Showing 66001 words to 69000 words out of 107295 words
Chapter 23 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
(peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) says:
'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk."
[Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه)
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 21*~
Abdul kuwa ɗakin su Husna kawai ya shiga, a tsaitsaye ya same su sai zare idanu suke yi, ba tare da yabi ta kansu ba ya ɗauki jakar kowanne ya rataya mishi sannan ya riƙe hannun su suka fice daga gidan.
Salma kuwa ɗaki ta wuce tana kuka tana sanar da Jameela, ita kuwa Jameela babu abinda take yi in banda murmushi ganin tarkon data ɗana ya yi babban kamu, Salma na gamawa Jameela ta zunduma ashar sannan tace; "kika yarda har ya dake ki, to wallahi yana dawo wa kici kwalar sa", Salma tace; "ni ai da gida kawai zan tafi".
Cikin sauri Jameela tace; "a'a ba za'a yi haka ba, kada ki sake ki bari yaci ki a yaƙi ai an daina wannan yayin kin san mutane me zasu ce sannan can gidan idan kinje ba zasu goyi bayan ki ba", Salma jiki a sanyaye tace; "hakane kuma to ke yaushe zaki zo".
Jameela tace; "zan zo amma da wata babbar magana zan zo insha Allahu", Salma tace; "shikenan ina nan ina jiran ki Allah ya kawo ki, kin san jiya anyi taron *Muna Wuta* na Kaduna state?".
Salma ta ɗan taɓe baki tace; "naga ana ta magana a whatsapp dana hau jiya da daddare", Jameela ta ɗora da cewa; "aikuwa abu ya ƙayatar an bawa Hibba ma kambu na girmamawa".
Salma tace; "ai ta cancanta domin yarinyar akwai bada wuta wallahi, amma ni yanzu ba wannan bane damuwa ta damuwa ta shine yadda Abban Husna zai fasa wannan auren".
Jameela taja tsaki tace; "to ki zauna baƙin cikin ɗa namiji ya kashe shi, kinji zan turo miki da video clip din ki kalla", Salma tace; "shikenan ina jira", a haka suka yi sallama.
Salma ta faɗa saman gadon tana me ajiyar zuciya, babu batun wanka ko wanke-wanke balle gyara inda ta ɓata, ta shafa cikin ta jin yana kukan yunwa, cikin sauri ta tashi ta fice, tana shiga kitchen ta hau buɗe-buɗe ta kuwa tarar da Abdul ɗin ya rage mata nata abin karin haka ta juyo kunun ta kuma kwashe ragowar doya da ƙwan daya bari a food flask.
Bedroom ta shige a tsakiyar kan gado anan ta ajiye abin karin nata ta kuma janyo waya ta buɗe data ta hau whatsapp tana karyawa tana chating.
Ganin Jameela ta turo mata da wannan video clip ɗin yasa ta buɗe ta hau kalla, yadda aka yi abin ba ƙaramin birge ta yayi ba, garin murna harta zunguri kofin kunun ya kife a nan saman gadon.
Ta kalle shi sai kuma taja tsaki, da hannu ta ɗauka ta cilla shi ƙasa sannan ta cigaba da abinda take yi ba tare da ta damu ba, tana kallo tana jin ina ma itace a wajen, nan fa ta turawa group ɗin su na *Manyan Mata* da kuma *MU HAƊU A SAMAN GADO* ai fa nan aka fara fira akai wa'inda basu gani ba suka kalla suna nasu sharhin yayin da wa'inda suka kalla suke ƙara yi musu sharhi akai.
Salma dai a nan ta wuni babu abinda yake tada ta sai cikin ta idan kuma ta ci to nan zata dawo ta kwanta, tana me cigaba da latsa wayar.
Ƙarfe uku Abdul ya kwaso yara daga makaranta, gidan ya nufo amma gaba ɗaya bashi da walwala dan be san me zai zo ya tarar ba gashi a office an dawo da yi mishi warning akan yadda yanzu aikin shi yayi ƙasa sosai.
Su kansu yaran idan ka kalle su babu wani kuzari a tattate dasu, ba wai rashin cin abinci bane domin sai da suka biya gidan wata yayar Abdul ɗin suka ci abinci sannan suka wuto gidan.
Da sallama suka shiga amma babu wanda ya amsa hakan yasa suka kutsa kai ciki, Abdul yabi falon da kallo cike da baƙin ciki yadda ya bar komai haka ya dawo ya same shi har kunun daya zube ya bushe ga ƙuda duk sun gama bin wajen, abincin da basu ci ba kuwa yana nan a yadda yake kuma dan wulaƙanci a buɗe yake.
Ya kalli yaran sannan yace; "ku wuce ɗakin ku", shi kuma ya wuce nata ɗakin, yana shiga yaci karo da kofin data cillo tun safe, ya kalli kofin sannan ya kalle ta.
