Showing 9001 words to 12000 words out of 107295 words
Chapter 4 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
na Mutawassiɗa na isalamiya, haka shi ma Hamza yayi nashi karatun, kasancewar ba wani karutun boko suke yi ba yasa suka aurar da Maryam tun tana shekara goma sha takwas.
Hamza ya gina musu ɗan madaidaicin gidan su, a Kurmin Mashi, wanda ba wani nisa sosai a tsakin unguwar da su. Ana ɗaura aure aka kawo amarya gidan mijin ta. Zaman mutunta juna da girmamawa suke yi, har Allah ya bata cikin Hunayda.
An haifi Hunayda da shekara ukku da rabi aka haife Hajna, wanda a yanzun shekarun Hunayda goma sha bakwai kenan.
Hunayda mai kyau ce, ita ba mai qiba ba ita ba siririya ba, tana da zati dai-dai ƙirarta, sannan tana da haske ba irin mai yawan nan ba, daidai-daidai.
Hunayda yarinya ce mai shauƙi,(Wacce abubuwa ke saurin birgesu), amma tana da tsoro,tana da rauni sosai da shagala.
Haɗuwar su da Saha ya samo asali ne sakamakon burgeta da take yi, tana sha'awar yadda take rayuwarta, yadda take kwalliya, shiga da dai makamanta su, tana son yin wasu abubuwan amma tsoro ke hana t, tana son soyayya da labarin soyayya, wanan dalilin yasa tayi ƙokari a karatun ta na candy, dan samon waya, domin mahaifin ta Hamza(Abba) yace sai ta kammala candy zai bata waya, Hakan kuwa ta faru, tana gamawa ya siyo mata waya sabuwa Camon 12, yanzun watan su ɗaya da kammala candy.
Hunayda taji daɗin samun wayar nan, haka ma Aminiyarta Saha, ita ke turo mata littafai ta WhatsApp.
Primary daban suka yi, a candy ne suka haɗu, Gombe International school, a nan suka haɗu, sannan kuma islamiyar su ɗaya, kasancewar makarantar haɗe da isalamiya ne.
Wanan kenan akan Labarin rayuwar Hunayda.
********************
Bayan ya fito daga toilet ya saka kaya mara nauyi a jikin shi sannan ya fito, har zai shiga ɗakin yaran inda yake jin surutun ta, sai kuma ya fasa ya nufi kicin, haka nan ya ɗaura indomie ɗin dan yunwar da yake ji. Cikin ƙanƙanin lokaci ya gama dafawa ya fito, a falo ya ganta tana danna waya, xama yayi kan kujerar dake fuskan tata bai ce mata komai ba ya fara cin abincin shi.
Ƙamshin turaren da taji ne yasa ta tabbatar ya shigo falon, lumshe ido tayi domin tana bala'in son ƙamshin turaren shi, tsaki tayi a ran ta ce;
"Idan ka ganshi ka ɗauka wani jarumin namiji ne, ga kwarjini amma na banza, tirr! da miji irin ka, ni dai ban yi sa'ar miji ba".
Bayan ya gama cin abincin ya tashi ya maida kwanan kicin yasha ruwa sanan ya dawo kusa da ita ya zauna.
Cikin marairaicewa ya ce,"Salma! kin san ganin fushin ki yadda yake wahalar da zuciyata kuwa? Pls ki tausayamin Matata, ki tausayawa mijin ki, ki daina wannan fushin, idan kuma wani laifi nayi miki ki gayamin, zan gyara kuma na baki hakuri da hannu biyukin ji?!".
Ya ƙarasa maganar cikin sigar naiman yafiya.
Wani uban tsaƙi taja a ranta, "Wai zaka gyara, tayaya?, haka kake ba zaka taɓa canzawa ba, ni da lafiyata haka kawai ka ɗinga ƙwarata".
"Dan Allah!".
Katse mata tunanin da take yi yayi, kallon wulaƙanci tayi mishi sannan ta ce;
"Ni ba komai ka ƙyale ni plss, ni ban san takura da naci haba!", ta faɗa tare da turo baki.
"Ban yarda ba, akwai wani abu, ki gayamin, wanan fushin ba lafiya ba".
"To ai sai kayi". Tashi tayi tabar gurin.
Dafe kanshi yayi wanda yake jin yana sara mishi, a hankali a hankali zuciyar ta fara mishi zafi, "Meke faruwa ne?!".
"Taya zata ce min ba komai, bayan akwai wani abun? Taya take ganin zan jurewa fushin ta akai ta na *MENENE* *RIBA* *TA ??* anan na ganin fushin ta?".
Tashi yayi ya bita ɗakin, yana zuwa ya ganta a kwance har lokacin wayar na hannunta, yana kwanciya kan gadon ta tashi.
Tsaki tayi, "Mtseeww! ni wllh naci ne ban so, da takura, haba mutum kamar maye, duk inda nayi ka biyo ni kamar bindi!". Ta tashi ta fita tana tsaki.
Kallon tsoro ya bita da shi, dan lamarin yanzun tsoro ya bashi, dan tunda yake da Salma bata taɓa yi mishi magana cikin rashin kunya irin haka ba, balle tsaki.
