammin ce ta leƙa ɗakin nasu ta tadda ta zaune bisa gado, duka hankalin ta na kan wayar tata. Ta fara gajiya da wannan latse latsen wayar na Hunayda, ga karance karance abubuwa marasa ma'ana.

Tsaye tayi tana kallonta, wanda bata ma san tana wajen ba. Ta daɗe kafin ta juya tabar ƙofar ɗakin tana mai girgiza kai. Tana lura da Hunaydan koda ta gama haɗa kalacin, bata wani ci na kirki ba, gashi har Hajna ta shirya zuwa islamiyyar ta safe Amman ita tana zaune.

Tasan yanda Zatayi mata, tasan ta inda zata ɓullo nata, ai in tasan wata batasan wata ba. Sake dawowa tayi, aikuwa ta balbaleta da faɗa, dan dole ta ajiye wayar ta tashi ta fara shiryawa.

Wayar Ammin ta ɗauka domin duba ire iren litattafan da Hunaydan Ke karantawa, wanda ta tabbata Saha ce kan gaba wajen turo mata. Saidai me wayar an kulle ta da pass words, tasan saboda Hajna ne tayi hakan, ajiye wayar tayi tana mai juyawa ta fice daga ɗakin.

Wayar ta ta ɗauko itama bayan ta shiga ɗakin, ta kai zaune bakin gado bayan ta latsa kiran wata number.

"Hello Hajiya Gambo mun tashi lafiya?"

Ɗaya ɓangaren akace "Lafiya Lau Hajiya Hauwa, fatan mun tashi lafiya?"

"Lafiya lau wallahi sai godiya, ya iyali da kuma su Sulaym?"

"Sulaym suna lafiya ai kinsan tana makaranta bata ma kai ga dawowa ba"

"Oh ke duniya, Sulaym fa har ta shiga university fa ko?" cewr Ammi.

Daga cen ɓangaren wadda aka kira da Hajiya Gambo tayi dariya. "Hajiya Hauwa kenan, ince ko kin manta Sulaym taba Hunayda kusan shekara guda? Kin manta lokacin da kika zo sunan Sulaym kina amarya, ba ko cikin Hunayda?"

Dariya Ammi tayi "Ahaf, aifa wallahi na manta shaf, ashe fa Sulaym gaban Hunayda take, Amman yaran nan fa ba wani sanin juna sukayi ba sosai Hajiya, kinga ba zasuyi zumuncin da mu iyayen su mukayi ba"

"Ai laifinki ne Hajiya Hauwa, kece baki barinsu suna zuwa gaida iyayen su, kuma gashi ke bakya kawo su, kullum idan kika zo sai kice suna makaranta, gashi ma sun gama amma har yanzu haka, gara gara ma Hajna yanzu ita ce ke makaranta"

Dariya Ammi ta sake yi, "Insha Allahu ƙawata ki kwantar da hankalinki, yara dai zasu zo yi maki hutu har Katsina, Amman sai Hajna ta samu hutu, yanzu dai ba ma wannan maganar ta sanya na kira ki ba, wai ya rubutu kuwa? Har yanzu kina yi ne?"

"Toh kinji hajiya, Allah na tuba me za'a fasa ne? Har yanzu muna ɗan taɓawa, saidai kinsan yanayin jiki gashi kuma Baban su Sulaym ba cikakkar lafiya ba Shiyasa wani lokaci sai in kwana biyu ban rubuta ba, kinsan yanzu ci gaba yazo, an maida rubutun online, to idan na rubuta na wallafa, sai in samu kuma in maida shi online, inda nan ma kuma akwai masu karantawa"

Itama Ammi ta ɓangaren ta sai ta miƙe, "Yauwa Hajiya Gambo dama gaɓar da nake so azo kenan, dama Hunayda ce ta nace ma karance karancen nan, to kinsan Baban su yana da ra'ayin riƙau, yace makarantar bokon nan dai ta gama, sai idan tayi aure taci gaba, gashi kuma har yanzu Hunaydan dududu nawa take? Shine nake so idan ba damuwa, ki saka ta group ɗin litattafan ki, indai har ƴan mata zasu iya karantawa ba matsala"

"A'ah ba wata matsala insha Allahu, ai nima har Sulaym na karantawa wallahi, kinsan fa Rubutun namu ma ai mun fi so ƴan mata na karantawa, ni bana daga cikin irin Writers ɗin nan na zamani da rubuce rubucen batsa ya rufe masu ido, ke in tabbatar maki ma, gabaki ɗaya ƙungiyarmu bama irin waɗannan rubuce rubucen, abu mai amfani da zai amfani goben yaran mu shi muke rubutawa, yanda zasu kula da kansu, da kuma girke girke da haɗa mayuka da sabullai, sai kuma yanda zasu zauna da kowa lafiya, da kuma rayuwar duniyar nan, sai rayuwar gidan aure da zasu iya fuskanta nan gaba. Kaman yanda bana son rayuwar yarana ta ɓaci, haka ma bana son rayuwar yaron kowa ta ɓaci ta dalili na"

Wannan magana tayi ma Ammi daɗi, saboda haka ne tayi ma ƙawarta godiya, haɗi da Sallamar cewa lallai ta saka Hunayda cikin wannan group na Hajiya Gambo. Tasan Hajiya Gambo tsohuwar marubuciya ce, hasalima tana daga cikin marubutan da suka amshi kambun girmamawa ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, haka kuma tana wakiltar manyan marubuta, zuwa taron ƙara ma juna sani da kuma haɓɓaka Rubutun zube, da adabin baka.

