Showing 99001 words to 102000 words out of 107295 words

Chapter 34 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1252



"Allah (mighty and sublime be He), had said: 'I have divided prayer between Myself and My servant into two halves, and My servant shall have what he has asked for. When the servant says: 'Al-hamdu lillahi rabbi l-alamin' (3), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has praised Me.' And when he says: 'Ar-rahmani r-rahim' (4), Allah (mighty and sublime be He) says: 'My servant has extolled Me,' and when he says: 'Maliki yawmi d-din' (5), Allah says: 'My servant has glorified Me' - and on one occasion He said: 'My servant has submitted to My power.' And when he says: 'Iyyaka na budu wa iyyaka nasta in' (6), He says: 'This is between Me and My servant, and My servant shall have what he has asked for.' And when he says: 'Ihdina s-sirata l- mustaqim, siratal ladhina an amta alayhim ghayril-maghdubi alayhim wa la d-dallin' (7), He says: 'This is for My servant, and My servant shall have what he has asked for.'"

(1) Surat al-Fatihah, the first surah (chapter) of the Qur'an.

(2) i.e. standing behind the imam (leader) listening to him reciting al-Fatihah.

(3) "Praise be to Allah, Lord of the Worlds."

(4) "The Merciful, the Compassionate."

(5) "Master of the Day of Judgement."

(6) "It is You we worship and it is You we ask for help."

(7) "Guide us to the straight path, the path of those upon whom You have bestowed favors, not of those against whom You are angry, nor of those who are astray."

*Narrated  by Muslim and also by Malik, at-Tirmidhi, Abu-Dawud, an-Nasa'i and Ibn Majah*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*

♣ _Scene Eight_

   ~*Page 29*~

Wani irin dummm taji maganan Ummeen nata kaman saukan aradu akan ta,cikin kid'ima da rashin fahimta ta d'ago da kai ta zubawa Ummee ido tana tantaman abinda kunnenta suka jiyo mata yanzu gaskiya ne ko kuma mafarki take?

Saukan wani bahagon  mari da Ummee ta kifa mata shiya dawo da ita daga suman zaunen da tayi kuma ya tabbatar mata ba mafarkin take ba, da ido take kowa na parlour ga bakinta na rawa amma ta kasa furta ko kalman A.

Cikin wani irin tashin hankali da Ummee bata san dashi a duniya ba ta tsinci kanta a ciki jikinta sai karkarwa yake cikin d'aga murya tace" Saha magana nake miki uban wa ya miki cikin nan ki gaya min nace?"ta karasa da wata irin murya.

Kuka mai cin rai wanda yafi karfin a kira shi dana nadama Saha ta fashe shi tana jin zuciyar ta kaman ya fito haka yake ta harbawa da sauri-sauri,yanzu shikenan Zaiyad ya yaudare ta ya gama da ita,ciki fa ina zata je da ciki?gashi tun ba'a je ko ina ba ya watsar da ita ya samu wata....

Ummee kuwa zuciya ne yazo mata wuya ganin tana  tambayan ta maimakon ta bata amsa ta kama mata kuka mara amfani,duka kawai ta rufe ta dashi ko ta ina abinda bata tab'a yi ba kenan domin Ummee na matukar kaunar yayan nata tana yi tana magana" ba zaki gaya min uban da yayi miki cikin nan ba ko Saha ina magana kina jina? Wallahi gwara in kashe ki kowa ya huta ba zaki dasa min bakinciki ba,ba zaki b'ata min suna ba" sai haki take tana suratai da itama bata san ma'anar su,Saha kuwa ko ihu batayi ba bare neman ceto saboda radadin da zuciyar ta ke mata yafi karfin dukan da Ummee ke mata,Suraiya dake gefe itama tana kuka tana bawa Ummee hakuri amma ko jinta bata yi.

Duka tayi mata sosai amma Sahabbat bata da niyyan cewa komai,Ummee dan kanta ta gaji ta kyale ta ta nemi guri ta zauna tana maida numfashi can kuma ta fashe da kuka mai cike da d'acin zuciya tace" Innalillahi wa inna ilahi rajiun!!! Na shiga uku yau me zan gani wannan wace irin bakin rana ne haka a rayuwa ta? Sahabbat kin cuce ni kinci amanar tarbiya dana baki me nayi miki zaki saka min da wannan mummunar sakamakon?".kuka ne ya ci karfinta ta kasa karasa maganan taci gaba da kukanta ita da 'yan mata ta babu mai rarrashin wani.

