Showing 78001 words to 81000 words out of 107295 words
Chapter 27 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
[un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire."
[Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي)
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 23*~
Tana tura ƙofar Zaiyad na turowa dan haka a wajen suka ci karo, cikin sauri ya rungume ta haka da dabara ya ja ta zuwa falo.
Yana zama ta zauna saman ƙafar shi sannan ta shafo fuskar shi tace; "nayi kewar ka Sweetheart sosai", ya riƙo hannun ta sannan yace; "nima nayi kewar ki sosai, yanzu sai ina dan na san akwai insa zaki je".
Sahabat tace; "zan je Unguwar Rimi ne wajen ƙawar Ummi na", Zaiyad yace; "to Allah ya kiyaye hanya".
Saha tace; "korata kake yi ne wai?", Zaiyad yayi saurin girgiza kai yace; "a'a, kawai dai bana so ki shiga cikin matsala ne, muje na sama miki abin hawa".
Saha ta shafa gefen fuskar shi sannan tace; "nayi tattaki tun daga gida domin kawai na ganka amma ka kasa bani komai daga gare ka", kan Zaiyad yayi magana Saha ta haɗe bakin su inda ta shiga kissing ɗin shi.
Zee dake leƙe ta jikin kafar makulli ta girgiza kai cike da kishi tana faɗin; "zaka dawo ka same ni ne".
Da ƙyar Zaiyad ya iya control ɗin kan shi dan Saha ta wuce duk ƴan matan shi ya san da cewa ita ɗin daban take, dan ma dai shi ɗin baya gani ya ƙyale ne amma da be kula ZeeZee ba domin kwata-kwata bata kai Saha ba.
Hannun su sarƙe dana juna, Saha ta kalle shi tace; "meya faru kwana biyu ka canza mini, baka son kira na yanzu Sweetheart ko ka fara gajiya dani ne?".
Zaiyad ya girgiza kai sannan yace; "kik gane ne bana son abinda zai kawo zargi tsakani na da Dad nafi so idan yazo ya tabbatar da cewa kece zaɓin ɗan nashi", Saha tayi murmushi jin abinda Zaiyad ya faɗa.
Ya kamo hannun ta yana shafawa cikin salon yaudara yace; "ina ma ace zamu kwana a haka da zan fi kowa jin daɗi", Saha ta miƙe da sauri tana faɗin; "bari na tafi na bar me Keke Napep a waje", ba tare da ya miƙe ba ya cillo mata kiss, ta fice tana dariya.
Koda ta shiga Keke murmushi kawai take saki idan ta tuno yadda Zaiyad ke matuƙar son ta da kuma ƙaunar ta.
Dai-dai wani tamfatsetsen gida tace ya sauke ta, sai da ta ƙara duba takardar hannun ta domin tabbatar da gidan ne kuwa, lallai shine, kuɗin ta ciro ta bawa me Keken sannan ta fara ƙwanƙwasa get ɗin.
Ta ƴar kafa me gadin ya leƙo, tace; "nazo wajen me gidan ne?", komawa yayi ciki ya kira wayar Hajiyar.
Hajiya Kareema dake tsakiyar aikata masha'ar ta, taja tsaki tana me shafa gashin yarinyar sannan tace; "bari na amsa wayar", ba tare da ta jira amsar yarinyar ba ta ƙarasa kusa da wayar, ganin me gadi ne yasa ta kuma jan tsaki sannan ta ɗaga, nan ya sanar mata da zuwan baƙuwar, tace ya barta ta shigo.
Ya buɗewa Sahabat get ɗin ta shigo, tun daga farfajiyar gidan ta fara haɗiyar miyau domin irin kyawun da gidan yayi mata, ko'ina interlocks ne a shinfiɗe a wajen sai dai gefe da gefe inda aka shuka shukoki domin su ƙara ƙawata gidan.
Hanyar data gani wacce ta miƙe samɓal ita ta cigaba da bi har ta iso ƙaramar farfajiyar gidan, a hankali ta tura ƙofar ta shiga dogon corridor wanda tun daga nan ta fara jin sanyin Air Conditioner tana ratsa ta, Sahabat ta lumshe idanu jin har tsigar jikin ta na tashi.
Sai da tayi tafiya me nisa kaɗan sannan ta iso waje me kama da varender wanda aka sakawa labule me zare-zare yana kuma walwali, a hankali ta ɗaga bakin ta ɗauke da sallama.