"Anya kuwa ba Aljannai ba ne suka taɓa ta!?".
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷♀
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
*~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~*
*~We are bearier's of so golden pen~*🖊
*~We write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
https://www.facebook.com/groups/156937942662161
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN.*~👇...... ✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say:
"The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire."
[Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي)
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Two_
~*Page 5*~
Cike da tunanin abinda ke damun Salma Abdulkareem ya kwanta, dan har ya fara tunanin ko bata da lafiya ne, dan bai taɓa tunanin makamancin irin wannan saɓanin zai shiga tsakanin su da Salma ba, ko a mafarki bai yi ba.A haka cike da ɓacin rai bacci ya ɗauke shi.
Kiran Sallar asubar farko a kunnen Abdulkarim, yana ji ya tashi daman baccin ya gundure shi, gefen gadon ya duba, wayam ba Salma, saɓanin yadda ya saba ganinta, idan bata jikin shi tana gefe, guntun tsaki yaja mai cike da ban haushi.
Ɗakin yaran ya nufa a hankali ya buɗe kofar ya shiga, kwance ya ganta a tsakiyar yaran tana baccinta hankali kwance, ɗan murmushi yayi wanda bai kai zuci ba ya ce, "Allah ya baki lafiya Salma, idan wani abun ne yake damun ki, Allah yai miki maganin shi yasa ki gane gaskiya".
Ya daɗe a tsaye yana kallon su, sai da yaji an kira sallah na biyu sannan ya juya ya tafi masallaci.
Bayan ya dawo zai shige ɗakin su yaji motsin ta alamar ta tashi, murmushi yayi na taikaici, "wato shi kaɗai ta canja mawa, komai na halaiyarta yana nan".
Ɗakin ya shiga ya fara shiri dan yau da wuri yake so ya fita, yana jin ta ita da yara suna ta hayaniyan su cikin walwala.
Salma kuwa yana fita ɗaga ɗakin ta tashi dan yin sallah, abin yabi jikin ta, ana kiran sallah take tashi, ranta fes ta tashi tayi sallah sai dai tana tuno shi a ranta zata yi tsani cikin takaici.
Bayan ta idar ta shiga kicin, indomie kawai ta dafa ma yara ita kuma ta dafa lipton ta soya ƙwai.
Abdulkarim yana jin su ita da yara tana shirya su, bayan sun gama shirin makaranta su ka fito falo.
Shi ma fitowan yayi da shirin shi na office, su Husna na ganin shi suka rugo suka rungume shi.
"Ina kwana Abba?"
"lafiya lau kun tashi lafiya?"
Falon ya ƙarasa ya zauna ya ɗau Mussadiq yana mishi wasa.
Ta gefen ido ta kalle shi tare da da kintsa fuskan ta sannan a hankali ta furta
"Ina k'wana."
Har ranshi baiji dad'in yanda tayi ba ammaya waske tare da qaqalo murmushi cike da kulawa ya dube ta.
"Lafiya lau Madam, dafatan kin tashi lafiya?".
Ya faɗa yana kallon ta,
ciki-ciki ta amsa da.
"lafiya lau."
"Ina breskfast ɗina?".
"Banyi da kai ba".
Ta amsa a takaice tana kallon gefe. Kallonta yayi na yan dakiku kafin ya gyada kai.
"Ok sai na dawo".
Ya faɗa tare da miƙewa ya fita.
Su Husna har ƙofa suka raka shi.
*ASALIN SU.*
Salma Ɗahiru Bala, shi ne cikakken sunan Salma, ƴar wani ƙauye ne dake yankin Kaduna ta yamma. Buruku ƙaramin gari ne, zaman lafiya da son juna shi ne ɗabi'ar mazaunan Buruku. Garin Buruku basu da wadataccen makarantun islamiya da na zamani, su kansu mutanan garin basu son karatun haka suke rayuwa tsangangan, sai ka ga babban mutu ko matashi amma bazai iya rubuta koda sunan shi ba, haka ta ɓangaren islamiya sun fi ba makarantar allo muhimmanci.
Mahaifin Salma Ɗahiru Bala, mutum ne mai son ilimi a rayuwar shi, kasancewar shi bai yiba yasha alwashin yaran shi sai sunyi. Babban ɗan shi namiji wanda ya fara ɗaura burin akan shi, sai Allah yasa shi baya son karatun ko kaɗan, Ɗahiru yayi-yayi da shi har ya haƙura, sai mace mai bi mishi ita ma dai Ɗahiru baiyi ƙasa a gwiwa ba gurin ganin tayi karutu, nan ma abin yaƙi domin ita rayuwar bariki ta ɗaukar wa kanta, haka nan ya ƙara hukuri ya ɗau kaddara har ya cire rai akan burin shi da kudurin shi na son ganin yaran shi sun yi karatu.
Salma ita ce ta uku a gurin iyayenta.Yarinya ce mai fasaha da basira, ga saurin ɗaukar abu, tun tana ƙarama take ba mutane mamaki dan duk abinda akayi a gabanta komai wuyar shi zata ɗauka.
