Showing 96001 words to 99000 words out of 107295 words
Chapter 33 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
having lanterns suspended from the Throne, roaming freely in Paradise where they please, then taking shelter in those lanterns. So their Lord cast a glance at them (1) and said: 'Do you wish for anything?' They said: 'What shall we wish for when we roam freely in Paradise where we please?' And thus did He do to them three times. When they say that they would not be spared from being asked [again], they said: 'O Lord, we would like for You to put back our souls into our bodies so that we might fight for Your sake once again. And when He saw that they were not in need of anything they were let be.'"*
*(1) i.e. at those who had been killed in the cause of Allah.*
_[Narrated; Muslim also by at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah.]_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
*~Scene 7~*
*Page 28*
"Innallilahi wainnailaihi raji' un, na shiga uku na lalace! Yanzu Abdulkareem saki na kayi akan Jamila? Dama akwai ranar da zata zo kaci mun mutunci haka? Wallahi sai Allah ya saka min. Ke kuma Jamila in sha Allahu abunda kika yi mun Allah bazai barki ba, saboda Allah ba azzalumin bawan shi ba ne".
Ta ƙarashe maganar tana komawa kan gadon tare da saka kuka kamar ranta zai fita.
Jamila ce ta kama hannun su Husna zasu bar ɗakin, ranta fari ƙal abunda take so yau ya faru, ji take inama zata iya rawa a gurin, da sai ta ɗan taka saboda yadda lamarin ya mata daɗi.
_Ohhh Jamila akwai barikanci_.
"Ki sakar mun ƴa ai ba ke kika haife ta ba da zaki kama hannun ta ku tafi saboda tsabar munafurci".
Abdulkareem kam tunda ya furta kalmar sakin sai kuma yaji jikin shi yayi sanyi ya kasa magana ma, har saida Salman tace wa Jamila ta sakar mata yara.
"A guri na za su zauna. Jamila wuce mu tafi gida".
Wani kukan Salma ta ƙara fashewa da shi, ji take kamar ranta zai fita.
"Shikenan an rabani da yara na, na shiga uku ni yanzu ya zanyi, Fatima ku temaka mun, ku hana shi tafiya da su Husna ko idan na gansu Hankali na zai dinga kwanciya".
"Aunty kiyi haƙuri akwai Allah".
Haka dai Salma tayi ta kuka tana dana sanin abunda ya faru yanzu, ga kuma wani zazzaɓi da ya ƙara rufar mata.
A ɓangaren su Jamila kuwa suna fita Abdulkareem yayi gida dasu, bayan sun shiga gida ya samu guri ya zauma tare da haɗe kai da gwiwa yana jin ciwon abunda ya aikata.
_"Salma duk ke kika ja mana wallahi, ga abunda kika janyo nan, har sai da kika sa na sake ki, nace miki bana so bana so amma sai da kika tunzura ni na aikata abunda Allah baya son shi, to yanzu wa gari ya waya, ai gashi nan kin cuce ni mu da yaran mu, kin saka za su zama marasa uwa, duk da na san Jamila zata basu kulawa, amma baza ta so su kamar yadda ke da kika haife su ba_".
Haka dai yayi ta mitar shi cikin ranshi.
"Haske na, na kawo maka abincin ne ka ci ko kafi samum nutsuwa?"
Yaji muryar Jamila ta daki kunnen shi.
Kallon ta yayi yana wani ɗan yatsina fuska kafin ya ce"Please Jamila ki ɗan bani lokaci kaɗan, i want to be alone, i want to be my self, please".
Ya faɗa yana haɗe mata hannayen shi guri ɗaya..
"Sweat heart kenan" Ta faɗa tana shafa gefan kumatun shi. "Ka ɗau duk lokacin da kake buƙata nayi maka uzuri, na kuma fuskanci irin halin da kake ciki".
"Nagode sosai" ya faɗa kafin ya kwanta akan kujerar....