Numfashinta ya kusa ɗaukewa ganin wani irin haɗaɗɗen falo, komai na ciki lemon green da milk ne har long chairs ɗin dake falon, ga ƙaton tibin bango wanda yake ta aikin shi, ƴan mata biyu ta samu a zaune, suna ganin ta suka zuba mata idanu, tayi murmushi sannan tace; "sannun ku", babu yabo ba fallasa suka amsa da "yauwa.
"Amm, Hajiya fa ko tana nan?", Sahabat ta tambaya, ɗaya ta kalli ɗaya sannan suka juyo suka ƙara zubawa Sahabat idanu har ta fara tsarguwa.
Ta kalli kayan jikin ta, riga t shirt ja sai pencil skirt baƙi inda ta ɗora top har ƙasa me baƙi da ja a sama, mayafi ma baƙi ta yafa sosai shigar tayi mata kyau abinka da ƴar duma-duma😉.
"amm.....nace dan Allah Hajiya na nan?", ta sake tambaya a ɗan ƙufule dan ita gani take kamar sun raina wankan ta.
Sai lokacin suka dawo daga duniyar yabo da kwaɗayin tsarin halittar yarinyar dan suna ganin ta sun tabbatar zasu girmeta.
Baƙar me ƴar siririyar mara kuma tsayi tace; "eh tana ciki, Suhy ɗan kira ta", ta ƙarasa tana kallon baƙar me tsayi.
Wacce aka kira da Suhy tace; "to zauna ina zuwa, Zuby ki bata wani abun mana", ta miƙe ta nufi wata ƙofa itama ta glass ce wanda Sahabat tana iya hango komai ta nan, inda kuma karamin wajen.hutawa ne me kyau da tsari.
Sahabat tabi Suhy ɗin da kallo, riga ta saka me kama da vest sai wando legines iya gwiwa, eh to babu laifi dan tana da ƙugu sai da fa babu komai a ƙirjin.
Ta kai kallon ta kan Zuby wacce ke ƙoƙarin shigewa Kitchen ita kam babu gaba babu baya amma duk da haka sai faman iyayi take ita a dole ga mace, dan ita riga ce iya cinya ta saka wacce a mutunce sai dai ka saka ta da wando.
Kan ta gama tunanin har Zuby ta dawo hannun ta ɗauke da lemo da kuma glass cup sai ƙaramin bowl cike da kayan ƙwalama.
Koda ta ajiye kasancewar rigar samanta a buɗe yake hakan yasa Sahabat ta hango brezier guda biyu da Zuby tayi ciko da ita.
Saha ta matse bakin ta, tana faɗin; "kai Saha idanun ki ya cika kallon abinda babu ruwan shi", ta faɗi hakan a ranta tana me murmushi.
Bayan Zuby ta ajiye ta koma saman kujera ta zauna tana me zubawa Sahabat ɗin idanu, Sahabat kuwa hankalinta ta mayar kan plasma dake aiki.
Wani irin fitanannen ƙamshi ne ya dinfaro falon wanda babu shirin Sahabat ɗin ta juya domin kallon inda take jiyo ƙamshin.
Hajiya Kareema ce tana tafe hannun ta riƙe dana wata budurwar ƴar kyakkyawa mara tsayi, sai dai tayi ɗoɗar sunan wani mulki namu daga gani kasan mai ke aiki dan har wani kashe idanu take yi.
Sahar ta taɓe baki ganin Hajiya Kareemar sanye da wando da riga, ita kuma yarinyar sanye da riga doguwa ta ɗame ta.
Hajiya Kareema na ganin Sahabat ta fara sakin murmushi tana faɗin; "Lale maraba da Beauty", Saha tayi murmushi tana me saukar da kanta ƙasa.
Hakan ne yayi sanadiyar rashin ganin lokacin da Hajiya kareema ta kai bakin ta saman ƙirjin wannan yarinyar yayin da hannun ta kuma yake saman ƙugun ta, ta shafa kaɗan sannan ta sakarwa yarinyar kiss a ƙirjin ta, sannan ta sake ta.
"Amm..... Safeena kije gida kawai zamu yi waya zuwa anjima kinga yanzu nayi baƙuwa me mahimmanci, Suhy ki bata wannan jakar babu yawa wannan kuma gashi ki yiwa ƙannen ki tsaraba".
Safeena ta washe baki tana murna, bata taɓa tunanin harka da manyan hajiyoyi haka yake ba sai yanzu lallai ne dole ta godewa ƙawarta Suhy wacce ta ɗora ta akan wannan harkar.
