Showing 102001 words to 105000 words out of 107295 words
Chapter 35 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
shi yace dole ya aure ta bayan ta haihu, Ummee tayi farinciki da jin haka ko ba komai asirin su zai rufu amma tasan akwai babban kalubale gaban ta wajan fuskantar mutane da yan uwa saboda ta sani ko a wajan 'yan uwan ta ba zata tsira ba bare a je ga dankin Baban su Saha.
Ita kuma Saha tunda taji labarin bai dame ta ba saima kara kaimi tayi wajan yiwa Ummee iskanci son ranta dan wani lokacin in taga Ummee zaune a parlour sai ta zo itama ta zauna d'an nesa da ita tayi ta maimaita novels na Ummee wanda zai sata ta bar wajan ba shiri dan kunya ne yake lullub'e ta ji kaman ta nurse kasa,yau ma ganin Ummee zaune yasa tazo ta zauna tana" wash na kwana 2 ban karanta sabin novels masu saka ni nishad'i ba amma bari in karanta na bayan saboda bana gajiya da karanta wannan novel d'in saboda dad'in ta". Ummee tana jinta bata tanka mata ba kamin ta ankara taji ta fara karanta wani zazzafan page data rubuta wanda sai da fans dinta a ranan suka cika mata waya da recharge card saboda yanda ta zuba shaid'ancin a ciki abun ba'a magana.
A zuciye Ummee ta kwace wayar tayi jifa dashi ya fad'a kan kujera tace" ya ishe ki haka Sahabbat kada kiga ina kyale ki kina abinda kika ga dama hakan ba wai yana nufin kin gagare ni bane kuma kada ki manta har abada nice mahaifiyar ki....." Ummee kenan na san kece mahaifiya ta shiyasa Kika ga ina kokarin nuna miki yanda zaki gyara lahirar ki,ko kunnuwanki sun gaza sauraron abinda kika rubuta da hannun ki saboda munin su amma kuma a haka wasu yaran da basu fi 13 ko 15 years ba suma sun karanta kuma yana cigaba da yawo a social media Allah kad'ai yasan shekarun da za'a dauka kamin ya b'ace sannan duk wanda ya karanta ya lalace ta sanadiyan novel dinki kina da naki kason a kowani abinda ya aikata" kukan Ummee daya tsaanan ta shiya hana ta karasa abinda tayi niyya tayi shiru ta zuba mata ido tana share nata hawayen.
"Nayi nadama Saha nayi nadaman ban tab'a yin irin shi ba a rayuwa ta bana cikin kwanciyar hankali kullum idan na tuna cewa babu yanda zanyi na goge abinda na rubuta kullum kara yaduwa yake kuma zunubai na kara hauhawa suke abin yana kara firgita ni,koda yaushe cikin istigifari nake ko Allah zai yafe min " Ummee ke fad'an haka cikin marairaicewa" Allah zai yafe miki Ummee na tunda kinyi nadama kuma kinyi tuban gaskiya, Ummee nima ko yaushe a cikin ta nake na biyewa son zuciya da rudin shaidan na b'ata rayuwata Allah ka yafe min...." Rungume juna sukayi dukan su 2 suna kuka kaman ransu ya fita kana ganin su zaka san sunyi tsatattaciyar nadama.
Zaiyad saida yayi sati 1 a hospital bed sannan ya samu sauki aka sallamo shi ya dawo gida zuciyar shi na masa ciwon abinda Baban shi yayi mishi wai ace mahaifin shi da kan shi ya mika shi ga police maimakon ya kare shi,tunda ya dawo yake ta cincin magani shi a dole fushi yake ,Baban shi yana ankare da shi amma bai kula shi ba saida yayi kwana 2 da dawowa sannan ya kira shi suka zauna dashi a parlour harda Maman shi sannan ya fara bayanin dalilin da yasa ya kira su yace" na dad'e ina jin rad'e-rad'in abinda kake aikatawa amma banyi saurin yanke hukunci ba saida naga zahiri shiyasa na bari police suka koya maka hankali ka sani Zaiyad shi zina da kake gani bala'i ne banda azabar Allah dake jiranka acan kiyama anan duniya kuma bashi ne in kayi da 'yar wani sai anyi da 'yar ka na tabbata ba zaka so ace wani ya aikata maka abinda kakewa 'ya'yan mutane ba.