**** **** **** ****
"Surayya don Allah, don girman Allah, don sonki da manzon Allah (S. W. A) kar ki faɗawa Ummi abunda ya faru tsakani na dake jiya da daddare na roƙe ki, don Allah, wallahi kema kin san idan taji maganr nan kashe ni ne kawai Ummi ba zata yi ba, so plss ki rufa mun asiri kema wata rana sai ki ga Allah ya rufa miki asirin, kuma ko ba komai ni fa ƴar uwar ki ce ta jini".
"Ya Saha kenan, ai in sha Allahu in Allah ya yarda bazan aikata abunda kike aikatawa ba ballantana ma har na ɓoyewa Ummi, ke kanki kin san abunda kike aikwata ba daidai bane, don Ummi bata yin abunda ya kamata akan mu sai akace ki bi hanyar lalata rayuwar ki? to ki sani idan da akwai lefin Ummi to kema akwai naki, domin kuwa ke ba jahila bace Allah ya hore miki ilimin islama dana boko dai dai gwargwado, amma ke kin kasa amfani da shi, da jahili ne yayi irin wannan abun sai ace mai ai jahili ne be yi karatu ba, be san abunda yake yi ba, to ke kuma me za a kira ki umm? Duniya ce ta ishi kowa riga da wando, ni dai In sha Allahu zan yi ƙoƙarin kare mutunci na, amma ki sani akwai ranar da za ta zo dole sai kin girbi abunda kika shuka wallahi, kuma zancen faɗawa Ummi tunda har bata bari na sanar da ita yau ba, to kuwa sai dai ta farga da kanta, Allah ya kyauta amma gaskiya idan bacci kike to ki farka, ki kuma san halin da kike ciki yauwa".
"Haba Surayya ya zaki ce haka, wallahi zaiyad kaɗai da shi nake mu'ammala kuma shima don yace zai aure ni ne shiyasa".
"Ya Saha kenan, a barshi ma a auren naki zai yi, sai kuma aka ce saboda zai aure ki ki sakar mai jikin ki yayi yadda yake so da ke ummm? Haka addinin ki yace kiyi, to ai ko aure kika yi bazai yi ɗaukin ki ba, saboda ya riga da ya san komai game da ke, kuma bazai daraja ki ba, sai ya dinga zargin anya ma kuwa baza ki bi wasu mazan idan baya nan ba, tunda haka kuka yi kafin kuyi aure, ko kuma ke ki dinga zargin shi da hakan. Allah dai ya kyauta kawai".
"Amin" Saha ta amsa mata don ita gani take Zaiyad bazai yi mata haka ba...
_Ni kuwa nace tabbb kin tafka babban kuskure_
"Saha ni na fita sai na dawo, kawun ku zai zo anjima ya kawo mana kayan abinci munyi waya da shi ni kuma bazan iya jiran shi ba jira na ake yi idan yazo kuce ina gaida shi don Allah!!!
Sahan leƙowa tayi daga ɗakin su kafin tace" to Ummi sai kin dawo Allah ya kiyaye hanya.
Bayan fitar Ummi da kamar awa ɗaya, sai ƙanin Abbun su Saha yazo gidan.
Gaida shi suka yi cikin mutunci da girmamawa.
"Ina Ummin taku take ne?
" Wallahi kawu bata daɗe ta fita ba, wai anata jiran ta ne, tace tana gaida ka".
Ɗan jimm yayi kafin ya ce"To ina amsawa, muje ku tayani ɗebo kaya a waje.
Boot ɗin motarshi ya buɗe ya ciro buhun shinkafa su kuma su Saha suka ɗebo cartoon ɗin indomie dana su spaghetti da macarooni da dai sauran kayan abinci zuwa cikin gidan.
10 minutes ne ya ɗauke su gurin shigo da kayan, bayan sun gama ya basu wasu kuɗi da ina tunani za su kai 20k ya ce"Gashi nan idan ta dawo ku bata wainnan kud'in cafane".
"To shikenan kawu Insha Allah zan bata, mun gode sosai."
Sahabat ne ta d'an marairaice tace "Kawu kafin ka tafi ko zaka ara min wayar ka na kira ta".
"Affff wai har yanzu bata baki waya ba?"
" Eh Kawu".