Ɗahiru ya fahimce hakan daga ƙareta saidai bai damu ba dan sauran ma haka suka taso da fasaha da kaifin kwakwalwa, duk da kasancewar tafi su.
Salma tana da shekara goma wata ƙanwar mamanta taje da ita cikin garin kaduna, anan Salma taga yara na zuwa makaranta, sai son karatu ya shiga ranta. Suna dawowa kuwa taje ta samu baban ta maganar tana son ya sakata makaranta, wai ranar kamar Dahiru ya zuba ruwa a ƙasa ya sha dan murna da jin daɗi, tun a ranar yakai ta makarantar primaryn garin, aji ɗaya suka saka ta ganin ta ɗan girma.
Salma kuwa ga son karatun gashi guru wa ce by nature, sai abin ya fara ba malaman mamaki jin abinda ake yiwa ƴan aji ukku Salma ta iya, ana koyar da su arabic a makarantar, ganin kaifin basiri irin na Salma yasa malaman suka kai ta aji huɗu.
Ɗahiru kuwa yayi farin ciki ya kuma godewa Allah.
Shekara huɗu da shigar Salma primary ta gama, nan Ɗahiru ya fara tunanin saka ta candy, Malaman suka bashi shawara da ya kai ta cikin garin Kaduna ta cigaba a can, dan na nan ɗin ba wani koyarwa sosai.
Ɗahiru yana da yaya a cikin garin kaduna unguwar Sunusi, shi da kan shi yakai ta ya damƙa musu amana.
Haruna shi ne yayan Ɗahiru uwa kawai suka haɗa da shi.Haruna ɗan kwangila ne yana da shi dai-dai gwargwado, mutum ne mai son mutane da mutunta su.
Yaji daɗin zuwan Salma gurin shi dan yana son ɗan uwan shi,gashi daman yaran shi huɗu mata duk sunyi aure.
Maryam matarshi ita har tafi shi jin daɗi da zuwan Salma dan Salma tana da shiga rai.
Ba ɓata lokaci suka kai Salma makaranta haɗe da islamiya da bokon ma.
Salma kuwa ta maida hankali sosai gurin karatun ta, sannan tana jin daɗin zama da su domin tamkar ƴar cikin su suka ɗauke ta, duk lokacinda suka samip hutu tana zuwa gida gurin iyayen ta.
Cikin shekara uku Salma ta haddace izufi arba'in da biyar na al-qur'ani.
Lokacin tana ta gama ji uku na candy.Mahaifin ta yaji daɗi matuƙa sanan ya godewa Haruna.
Salma yarinya ce mai natsuwa ga hankali da zurfin tunani, ga riƙo da addini, way'annan halayen nata suke sa duk wanda ya zauna da ita sai ya ƙaunace ta.
Tana da kyau dai-dai misali, irin manyan kyawun nan gareta, gata fara da yalwataccen gashin kai dana ido.Salma na da tsabta sosai komai nata acan-acan.
Wata rana tana tafiya cikin shigar kayan makarantarta, hijabi ne ruwan madara sai wandon pink, cikin natsuwa take tafiya.
Tun daga nesa Abdulkarim ya hangota, yanayin yadda take tafiya cikin natsuwa shi ya fara gani, sannan ya fita daga cikin motorshi.
Yana kallon ta har ta samu abin hawa ta hau, bin su ya dinga yi har suka isa unguwar su, ta ba mai mashin ɗin kuɗin shi sannan ta ƙarasa, duk yana biye da ita bata sani ba, tafiya ƙatan tayi ta isa gidan su, yana ganin ta shiga gidan yayi parking, ya daɗe ganin ko zata ƙara fitowa da ya tabbatar gidan su ne, ya juya, cike da tunanin ta dan tun daga kallo ɗaya ta tafi da shi.
Abdulkarim Khalil Yahaya shi ne cikakken sunan Abdulkareem, mazauna garin Kaduna ne a unguwar Mu'azu, anan aka haife shi kuma nan ne iyayen shi ke da zama.
Shi ne Auta gurin iyayen shi yayyan shi duk mata ne su biyu,shi ma su ukku ne a ɗakin su.Yaro ne matashi mai jini a jika,kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar da hakan.
Domin iyayen shi nada shi,a kamfanin baban shi yake aiki.
Ga nutsuwa shi ma yasha addini ya ƙoshi domin ita Kaduna garin addini ce indai kana son yin ilimi zaka yishi,tamkar a misra,ga boko ga addini duk Abdukareem ya haɗa su shiyasa yake da gwarjini kamar zaki ga kyau,ga gata baya da matsalar komai a rayuwar shi.
Kai tsaye gida ya nufa. Dama iyayen shi basu da burin da ya wuce ace Abdukareem yayi aure, sun mishi maganar ya ce bai samu wacce yake son ya aura ba ne, mahaifiyar shi Hafsa har ƴan mata take kawo mishi amma yace basu yi ba.
Yana zuwa ya sanar da ita yaga wacce tayi mishi, sai farin ciki, kasa haƙuri mahaifin shi ya dawo gida suka yi,sai da suka kira shi suka sanar mishi.
Abdul