Showing 33001 words to 36000 words out of 107295 words

Chapter 12 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1318

yaji sosai ya fara shawo kan Sahabat ɗin, ko ba komai ya sani turaren da yayi amfani dashi mai ƙarfi ne yana fizgar hankalin mace zuwa gareshi, shi ɗin dai ne yake shafawa, duk lokacin da yaso samun kan yarinya.

Karkacewa yayi, yana mai fiddo wani ɗan ƙaramin chewing gum daga aljihun shi. Guda biyu ne kacal, saboda haka ya sanya mata ɗaya a baki shima ya sanya ɗaya, har yanzu kanta na saman jikinshi.

Kalamai masu daɗi yake fesa mata, ta narke sosai a ƙaunar shi sai wani irin yamm take ji sosai a jikin nata, lokaci guda kuma video ɗin da yake turo mata tana kalla suka shiga playing a ƙwayar idanun nata.

Zataso ta kwatanta, masalan yanzu da suka keɓe tsakanin su su biyu, babu mai ganin su, ɓangare guda kuma update ɗin Ummin nata na jiya yana sake dawowa tiryan tiryan a kwakwalwar ta, masalan inda take bayyana irin daɗin da mace take ji idan ta kasance da namiji.

To ita me zai hana ta itama? Shine fa zai aure ta, ga Zaiyad ɗin ya haɗu, abun alfahari ne a gareta kuma cewa tana tarayya da namiji kaman Zayyad ɗin.

Bata dawo daga tunanin da ta tafi ba, taji hannun shi a gadon bayan nata, ƙoƙarin zipping rigar ta yakeyi, ga mamakin ta, babu wani yunƙuri na hana shi da tayi, Saima sake gantsarewa da tayi, domin yaji daɗin zagewa.

Ta ko ina hancin shi na bisa jikin ta, sun shagala sosai, da taimakon desire chewing gum da ya saka mata take tauna bata sani ba, ta miƙa mashi kanta sosai da sosai, enjoying moment ɗin take a hankali, inda shi kuma cikin salo da ƙwarewa a yaudara ya dinga raɗa mata Kalamai, wanda zasu taimaka mashi wajen yarda cewa shi ɗin nata ne, kuma kome ma yayi mata a yanzu, shi ɗin dai ne zai aure ta.


Lallai Ummanta nayi gaskiya, ashe haka ake ji? Abu ɗaya ne bata yarda ba, ya kusance ta takanji ance ana shan wahala sosai da sosai a yi na farko, Amman inda ba haka ba, babu Abunda zai hana ta miƙa mashi ragamar kanta a wannan daren na yau, inda wajen yake tsit, baka jin sautin komai, sai tashin kiɗa daga cen nesa da inda mitocin nasu suke.


Hasken fitilar motar data dalle wurin, shi yayi sanadin firgitarsu sosai da sosai, daga irin duniyar da suka wulla, sai tayi saurin ture shi ga inda yake nufa ɗin, gyalenta ta jawo tana mai gyara lulluɓin ta, jikinta sai ya ɗauki rawa, tunani take an gansu, saboda haka ne tayi saurin ɓalle motar ta fito tana mai zare idanu.

Ashe wasu ƴan party ɗin ne da basu samu isowa da wuri ba sai yanzu, sun ma riga sun wuce zuwa ciki kai tsaye, da sauri tayi zipping rigar tata zuwa sama, bayan ta maida hannun bra ɗin tata da ya zame mata. Sai lokacin ta lura da shima ashe ya fito, ya jingina kanshi bisa fuskar motar yana maida numfashi da sauri da sauri, saboda ya kai iya matuƙa, kuma bai taɓa kawo ma ranshi cewa ba zai samu yadda yaso ba a lokacin...

















~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~






© *2020*



_~We Love U All~_❤
🤷‍♀🤷‍♀🤷



*_MENENE RIBA TA ❓_*


🙆🙆🙆


© *2020*

🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*


*~we write assidiously perceive no pain~.*


*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*


*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_



~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻........✍

♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*

♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*



~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_


~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._



*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:*

*"Allah (mighty and sublime be He) says:*

*'The first of his actions for which a servant of Allah will be held accountable on the Day of Resurrection will be his prayers.' If they are in order, then he will have prospered and succeeded; and if they are wanting, then he will have failed and lost. If there is something defective in his obligatory prayers, the Lord (glorified and exalted be He) will say: 'See if My servant has any supererogatory prayers with which may be completed that which was defective in his obligatory prayers.' Then the rest of his actions will be judged in like fashion."*

