Showing 105001 words to 107295 words out of 107295 words
Chapter 36 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
albarka" Ameen Ammee" ta amsa tana mikewa ta shiga d'akin su hijabi kawai ta saka ta fito Ammee ta bata kud'in napep ta fita.
A kofar gidan su Saha mai napep d'in ya sauke ta,kudin shi ta bashi sannan tayi sallama ta shiga ciki Ummee ta gani zaune a tsakar gida tana taya Suraiya tsifa har kasa Hunayda ta durkusa ta gaishe ta kaman yanda ta saba kallon sha'awa Ummee ta bita dashi tana amsa gaisuwan tana mata fad'an me yasa ta d'auke kafa a gidan su sannan tana tuna lokacin da suke tare da Saha haka take itama.
"Ki shiga tana ciki" cewar Ummee da toh ta amsa tana mikewa tana tsokanan Suraiya wai sun fara zama seniors a islamiya shiyasa ba'a ganinsu.
Kaman yanda ta saba da haka ta fad'a d'akin tana mita" kina jina shine kikayi lakwas a daki kaman wata mara gask...."maganan ne ya makale mata ganin Sahabbat ta turo katon cikinta a gaba tana zaune tana mata murmushi amma idonta cike tab da hawaye tace" hakane Hunayda ina nan a daki ko a tsakar gida bana iya zama saboda rashin gaskiya ina tsoron kada mutane suzo su ganni,kinga abinda son zuciya ya jawo min kina bani shawara amma ina miki kallon bagidajiya ga sakamako ban na sam......" Kuka ne yaci karfin ta kasa karasawa da gudu Hunayda tazo ta rungume ta ta fashe da kuka sosai itama tana" Inna lillahi wa inna ilahi rajiun Sahabbat yaushe hakan ya faru me yasa baki name ni ba" da wani ido zan kalle ki Hunayda bayan irin abubuwan da nayi miki akan fad'a min gaskiya da kike ki barni in girbi abinda na shuka" sun dad'e suna kuka ba mai rarrashin wani da kyar suka rarrashi junan su sukayi shiru.
Bayan Saha ta bata labarin duk abinda ya faru sannan itama Hunayda ta bata labarin bayan rabon su da katin auren ta da ta kawo mata tace yanzu saura wata 1 ya rage bikin nasu,sosai Saha ta taya ta murna tace sai dai ita ba zata iya zuwa ba saboda watan haihuwar tane lokacin bikin,addu'an Allah ya sauke ta lafiya tayi mata sun dad'e suna hira sannan tayi musu sallama ta tafi tare da alkawarin zata kuma dawowa kamin bikin nata.
A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah dan yau ake walimar auren Hunayda wanda ya kayatar sosai saboda ya tara manyan malamai,da washe gari aka d'aura auren su bayan sallahn juma'a Mallam bai yarda anyi wani bidi'a ba dan haka bayan sallahn isha'i aka mika ta gidan mijinta bayan ta sha dogon nasiha daga wajan iyayenta. (Sai muce happy married life Hunayda).
""""""""""""""""""""""""""""'''""'''''''''
Rayuwar Salma a gidan Naseer ba abin cewa saboda abin kullum kara muni yake domin Naseer irin mutanan ne da zaka gansu a nesa kaman mutanen Kwarai amma da zaka kebe dasu zaka san ba haka suke ba domin ada kamin ta aure shi akace ga halin shi ba zata tab'a yarda ba domin ya kasance cikin mazajen nan ne masu nunawa mace so kaman su lashe ta amma da zaran kin shigo kuma shikenan kin zama bola saima son nuna iko da kokarin maida mace baiwa,duk wani d'auki da soyayya daya yake nuna mata a waje tunda ta shi ko a ido bata ga ya nuna mata ba balle a aikace.
Na 2 kuma tunda suka cinye garan da akayi mata a gidan su ta daina cin wani abu mai dad'i gashi da kudi amma ko shinkafa baya saya sai garin masara wai yafi dad'i bare tasha tea mai madara ga bakin magana da yake yab'a mata sai in dare yayi yazo mata da bukatar shi wanda a dole Salma take bashi kanta domin in har ya kusance ta toh da ciwon mara take kwana domin Naseer in har ya biya nashi bukatar toh ita ko oho gashi baya wuce minti 15 ko 20 gaba daya.
Salma duk ta rame saboda bakinciki amma ta had'iye kayanta domin ko su Aunty Jidda bata tab'a fad'awa matsalar ta ba saboda tayi abaya bata ji dad'i ba shiyasa tayi gum da bakin ta,ga kewar yaranta dake cinta a cikin ranta yau sama da wata 8 rabon da ta saka su a idon ta,duk yanda tayi yaki da zuciyar ta na ganin batayi tunanin Abdukareem ba abin ya faskara sai yanzu tasan lalle tayi sake ta rasa gwarzon miji kaman Abdukareem babu abinda ta nema ta rasa a gidan shi duk wani gata da jin dad'in duniya babu wanda bai nuna mata ba amma ta biye shirmen yan *muna wuta* gashi sun kaita sun baro nadama tayi shi yafi cikin trailer amma haka ta daure ta rungumi kaddara ta zauna domin ta tabbata alhakin Abdul ne yake bibiyanta.