*Zuby ainihin sunanta shine Zubaida haifafiyar garin Katsina ce karatu ya kawo ta nan kaduna inda ta haɗu da Suhaila(Suhy) wacce take ita kuma ƴar Jos kasancewar halin su yazo ɗaya na son kuɗi wannan shine silar da suka ƙulla abota kuma suka fara gantalin su cikin garin kaduna, sun haɗu da Hajiya karima inda nan ta zama Mummyn su yayin da suke biya mata buƙata itama tana biya musu nasu, yawan carry over da suke dashi yasa aka kore su daga jami'ar dake kaduna shine fa suka tare gidan Hajiya Kareemar kuma har lokacin iyayen su basu san da an sallame su a makaranta ba( iyaye ya kamata ku dinga kula da makarantun yaran ku dan sau da yawa akan kori ƴaƴan naku amma baku sani ba Allah yasa mu dace)*.
_Safeena kuwa talauci ne yayi musu katutu, ga mahaifin su da Allah ya yiwa rasuwa, hakan yasa suka shiga cikin ƙunci wannan dalilin yasa har makaranta suka dena zuwa, ga Safeena tana ƙaunar cigaba da karatu wata rana sai ta haɗu da Suhaila dama sune ke yiwa Hajiya Kareema farautar ƴan mata, bata wani sha wahala ba wajen shawo kan Safeenar, yau shine ranar da suka fara ita da Hajiya Kareemar_.
Ragowar kuma ta kan ja ra'ayin masu zuwa ganin ta wato masoyan littattafanta na batsa da maɗigo wannan shine ta hanyar da takan samu ƴan mata.
"haba Beauty kamar ba ƴar gida ba kin ƙi sakin jiki kici abinci ko dan ganin wa'innan ne", Saha ta girgiza kai.
Hajiya Karima ta kalli Suhy da Zuby fuska ɗaure domin ita kanta ta lura da kallon da suke bin Sahabat ɗin dashi tace; "maza ku wuce naku ɗakin", ba dan ran su yaso ba suka nufi ɗakin suna me baƙin cikin hana su kallon yarinyar.
Hajiya kareema ta taso ta dawo kusa da Sahabat ta zauna, sannan ta riƙo hannun Sahabat ɗin cikin salon yaudara da iskanci tace; "haba Beauty na faɗa miki ki dauke ni kamar Ummi mana bana jin daɗin yadda kike jan baya daga gare ni", Sahabat kuwa ta kasa cewa komai tsabar mamakin iskancin matar.
Cikin dabara ta ƙwace hannun ta sannan ta ɗauki glass cup ɗin ta kai bakin ta, Hajiya Kareema kuwa har lokacin hankalin ta be wani dawo dai-dai ba, gashi dama bata gama samin natsuwa da Safeena ba Sahar ta zo gashi kuma zama da tayi kusa da Saha ya jifata wani hali.
Saha kuwa banda jan tsaki babu abinda ta ke yi itafa ta fara lura da take-taken wannan matar kamar ƴar maɗigo ce, batama san a ina Ummi ta haɗu da ita ba, gashi dama can ita ƴan maɗigon ba birge ta suke yi amma zata zuba mata idanu taga gudun ruwan ta.
Ko minti biyar bata ƙaraba ta miƙe akan zata tafi, Hajiya Kareema jikin ta har rawa yake yi wajen kwasowa Saha kayan kwalliya turarrurruka, atamfa da abin hannu wai gashi nan taje tayi gayu dasu.
Saha tace; "nagode sosai", Hajiya Kareema ta riƙo hannun ta tace; "kada ki damu ni me son ki ce, ni dai ina roƙon ki da kada ki juya mini baya", Saha ta ɗaga kai.
Hajiya Kareema taja Sahar zuwa waje inda suna tafiya tana samun damar murza lallausan tafin hannun Saha ɗin, da Saha na gyara tafin hannun ta sosai don ta san Sahibinta na so wato Zaiyad.
A harabar gidan ta tsaya sannan ta ƙwalawa Idris driver kira, babu ɓata lokaci yazo ta miƙa mishi key na mota sannan tace; "gashi ka kai mini Sweet Baby na gida", Saha ta bita da wani kallo wai Sweet Baby.
Mota jibgegiya High lander ita ta buɗewa Saha baya ta shiga, sannan Idris ɗin yaja motar, tana tsaye tana ɗagawa Saha hannu har suka fice daga gidan.
Hajiya Kareema ta sauke ajiyar zuciya sannan tace; "ai tunda na ƙwallafa rai akan ki sai na sami abinda nake so yarinya ki gama gudun ki", ta faɗa tana ƙarasa shigewa ciki.
Tun daga falo ta fara ƙwalawa su Suhy kira, Suhy da Zuby da suke manne da juna dan suma ganin Sahar ba ƙaramin tayar musu da hankali yayi ba.
Hajiya Kareema ta kuma ƙwala musu kira babu shiri suka saki juna suka yo waje domin jin me yake faruwa, Hajiya kareema na ganin su ta ƙara kusa dasu ta janyo Zuby jikin ta yayinda ta haɗe bakin ta dana Suhy da sauri nan suka shiga aikata masha'ar su.
*wa'iyazubillah*
********** ***********
Kwanaki nata shuɗewa inda a yanzu saura kwana uku a ɗaura auren Abdulkareem da Jamila, babu masifar da Jamila bata yi ba amma Abdulkareem yaƙi fasa auren saima Allah yake a kawo masa amaryar sa koya sami sauƙi.
Yauma ƴan uwan shi ne suka kawo mata kayan faɗar kishiya, Salma ta tuna da huɗubar Jameela inda take cewa kada ta yarda ta raga musu dan suma munafikai ne.
Salma tabi matar yayan shi da kallo bayan ta gama ɗaga mata kayan wai nan tana nuna mata, Salma tayi yaƙe sannan tace; "ina zuwa", sun ɗauka tukwuici zata basu har suna washe baki dan basu san me take yiwa Abdulkareem ɗin ba dan baya zuwa gida ya faɗa musu.
Salma kuwa galan na kalanzir ta ɗauko da ashana, suna zaune sai ganin ta suka yi da kalanzir da ashana ta buɗe galan ɗin ta fara tsiyayawa saman kayan.
Duk suka zuba mata idanu, sai da ta gama tass sannan tace; "kune munafikai wato ko harda ku za'a haɗa baki a kawo wata cikin gidan nan to zaku ga aiki da cikawa kuma na tabbatar muku yadda na ƙona kayan nan haka zan ƙona amaryar zaku san dani kuke magana", tana gama faɗar haka ta cilla asha saman ƙaramin akwatin.
Da sauri ƴan uwan suka ɗauke ragowar biyun da kada suma su kama yayin da ƙanwar Abdulkareem ɗin ta yi waje da gudu domin ɗebo ruwa tazo ta sheƙawa akwatin da yake ci.
Cikin fushi Gwaggon su tace; "Salma wannan wane kalar rashin hankali ne?, bafa kanki aka fara kishiya ba kuma ba'a kanki za'a gama ba kiyi haƙuri mana komai zai zo ya wuce amma kina ƙona dukiyar mijin ki kamar wani kayan bola babu damuwa babu komai".
Salma cikin rashin kunya tace; "dakata Safiya ai ban ga hakan a cikin gidan ki ba idan kina so ki nuna mini zahiri sai kije ki cewa Habu ya ƙara miki wata daga nan nima zan yarda da abinda kike faɗa amma ke kina zaune a gidan ki tsofai-tsofai dake kin kanainaye naki mijin da asiri da tofe-tofe da jiƙe-jiƙe ni kuma sai ki kwaso ƙafa kizo don ki taimaka wajen a kawo mini kishiya to wallahi ki kwashi ƙafafun ki dake da ƴan koron naki kan nayi muku na cikar shekara", bata gama rufe baki ba Ƙanwar Abdulkareem ɗin ta kwashe ta da mari, Salma ta buɗe baki zata kuma magana ta ƙara kwashe ta da mari.
Cikin fusata tace; "ko Yaya Abdulkareem ba zai kalli Gwaggo ya kirata da sunan ta ba balle ke da kike cin arziƙin zama dashi, wallahi kika sake kika kuma kallon Gwaggo da sunan zaki yi mata rashin kunya sai mun lalllasa ki a gidan nan kuma aure babu fashi sai mun shigo da Amarya gidan nan ko ki so ko kada ki so banza ballagaza ke waye yace kada ki kama naki mijin tunda kin saki wata kuma ta cafke a waje ba shikenan ba Shashasha soloɓiyo".
Gwaggo ta dakatar da ita tace; "barta Halima ta cigaba da abinda take yi idan har hakan shi take ganin dai-dai lallai Salma kin canza dole Abdulkareem ya ƙaro