Tana ajiye wayar Hunayda ta shigo ɗakin sanye da kayan islamiyya.

"Ammi na shirya zan wuce, Hajna tayi tafiyar ta ta barni"

Ammin ce ta haɗe fuska tamau, "to ba dole tayi tafiyar ta ba? Kin tsaya caccakar waya, kuma bayan kinsan da zuwa makarantar? Sai ki tafi, Allah ma yasa malamin ku ya zane ki, gobe ai ba kin ƙara ba"

Haka Hunayda ta fito jikin ta duk a sanyaye, bata so take ɓata ma Ammin tata rai, ta sani sarai Amminta tsaye take kan su, da tarbiyyarsu, to saidai Page ɗin da Saha ta turo mata ne jiya ya tsumata sosai, Page ɗinɗa har wanka saida yaja mata tayi cikin dare, duk da hakan bata ji ta gamsu ba, saida ta buɗe video ɗinɗa Sahar ta sake turo mata jiya, wanda ita har yanzu ma dai ta rasa inda take samo su wlh, bata so take kallo, Amman idan suna fira da Sahar kan ƙara jan hankalinta zuwa ga kallo da karantawar. Ta sani sarai yau Sahar ba zata je islamiyya ba, wai suna da biki, inda ta ɗan guntsa mata cewa zata haɗe da Zaiyad mutumen nata, duk yanda sukayi zata zo ta bata labari. Hankalin Hunaydan kan ƙara tashi, ita dai ko da wasa wallahi ba zata iya aikata abunda Saha ke aikatawa ba, tana tsoron Amminta da Abban ta, saboda haka ne ta sake ɗaga ƙafa har bakin makarantar.

Daga nesa ta hango shi yana taron makara. Malam Suhail ne, saboda haka sai duk taji ba daɗi, Tunda ya furta mata kalmar so, sai take takura a gaban shi, tana hango Hajna daga cikin makaranta tana mata dariya, ta raya a ranta cewa ko ranƙwashi ɗaya ne sai ta bata idan suka koma gida.

Yanda yayi ma kowa bulala uku a hannu haka itama yayi mata, saidai ya sassauta mata wajen bugawa da ƙarfi. Yanayi yana tsare ta da kallon tuhuma, na cewa kullum ita sai ta makara, saidai ta sauke kanta ƙasa kawai tana mai shigewa islamiyyar. Tana jin kunya da nauyin shi, saidai bata so ta bari sonshi ya kamata, kaman yanda Saha ke faɗa mata cewa tafi ƙarfin malamin islamiyya.

A cikin ranta kuwa rayawa take yi cewa, lallai bakin iyaye abu ne daya kamata kowa ace ya guje shi, gashi dai Ammin tata cikin ɓacin rai ta mata addu'ar a doketan, kuma gashi yabi ta, saida akayi mata bulala uku a hannu, duk da tasan har cikin zuciyar Ummin ba Zataso ace an doke ta ba.



Yau ma dai saida Malam Suhail ɗin ya biyo ta, yana mai jaddada mata cewa baya so ne yake tsayawa da ita a waje haka kan hanya, saboda haka ta bashi damar ya tura gidan nasu, ga mamakin ta, maimakon ma taji ya bata haushi kaman yanda ya doke ta ɗazu, sai yayi mata kwarjini sosai a fuska, Gaza mu santa mashi tayi, tunda ma yau Saha bata nan, kawai sai ta amsa mashi, tana mai ce mashi kada yace da saninta aka je gidan nasu,

Dariya yayi, ya kula akwai ƙuruciya sosai da wauta a cikin al'amarn ta, duk dai da haka shi yaji ya amince, indai zata aure shi da zuciya ɗaya, insha Allahu shikam babu abunda zai hana shi auren ta.

Yayinda ita kuma take rayawa a ranta cewa idan Saha taji ko ya zata ce? Gaskiya koma dai me zata ce gara tace, Amman ita ta gaji da ƴan matse matse da ulƴan kalla ce kallace, gara kawai taje tayi mai digi, wanda har lada sai ta samu, kuma gashi tayi sa'a malam Suhail ɗin nata akwai tarin sani da ilimi a cikin kanshi, ta fanni guda kuma gashi ɗan gayu, wanda zamu iya cewa idan da halin yaran zamani gareshi, toh fa da babu abunda zai kaishi makarantar islamiyya koyarwa, zai ga ne ai kaman yafi ƙarfin hakan.