*********************
Cikin dare Saha suna kwance da suraiya suna bacci kaman a mafarki ta rinka jin ciwon ciki kad'an-kad'an har abin yayi yawa ya tashe ta a bacci,cike da azaba ta d'aura hannunta akan tirtsesen cikin nata tana cizon leb'e da kyar ta yunkura ta tashi zaune taji duk zaninta ya b'aci ga kuma fitsari da take ji ya matse ta bangoi ta rinka bi har zuwa bathroom d'in ta cire zanin daya b'aci ta gyara jikin ta ta tsuguna dan yin fitsain taji cikin nata ya wani irin murdawa har bayan ta ya amsa,tana durkushen ta fara kokarin fitsain taji yazo mata da wani nishi mai karfin gaske wanda tunda take a duniya ba ta tab'a jin irinsa ba.
Kokarin danne nishin take saboda azaba da take ji sai dai ina nishin yafi karfin dannewa tana yi kuma tana jin abu yana zuwa,wani nishin ne yazo da karfi wanda yafi na bayan sai ji tayi muryan baby na callara kuka da iya karfin shi zubewa tayi a wajan tana maida numfashi ko dagowa batayi ba dan abinda ta haifa saboda yanda take jin jikinta kaman ba nata ba.
Ummee tana zaune kan sallaya tana lazimi wanda yanzu kullum dare sai ta tashi tana neman yardar mahallacin ta, taji kaman kukan jariri sa kunne ta karayi taji da gaske take ji jiki na rawa ta fito tsakar gida ta ji daga bayan gida kukan jariri ke fitowa kaman ta kifa haka take sauri wajan nufan bayan gidan tana bud'ewa taga Saha kwance da jariri,da gudu ta karasa ta d'aga ta tana ambatan sunan ta a galabaice ta amsa.
Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi jin tana da rai dan ita a yanda ta ganta batayi tsammanin da rai a tattare da ita ba,gyara su tayi tsab ta kai su d'aki ta miko mata baby amma ta kasa sa hannu ta karb'a kallo 1 ta mishi ta d'auke kanta gefe ganin yanda yaron yake tsananin kama da Zaiyad,kuka ta fashe da shi sosai tana jin dama mutuwa tayi da ganin wannan rana shikenan ta tabbata uwar shege kukan tane ya tashi suraiya daga bacci taga Ummee rike da yaro suna kuka dukan su,cike da murna ta karb'i yaron a hannun Ummee tana kallon kyakkyawan fuskan shi.
Da washe gari Ummee ta kira number Kawu ta fad'a mishi cewar Saha ta haihu shima a take ya kira Baban Ziyad ya fad'a mishi.
"Allah ya isa tsakanina da kai Zaiyad ka min tabon da ba zai tab'a goguwa ba a rayuwa ta ba kasani sai Allah ya saka min,ga dan ka nan kazo ka d'auke abinka" text din da Saha rubutawa Zaiyad kenan.
Ya karanta text din yafi a kirga bai tab'a jin wani emotions game da abinda yake aikatawa ba sai yau kuma a take Allah ya saka mishi son ganin yaron a ran shi.
Baban shi yasa shi a gaba har zuwa gidan su Saha ganin baby da kaya sha tara na arziki,baban bai shiga ba yace shi ya shiga haka dole shi ya shiga akawo mishi yaron shi bayan sun gaisa da Ummee, ido ya tsurawa yaron yana kallon photo copy shi,yaso yaga Saha amma ko mai kama da ita bai gani ba dan tana can daki tana kukan daya zama mata jiki tun da ta haihu ta maida shi ibada Ummee tayi tayi har ta gaji ta zuba mata ido shiyasa yanzun ma bata takura kan ta fito ba,haka ya karaci zaman shi ya tafi.
Sati na zagayowa aka rad'awa yaro suna Muhammad raguna har 2 Baban Zaiyad ya aiko kuma a ranan aka d'aura auren su sai dai an bar tarewan nata bayan ta gama wanka.
****************
Jameela sai kukan kissa take a gaban Abdul dan zaiyi tafiya na kwana 2 zuwa Kano wanda aka tura shi daga wajan aikin su yana ta faman rarrashin ta tana nuna mishi kwana 2 yayi yawa ba zata iya rayuwa babu shi ba,da kyar ya lallab'a tayi shiru da zai fita ma saida ya nemi ya gana da yaran shi amma tace ta tura su gidan su gaishe da Mamanta cike da jin dad'i yanda take kula da yaran shi ya fita ya shiga mota tana tsaye harya tada mota ya fita tana d'aga mishi hannu tana shigowa ta daka wani uban tsalle ta d'auko wayanta cikin sauri ta kira wani no ta tsaya jiran a daga,ana d'agawa tace" baby ya tafi kazo kawai kuma sai bayan kwana 2 zai dawo" tana gama wayan ta nufi d'akin su Husna tana bud'e kofan saida suka firgita sun zuwan ta ba alkhairi bane ai kuwa saida ja kama kunnen su taja tace su zauna kada su fita sai ta kira su suka amsa da toh duk da suna jin yunwa kuma son fad'a mata amma saboda tsoro suka kasa yi . mata magana har ta fice ta rufe su harda murza key sannan ta shiga shiryawa cikin wasu arnen kananan kaya ta zauna jiran kwarton nata,bata dad'e da zama ba kuwa sai gashi nan ya iso cike da murna ta tare shi suka shige ciki abin su suka fara badalar su cikin kwanciyar hankali.
Shi kuma Abdul koda ya isa office d'in su director su yace an d'aga tafiya sai next week,cikin sauri ya nufi gida dan kawowa Jameela wannan daddadan labarin koda ya shigo yaga sabuwar mota da bai sani ba amma bai wani dame shi ba ya wuce cikin sauri har ya nufi hanyan bedroom dinsu yaji kaman kukan yaran shi koda ya matso bakin kofan nasu yaji kukan daga d'akin yake fitowa murda kofan yayi amma yaji ta a kulle saida ya lura yaga an saka key cikin sauri ya murda key ya bud'e kofan ba shiri yayi baya saboda abinda idon shi ya gani yaran shine kwance male-male cikin amai ga jikin su duk daud'a ko almajirin kan hanya ya fisu haske da gudu ya shigo d'akin yana daga su amma ba magana saboda duk sun galabaita a fusace ya nufi d'akin su dan ya samu Jameela tayi mishi bayanin meye dalilin ta rufe mishi yara a daki kuma tace basa gidan,tun kamin ya karasa d'akin ya fara jin wani irin nishi daya saka shi fad'uwar gaba a bakin kofan d'akin yayi suman tsaye ganin Jameela da wani kwance tsirars kan gadon na sunnan su suna aikata masha'a.
Wani flower vase da hannun shi ya Ture ya fad'i kasa ya tarwatse shiya dawo dasu daga duniyar da suka lula tsoro,firgici da tashin hankali karara a fuskan Jameela shi kuwa kwarton nata karkarwa ya fara yana neman hanyan gudu,Abdul idon shi ya rufe ko ta kan shi bai ba yayi kukan kura yai kanta ya shake ta yana maimaita Kalmar" why....why!!!!"
A takaice dai Jameela saida ta sha bakar azaba a hannun Abdul sannan ya mika ta ga police su Husna kuma saida suka kwanta gadon asibiti saboda ulcer da yayi musu mugun kamu,jamerla daga karshe kotu aka mika ta aka yanke mata hukunci kan abinda tayiwa su Husna.
******************
Salma yau tunda ta tashi gaban ta ke faduwa haka ta daure ta fito ta d'aura d'umamen tuwon miyan kuka data rage musu na breakfast,bayan ta gama ta kawo ta ajiye kan dinning zata shiga ciki ta kira Naseer suka had'u a hanya ya sha wanka yace mata shi Katsina zai wuce auren 'yar abokin shi dan haka sai dai ita taci bashi da lokaci abokanen shi suna jiran shi ,da addu'a a dawo lafiya ta bishi amma ko amsawa bai yi ba ya fice abin shi.
Tunda ya fita Salma ta zauna shiru saboda gaba daya bata jin dad'in jikinta dan haka ko kallon d'umamen batayi ba, kusan karfe 10 taji wayarta ya fara ringing wanda ya kara mata fad'uwar gaba da kyar ta kai hannu ta d'auki wayan amma taga bakuwar number tana d'agawa taji muryan wani mutum yake ce mata tare da Alhaji Naseer suka yi tafiya amma ko Kano basu wuce ba sukayi hatsari kuma ya rasu,tashin hankali sosai Salma ta shiga taji mutuwar nan har cikin ranta,haka aka dawo da gawan Alhaji Naseer akayi mishi sutura Salma ta fara takaba.
A gurguje pls Saha ta tare a gidan Zaiyad an barwa Ummee yaron data haifa wanda kullum in ta kalle shi sai ta zybar da hawaye itama Saha zaman su ita da Zaiyad sai a slow kowa na kallon hanjin dan uwan shi babu yarda ko kadan tsakanin su kullum ciki zargin juna suke ga dangin miji sun saka ta a gaba da zai da habaici,haka Salma itama ta gama takaba wanda Abdul kullum cikin irga kwanaki yake yake dan haka tana gamawa aka maida auren su ta dawo ta rungumi mijinta da yaranta hannu 2-2.
Alhamdullilahi anan muka kawo karshen wannan short novel namu da fatan ya isar da sakon da muke son isarwa.
Allah ya bamu ladan ilmantarwa dake ciki ya yafe mana kurakuren dake.
Kaman yanda Allah ya nuna mana wannan wata mai alfarma ya nuna mana karshen ta lafiya.
Allah ya bamu lafiya tare da wadatan yin ibada Ameen.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