A bangaren Salma kuwa bayan fitan Abdul da Jameela tun tana kuka su Fatima suna bata baki har suga idonta ya kafe tayi baya luuuu ta fad'a kan gadon babu numfashi a tare da ita,ihu su Fatima suka saka suna ambatan sunan ta tare da girgiza ta babu wanda yayi tunanin kiran doctor a cikin su,a haka su Aunty Maryam da Aunty Jidda suka shigo suka same su.


Da gudu suka karaso ciki tare da tambayan meke faruwa? Abinda ya faru Fatima ta fara fad'a musu sai dai Aunty Maryam bata tsaya jin karshen zancen ba ta garzaya zuwa office d'in Doctor ta kira shi suka taho tare da wasu nurses 2,ba b'ata lokaci suka fara kokarin ceto rayuwarta bayan sun kora su Aunty Jidda waje dan su samu daman yin aikin su.

Suna fita Aunty Maryam ta kira gida cikin kuka ta zayyane musu abinda yake faruwa,ba sufi 15 mints da waya ba sai ga iyayen su da Yayan su namiji sun shigo asibitin cikin tashin hankali suna tambayan ya jikin nata kuma tana wani d'akin dan su shiga su ganta,Fiddausi ce tayi karfin halin basu amsa cewa ga d'akin da take amma Doctors suna ciki har yanzu basu fito ba.

Cike da jimami suka nemi guri suka zauna jiran tsamani zuciyoyin su cike da fargaba Maman ta sai share hawaye take,sun kai good 20 mins da zama sannan suka ga an bud'e kofan d'akin da take ciki Doctor ya fito yana goge zufan dake goshin sa nurses na take masa baya,gaba dayan su suka taso sukayi kan shi suna tambayan ya jikin nata?

Cikin natsuwa yake bin fuskokin su da kallo daya bayan d'aya amma baiga fuskar Abdul a cikin su ba dan haka no wasting of timw ya tambaya " ammm nace ba ina mijin nata yake akwai abubuwan da nake so mu tattaunawa dashi".

Su Aunty Maryam zasu bada amsa Abban su yayi saurin cewa baya nan an kira shi a wajan aiki amma zai iya gaya mishi ko menene dan shi mahaifin tane,office d'in shi yace su je zai masa bayani a can yana fad'an haka yayi gaba Abba ya rufa masa baya har office d'in.

Suna shigowa Doctor ya zauna tare da nunawa Abba kujera yace ya zauna,a d'osane ya zauna dan shi ba zama ne a gaban shi ba halin da 'yar shi take ciki shine a gaban shi,bayani ya fara mishi na yanayin cutan nata kuma yace a kiyaye abinda zai b'ata mata rai komin kankantar sa domin yanzu haka anyi mata wani abinda ya bata mata rai sosai ne bayan warning da yayiwa mijinta amma Allah  ya kawo da sauki domin sunyi nasaran shawo kan matsalar a yanzu sai dai su kiyaye gaba.

Godiya Abba yayi mishi ya fito daga office d'in jiki a sanyaye,suna ganin fitowar shi duk suka mike tsaye suna jiran suji me Doctor yace, a takaice ya fad'a musu abinda yake damunta da kuma yanda Doctor yayi warning kan kiyaye bacin ranta.

Mama ba abinda take sai hawaye,da daddaya suka fara shiga suna dubo yanayin jikin nata gudun kada su tashe ta daga baccin hutun da take,matan duk in sun shiga da kuka suke fitowa saboda yanda cuta ta maida lokacin guda kaman ba Salma 'yar gayu ba.tun daga wannan rana iyaye da 'yan uwan Salma suka shiga bata kulawa ta musamman suna tarairayan ta sannan suna matukar kokari na ganin basu bar ta tayi tunanin past rayuwar ta ba.

Salma ta kanyi pretending na bata tuna komai abinda ya danganci rayuwar ta na da but yana damunta kuma kullum cikin dare ta kan tashi tayi ta kuka tana yiwa Jameela Allah ya isa sannan tayi ta nafila cikin dare tana kaiwa mai sama kukanta tare da neman ya sassauta mata radadin dake cinta a rai,cikin ikon Allah kamin ta cika wata 2 a gidan su sosai zuciyar ta ta rage jin zafin abinda Abdul yayi mata.

A gidansu Saha kuwa wannan rana babu wanda ya runtsa saboda tashin hankali kowa da irin tunanin da yake,ita Saha abubuwa sun gama cakude  mata tana tunani ta fad'awa Ummee gaskiya ne ko kuma ya zatayi gashi sai gwada layin Ziyad take amma yaki shiga hakan ya tabbatar mata da cewa yayi blocking din number ta,tun tana da karfin kukan har karfin ta ya kare ta kwanta lamo sai ajiyar zuciya take tana tuno yanda ta fara had'uwa dashi da yanda yayi amfani da Kalmar aure ya yaudare ta har ya cimma burin shi akanta take" Hunayda....." Ta furta can kasan makoshi Allah sarki k'awa ta gari kuma masoyiya,inama ta d'auki shawaran da take bata tun farko da haka bata faru gare ta tana ganin hakan shine so da wayewa.