*******



Taji daɗin yanda Ummin tata take shaida mata akan cewa ta kula da su Surayya da Na'eef, ita ba zata samu damar zuwa ba, kuma dama bikin dangin baban nata ne, wanda dama ta sani da wuya Ammin taje, kayansu suka haɗa akwati guda, duk da cikin gari ne inda ake bikin, saidai Ummin tace ba zata lamunci kai komi ba, har zuwa kwana biyu da za'ayi ana shagalin bikin.


Haka ta basu kuɗin a Bus, wadda zata kaisu har ƙofar gida, jama Sahabat ɗin kunne Ummi tayi sosai, duk da tasan cewa Sahabat ɗin dai akwai ɗan rashin ji, saidai ta tabbata bata kula kowa, balle ma samari, wanda ko wayar har yanzu ta ƙi barinta ta riƙe, to yanda duniyar social network ɗin nan ma ke cike da ƙalubale iri iri yaushe zata bar ɗiyar ta ta shige ta? Ai saidai idan tayi aure, wannan kam zata iya bari, Amman ita kanta tasan irin rubuce rubucen da take yi, ko ƴaƴan ƙannenta bata so su kasance suna karantawa, na daga cikin dalilin ta na cenza suna kenan daga Maryam zuwa Hibba.

Bakin tanƙamemen gidan Mai Bus ɗin ya ajiye su, zuciyar Sahabat wanke tas, wanda tun da sanyin safiya dama tayi ma Zaiyad text akan cewa yau fa zasu haɗu, dan haka sai yayi mata shiri mai kyau, jiya kwana suka yi a waya yana mata ƴan abubuwa, wanda har saida ya sanya ta fidda kayan nata, yana ce mata ta ayyano shi yana kusa da ita, subhanallah, abubuwa dai iri iri, saidai ta shige toilet, domin sai zuciyar ta ke raya mata ko Surayyan ba bacci take ba tana sauraren ta.


Ƴan uwan baban su sunyi murna da zuwan su, sai suke tuna masu da ɗan uwansu marigayi, dama kuma gashi Ummin ba barinsu take zuwa ko ina ba, sai in irin hakan ta tashi, ita duk a tunanin ta zatayi ma Allah wayau ne.


Yau kam sai Allah, domin tun da sanyin marece aka fara shirin kai amarya ɗakin ta bayan an ɗaura aure, inda daga cen ne za'a kwashi mutane aje wajen dinner.

Sahabat na gaba gaba, duk da ƙawayen amaryar sun fita a shekaru, saidai ba zasu nuna mata raɓar jiki ba, kusan ma zamu iya cewa tafi wasu da dama cikin ƙawayen cika da haɓɓaka. Hakan take kuma a ɓangare guda tun ɗazu Zaiyad keyo mata wayan cewa ta kwatanta mashi wajen da ake dinner ɗin.

Aikuwa ba shayin komai ta kwatanta mashi.

Ihun murna ya saki, lokacin da text ɗin ya shigo, ya hararo cewa yau akwai shan gara, dole ne ya huce gajiya da tarin buƙatun shi akan yarinyar, masalan ma da yaga cewa ya shawo kanta da sauri, har alƙawarin kwatanta mashi abunda ya tura mata jiya a waya tayi.

Ankai amarya lafiya, bayan isha'i ne aka fara shirin tafiya dinner, dama ba kowa zai je ba, kuma gashi ita ta shige cikin ƙawayen amarya, inda har anko ma duk Ummi tayi mata, a cewarta kada ace ta raba zumuncin dake tsakani.


Babban Hotel ne daya amsa sunanshi kaf faɗin garin na Kaduna, an ƙawata wurin sosai da kayan ado da manyan speakers na kiɗa.

Zaiyad da tun ɗazu ya isa, a waya ya kira Saha, sai gata ta fita domin shiga dashi wurin. Maimakon ya bita, saima jan hannun ta yayi zuwa bayan motocin da suke fake a wajen.

"Menene haka Sweet heart? Kada fa wani ya gammu" ta faɗa cikin ɗan zaro idanu, lokaci guda tana yi tana waige waige.

"Is ok my Habat!, babu wanda zai gammu nan we are safe"

Ɗan girgiza mashi kanta tayi, har yanzu hannuwan ta suna cikin nashi, ya tallafo gefen ƙugun nata ɗaya da hannun shi ɗaya zuwa cikin jikin nashi.

Jikin ta na gogar nashi jiki, har yanzu kyarma take yi, bata so a samu matsala, masalan ma da bikin yake na dangin mahaifin ta.

Lura da hakan ne da yayi, ya sanya shi buɗe motar tashi back seat ya saka ta shima ya shige, sai a lokacin ne ta saki ajiyar zuciya, tana mai kai kanta saman kafaɗar shi, ba tare data san tayi hakan ba.

Shi kuwa daɗi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login