Showing 54001 words to 57000 words out of 107295 words
Chapter 19 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
dawo idan Ummi taji abinda ya faru.
Hannu ta kai ta yaɓa saman girar shi zuwa idanun shi, lallai Zaiyad ya nuna mata shi cikakken namiji ne wanda kowacce mace take burin samu.
Idanun shi ya buɗe sannan ya kalle ta, cikin muryar barci yace; "my Habat har kin tashi", ta saki murmushi tace; "kai my love tun ɗazu fa nake barci", yayi murmushi yana miƙewa yace; "muje muyi wanka".
Kamar tace a'a sai kuma ta tuna da littafin Ummin nata inda take cewa jaruman littafin tare suke wanka, tayi dariya wato dai Zaiyad shine dai-dai ita kenan wanda zai bata kulawa sosai.
Bata idasa tunanin ba taji anyi sama da ita, shagwaɓe fuska tayi tana faɗin" kai My love ka sauke ni zan iya tafiya da kaina", ya ƙara haɗa ta da ƙirjin shi yana faɗin; "ai naga kin tsaya tunani da shakkun so da kulawar da zaki samu ni kuwa so nake na tabbatar miki da irin son da nake miki ne".
Ta ƙara shigar da kanta cikin ƙirjin shi tana me farin ciki da murnar samun Zaiyad ɗin a matsayin masoyin ta, a wajen wankan ma haka ya dinga jagwalgwala ta sai da ya gama son ranshi sannan suka yi wankan suka fito.
Kayan jikin ta ta maida sannan ta fito falo, a zaune ta same shi saman kujera ya kalle ta yace; "kai My Habat kinyi kyau sosai nazo na maida ke gida ko?".
Ta kalli agogo ƙarfe huɗu da mintina, ta girgiza kai tace; "ai da sauran lokaci na cewa Ummi sai shida", yayi dariya yace; "ba zaki shiga islamiyya ba kenan?".
" ka bari sai shida saura sai kawai ka ajiye ni a bakin makaranta", ta ƙarasa tana yamutsa fuska, haka suka ƙarasa zaman tare har shida saura sannan ya ɗauke ta har ƙofar makarantar tasu.
Suna cikin mota suka hango an fara fitowa hakan na nuna an tashi kenan, Zaiyad ya buɗe locker dake motar ya zaro ƴan dubu-dubu guda takwas ya miƙa mata.
Tayi murmushi ta amsa tana faɗin; "thanks my love", ya ɓata fuska yana faɗin; "ni bana son irin wannan godiyar", tayi dariya sannan ta haɗe bakin su.
Zaiyad kuwa kamar jira yake ya cafke harshen ta suka hau sumbatar juna, tsayin lokaci suka ɗauka a haka sannan suka saki juna suna maida numfashi.
Zaiyad ya maida numfashi yana faɗin; "My Habat wannan irin salo haka, gaskiya na more sosai da samun ki, ji nake kamar kada mu rabu".
Sahabat tayi murmushi tace; "gobe ma ai zan fito mu sake haɗuwa", cikin jin daɗi yace; "dats my Habat", haka suka yi sallama ta fita kasancewar da ɗalibai a wajen yasa babu wanda ya damu da fitowar ta dan babu wanda ya lura da ita ma.
Har cikin makarantar ta kutsa sannan suka haɗu da Hajna da Na'eef da alamu ita suke nema, nan ta riƙo hannun su suka nufi gida.
Koda suka shiga gidan kamar yadda ta zata haka ta tarar da Ummi hannun ta riƙe da waya tana faman dannawa, tana ganin su tace; "yauwa Sahabat tunda kin dawo ɗan wanke tukunyar can ki ɗora mini ruwan wanka".
Sahabat kamar ta fasa ihu haka take ji shiyasa fa bata so ta dawo gidan nan saboda aikin da Ummi zata dinga saka ta, haba ita kenan aiki kamar engine.
*************
Hunayda ke zaune tayi tagumi tana tunanin Malam Suhayl bata taɓa tunanin zata so wani har haka ba, ashe dama haka soyayyar take gashi daga tafiya ko kwana biyu be yi ba amma ji take kamar an shekara, taja wata irin nannauyiyar ajiyar zuciya.
Ammi dake tsaye a kanta tace; "Hunayda!", cikin sauri ta ɗago ta kalli Ammin nata sannan tace; "na'am Ammi".