Kai ba yaro bane haka kuma kai ba jahili bane amma ka biyewa son zuciya ka yi gaggawar tuba ka koma ga Allah tun kamin lokaci ya kure maka,munyi magana da shi Baban yarinyan kan cewa tana haife cikin dake jikinta za'a d'aura maka aure da ita". A razane ya d'ago yana kallon Baban shi dan yanda yaji saukan maganan kaman saukan guduma a tsakiyan kan shi tayaya za'a ce za'a aura mishi Sahabbat duk dacikin 'yan mata da yayi mu'ammala dasu babu wacce yake jinta a cikin ran shi kaman ita amma gaskiya ba zai iya auran ta ba domin ba shida burin daya wuce ya samu sweet sixteen kuma virgin ya aura sai gashi Baban shi yana son rusa mishi tsari,a raunane ya d'ago yace" nayi kuskure Baba ka yafe min amma dan Allah ina rokon alfarma kada kace inyi aure yanzu wallahi ban shirya ba".
"Haba Alhaji taya zaka ce ya auri yarinyan da ta gama wastewar ta harda cikin shege,kasan mutane da sharri kai kuma ka biye su ba tare da wani bincike ba".cewar Hajiya kenan dan tunda ya fara maganan take ta faman tab'e baki.
Murmushi Baban yayi yace" wannan maganan da kikayi shi ya kamata ki tambaya zai baki amsan cewa cikin nashi ne ko ba nashi ba,kai kuma bud'e kunnen ka kaji in kaga ba'a d'aura auren ka da yarinyan nan ba ka tabbata ita tace bata son ka dan haka tashi ka bani waje mutumin banza kawai". Zuciyar shi a jagule ya mike ya fita daga parlour kuma ya d'auri d'amaran yaki da ita Sahabbat har sai tace bata ce bata son shi da kanta.
Yana zuwa d'akin shi a fusace ya ficiko wayar shi dake jikin charging ya fara neman layin Sahabbat,kusan 5 missed calls ya mata amma bata d'aga ba.
A zuciye yayi cilli da wayar yana huci shi kad'ai yaso ace ta d'aga wayan nan domin abinda yayi niyyan yi mata sai tayi nadaman sanin shi da tayi a rayuwar ta.
Saha kuwa tana bacci bata san ya kira ba saboda wayar tana silent duk da yanzu kowa ya san tana da waya amma ta kasa cire shi a silent saboda sabo,tana tashi daga bacci taga missed calls d'in Zaiyad saida taji fad'uwar gaba kasancewar tayi iya kokarin ta ta cire tunanin shi a ranta kuma ko lokacin da Ummee ta bata labarin hukuncin da aka yanke na had'a su aure abin bai wani d'aga mata hankali ba amma yanzu gainin kiran nashi yasa taji duk hankalin ta ya tashi.
Tana shirin tashi taje wajan Ummee dan ta fad'a mata domin yanzu bata da abokiyar shawara sai Ummeen ta itama Ummee yanzu sai take jinta kaman ba ita ba saboda tana samun time ta zauna tare da yaran ta suyi hira ta fuskanci matsalalolin su ba kaman baya da bata da lokacin kowa saina fans nata,kara shigowan kiran Zaiyad ne ya hana ta tashi ta tsurawa wayar ido tana ji kaman kada ta d'aga saida ya kusan tsinkwa sannan ta d'aga ta kara a kunne ta ba tare da tace komai ba tana jira taji me zaice mata taji ya fara mata ihu a kunne yace" Sahabbat or whatever you are I don't care abunda nake so dake shine ki bud'e kunnen ki da kyau ki saurari me zance miki tun kamin dare yayi miki ki maza ki cewa wannan tsohon naki ba kya son auren nan if not kika yarda akayi auren nan wallahi sai na lahira yafi ki jin dad'i in yayi aiki mai kyau sannan kuma....." Dakata Zaiyad kada kace zaka cika min kunne da haushinka na banza ce maka akayi ni son auren naka nake? Amma tunda har kayi kuskuren nuna min kin auren nan a zahiri toh wallahi sai dai ka mutu dan wannan auren babu fashi". Tana gama fad'an haka ta katse wayar tana huci yau wai Zaiyad ne yake mata wannan bala'in dan ance ya aure ta amma da saboda ya cimma burin shi akan ta kullum sai ya ambato mata maganan aure da yanda zasuyi rayuwar su in sunyi.