"To shikenan in Allah ya yarda zan samo miki ko ƙarama ce, saboda ai wayar tana da amfani, what if wata matsalar ta taso muku bata gidan fa ya zaku yi kenan?
Ya ƙarashe magnar yana miƙa mata wayar.
" Hello Ummi ".
" Na'am Saha, har yazo kenan?
"Eh, dama cewa nayi me za a dafa ko may be ba a kusa zaki dawo ba.
" Ai kuwa dai, ku dafa white rice and stew kawai".
"To shikenan sai kin dawo".
Nan ya karɓi wayar yayi musu ƴar nasiha kafin ya wuce.
Yana tafiya Saha ta fara shiri daga gani fita za tayi sai wani sauri take yi.
"Ammm Surayya zan je gidan su Hunayda yanzu zan dawo".
"Uhmmm sai kin dawo".
Tana fita ta nemi me adaidaita saho yayi gidan Zaiyad da ita saboda tun jiya take gwada no. Shi amma yaƙi shiga, bayan me adaidaita sahu ya ajiye ta bakin ƙofar gidan Zaiyad ɗin nan taci karo da wata sabuwar picanto pake a wajan, sai mamakin ko waye me motar oho, ko may be abokin shi ne, haka dai ta gama tunanin ta har tashige cikin gidan kuma ƙofar a buɗe take , tana shiga ta jiyo shewar Zaiyad ɗin da alamun fitowa ma zai yi daga ɗakin shi.
Shi kuwa sun gama harka da zeeee suna shirin fitowa. liƙe da juna suka fito while bakin su yana cikin na juna suna tafiya suna abun su ko a gefan slipper nasu.
Ita kuwa Saha tun da suka fito ta suma a tsaye ko motsi ma ta kasa yi.
Sai da suka sakko daga stairs sannan Zaiyad ya hangota, ai kuwa da sauri ya saki zeeee"Sa.... ha... bat... Me kike yi a nan??
"Dama abunda kake yi kenan Zaiyad? dama cin amanata kake yi, shiyasa ka dena ɗaga waya ta saboda ka gama yayi na ko? Shiyasa ka kashe wayoyin ka saboda kar na dame ka, ba a gabanka nake ba yanzu, na gode sosai".ta faɗa, tana share hawayen da suka wanke mata fuska.
"Ba haka bane don Allah ki tsaya mana kiji Saha".
🖐️"Ya isa haka Zaiyad babu abunda zaka faɗa mun kaji ko, enough, na gaji dajin ƙaryeyya kin ka".
Fuuu ta fita daga palon
"Umma ta gaida ashha ya faɗa yana keɓe baki".
"Wannan kuma wacece Zaiyad?
" Wata tsohuwar hannu na ce, batta can da yawar ta, can ta matse mata a matse matsin matsalar ta wallahi....."
Bayan mai adaidaita ya sauke Saha direct ta shige gida gaba ɗaya ba a cikin hayyacin ta take ba.
Ita kuwa Surayya har ta ɗora tafashen nama don girikin rana.
Wannan dalili ne ya saka, Saha na shiga ƙamshin tafashen ya daki hancin ta, nan da nan taji ƙanshin gaba ɗaya ya hargitsa mata kai, nan fa zuciyar ta ta fara tashi da gudu tayi toilet nasu tana kwarara amai kamar ƴan hanjin ta za su fita, sai da ta amaye kafff abunda tayi breakfast da shi kafin ya sarara mata.
Ita kuwa Surayya sororo tayi tana ganin ikon Allah.
Bayan ta fito ta baje a gado tana sake fashewa da kuka.
"Shikenan ya cuce ni ya gama dani, wallahi sai Allah ya saka mun, azzalumi macuci kawai".
"Wai me ya faru ne ya Saha?
"Surayya Zaiyada ya gama da rayuwa ta, kuma wallahi bazan yafe mai ba Allah ya isa tsakani na da shi mugu kawai..
Ita dai Surayya bata sake ce mata komai ba sai Allah ya kyauta nan ta koma palo ta cigaba da kallon ta, har nepa suka ɗauke wuta.
Haka dai ranar Saha ta wuni tana jin kasala ga kuma baƙin cikin abunda Zaiyad yayi mata abun ya haɗun mata huɗu da biyar..