Cikin jin haushi ya daɗa mata duka a gadon baya, Salma dake faman ƙalƙala dariya babu ɓata lokaci dariyar ta koma, fuska ta dago taga waye ishashshe da mai wanda har ya kai ya dake ta.
"lallai ma wuyan ka ya isa yanka, ni kake duka Abdulkareem to wallahi ka sani ni ba baiwar ka bace kuma ka duki auren kane".
"in dai dan wannan irin rayuwar auren ce sai me dan na daki aure na Salma, wallahi kin bani mamaki kuma kin yiwa kanki, yanzu dan rashin mutunci sai ki kasa kwashe kayan da kika ɓata a falo, nan ma kuma kin lalata amma baki san ki gyara ba to wallahi wannan abubuwan naki ya fara isa ta dan haka ko dai ki gyara ko kuma na ɗauki mummunan mataki akan ki banza shashasha kawai", yana gama faɗin haka ya fice a ɗakin.
Ɗakin su Husna yaje inda ya tarar dasu sun gama shiryawa zuwa islamiyya, dan haka ya jasu kawai suka fice daga gidan gaba ɗaya.
Salma kuwa babu abinda ya dame ta banda alwashi da take ci akan mijin nata na yadda zata ɗauki fansa akan abinda yayi mata don bata jin zata iya ƙyale shi.
********* ***********
Sahabat tana gama girki ta wuce ɗaki, kwanciya tayi kawai tare da jan tsaki, yau saura kwana biyu ƙaryar da ta yiwa Ummi ya ƙare domin kuwa an kusa gama rehersal ɗin masu tafiya musabaƙar da tayi ƙarya dasu.
Ta ɗaga kai ta kalli agogo ko ina Ummi ta tafi yau oho?", kayan ta ta tuɓe ta ɗauki haɗin sabulun da take wanka dashi me gyara fata da ƙamshi ta fice domin yin wanka.
Ta kai minti talatin a bayin tana wanke jikin ta sannan ta gama ta fito, ta tsane soson ta shanya a sama tana ƙoƙarin shiga ɗaki Ummi tayi sallama ta shigo ita da tawagar mutanen da suka rako ta.
Duka idanun su na kan Sahabat kasancewar towel ɗin jikin ta ɗan ƙarami ne ko gwiwa be ƙarasa ba ga kuma sirrin kyau da take ƙara yi wanda duk aikin gyarawa Zaiyad din ta da take yi.
Tana gama yi musu sannu da zuwa ta wuce ɗaki, Matar da idanun ta kamar ya faɗo tayi saurin lashe leɓen ta tana faɗin; "masha Allah".
Ummi kuwa abinda Malam Mukhtar ya faɗa mata ne ya faɗo mata a rai ganin yadda yarinyar tata take ƙara cika da kyau.
Amma koma meye zata ƙara sawa Sahabat ɗin idanu don ganin meke faruwa duk da ta yarda da tarbiyar data bawa ƴar tata.
Ummi ta kalli tawagar tata tace; "to na gode da wannan rakoni da kuka yi, yanzu sai ƙarshen sati insha Allahu idan mun haɗu a meeting".
Matar nan ta kalli Ummi tace; "wai ni Hibba waccen yarinyar fa ƴar ki ce", Ummi ta washe baki tace; "eh Shukra ƴa tace Sahabat kenan itace babba", Shukra ta kuma lashe baki sannan tace; "aikuwa dai yarinyar masha Allah, ga wannan a bata ta siya ƴan kayan make up", Ummi ta washe baki domin kuwa Shukra irin matan mayace mijin ta babban soja ne sai dai be cika zama a gari ba hakan yasa ta faɗa harkar banza wato mace tabi mace daga baya kuma ta shiga harkar rubutu inda take bada tata gudummawar wajen ganin ta ɓata yaran jama'a.
Shukra nada masoya sosai domin littafin ta har ya fi na Ummi rashin mutunci dan yanzun ma itama ambata awward sannan kuma an bata muƙami itace chairwomen na ƙungiyar gabaki ɗaya, ta kan yi amfani da masoyan ta masu biyota gida domin su ganta, to anan ne idan taga wacce tayi mata ta kan kashe ko dubu nawa ne dan ganin ta mallaki yarinyar, ita da wacce aka bawa shugabar ƙungiyar gaba ki ɗaya wato *Hapcy* tafiyar su ɗaya kusan ma aminai ne sannan wajen wannan harkar ma tare suke yi.
Kuma Shukra duk wacce ta gani take muradi tofa sai ta same ta kota halin ƙaƙa ne kuma duk ustazanci da kamewar yarinyar, ainihin sunan ta shine Kareema Hassan laɗɗo, ainihinta ƴar garin Adamawa ce, saboda haka kyakkyawa ce sosai kuma ba wata me ƙiba bace a girme Ummi zata ɗarar mata domin ita Shukra ɗanta ɗaya ne kuma yana can ƙasar waje yana karatu.