*[At-Tirmidhi (also by Abu Dawud, an-Nasa'i, Ibn Majah and Ahmad).]*

عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ أَوَّلَ مَا يُحَاسَبُ بِهِ الْعَبْدُ يَوْمَ الْقِيَامَةِ مِنْ عَمَلِهِ صَلَاتُهُ. فَإِنْ صَلُحَتْ فَقَدْ أَفْلَحَ وَأَنْجَحَ، وَإِنْ فَسَدَتْ فَقَدْ خَابَ وَخَسِرَ، فَإِنْ انْتَقَصَ مِنْ فَرِيضَتِهِ شَيْءٌ، قَالَ الرَّبُّ عَزَّ وَجَلَّ: انْظُرُوا هَلْ لِعَبْدِي مِنْ تَطَوُّعٍ فَيُكَمَّلَ بِهَا مَا انْتَقَصَ مِنْ الْفَرِيضَةِ، ثُمَّ يَكُونُ سَائِرُ عَمَلِهِ عَلَى ذَلِكَ. رواه الترمذي وكذلك أبو داود والنسائي وابن ماجه وأحمد



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



*♣Scene Four*

~*Page 11*~



Wannan karon, irin fushin da Abdul ya ɗauka da Salmar tashi kam yayi tsanani. Duk wata hulɗa da zata haɗa shi da ita ya kauce mata. Hatta da ruwan wanka da abinci baya saurara daga gareta. Komai shine yake yi ma kanshi, haka kuma yayi ma yaran shi.

Hatta da wanka shine yake masu tun da safe idan ya tashi, yayi ma Husna shirin makaranta, ya saka ta gaban mota yaje ya ajiye ta, sannan ya wuce zuwa wajen aiki, idan rana tayi, haka zai ajiye abunda yake yi, yaje ya ɗauko ta, ya biya ya siya masu abinci a restaurant sannan ya wuce gida, haka zai tasa su gaba ita da musaddiq suci abincin, sai sun gama ci ne sannan zai mata shirin islamiyya, wata yarinyar maƙautansu da take tafiya da ita tazo ta ɗauke ta, sai a lokacin ne zai samu ya koma bakin aikin shi.

Duk wannan abun da yake Salmar na kallon shi, wai ta barshi ne ya ɗana irin wahalar da mace ke sha a cikin gida, wanda itama idan tazo da tata buƙatar namiji ya kasa yin kataɓus a gareta, bayan duk waccen wahalar aikin gidan da take sha.

Iyakarta tayi wanka ta shirya, sai shiga kitchen da take yi, ta sama ma kanta abunda zata kai bakin salatin ta. Ko gyaran gidan bata damu da tayi ba. Ita duk a ganin ta, da hakan ne zai iya gane kuskuren da yake aikata mata.

Abunda basu sani ba, su duka suna matuƙar shan wahala da wannan zaman doya da manja da suke yi. Ta fannin Salma kuwa, yanzu hatta da ƴan kuɗaɗen da Abdul ɗin ke bata na buƙatar ta, wanda dasu ne take amfani ta sanya data sai suka dawo suna gagarar ta.

Yayin da shi kuma Abdul cen wajen aiki suka fara mashi ƙorafi, inda Allah ya taimake shi ma, kuɗaɗen da sukayi waibuwa a kamfanin an riga da an gano inda suka shige. Kullum manager ƙorafi yake na rashin maida hankali kan aikin na Abdul.

Tuni fa ya fara ramewa, ya fita hayyacin shi, duk inda Kaga Abdul kai kasan baya cikin walwala. Ita kuwa Salma da ƴan kayayyakinta da bata ɗinka ba, su ta dinga ɗauka tana kaima wata dillaliya kusa dasu nan tana siye tana bata kuɗin, domin kawai ta siya data ta hau online, saboda bata da rashin ci dai balle sha.

Group ɗin da tafi jin daɗi a ko yaushe nan tafi shiriricewa. Matan aure ne da zawarawa cike taf da group ɗin, komai tattaunawa akeyi a ciki, kai hatta da abincin da suka ci sai sun ɗauki photon shi sun tura, ga maganganu marasa ma'ana da suke yawan yi, ga litattafai masu munin karantawa. Ita kuwa Salma a hakan komai yayi mata zam.

Ƙorafinta ta tura, gami da irin zaman ko in kula ɗin da suke yi da mijin ta, inda ta ƙara da cewa babu abunda baya yi mata amman, komai, ci, sha, sutura mai tsada, waya mai tsada, muhalli da kuma kulawa da dangin ta. Kwanaki ma har ya fara shawarar siya mata ƴar ƙaramar mota saboda kai Husna makaranta. To Amman ita matsalar ta dashi kawai wajen shimfiɗa ne. Yanzu yama daina kula ta, ko inda take baya kalla,tana so a sake bata wasu shawarwarin masu ƙarfi.