"Dole in fad'awa Ummee gaskiya meye amfanin b'oyewa tunda komai ya gama lalacewa ya daina sona ko kuma ince ya gama dani,dubi yanda muka rabu jiya dashi amma har yanzu ko text din shi ban gani ba bare kira...Ya Allah na cuci kaina..." ta cigaba da maimaitawa kuma duk a bayyane take wad'an nan kalaman suraiya da take kwance a gefen ta sai hawaye take sharewa saboda tausayin 'yar uwarta.

Ummee tana kwance a d'akinta sai kuka da tsinewa wanda ya lalata mata 'ya take duk taka tsantsan da take a kan ta sai da yayi nasara "wai wani d'an tsinanniya ne shi? Duk yanda akayi ba d'an halal bane d'an kwararo ne Allah ya isa tsakanina da kai..." Karan wayarta shi ya dakatar da ita ta juyo tana kallon wayar dan tashin hankali da take ciki yau bai barta ta tuna da wata waya ba bare tayi typing.

A hankali ta kai hannunta na dama ta d'auko wayar na hagun kuma tana share hawayen ta dashi tana duba screen d'in wayar taga wata fitattaciyar fan d'in tace da tafi kowa iya sharhi kan kowanne update da zatayi gata da iya turo mata recharge card kullum dan wai taji dad'in yi musu update, dan haka Ummee tana matukar ji da ita cikin fans d'in ta bata ganin kiranta ta kyale amma yau tana gani har tayi mata 2 missed calls ta.kasa d'agawa ta san ba zai wuce ta tambaye ta ya yau suka ji shiru babu sabon update kaman yanda ta saba musu dashi ba.

Bayan kaman minti 5 wani kiran ne ya kara shigowa na wata fan d'in a zuciye Ummee ta kashe wayar baki d'aya dan yau ita kad'ai tasan halin da take ciki.

Kamin gari ya waye Ummee ta tsayar da shawaran ta kira kawun su yazo ko in Sahabbat ta gan shi zata iya fadan wani abu game da cikin jikin ta kasancewar suna tsoron shi sosai duk da dai wani bangare na zuciyar ta na kwabar ta akan yin haka sai dai dole ne tayi dan bata da wani mafita sai wannan.


Da washe gari Saha sallah kawai tayi ta koma ta kwanta saboda jikinta duk ciwo yake mata ga wani zazzafan zazzabi daya rufe ta sai nishi take hawaye na bin gefen idonta,Suraiya ita tayi akin komai a gidan abinda ya had'a da girka abin karya har zuwa sauran aikace-aikacen gida,koda ta shigo dan sanarwa Ummee ta gama saida ta girgiza ganin yanda fuskan ta ya kumbura suntum saboda kuka da rashin bacci cikin ita da Saha bata san wacce tafi wata ba.


"Kije ina zuwa Suraiya" tace tana tashi daga kwancen da tayi ta zauna,wayarta ta d'auka ta kunna sai da ya gama booting sannan ta nemo no Kawu ta danna mishi kira,bayan sun gaisa tace tana son ganin shi yanzu in babu matsala.

Nan ya shiga tambayan ta lafiya dai ko? Da eh ta amsa mishi ta katse kiran ta zauna jiran shi tare da rabka tagumin da hannu 2, Kawu bai dad'e ba ya kamo hanyan zuwa gidan nasu jin muryan ta a shake ya san babu lafiya,a kofar gidan yayi parking na motan shi sannan ya fito ya nufi cikin gidan.

Sallamar shine ya dawo da Ummee hayyacinta kamin ta amsa har Suraiya ta amsa ta fito tana mishi sannu da zuwa,both Ummee da Saha kowanne su sai da suka ji fad'uwarta gaba,Ummee nata na fargaban ya zai d'auki zancen ne while Saha kuma nata na tunanin meya kawo shi gidan su da sassafen nan,ko kuma yaji labarin abinda ya faru ne? Kai ta girgiza da wuri tace" nasan Ummee ba zata fad'awa kowa wannan maganan ba saboda......" Banko kofar d'akin nasu da akayi yasa ta firgita ta mike jikinta na wani irin rawa ganin Kawu su d'auke da wata sharb'eb'iyar wuka da ake yanka musu ragon layya dashi ga fuskan nan a murtuke kaman mala'ikan mutuwa yasa ta kusan sake zawo a jikinta.

Baya-baya ta farayi yana binta har suka karasa jikin bango,ganin babu wajan guduwa yasa ta durkushe a wajan ta fara kuka tana yarfe hannaye tare da rokon shi,hannu daya ya d'aga mata alaman tayi shiru ai kuwa ba shiri ta had'iye sauran kukan sai jikinta da yake karkarwa.

A hankali ya karaso gaban ta ya durkusa yana mata wani kallo daya kara hargitsa mata hanjin cikin ta yace" abinda naji Ummee ku ta fad'a gaskiya ne?" Kasa magana tayi sai ido da ta d'ago ta kalli Ummee dake tsaye a bakin kofan shigowa,lafiyayyaen mari daya kifa mata wanda ya haddasa mata kurumta na 'yan seconds kamin jin nata ya dawo cikin razanannen murya da bata san Kawun nasu dashi ba taji ya daka mata tsaya yace" zaki amsa min ne ko kuwa?" Kamin ya karasa tayi saurin gyad'a mishi kanta yace" good! Gaya min wanene shi?"

Sanin halin shi yasa ba b'ata lokaci ta bud'i bakin ta na rawa tace" Za.....Za....Zaiyad".

"Good kin san inda zamu same shi?" Ya kara jeho mata tambaya,nan ma gyada mishi kai tayi.

Ya juya ga Ummee dake tsaye yace " ku same ni a mota" yana fad'an haka ya raba ta gefen Ummee yayi waje,wata muguwar harara Ummee ta jefe ta dashi sannan ta juya fita,jiki a mace Saha ta mike ta jawo hijabinta ta saka ta fito tana Jan kafa a lokacin Ummee har ta fita dan haka itama bata tsaya a tsakar gidan ba tabi bayan Ummee, gidan gaba Kawu ya nuna mata da hannu alamun ta shigo nan babu musu kuwa ta shiga tana shiga Kawu yaja sukayi gaba.

Kallonta kawo yayi da suka hau babban titin,jiki na rawa ta fad'a mishi sunan anguwan su Zaiyad dan tasan nufin sa kenan,suna zuwa cikin anguwan ta fara mishi kwatance har suka iso kofar gidan yayi parking ba Ummee kad'ai ba harda Kawu wajan mamakin ya akayi Saha ta san nan wajan har take zuwa bayan basa zuwa ko Ina daga makaranta sai islamiya.

Suna fitowa daga cikin mota Zaiyad shima yana fitowa daga cikin gidan sanye da farar jallabiya kan zai je restaurant ya sayo musu breakfast shida Zee shi.

Wani mugun firgita yayi ganin Saha da iyayen ta amma da yake d'an duniya ne nan da nan ya had'iye ya bisu da kallon wa kuke nema?

Kawu ne ya d'aure zuciyar shi ya d'an matso yayi mishi sallama,amsawa yayi har da d'an dukawa ya gaishe su wanda yin hakan har saida yasa Kawu shakku,Zaiyad dariya ya fara a cikin zuciyar shi d'an ya lura da yanda yanayin Kawu ya canza lokaci daya duk da haka Kawu ya daure yace" bawan Allah kasan wannan yarinyan"?

Kallon Saha yayi a yatsine kaman yaga kashi sannan ya girgiza kai yace" A'a Baba ban santa hasalima yau na fara ganinta,me yasa ka tambaya Allah yasa dai lafiya?"

A razane Saha ta d'ago tana kallon shi dan kunnenta sun kasa gaskata cewa wai yau Zaiyad d'in tane yake cewa bai tab'a ganin ta ba? Kamin tayi wani yunkurin magana taji Kawu na cewa" kada ka nemi raina mana hankali dan kaga ina binka a hankali,dole kace baka santa ba tunda ka gama lalata ta harda guzurin ciki".

"Innalillahi wa inna ilahi rajiun!!! Yarinya kiji tsoron Allah dan kinyi abinki a wani waje kada kizo ki shafa min kashin kaji"

~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~

© *2020*
   

        _~We Love U All~_❤
🤷‍♀🤷‍♀🤷


*_MENENE RIBA TA ❓_*

🙆🙆🙆


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_


~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍

♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*

♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



♣ _Scene Eight_

~*Page 31*~



*LAST PAGE*



Sahabbat sosai take nunawa Ummee cewa ta karanta abinda take rubutawa domin ko kad'an ta daina bawa Ummee wani girma saima nuna mata da take idonta ya riga ya bud'e babu abinda bata sani ba a rayuwa,wannan sabon halin nata kullum sai yasa Ummee zubar da hawayen nadama,WhatsApp d'in ma tuni ta goge shi a wayarta saboda shine musababin halin da take ciki yanzu.



Kawu ya kawo musu labarin an kama Zaiyad kuma ya amince ya amsa laifin shi sannan Baban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login