*************************
Salma duk an watse an barta a gidanta tana zaune shiru tana jiran zuwan angon nata tare da fatan ya kasance mata irin mijin dasu *muna wuta* suke fad'a a novels din su,sai sak'a da warwara take na meye ya rike shi har yanzu bai iso gare ta ba duk da yanda yake nuna d'auki sa akanta amma gashi har 11 ta wuce shiru,gajiya tayi da zaman ta kwanta bata dad'e da kwanciya ba bacci yayi awon gaba da ita sai kusan 12 sannan ya shigo gidan direct d'akin nata ya shigo saida ya zauna a bakin gadon sannan ta farka suna had'a ido ya sake mata murmushi mai sanyi yace" amarya ayi min afuwa na tsaya sallama da abokai nane"
Tashi tayi daga kwancen tana d'an murmushi ta zauna sannan tace" kada ka damu ba komai".nan yace ta sauko suci abinci daya shigo dashi,bata musa ba ta sauko kasa da kanshi ya d'auko musu plates,cups da spoons sannan ya juye gasassun kaji daya siyo musu a plate yana ce mata bismillah ya fara durawa cikin sa bai ko tsaya ya lura da tana ci ko bata ci ba,saida yaci yayi Kat sannan ya cika glass cup da fresh milk ya shanye yayi gyatsa sannan ya mike ya shige bathroom dake cikin d'akin ya wanke hannun shi ko brush bai tsaya yi ba bare wanka ya zo ya haye gado yacewa Salma tazo su kwanta bayan ya rage kayan jikin shi.
Cike da sanyin jiki take kallon shi yanda bai tsaya ya kimtsa jikin shi ba yazo ya kwanta gashi ko nafila basuyi ba tace" ba muyi sallah nafila ba kuma ina son yin wanka kamin in kwanta" haba ke kuma wani wankan bayan wanda da kikayi a gidan ku? Maganan nafila kuma mayi anjima ai nafila sai dare ya raba ake yin ta".zatayi magana ya katse ta yana nuna tana b'ata mishi lokaci take,da kyar ya barta ta wanke hannunta ta dawo ko tattare wajan bata samu daman yi ba ya jawo ta suka kwanta.
Bayan komai ya lafa Salma idon ta 2 tana kallon yanda yake ta sharan baccin shi hankali kwance ko tsarkake jikin shi baiyi ba ya baje da bacci,ita ba wannan ne yake bata takaici ba sai na yanda ya rinka nuna mata shi a matse yake kaman wanda zaiyi wani abin kirki amma basu fi 30 mins ba wai har ya gama komai ya kama bacci,toh shi kuma haka yake ko kuma yau din ne yayi hakan saboda gajiyar biki? Abdukareem ta tuna a daren su na farko ko wasa kad'ai ya kai gud 1 hr yana yi da ita sannan ya kai ga wani abun amma shi wannan ko wasan ma bai iya ba kuma bai wani tabuka mata abin kirki ba illa kara kunna mata wuta da yayi ya kwanta abin shi.
Haka ta rinka juyi har kusan asuba sannan bacci yayi nasaran d'aukan ta,koda sukayi sallah asuba zata koma bacci yace shi da sassafe zai fita dan haka ta d'aura mishi breakfast yanzu,duk da tana jin bacci na cin idon ta amma haka ta hakura ta fito kitchen ta had'a breakfast mara nauyi tana yi tana tuna ranan ta na farko a gidan Abdukareem shine ya shiga kitchen yayi musu breakfast in short sai da tayi good 1 week bai barta ta shiga kitchen ba.
Istigifari tayi a bayyane saboda a tana matar wani bai kamata tayi tana tunanin tsohon namiji ba,tana gamawa ta kai komai kan dinning ta shiga ta tarar da shi fitowar shi kenan daga wanka ta tsaya tana kallon yanda yake shafa mai sauri-sauri bata ankara ba taji yace" baki iya gaisuwa bane zaki zo ki wani zuba min ido haka?" Saurin gaishe shi tayi daga inda take tsayen,maimakon ya amsa binta yayi da wani mugun kallo yace" saboda rashin tarbiya daga tsayen zaki gaishe ni sai kace ni sa'an kine".
Cike da mamakin yanda yake treating d'in ta daga jiya zuwa yau ta durkusa ta gaishe shi,bai amsa ba ya fito parlour ya hau kan dinning ya bud'e abincin da ta girka mishi yaga kwai ne kawai ta soya mishi sai bread da ruwan lipton,ture abincin yayi ya fara kwala mata kira da dukan karfinsa,har tuntube take wajan fitowa dama tana nan durkushe a inda ya barta mamakin abinda yake mata bai barta.
"Wannan wani irin shashanci ne,wannan shirmen shi kike kira girki sai kace wani d'an goye kika samu zaki wani soyo min kwai 1 ki kawo min shi a matsayin abincin?" Jin ya ambaci sunan kwai 1 yasa ta d'aga ido ta kalle shi da mamaki yace mata" me kike min irin wannan kallon ko karya nayi miki ke ga mai gara kada in cinye miki ko?toh wallahi ina gaya miki ki gyara halin ki dan saboda ni ba zan d'auki wannan shashancin ba"yana gama banbanin shi ya fice ya bar mata gidan.
Hawaye ne ya zubo mata tasa hannu da wuri ta share tana rarrashin kanta kan cewa ba haka yake ba maybe wani abin ne ya bata mishi rai,gyaran gida ta hau yi duk da ko Ina tsab yake dan su Aunty Jidda saida suka gyara mata ko ina jiya kamin suka tafi,tana gamawa ta fad'a wanka bata d'auki dogon lokaci ba ta fito ta zauna gaban mirror tayi simple makeup sannan ta saka wani atamfan ta na super wax mai golden da pink a jiki anyi mata dinkin doguwar riga yasha stone work ta gaba sosai kayan.sukayi mata kyau,turaruka ta fesa sannan ta fito parlour lokacin kusan 8:30na safe dan haka kan dinning ta wuce ta had'a tea har ta bud'e kwai data soya mishi amma ta kasa ci saboda yanda take jin zuciyar nata a cunkushe tea kawai ta sha ta dawo kan kujera ta kwanta tana tunanin abubuwa da suka faru daga daren jiya zuwa yau da safe bata san da me zata fassara shi ba,tana cikin tunanin bacci ya sace ta kasancewar jiya da daddare baccin ta kad'an ne.
Tana cikin bacci su Aunty Jidda suka shigo kusan su shida,tashin ta sukayi suna tsokananta wai ango ya hana ta bacci ya tara mata gajiya dole tayi baccin safe,ita dai bata kula su ba saima hankalinta data mayar kan su suka gaisa a mutunce.
"Kuzo Kuga girkin ango" wata cousin din su mai suna fareeda take fad'a musu lokacin da karambanin ta ya kai ta kan dinning ta bud'e abubuwa da suke wajan tana kallo " ai dama yanda naga Alhaji Naseer yana ta rawar kafa akan ki nasan zaki sha tarairayan" cewar Aunty Maryam kenan ita dai bata ce komai ba sai yake da take ta bin su dashi,zuwan su ya debe mata kewar dan sai hira da raha suke tayi rana nayi kuma suka shiga kitchen suka girka cous-cous da vegetable soup sannan suka hada coconut nd pineapple juice suka ci suka zubawa ango rabon shi a sabobin warmers masu kyau sai kusan 4 sannan suka tafi ba dan Salma ta so ba.
******************
A gidan Abdukareem komai sai kara tabarbarewa suke kan yanda Jameela take gallazawa su Husna amma har yanzu bai sani ba domin Jameela ta kware wajan iya munafurci sannan yanzu ta koma ruwa tsundum shima babu abinda ya fahimta kasancewar ta iya takunta,in a gaban shine nuna mishi take babu wani d'a namiji sai shi amma daga ya fita wajan aiki kuma ta riga da ta san lokacin fitan shi da dawowan shi yasa yana fita itama take saka kafa tayi ficewar ta bayan ta tsamma yaran abinci ta kulle su a d'akin su.
Abdukareem har yanzu Salma tana makale a zuciyar shi dan ma Jameela tana d'auke mishi hankali da salon ta,sosai yaji wani abu a zuciyar shi lokacin da labarin auren ta yazo mishi amma ganin yanzu ta zama matar wani yasa ya rage tunanin ta zuciyar sa itama Jameela data ji labarin Salma tayi aure abu 2 taji a ranta na farko taji dad'i kuma tayi nasaran kwace Abdukareem a hannunta na har abada kuma hakan ya tabbatar mata ba zata kuma dawowa suyi rayuwa tare ba sannan abu na 2 bata ji dad'i ba da Salma ta samu mijin aure da wuri haka taso ace ta kwashi shekaru ba aure kaman yanda ita tayi a baya.
""""""""""""""""""""""
Zaiyad kullum sai ya kira Saha yaci mata mutunci kan wai lalle sai ta fad'a a gidan su kan bata son auren duk da itama bata raga mishi in yace as sai tace mishi cas,tun abin yana damunta harta saba wani lokacin tana ganin kiran shi ba zata d'aga ba.
Cikin Sahabbat yanzu ya shiga wata na 7 duk wasu laulayi ta daina su sai girman da cikin nata yayi kaman ba cikin fari ba,zagi da tsegumi ta sha su daga wajan mutanen anguwan su harda ma 'yan uwan su kowa da abinda yake fad'a,wasu suce sakacin ummee ne wasu kuma suce dama Sahabbat idon ta a bud'e yake ka haifi d'a ne baka haifi halin shi ba.
Ummee duk tana jinsu amma ta d'auke kanta tayi kaman bata san sunayi ba cos abinda yake gaban ta yafi mata mahimmaci ga 'yan kungiyar su na*muna wuta* sun saka ta a gaba kan ta dawo da rubutu ko kuma zasu karbe matsayi da aka bata a bawa active ones,nan ita kuma ta nuna musu ta daina rubutun kwata-kwata su cire ta a kungiyar ma gaba 1.bata san 'yan kungiyar nasu basu da mutunci ba saida suka fara kiranta daya bayan d'aya suna ce mata sunji 'yar ta tayi cikin shege ko shiyasa ta ajiye rubutun basu kad'ai ba harda fans dinta masu zugata a lokacin da take rubutu sai gasu suna kiran ta sunayi mata izgili suna dariya abin da yayi sai ta canza sim card kawai ta bar wanda duniya ta san ta dashi.
A wannan lokacin Malam Sulaym ya dawo daga karatu da good result bai sha wahala ba ya samu lecturing a nan ABU zaria a fannin Arabic a wannan lokacin aka saka ranan auren su da Hunayda wata 2 kacal masu zuwa.
"Ammee ina neman izinin ki zan kaiwa Sahabbat kati koda ba zata zo ba saboda a da banida aminiya kamarta"Hunayda ce tsugune a gaban Ammee take neman izinin cikin ladabi.
"Ba zan hana ki ba hasalima hakan yana da kyau Allah yayi miki