An bata shawarwari sosai da sosai, inda tayi ta jin daɗi, tana kwashe dukkan wani harafi na shawara da aka bata, saboda da yawa wasu ce mata suke ta cigaba da nuna mashi kuskuren shi, ai wannan abun babu abunda aka haɗa dashi, wata ma har ce mata take wai "Aini Namiji wallahi idan har ba zai iya gamsar dani a shimfiɗa ba, to gara a tasa mun naman balangu inta ci, ko ba komai dai nasan zan maida kwaɗayi na".

Nan dai suka ci gaba da tattaunawa, da bata shawarwari marasa ma'ana.

Wata da tafi kowa zaƙalƙalewa a group ɗince ta bita private chat. Bayan sun gama gaisawa ne ta nuna ma Salmar irin tausaya mata da tayi, nan ta nemi Salmar data bata dama ta zama ƙawarta.

Cikin kwanaki kaɗan suka wani irin ɗinke da matar data kasance bazawara, auren ta biyu, amman ta ɓoye ma Salmar, wajen ce mata aurenta ɗaya, kuma shima matsalar dangin shi ce, nan salma ta saki baki tana gaya mata, ita dai bata da matsala da dangin Abdul, kowa na sonta na ƙaunar ta, hatta da mahaifiyar shi.

Kafin kace me, Salma ta kwashe duk wani sirri nata kaf da abdul ta faɗa mata, hatta da yanayin yanda Abdul ɗin ke kwanciya da ita, da yanda bata kula shi yanzu, Amman wai duk da haka babu Abunda baya kawowa gidan shi, nama kuwa idan ka buɗe frezer ɗinta kaman yayi magana, banda sauran kayan ciye ciye da maƙulashe,da kuma yanayin aikin Abdul ɗin, harda abubuwan da yafi so mace tayi mashi, da kuma wanda baya so mace tayi mashi.

Wata irin shaƙuwa sukayi da matar da take da suna Jameela, kafin kace me har Salma ta bata adireshin ta, da kuma wai lokacin da zata zo gidan ta iske Abdul, domin ta ganshi, nan tayi mata alƙawurran shawarwari da kuma wasu magunguna da zata bata, wai ta sanya ka Abdul ɗin a cikin abun sha.


**********


Cikin kwana biyun da Saha tayi gidan biki, sau biyu suna haɗuwa da Zaiyad, yaro da kuɗi kenan, ɗan gayu mai tashe da faɗa aji. Duk wata hanya da Zaiyad zai bi yaja hankalin Saha ya bita kuwa. Ya zuwa yanzu tana jin babu abunda zai iya raba ta da Zaiyad ɗin nata, kai koda Ummi ce kuwa.

Ta fannin karatun littafi kuwa sai abunda yaci gaba. Kwana biyun da sukayi basa gida, sau uku Ummin tata ke sakin update a kullum, wannan ya nuna bata aikata komai cikin gidan nata sai typing, domin ta burge Fans. Comment kuwa da take so, tana masifar shan shi, wasu su zaga wasu su yaba, Amman da yawa cikin fans ɗin nata, suna jindaɗin abunda take yi, kaman yanda suke mata comment suna mai ƙarfafa mata guiwa akan ta cigaba, ai wannan ma faɗakantarwa ce a hakan. Ta kan ce, "Ahh to! duk wanda yaji ba zai iya ba sai ya barshi kada ya karanta" ko kuma tace "Ai bata sanya Uban kowa ya karanta ba", wani Page ɗin ma da tasan mai zafi ne, ta kan yi kandako a saman Page ɗin, da *"If you read, you are on your own"*

Wannan abu nama fans ɗinta matuƙar daɗi, da yawa ma tarawa suke sai dare yayi su karanta, matan auren wasu su nemi mazajen su, wasu kuma su biya ma kansu buƙata daga haka, wasu ƴan matan kuwa da hannu ko wata hanyar suke bi wajen samun gamsuwa. Ummi kuwa ba tare da tasan cewa, duk wani abu data rubutu a nan duniya sai Allah ya tada ta akan shi ba ranar gobe ƙiyama, sannan duk wanda yabi wata hanya da ba daidai ba wajen gamsar da kanshi, to fa tana da kamashon zunubi.

Duk abunda ake yi Sahan na kallo, domin tana cikin group ɗin Ummin, Amman ba tare da sanin Ummin ba. Kullum wayar Sahabat a silent take, hatta da hasken wayar ta kashe shi duka ta maida shi a (A)

Ana gama shagalin biki suka tattara suka dawo gida, abun baima Sahabat daɗi ba, domin ya bala'in takurata wajen haɗuwa da Zaiyad ɗin nata, saidai ta shige toilet suyi ta waya, ko kuma tayi ta playing xxx video ɗin da Zaiyad ɗin ke turo mata, wai tayi course akan su, idan sunyi aure ta dinga practicing a kanshi. Abun na mata daɗi, sai take yarda ma kanta cewa lallai Zaiyad ɗin kullum a shirye yake da auren nata.

Bata tsagaita da tura ma Hunayda pages ba, da kuma video's ɗin. Duk da ita kanta Hunaydan idan ta gama kalla, kuma ta tabbata ta samu gamsuwa, abun na mata ciwo, gashi cikin kwana biyun har Malam Suhayl ya turo gidan su wajen Abban ta.

Ba tare da ɓata lokaci ba, abban ya basu haƙuri da cewa Hunayda tayi ƙarama da aure, saidai malam Suhayl zai iya cigaba da zuwa gidansu da rana wajenta, kafin nan da ta cika ko shekara sha takwas ne, sannan sai ayi masu auren.

Ko a hakan aka tsaya yama malam Suhayl daɗi, dama kuma shi ɗinma ba wani aikin kirki gareshi ba, karantarwar ce kawai a Islamiyya, kuma mafi yawanci kowa yasan malaman islamiyya dan Allah suke yi. Saboda haka ne yake ma kanshi fatan zuwa lokacin da Abban Hunaydan ya ɗiba, shima ya samu abun yi, tunda ya riga ya kammala karatun shi, harda bautar ƙasar shi ma.


Sahabat taji matuƙar haushi, inda har saida ta balbale Hunayda da bala'i da masifa, akan me zata amsa ma malam Suhayl ɗin? Sam ba ajinta bane, ina ma laifin ta samu kaman Zaiyad ɗin nata? Koma wanda ya fishi? Ko ba komai dai ita gani take kaman Malam Suhayl bai iya soyayya kwatankwacin ta Zaiyad ba, kuma ma wai abunda ya ƙara bata haushi, shine wai zance ma saidai ya dinga zuwa da rana!

Ita ko Hunayda da kallo tabi Saha ɗin, har saida ta gama bambamin faɗan nata, sannan tace mata, "Idan kin gama ni zanje na ɗora ma Ammi girki, kinga yau bata nan, mu kaɗai ta bari cikin gidan, kuma so nake in kammala kafin lokacin makaranta yayi" ta faɗa tana mai miƙewa zata wuce.

Da hannu Sahan ta jawo ta, "Kinga malama bar wani sauri, ita Ammin me yasa bata tsaya tayi abincin ba kafin ta fita. Nifa Shiyasa nake bala'n jin haushin mahaifan nan namu, su kullum suna kan waya, suma basu iya taɓuka komai, wai saidai lallai kai ace kayi, kaman wani bawa, mtseww" ta ƙarashe tana mai jan tsoki.

Galala Hunaydar tayi tana kallon ta.


"Anya kuwa Sahabat?

Kin fa fara cenza hali wallahi, to ke in kina jin haushin Ummin ki, Nidai gaskiya bana jin haushin Ammi na, kuma Ammina tana yimin hakan ne domin in iya, karatu ne dai kinsan sai dare yayi nakeyi yanzu saboda Ammi tana neman ta hana, kuma nima gaskiya na fara gajiya, ina tunanin dena karatun ma baki ɗaya, indai irin waɗanda kike turo mani ne. Malam Suhayl rannan daya zo ya duba wayata yaga litattafan hausa faɗa ya dinga yiman, yana jawo man ayoyi, Allah ma ya sanya bai karanta ko kaɗan bane ai da na bani, tunanin in dena nake gaskiya, tunda babu wanda babu batsa ciki, ni kuma ina shiga cikin wani yanayi, bana so in dinga aikata ba daidai ba, kaman yanda kike yi keda Zaiyad"

Ai tana ƙarashewa Saha ta miƙe cike da bala'i, "Ke asiri zaki tona min? To wama yace maki bama aikata daidai ni da Zaiyad? Soyayya ce, to matar malam nace ko shi malamin naki ya faɗa maki inda aka haramta soyayya? naga ai kuma kuna yi ko?" ta faɗa cike da masifa, har tana riƙe ƙugu.

Girgiza kai Hunayda tayi, dayake ita ɗin mai sanyi ce, sai tace mata" Allah ya baki haƙuri malama, ba nufi na kenan ba, kuma koda muna soyayya ai bama yin irin taku, har yanzu ko yatsa ma malam Suhayl bai taɓa riƙewa ba, balle ma ni zan iya ce maki har yanzu ban san soyayya ba, koda nake tsayawa tare da malam Suhayl, kawai dai wanda yace yana sonka, ai yafi wanda yace shi maƙiyinka ne"

Tana gama faɗar haka ta juya ta shige kitchen. Itama Saha da tsabar masifa ta kwashi wayarta, tana mai ficewa daga gidan faɗi take "ai dan kinga ma ina biyo ki ne har gidan ku, kike neman gaya man magana, har ma zaki tona man asiri game da Zaiyad, da a gaban wani kika faɗi haka fa? Lallai ma yarinyar nan, dole ne kema in dinga ɓoye maki wani abu, kuma littafi ma daga yau na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login