"Hunayda ya kamata kiyi haƙuri haka ki dinga maida hankali akan sauran al'amuran dake gaban ki, kada ki manta tafiya fa ba mutuwa bace kuma insha Allah Malam Suhayl zai dawo ya same ki, haba kinji ta Suhayl".
Hunayda tayi saurin rufe fuskar ta tana dariya cike da kunyar abinda Ammi ta faɗa.
Ammi tace; "yanzu kije kiyi wanka sai kizo ki share tsakar gida kinga yamma tana daɗa yi", babu musu ta amsa da to tana nufar ɗaki domin cika umarnin mahaifiyar tata.
Ammi tayi murmushi tana bin ƴar tata da kallo, yanzu Hunayda ta natsu kamar ba ita ba, lallai dole ta godewa Allah ta kuma godiya ƙawarta Hajiya Gambo tare da Sumayya Babayo Abdullahi wa'inda suke taimaka wajen sai-saita ƴar tata har ta dawo nutsuwar ta.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
[2/24, 9:56 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) said:
'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'"
[Bukhari (also by Muslim).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ .
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 17*~
Jameela tayi sallama ta shigo cikin gidan, da sauri Salma ta ajiye wayar dake hannun nata ta tarbo ƙawar ta ko ince aminiyar ta, sosai suke farin ciki da ganin juna.
Salma tace; "ai na ɗauka da wasa kike ba zaki zo ba", Jameela tayi wata irin dariya sannan tace; "ai zuwa ya kama ni dole wace ni ai dole nazo", ta ƙarasa tana bin gidan da kallo.
Da hannu ta nuna ɓangaren da Abdul ke mata gini tace; "wancan fa da naga an tada ginin, ƴan haya zai zuba?".
"ina fa wai nan na amarya ne", Salmar ta faɗa tana taɓe baki, Jameela itama ta taɓe baki sannan tace; "au ashe da gasken yake kenan ai na ɗauka wasa yake yi wallahi, amma wannan amarya zata ga rashin mutunci,yanzu duk wannan tsantsara ginin da ake yi nata ne?".
Salma ta taɓe baki tana faɗin; "bar namiji munafiki, rigar ƙaya ki saka ya soke ki, ɗan bushiya sai kin goya shi ya sakar miki ƙaya, ƙanin ajali kenan kobe kashe ki ba ya barki jinya, ai duk wacce ta riƙi ɗa namiji uba zata mutu marainiya".
🙄Bani na faɗa ba inji oga Salma babu ruwa na a ciki🙊.
Jameela tayi shewa tace; "ashe kina fahimta ai lallai kin fara shigowa gari ai na ɗauka har yanzu kina nan cikin duhun kan naki".
Salma ta jefa mata harara tace; "aiko yanzu bayana zaki biyo dan na tabbatar a wayewa da rashin mutunci na ɗara ki".
Jameela tayi munafikin murmushi tace; "a'a fa tukunna dai Salma ai a halina idan aka kasa casa'in to ko kaso ɗaya baki gama sani ba, yanzu dai muje ki nuna mini ɗakin amaryar taki".
Salma tace; "au wai ke tunanin ki zan bari ta shigo ne ai ina hakan ba zai taɓa yiwuwa ba", Jameela tace; "kuma fa hakane amma shiya kamata ki tadawa ɓalli har ya fasa".
Salma ta juyo ta kalle ta tace; "ke wallahi ina yi mishi kawai dai kunnen uwar shegu yayi dani amma zan kuma dagewa zai san kaidin mace nada yawa".
Jameela tace; "ai dama kaidin mace yawa gare shi dan ina da tabbacin koke baki gama sani ba balle shi da yake namiji,lalala cancanɗi gaskiya masha Allah".
Sosai suka zagaya part ɗin komai yayi two bedroom da kuma falo sai kitchen da bayi komai yayi zam-zam abinda ya rage kawai fenti da pop shikenan.
Aikuwa komai yayiwa Jameela yadda take buƙata, suna tafe tana kuma zuge Salma akan irin rashin mutuncin da zata dinga yiwa Abdul ɗin.
Ita kuma da yake sauna ce sai naɗewa take yi kamar ana biya mata fatiha, sosai kuma yake zama a kanta.
Haka har suka koma falon Salmar suka zauna, fira suke sha sosai har zuwa azahar sannan Salma ta shiga kitchen ta girka musu taliya suka zo suka ci.
Sun gama kenan Jameela ta dube ta tace; "wai ya maganar wannan munafikar fatan dai baki kuma yi mata magana ba ko?".
