Showing 57001 words to 60000 words out of 107295 words

Chapter 20 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1271

walwala saboda komai tana yi ne ba tare da shayi ko shakkar wani ya ganta ba amma da kullum cikin tsoro take da fargaba.

Ammie kuwa Hunayda na fita tayi murmushi me cike da farin ciki, tun ba yanzu ta fahimci Hunayda tana cikin masu son ƙalƙali da kuma sha'awar kayan ado hakan shine ya kusa jefa ta a halaka.

Sai dai yanzu Alhamdulillahi ta fahimci yarinyar tayi hankali sosai, ita kuma tayi alƙawarin indai ta lura da wani abu daya birge Hunaydar to zata yi ƙoƙari ganin ta mallaka mata kalar wannan abin koda be kai wancan ba.

(To ƴan uwa sai ki lura wace kalar ƴa ko ɗa Allah ya baki idan har me zara ne sai kiyi ƙoƙarin ganin kin wadata shi ko kin wadata ta da abinda take buƙata ko yake buƙata gudun gurɓataccen aboki yazo ya janye miki shi ko gurɓatacciyar ƙawa tazo ta janye miki ita Allah yasa mu dace).

*************

Yau daren Juma'a Sahabat dake kwance tayi wani juyi cike da shiga wani yanayi mara misaltuwa, ta maida kallon ta kan Surayya dake faman barci hankali kwance taja tsaki.

Wayar ta dake hannun ta ta sake matso da ita tana me cigaba da karanta littafin da mahaifiyar ta ke karanta wai shi *RAYUWAR BARIKI* har yaso ya ɗara *NI DA SHI* don wannan ma na kuɗi ne kuma tana ɗaya daga cikin wacce ta biya har nera dubu ɗaya ta siya amma Ummin bata gane ta ba domin kuwa kati ta tura ba VTU ba hakan yasa Ummin bata gane ta ba.

Sosai littafin yake hargitsa duk wata ko wani me rai da lafiya, hannu tasa ta shafi ƙirjin ta jin ta kawai take wani iri.

Da ƙyar ta iya ƙarasa page ɗaya, ɗayan kuma tace ssi gobe idan taje wajen sweethert ɗin ta.

Lamo ta kwanta ta ɗora hannun ta saman marar ta, wani irin ciwo take mata gashi maganin ciwon yayi mata nisa.

Miƙewa tayi ta shige bayi da sauri, ta kunna wutar bayin sannan jiki na rawa ta hau kiran shi.

"My Habat ya akayi ne na jiki a irin wannan lokacin?", ya tambaye ta dan yau basu jima ba ta kashe datar ta saboda littafin da Ummi ta saki,shi kuma hakan dama ya bashi domin kuwa ya sami wata chicks ɗin yana ƙoƙarin tsara ta ne.

Habat tace; "Sweetheart ba zan iya barci ba shine na kira ka ko akwai abinda zaka yi mini".

Yace; "ok to yanzu ki buɗe datar ki zan kira ki", ta amsa da to tana me katse wayar, tana kunna datar ko minti uku bata yi ba kiran shi ya shigo.

Ta ɗaga suna kallon juna don video call ne, ganin yadda idanun ta yayi ja sai ta bashi tausayi domin shi yasan Sahar tana daga cikin mutane masu tsananin sha'awa.

"Yanzu ki miƙe ki cire kayan ki", babu musu ta miƙe ta cire kayan tsaf, yana daga kwancen ta kafa mata idanu.

Kullum sukan kasance tare in dai ta sami fitowa amma har yanzu be ji ta ishe shi ba, lallai yarinyar tana da zaƙi da yawa🙈.

Hannu yasa saman marar shi yana me shafawa yana lumshe idanu, don ganin da yayi mata haka ba ƙaramin tayar mishi da hankali yayi ba.

A haka ya dinga faɗa mata magan-ganu wa'inda wani har sata yake tana yi,wai ta dinga assuming shine ke yi mata.

Ta haka ya samu damar biyawa kan shi buƙata itama ya biya mata, nan suka yi sallama cike da kewar juna sannan ta katse kiran.

Hakan nan ta kunna famfo ta tara ruwa tayi wanka dan hakan shine rufin asirin ta, ga ruwan me sanyi amma gudun abinda zai je ya dawo yasa tayi wankan a haka ta maida kayan ta sannan ta zo ta kwanta.







~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



© *2020*



_~We Love U All~_❤
🤷‍♀🤷‍♀🤷


*_MENENE RIBA TA ❓_*

🙆🙆🙆


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_


~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍

♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*

♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._

On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:

"Allah (mighty and sublime be He) said:

'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'"

[Bukhari (also by Muslim).]

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ .


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



♣ _Scene Five_

~*Page 18*~


Hunayda ke gaba inda Hajna ke bayan ta, duka suna sanye da dogon hijab me hannu kalar Uniform duk suma sauran ɗaliban da suka fito daga makarantar kalar hijab ɗin dake jikin su kenan.

Gaban Hunayda ya faɗi ganin Sahabat tsayr gaban mota, inda na ciki kuma ya zuro hannu ya riƙe mata nata hannun, ita kuma sai murmushi take yi.

Kasa motsi tayi tana mamakin rayuwar da Sahabat ɗin ta ɗaukarwa kanta, Sahabat kuwa sai da suka yi sallama sannan ɗagowar da zata yi sai akan fuskar Hunayda.

Duk da gaban ta ya faɗi amma sai ta ɗaure fuska ganin kallon da Hunaydar ke jefa mata, Hunayda kuwa kallon mamaki, tsana da kuma jimami duka shi take bin Sahabat dashi.

Amma duk da haka ta ƙudiri aniyar yi mata nasiha ko zata ji ta dena, dan haka cikin sauri ta ƙarasa kusa da ita da niyar magana amma abin ban haushi Sahabat data lura da Hunaydar magana take son yi mata sai tayi saurin wuce ta.

Hunayda tabi bayan Sahabat da kallo, tana ƙara jinjina halin da ƙawar tata ta jefa kanta me wuyar fita.

Taja doguwar ajiyar zuciya sannan ta ja Hajna suka wuce jikin ta a sanyaye.

Koda suka isa gida sai da Ammi ta lura da canzawar tata, har sai da ta kai ga Ammin ta tambaye ta amma tace mata babu komai.

Dole Ammi ta haƙura domin kuwa bata so tana takura mata dan yaran yanzu sai Allah kawai.

Suna zaune suna cin abinci Hajna tace; "Ammi kin san meya faru yau kuwa?", Ammi tace; "a'a auta sai kin faɗa mini".

Hajna ta kalli Hunayda wacce ke cin abinci a sanyaye domin duk cikin minti ɗaya sai abinda Sahabat tayi ya dawo mata ƙwaƙwalwa.

Hajna tace: "yau munga Aunty Saha ta fito daga wata mota kuma na ciki har riƙe mata hannu yayi, sannan ko makaranta bata zo ba sai da aka tashi sannan motar ta ajiye........", bata sami damar ƙarasawa ba domin wani dundu da Hunayda ta sakar mata a baya.

Babu shiri Hajnar ta ƙwalla ƙara sannan tari ya biyo baya domin dukan ya shige ta, ita kanta Hunaydar bata san lokacin data yi mata wannan aika-aikar ba.

Ammi ta dakawa Hunayda tsawa; "Baki da hankali ne? Wannan wane irin duka ne ko kema irin abinda Sahabat ɗin take aikatawa kike aikatawa kina tsoron ta tona miki asiri yasa kika mata wannan dukan?".

Hunayda ta girgiza kai, idanun ta kamar zai kawo ruwa, Ammi ta kuma daka mata tsawa; "dalla tashi ki bawa mutane waje kina girma kina rashin hankali", cikin sauri Hunaydar ta miƙe ta bar wajen ƙwalla na zubo mata.

Tana zuwa ɗaki ta fashe da kuka wanda ita kanta bata san takamai-mai ta meye ba, shin na faɗan da Ammi tayi mata ne?, na zargin da Ammi ta jefa a kanta ne?, tausayin dundun da ta yiwa ƙanwarta ne ko kuwa tausayin halin da ƙawar ta ke ciki ne?".

Nace; "kya tambaye ni Hunayda taya zan sani ni kuwa🙄.

Sahabat kuwa tana ɓacewa ganin Hunaydar taja tsaki tana faɗin; "aikin banza yarinya ƙarama sai iyayi", haka taje ajin su Na'eef sannan ajin su Surayya.

Kamar koda wane lokaci Ummi na zaune da waya a hannun ta, Sahabat ta kuma jan tsaki tana faɗin; "wallahi Ummi wata rana sai an sace ta hankalin ta na kan waya bata sani ba".

Sahar ce ta share gidan, sannan tayi alwala din yin sallah, tana idar da sallar ta fito don ta ɗorawa ƙannen nata ruwa, Ummi har tayi sallah ta dawo ta zauna.

Tsabar haushi Sahar ko kallon ta bata yi ba ta wuce, Ummi tace; "Saha ɗan zubo mini abinci mana", sai da ta turo baki sannan ta amsa da to.

Sai da ruwan yayi zafi sannan tace; "Surayya ki fara yiwa Na'eef sai kema kiyi kinji, ki maida mini nawa idan kin juye", Surayyar ta amsa da to.

Tana shiga ɗaki wayar ta fara vibrating, cikin sauri ta zaro ta daga ƙaramin wandon da take sakawa a jikin ta me aljihu.

"My Habat na kira ne naji ya kika je gida?", ya faɗa in cool voice.

Tace; "lafoya lau nazo gida sai dai kewarka da nake yi".

"ɗazu fa muka rabu, kuma gobe zamu sake haɗuwa", ya sake bata amsa, tace; "umm hakane amma aini ko kwana zamu yi tare ba zan gaji da kai ba".

Yayi wata ƴar iskar dariya irin ta ƴan duniya sannan yace; "nima ai ba zan taɓa gajiya dake ba kin san irin son da nake yi miki kuwa?".

jin alamar tahowa yasa tayi saurin katse wayar ta maida cikin wandon, Surayya data shigo ta kalle ta sannan tace; "ruwan ki yayi zafi".

Batace komai ba ta fice, Surayya ta girgiza kai tana neman shiriya ga ƴar uwar tata dan alamu ya nuna bata jin kira yanzun.

******** *******

Hunayda ta tashi ta ɗora alwala domin yin sallah, Hajna kuwa na saman gado tana kwance.

Bayan ta shigo itama Ammi ta shigo, Hunayda dake riƙe da Sallaya tayi saurin saukar da kanta ƙasa.

"Ammi na bata haƙuri tun ɗazu", Ammie tayi murmushi tace; "kada ki damu ai ya wuce kinji", Hunayda tayi ajiyar zuciya.

"yanzu kiyi sallar sai ki kwanta kuyi barci sai da safe", tana gama faɗin hakan ta fice daga ɗakin.

Hunayda ta tada kabbarar sallar isha'i wacce bata yi ba saboda halin da take ciki, tana idarwa ta ɗora da shafa'i sannan tayiwa ƙawarta addu'a akan Allah ya shirye ta.

Sai da tayi Addu'a ta shafe jikin ta sannan ta nemi waje ta kwanta, tana me kara neman tsari Allah akan duk wani abinda zai cutar da ita ko ƴar uwar ta.

Sai tsakiyar dare sannan ta tashi, sai da tayi murmushi tunawa da Malam Suhayl domin shiya saba mata da tashi wannan lokacin.

Haka ta janyo wayar ta cike da hope ta sake dannawa number ɗin shi kira sai dai kamar koda wane lokaci is not reachable.

Haka ta miƙe jiki a sanyaye ta nufi bayi ta ɗoro Alwala tazo ta tada kabbara, raka'o'i guda biyu tayi kamar yadda manzon Allah(S.A.W) ya faɗa; "Idan ɗayan ku ya tashi da daddare to ya buɗe sallar sa da raka'o'i guda biyu sauƙaƙa", Muslim ya ruwaito.

Haka ta buɗe Alqur'ani me girma ta fara karantawa cikin natsuwa da fitar sauti me daɗi wanda ke ratsa zuciya da gangar jiki baki ɗaya.

Ammie dake ɗakin ta itama tana nata ibadar sai da ta ɗaga hannu ta kuma godiya ga Allah akan shiryartar mata da yarinya da yayi tana me kuma jinjinawa mutanen da suka taimaka wajen faruwar haka.

Sai da aka kusan kiran sallar asuba sannan ta tashi ta kawo raka'a ɗaya wato witri tana zaune tana istigfari aka fara kiraye-kirayen sallah dan haka ta miƙe taje ta tada Hajna akan ta tashi sannan ta koma ta tada raka'atanil fajr.

Tana idar da sallar asuba ta kuma cigaba da karatunta har zuwa shida sannan ta miƙe ita da Hajna suka fita domin aikin gida wanda har Ammi ta fito itama.

Sai da suka gaishe ta sannan Hunayda ta fara ƙoƙarin ɗora ruwa, Hajna kuma ta fara shara suna dai ƙoƙarin taimakawa mahaifiyar tasu.



************

Jameela ta ƙara damƙe hannun Husna tace; "kada ku damu ku shiga ciki wajen Mama yanzu zan shigo nima kunji", babu musu Husna ta rike hannun Musaddiq suka yi cikin gida domin sun san gidan dan suna zuwa da Abban su sannan sun ɗan saba da mahaifiyar Jameelar.

Jameela ta kai kallon ta wajen Abdul tace; "gini yayi kyau Allah ya saka da alkhairi ya ƙara buɗi, komai yayi dai-dai".

Rabon da ya samu irin wannan godiyar da addu'ar har ya manta amma yau gashi ya samu a bakin wata wacce ma be kai ga auren ta ba.

Cikik farinciki yace; "na gode sosai da sosai, yanzu zuwa nan da sati ɗaya za'a zo saka rana".

Jameela tayi murna sosai har farin cikin ta ya kasa ɓoyuwa, haka suka ɗan taɓa fira kan yace ta shiga gida ta turo masa su Husna.

Ta amsa da to sannan ta tafi, tana shiga ta tarar dasu suna ta wasa nan ta miƙar dasu, ruwan zafin da Mama ta ɗora shi ta juye domin tayi musu wanka.

Ta kuwa rangaɗa musu wanka sannan ta shafe su da mai, ta ɗauko wata doguwar riga wacce ta ɗinka da wani ragowar atamfa ta sakawa Husna, Mussadiq kuma kayan ƙanin ta ta saka mishi yayinda nasu kuma na linke ta saka a leda baƙa ta basu a hannun su.

Tana riƙe da hannun su, suka fito yaran sun birge Abdul ganin yadda sika fito tas dasu kamar lokacin da mahaifiyar su take kula dasu.

Duk da beyi magana ba amma ya nuna yaji daɗin haka a fuskar shi, Jameela tace; "to gasu ko? Sai anjima idan mun yi waya".

"yanzu harda musu wannan aikin, kuma kika wahalar da kanki?", ta langwaɓar da kai tace: "ayya na ɗauka cewa yaran ka yara na ne shiyasa amma idan nayi laifi ayi mini haƙuri".

Wai! Lallai wannan ta shirya samun babban matsayi a wajen shi ganin yadda take ƙoƙarin kyautata mishi.

"yauwa dan Allah gobe ma ka kawo mini Husna", ya juyar da kai yace; "Allah ya kaimu", ta ɗaga mishi hannu tana godiya a haka har ya bar ƙofar gidan.

Koda suka isa gidan Salma na nan a jaɓe tana faman danna waya tana dariya, cikin murna Musaddiq ya nufi inda take.

"Mama munje wajen Aunty tayi mana wanka", Salma ta ɗago ta kalle shi sai da zuciyar ta ta buga ganin yadda yaron aka mishi wanka sosai wanda a da baya samu.

"wace Aunty kenan? Kuma tare da waye kuka je?", yaron ya kuma cewa; "tare da Abba kuma wajen wannan Auntyn me zu.........", cikin sauri ta daka mishi tsawa tana ture shi daga jikin ta har ya kai ga faɗuwa.

Ran Abdul a ɓace yazo ya ɗaga shi sannan ya kalle ta yace; "Bafa tsoron ki nake ji ba dan kinga ina ƙyale ki, wallahi duk rashin mutuncin da zaki yi ya tsaya kaina idan ya haura kan yarana zan ɗauki matakin da baza ki taɓa jin daɗin shi ba".

Salma cikin masifa tace; "nayi ɗin kayi duk abinda zaka iya, ko an faɗa maka ina tsoron matakin da zaka ɗauka a kaina ne?, banzan Ragon Namiji kawai".

Abdul da zuciyar shi ta kai matuƙar ɓacewa ya ɗaga hannu ya kwashe ta da mari sannan ya nuna ta yace; "haka kika ce ko?, to ki sani ni nake auren ki ba wai ke kike aure na ba", yana gama faɗin haka ya wucewar shi.

"to dan ka rabu dani sai me ga maza nan a gari wa'inda suka fika komai da komai, me ake da miji soloɓiyo kalar ka wanda be san haƙƙin matar shi ba *meka taɓa mini a rayuwa?*".

Jin wannan kalma ta ƙara fusata shi yayo kanta kamar zai dake ta, sai kuma ya fasa ya juya yayi ficewar sa daga gidan gaba ɗaya ma.

Nan Salma ta dinga balbalin masifar ta har ta gaji kamar mahaukaciya tayi ɗakin su Husna kan su ta nufa ta rufe su da duka tana faɗin; "wallahi baƙin cikin uban ku ba zai taɓa kashe ni ba shegu matsiya ta🙊".

Habiba data shigo gidan ta girgiza kai yana ƙara kwaɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login