Ita kuwa Surayya har ta gama abincin ta ta zuba su a kula.
Ummi bata dawo ba sai wajen qarfe shida na yamma, ana shirin kiran sallar magrib.
"Surayya tun yaushe nepa suka ɗauke wuta ne, na dawo waya ta babu charge gashi na tarar babu wuta".
"Wallahi Ummi sun daɗe kam, don kusan awa huɗu kenan".
"To Allah yasa su dawo da ita nan kusa, wai ina Saha ne tunda na shigo ban ganta ba?
"Tana ɗaki kamar bata jin daɗi ne, ga wannan Kawu yace mu baki".
"Allah sarki, shidai baya gajiya, tunda mahaifin Ku ya rasu kullum cikin dawainiya da hidima yake. Wannan yasa kuke rayuwar ku cikin wadata kamar sanda mahaifin Ku take raye. Allah ya saka musu da alkhairi, Ku kuma Allah ya muku albarka ya gafartawa mahaifin ku."
" Amin Surayya." ta amsa had rants taji farin cikin aduar Ummi a yau.
" Ai kuwa an gode, Bari na dubo Sahar".
"Saha me yake damun ki ne? Ummin ta faɗa tana shafa jikin ta.
" Suhannallahi"Ummin ta faɗa jin jikin Sahan da zafi sosai.
"Kin sha magani kuwa?"
"A'a Ummi ban sha ba" tayi maganar cikin muryar marasa lafiya.
"Ayya sannu tashi kici abinci sai ki sha ko panadol ne kafin zuwa gobe idan jikin be yi sauƙi ba sai mu tafi asibiti.
Bayan Saha tayi Sallah taci abinci ta sha magani, nan Ummin take ta jera mata sannu, ko 15 minutes ba ayi ba Saha taji abincin na taso mata, ai kuwa da gudu tayi toilet nan ta fara amayar da abunda taci ko narkewa ma basu fara yi ba.
Itama Ummin bayan ta ta biyo.
"Sannu Saha, dama kinyi amai ne ɗazu?
" Eh Ummi nayi".
"Ayya sannu ko? May be malaria ce take damun ki, zuwa gobe zamu gwada zuwa asibiti mu gani".
Jinjina mata kai kawai Sahan tayi, don ita kaɗai tasan abunda yake damun ta.
Haka ranar suka kwana jikin Sahar babu daɗi, don yau ɗakin Ummin ma suka kwanta.
_Ni kuwa nace ba wuta, ballantana ayi typing dole aja yara jiki_
Har safiya nepa basu kawo wuta ba, Ummi kuwa sai mita take yi.
Bayan sun ci breakfast nan ma Saha ta ƙara amayar da shi, ga kuma jikin ta babu zafi sanyi ƙalo sai wani bin kujera take kamar me jaririn ciki.
Nan fa Ummi ta fara shan jinin jikin ta tana yiwa Sahar wani irin kallo me wuyar fassarawa.
"Saha shiryawa zaki yi mu tafi asibiti kawai, don jikin nan naki ya fara bani tsoro wallahi"
"To Ummi" tayi maganar ko a jikin ta.
Bayan kamar one hour Saha ta gama shiryawa suka nufi asibiti, lokacin da likita ya kawo wa Ummi result ji tayi gaba ɗaya komai ya ɗauke mata, duniyar tayi mata zafi, dena gane komai tayi sai wani zufa take yi, har wani gudawa gudawa taji yana shirin kama ta a asibitin.
Haka nan dai ta daure ta kama hannun Sahar suka yi gida saboda kar ta kwafsa a asibiti.
Ita dai Saha bata gane kan Ummin nata ba, har suka ƙarasa gida.
Suna shiga ta cilla ta kan kujera tare da faɗin.
*"SAHABAT KI FAD'A MIN UBAN WA YA MIKI CIKI⁉️⁉️⁉️😡😡.......*"
*** *** *** ***
"Kai Ammi kinga yadda kayan suka yi miki kyau kuwa?"