Salma tace; "tun yaushe nayi blocking ɗin ta ai naga ba zamu dai-dai ta ba, na ɗaga mata red card", suka saki shewa suna tafawa.
Sai uku da rabi sannan suka ji shigowar me gidan shida yaran, cikin dabara Jameela ta ƙara gyara ɗaurin dake saman kanta.
Da sallama a bakin shi ya shigo riƙe da hannun Mussadiq da kuma Husna, Jameela ce ta amsa tana me jefa mishi wani kallo cike da so ƙauna.
Salma kuwa tsaki taja ta juyar da kanta hakan ya hana ta hango Jameelar yadda take bawa filawar ruwa.
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke yana me ƙaran binta da kallo, sanye take da baƙar abaya sai gyale wanda shita naɗa a kanta tayi ɗaurin zamani, shigar da Abdul ke matuƙar so kenan.
Ya maida kallon shi kan salma da har lokacin take sanye da doguwar riga ta barci alamu ya nuna tunda ya fita har ya dawo bata yi wanka ba.
Mamakin shi ɗaya taya akayi Jameela ta san shigar da yafi so, taya ba zata sani ba bayan matarka sauna ta karance mata tas🙄.
Cike da kasala ya ƙaraso domin irin gajiyar da yayi ga kuma halin da Jameelar ta jefa shi wanda inama ace Salmar ce tayi wannnan shigar da yafi jin daɗi.
Cikin wata iriyar murya Jameelar ta gaishe dashi ai sai da ya nemi waje ya zauna yana me sauke numfashi.
Ya saci kallon Salmar ya kamata ace zuwa yanzu ta harbo jirgin nasu amma da yake ƴar can kwanar ce bata fahimci komai ba.
Ko sannu da zuwan da ƙyar ya samu daga Salmar, ya kalli Husna yace; "yau kuma fushi ake yi dani ko sannu da zuwan ba zan samu ba".
Ke da bakya wajen idan kin tanka to Salma ta tanka, ya juya ya kalli Jameela wacce har lokacin shi take kallo ji yayi kamar ƙasa ta buɗe ya shige.
Cikin sauri ya nufi bedroom ɗin su, Salma tabi hanyar da yabi da harara tana jan dogon tsaki, Husna da Musaddiq kuwa ɗakin su suka wuce domin canza kaya.
Ya ɗan jima a ciki a tunanin shi ko Salma zata biyo shi amma shiru haka ya haƙura ya fito, suna a yadda ya barsu alamu ya nuna kenan bata shiga domin taimakawa yaran ba.
Ɗakin yaran ya shiga, ya sami Husna har ta cire nata kayan tana taimakawa Musaddiq ɗin domin shima ya cire nashi.
Hannun su ya riƙo suka fito tare, tsabar haushi ko kallon inda Salmar take beyi ba, ya fice abin shi.
Jameela na ganin ya fita, tayi shewa tace; "kina wuta matar nan, gaskiya kina birge ni ai kada kiyi mishi da wasa kwata-kwata".
Salma ta ƙara hura hanci jin abinda Jameelar ta faɗa tace; "ai masifa da bala'i yanzu ya fara gani cikin gidan nan wallahi".
Jameela tayi mata jinjina tace; "wallahi kina birge ni ƙawata bari na tashi na tafi gida", Salma ta taɓe baki tace; "tun yanzu?.
Jameela ta miƙe tana ɗaukar ƴar ƙaramar jakarta tace; "gwara ke a gidan ki kike nifa Mama na can na jira na", haka Salma ta rako ta har bakin get yayin da Jameela ke ƙara zuga ta.
*******************
Yanzu Sahabat liƙafa ta cigaba domin kuwa a koda yaushe tana gidan Zaiyad don ƙaryar da tayi akan musabaƙa da zasu je hakan yasa Ummi barin ta ba tare da wani tunani ba.
Ta ɓangaren su kuwa rayuwar su suke kamar ta miji da mata kullum ya kan ɗauke ta haka suke wuni tare bayan sun gama holewar su ya kaita bakin makaranta inda anan zata jira ƙannen ta suzo su wuce gida.
Kuɗi da sauran abubuwan ƙwalam da maƙulashe babu abinda Zaiyad baya siya mata, idan ka ganta yanzu tayi kyau har wani ƙyalli take domin kuwa ruhin ta da gangar jikin ta na samin abinda take so.
Hajna kuwa ga abin magana amma babu bakin yin ta, daga um sai um wai uwar gulma tayi cikin shege, ita dai ta zubawa ƴar uwar tata idanu ne tana tsoron yi mata magana yayar tata ta dena ƙara mata kuɗin tara hakan yasa taja baki ta tsuke.
Yau Alhamis dan haka babu yadda Saha bata yi ba amma Ummi ta hana ta fita ko'ina hakan ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba.
Tana shiga ɗaki taja dogon tsaki, dan ita yanzu ji take dai-dai da Ummi ganin cewa abinda Ummin ta sani itama ta sani.
"yanzu mutum ba dama ya sami ƴancin kanshi, sai ayi ta faman damun shi mtsew, ashe abinda take mini baƙin ciki kenan, ita da mutuwa ta ɗauke nata shi yasa nima take so ta hana ni hutawa da jin daɗin rayuwa ta, mtseew gidan ku amma baka da sakewa", cewar Sahar kenan cikin zunɓurar baki.
Allah ya shirye ki Sahabat, da alamu kinyi nisa bakya jin kira🙄.
Sai da ta kuma tura ƙofar ta rufe sannan ta ciro waya ta fara kiran layin nashi, be ɗauka ba har ta katse, babu jimawa sai gashi ya biyo kiran.
Tana ɗagawa ta sakar mishi wani kuka irin na shagwaɓa har da sheshsheƙa, Zaiyad ya ruɗe gaba ɗaya.
"haba matar Zaiyad me yake faruwa ne?", cikin shagwaɓa tace; "ba Ummi bace ta hana ni fitowa", ya ɗan yi jim sannan yace; "babu komai Allah ya kaimu asabar ɗin".
"nifa yanzu ina son ka ji nake kamar ba zan iya rayuwa babu kai ba", faɗar Sahabat kenan.
Zaiyad yayi murmushi yace; "kada ki damu insha Allah Daddy yana dawowa zamu yi aure".
Sosai hakan ya faranta ran Sahar har tayi murmushin da haƙoran ta suka bayyana, kaɗan suka yi fira sannan suka suka yi sallama.
Haka ta tura wayar cikin rigar ta sannan ta fito, abin ban haushi shine Ummin tana zaune da waya a hannun ta tana dannawa kamar ko wane lokaci.
Saha tayi ƙwafa a ranta tace; "anjima za'a sake sakar mana me zafi kenan?".
Ummi ta kalle ta tace; "Saha aje a ɗora abinci, yanzu Hajna ta tafi siyo Kabeji, kafin ta dawo kin ɗora kinji ƴar albarka".
Saha ta ɗan turo baki gaba sannan ta wuce kicin ɗin tana ƙunƙunai, wanda ita Ummin bata ma lura da me take ba.
******************
Ammi data shigo ɗakin ta kalli ko'ina tayi murmushi, a koda yaushe tana ƙara godewa Allah akan shiryar mata da yarinya da yayi.
Wayar Hunaydar ta hango saman dressing mirror ɗin ɗakin nata, cikin sauri Ammi ta ɗauka.
Koda ta bincika babu wani abu wanda zai nuna ma na ɓatanci ne, hakan yasa ma Hunaydar bata sakawa wayar Password ba.
Hunayda ta fito daga bayi hannun ta riƙe da Izal, tayi murmushi tace; "Ammi sannu da hutawa".
"sannu da aiki ke kuma ƴar albarka", Ammi ta faɗa cike da jin daɗin yadda ƴar tata take yanzu.
Hunayda ta ɗan langaɓe kai, Ammie tayi murmushi tace; "ya akayi me kike son cewa".
Hunayda tayi murmushi tace; "dama Ammie ina so ne na idan babu abinda zan miki gobe zamu je kasuwa nida Surayya".
Ammie tace; "babu komai Allah ya kaimu sai dai zamu je tare ne daku sai ku zaɓi abinda kuke so ko?".
Hunayda tayi murmushi tace; "shikenan yadda kika ce Ammi", tana faɗin hakan ta ɗauki wayar ta fice daga ɗakin.
Koda taje ɗakin su Surayya har ta gama gyara ɗakin don haka bayi kawai Hunayda ta wanke.
Ta koma ta zauna kusa da Surayya tace; "Ammi ta amince tace ma tare zamu je", Sosai Surayyar tayi murna da shiriyar ƴar uwar tata.
Ita kanta Hunaydar yanzu tafi jinta cikin