Yau tunda ta ɗora idanun ta akan Sahabat taji yarinyar ta gama birge ta tana kuma muradin kasancewa tare da ita dan haka dole wannan labari yaje kunnen Hapcy domin su san yadda zasu yi.
Ummi ta ƙwalawa Sahabat kira, jin hakan yasa Shukra kafawa ƙofar ɗakin su Sahabat ɗin idanu tana fatan fitowar ta domin ta ƙara samin damar ganin yarinyar.
Sahabat ɗin ce ta fito cikin sauri jikin ta sanye da wando jeans kalar blue da kuma riga pink sai ta ɗora top fara a sama, wani irin jan numfashi Shukra tayi domin ji tayi kamar ta janyo ta ta rungume haka take ji.
Ummi tace; "ga kyauta daga Hajiya Kareema" Ummi ta ƙarasa tana nuna mata Shukrar, Sahabat ɗin ta kalli Shukra tayi murmushi sannan tace; "nagode sosai".
Shukra ta janyo ta ta rungume tana faɗin; "kada ki damu ai kin wuce haka a wajena", Ummi kuwa murna fal ranta ganin ƴar tata ta sami shiga wajen manyan mutane kamar Shukra, ita kuwa shukra haɗuwar jikin nasu yasa gaba ɗaya wutar kanta ta ɗauke dan haka ta ɗan shafa bayan Sahabat ɗin.
Sahabat kuwa jin sabon abu wai harda wani runguma cikin sauri ta janye jikin ta, Shukra ta ƙara faɗin; "ina wayarki in saka miki number ta duk abinda kike buƙata ki kirani kawai kada ki biye Ummin ki".
Ummi tayi saurin tarar numfashin Shukra wajen faɗin; "ai bata da waya ni bana bari suna riƙe waya ba yanzu ba".
Shukra tace; "abin mamaki yarinya kamar wannan ace bata da waya a hannu gaskiya akwai abin mamaki, amma hakan yayi kyau to shikenan abinda za'ayi shine zan dinga neman ki data mahaifiyar ki, kinji".
Sahabat ta daga kai kawai cike da mamakin irin kallon da Hajiya Kareemar take binta dashi, sai da Ummi ta gama godiyar ta sannan suka yi sallama.
Shukra ta kalli Sahabat ta marairaice fuska tana faɗin; "haba Beauty babu rako?", Sahabat ta kalli Ummi, Ummi ta mata nuni da taje kawai domin ita har ranta ta yarda da Shukrar.
Sahabat tabi Shukrar a baya har zuwa waje, Shukra dama ita kaɗai ya rage bata tafi ba itama kuma Sahabat ɗin ce ta hanata tafiya.
Ta riƙo hannun Sahabat ɗin tace; "dan Allah kada ki ji nauyi na ki ɗauke ni kamar ƙawarki kinji, zan dinga jin lafiyar ki wajen Ummin ki sannan zan dinga kiranki a wayar ta ki saki jikin ki dani kinji".
Sahabat ta ɗaga mata kai, Shukra ta shafa fuskar Sahabat ɗin sannan tace; "dat's my girl", daga haka tace; "zan tafi amma bada jimawa ba zan dawo saboda ke kinji, take care", ta karasa tana me bawa Sahabat ɗin peck a kumatu.
Sahabat kuwa tama kasa motsi ganin abin yafi ƙarfin ta, Shukra kuwa motar ta ta shiga ta ɗagawa Sahabat ɗin hannu sannan taja motar ta tafi.
Sahabat kuwa ganin Shukrar ta bace yasa taja tsaki tana faɗin; "karuwar banza kawai", daga haka ta juya zuwa gida.
A falo ta sami Ummi sai faman irga kyaututtuka da kuma kuɗaɗen data samu take yi, Sahabat ta zauna kusa da ita sannan ta ajiye mata kuɗin da Shukra ta bata .
Ummi ta kalle ta tace; "har ta tafi kenan", Sahabat ta amsa da; "eh, ta tafi", Ummi tace; "Allah sarki Hajiya Kareema".
Kuɗin ta ɗauka ta kuma miƙawa Sahabat ɗin sannan tace; "gashi nan ki riƙe gobe sai kuje kasuwa keda Surayya ki siyo abinda kike so", Sahabat ta amsa da; "to".
Tana shiga ɗaki ta ciro wayar ta, abin mamaki shine da har yanzu Zaiyad be kira ta ba, ta san dai a duk lokacin da ya ajiye ta ƙofar makarantar su to ya kan kira yaji yaya taje gida amma kuma yau shiru kome ya faru kuma oho?.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
[3/12, 8:32 PM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) says:
'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion."
[At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 22*~
Koda daddare da Abdulkareem ya dawo be shiga inda take ba, itama kuma bata wani damu ba amma tana nan ta ƙudurci aniyar sai ta rama.
Sai da ya yiwa su Husna addu'a suka kwanta sannan ya dawo falon ya kawar da duk kayan dake wajen tun na safe sannan ya share ɗakin ya