"Wallahi kuwa nima na gani tun da na saka kayan ina shiryawa a jikin dressing mirror, ai ta iya ɗinki sosai, ga itama atamfar tana da kyau".
"Gaskiya kam, ai yau sai Abba ya kasa gane ki tabbb". Hunayda ta faɗa tana guntse dariyar ta.
"Gidan ku Hunayda" Ammin ta faɗa itama tana dariya.
"Ai kam dai Ammi wallahi kinyi kyau sosai".
"Allah ko Hajna?
"Sosai kuwa"
"To na gode muku da yaba kwalliya ta, kuma idan kunje gidan miji haka zaku dinga yi , ba aje ayi ta zama da ƙazanta ba".
Suna cikin haka wayar Hunayda ta fara ringing, da mamaki take kallon screen ɗin ganin sunan malam Suhail.
Da sauri ta shige cikin ɗakin su tana kara wayar a kunnen ta.
"Salama Alaikum" ya faɗa daga can ɓangaren.
Sai da ta lumshe ido kafin ta ce "Wa alaikumusalam".
Shima anashi ɓangaren haka ne, ga wani farin ciki da ya ziyar ce shi jin muryar sahibar tashi.
"Hunayda ya kike? ya gida? Ya su Ammi da Abba da Hajna kuma?
"Duk suna lafiya lau, ina wuni".
Be amsa gaisuwar tata ba yace "Kiyi haƙuri rashin network ya hana mu kasancewa tare nayi kewar ki sosai wallahi".
"Uhmm Allah sarki babu komai nima nayi kewar ka, ya karatun?
" karatu Alhamdulillahi, mun kusa kammalawa ma in sha Allahu".
"To Allah ya bada sa'a, don Allah ka dawo da wuri".
"In sha Allah zan dawo har muyi aure Hunayda, ke de wai ki kula da kan ki......
~_From The Everlasting Golden Pen Of Golden Pen Writers Associotion Team Of MENENE RIBA TA AND ALLAH GATAN MARAYA_~
_~WE LOVE YOU ALL~_❤️❤️
🤷♀🤷♀🤷♀
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ،* عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ صَلَّى صَلَاةً لَمْ يَقْرَأْ فِيهَا بِأُمِّ الْقُرْآنِ، فَهِيَ خِدَاجٌ ثَلَاثًا، غَيْرَ تَمَامٍ، فَقِيلَ لِأَبِي هُرَيْرَةَ: إِنَّا نَكُونُ وَرَاءَ الْإِمَامِ، فَقَالَ: اقْرَأْ بِهَا فِي نَفْسِكَ، فَإِنِّي سَمِعْتُ النبي صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: قَسَمْتُ الصَّلَاةَ بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي نِصْفَيْنِ، وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ الْعَبْدُ:{ الْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: حَمِدَنِي عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ } قَالَ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: أَثْنَى عَلَيَّ عَبْدِي، وَإِذَا قَالَ:{ مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ } قَالَ اللَّهُ: مَجَّدَنِي عَبْدِي - وَقَالَ مَرَّةً: فَوَّضَ إِلَيَّ عَبْدِي، فَإِذَا قَالَ:{ إِيَّاكَ نَعْبُدُ وَإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ } قَالَ: هَذَا بَيْنِي وَبَيْنَ عَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ، فَإِذَا قَالَ:{ اهْدِنَا الصِّرَاطَ الْمُسْتَقِيمَ صِرَاطَ الَّذِينَ أَنْعَمْتَ عَلَيْهِمْ غَيْرِ الْمَغْضُوبِ عَلَيْهِمْ وَلَا الضَّالِّينَ } قَالَ: هَذَا لِعَبْدِي وَلِعَبْدِي مَا سَأَلَ. رواه مسلم (وكذلك مالك والترمذي وأبو داود والنسائي وابن ماجه)*
*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said: *
"A prayer performed by someone who has not recited the Essence of the Qur'an (1) during it is deficient (and he repeated the word three times), incomplete."
Someone said to Abu Hurayrah: [Even though] we are behind the imam? (2)
He said: Recite it to yourself, for I have heard the Prophet (may the blessings and peace of Allah be up on him) say: