Showing 45001 words to 48000 words out of 107295 words
Chapter 16 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
"You are always Welcome my love. Sleep tight"
Ya maimaita karanta saƙon yafi sau biyu, sai cen ya saki dariya, yana mai furta "Mata! Salon yaudarar ku daban ce"
Sai kusan ƙarfe sha biyu salma ta shiga ɗakin, shima har ta kwanta latsa waya take yi, wai style take gani na kwanciya, dayake group nasu ana tutturo su da yawa. Dalili kenan da yasa take ji bata iya barin yin WhatsApp koda kuwa za'a mutu. Gashi tana ta samun friends ta ko ina, kasancewarta yanzu ta idasa gogewa, ko ina shiga take ana damawa da ita yanzu. Ta ɓangare guda ga Jameela tight friend tata, wanda kaf, duk wani sirri nata kwashewa take ta faɗa mata, ita kuma wai tana bata shawarwari. Hatta da gyaran gida, da wankin toilet ɗin da yayi mata daga dawowar shi, saida ta kwashe ta faɗa ma Jameelar. Ita kuma sai bugun cikinta take ƙara yi. Tana ƙudurcewa a ranta, zata gane bata da wayau.
Cikin farin ciki Jameela ta tashi ta fara murza dulka a jikin ta. ko ba komai so take ta fita daban a idanun shi, duk da kasancewarta ba kyakkyawa ba, saidai zama da namiji fiye da ɗaya, ya sanya ta gane inda maza suka fi so.
Bata kwanta ba, saida ta tabbatar da ƙalƙale ko ina, ta sani Salma ta ɗara ta kyau nesa ba kusa ba. Amman ina amfanin kyawun da ba gyara.?
Saboda haka ne ta kwanta cike da farinciki. Tun da safe ta tashi ta fara toye toye da kimtse kimtse. Duk da kasancewar gidan su masu rufin asiri, ba dai makusa, kuma Maman ta tsaye take akan gyaran gida. Sam ita ba mace bace mai hayaniya, saidai ko ita kanta bata jin daɗin halin Jameelar, duk da yanzu haɗuwarta da sabon saurayin nata, kaman yanda tace. Ta lura ta fara cenzawa sosai.
Ƙarfe uku daidai bakin mirror tayi mata, bayan ta gama gyare ko ina, tare da sharewa da tsaftacewa. Ita dai maman tata sai binta take yi da kallo, duk da taji daɗi, amman sai take jin tsoron sabon saurayin na ɗiyar ta ya sake kufce masu, a karo na barkatai.
********
"Sweet heart gaskiya nidai tsoro nake ji, Ummi zata yayyanka ni, wallahi duk ranar data gane, kuma kaga Hotel ɗin nan akwai ƴan sa idanu, saboda haka dan Allah ka maida ni gida kawai haka, hakan ma ai ya isheka, ko ba komai Kaga yau daga ni har kai lafiya ƙlau muke jin kanmu... "
Saurin katse mata maganar da take yayi.
" My Habat! Haba me yasa kike haka ne? Wannan fa yawa ne wallahi, kinsan ko nawa na kama ɗakin nan? Beside ma wa zai gammu? Na faɗa maki gidana an fara sanya man idanu ne, har ma an kira Dad ɗina wai an faɗa mashi ina kawo mata da abokai a gida, shine ya kira fa yana ta man faɗa, wai ni rashin haƙurin me nake, ai daya dawo zai je gidan ku kawai, wajen su kawu a gama magana"
Da sauri Sahabat da kalle shi.
"Dagaske kake dear?" shima gyaɗa mata kai ya shiga yi.
"Eah da gaske mana, just remain a little ki shigo gida na, as my Bride" shima ya ƙarasa cikin zaulaya da iya yaudara.
Sai Sahabat ta samu kanta tana mai jin daɗi, bata san sadda ta kai hannu ta jawo shi zuwa jikin nata ba.
"I wished so my dear" ta furta a hankali.
Cikin wani irin sauƙi shima ya fara kai hannu saman jikin nata. Sun jima a haka, hatta da rigar ta saida ya raba ta da ita, ƙoƙarin kai hannu yake inda ba'a so, tayi saurin riƙe hannun.
"Not now dear" ta furta a wahale. Yana da matuƙar wahala ta iya daurewa ra riƙe kanta, masalan idan tana tunano yanda take ji ana wassafawa a littafi, da yanda take ji ana labarin farkon yi. Akwai zafi, kuma ance tafiya na cenzawa, to ita me zai kaita ta bari yayi amfani da ita? Duk da dai zuciyar ta na raya mata tana so, ai akwai inda ta taɓa ji a littafi, ance akwai abunda ake ba mutum ya tura ƙasan nashi, sai ya koma ya haɗe kaman budurwa, gashi irin saƙonnin da take ji daga Zaiyad ɗin, abun bai misaltuwa,tana jin kaman ma yafi sauran mazan da take kallo a cikin video ɗin da yake tura mata.
Shima a wahale yake kallon ta. Ya kai matuƙa wajen buƙatuwa, ya kai geji.
A ɗan hasale ya ture ta daga bisa jikin nashi, ya matuƙar jin haushi, duk yanda yaso da daurewa yau ya kasa, dole ne ma yaje ya nemi wata, dole ya samu mai rage mashi zafi.
Kunna motar yayi a fusace, yana mai jan motar daga ƙofar Hotel ɗin. Yaso yau ya kammala komai, ya gaji da yi mata ƙarya, Amman yaga yarinyar tsoron Ummin tata ya shige ta sosai, me zai sa ya tsaya yana ɓata ma kanshi lokaci? Shi dai ba zai taɓa mata fyaɗe ba, saboda yasan illar yin hakan, kuma asirin shi na iya tonuwa watarana. Amman in ita ce ta amince fa? In ita ta kai kanta fa?
Har ya isa kusa da gidan nasu, yana mai goga parking. Sannan ya juya ya kalle ta.
"You can go, kada kuma ki sake kirana, zanje in ta addu'a Allah ya cire man sonki a cikin raina, Tunda babu yadda da amana tsakani na dake, kuma sai yau ne na gane baki sona, ashe dama yaudara ta kike, Tunda har kike tsorona, kuma kike faɗa man wai Ummin ki, ashe baki yadda da soyayya ta ba? To ki sani, zanje in samu wadda take sona da gaske, wadda koda yanka ta zanyi gutsi gutsi in cinye, ba zata taɓa tanka man ba. Nagode da kika nuna man rashin soyayyar ki a zahiri, kinga ba sai su Dad sunsha wahalar zuwa gidan ku ba"
Yana gama faɗar haka, ya sake jan motar shi a fusace.
Sai ta fashe da kuka. Zaiyad bai taɓa mata haka ba, laifin me ta aikata mashi? Dan ta hana shi kanta? Me yake so tace ma Ummi?.
A sanyaye taja ƙafar ta tana mai shige wa gidan, magariba ta kawo jiki sosai, daga taje saloon ta dawo, shine taje ta biye ma Zaiyad, bayan an gama salon ɗin ta kira shi suka ɗan fita.
Koda ta shiga gidan, sa'a taci Ummi ta tashi yin sallah, saboda haka sai basu haɗu ba har ta shige ɗakin nasu.
Tana cikin tashin hankali, sai bayan data kammala sallah ne, sannan Ummin ta leƙo tana mai cewa, ta fito taci abinci.
Haka taci abincin a ɗarare. Ummin har taso ta kula, sai ta wayance da cewa wai kanta ne ke mata ciwo, saboda jan da akayi mashi. Addu'a Ummin tata tayi mata. Tana mai ɗauko mata magani ta bata tasha. Sannan tace taje ta kwanta.
Maimakon ta kwanta ɗin, sai ta shige toilet tana mai danna kiran Zaiyad. Tayi mashi kira ya kusa hamsin bai ɗaga ba, kuka take sosai, saidai mara sauti, son Zaiyad zai kashe ta. Ta yadda zata bashi dukkan wani abu da yake so daga gareta, indai zaibar jin haushi, kuma ya dawo gareta, sannan kada yaje wajen wata, kaman yanda ya faɗa.
Sai ta samu kanta da kiran Layin Hunayda.
Har ta fara bacci taji kira ya shigo wayar tata. Ɗagawa tayi cikin muryar bacci "Hello Saha" ta faɗa a hankali, gudun kada ta tashi Surayya.
"Hunaida ki taimaka man, Zaiyad ya rabu dani, ya gujeni, please ki faɗa man ya zanyi? Na kira wayar shi yaƙi ya ɗaga, nayi mashi text ba reply" ta faɗa cikin kuka ƙasa ƙasa.
Ɗan tashi zaune Hunaydan tayi. Mamaki take sosai, to me Sahar take so tayi mata? Ta gama bashi kanta, ai dole ne ya guje ta. Kuma inma bata manta ba, rabon ta da Saha an kwana biyu, dama ita Ammi ba barinta take yi zuwa gidan su Sahar ba. Sahar ce mai zuwa, to itama ta ɗauke ƙafar ta, saboda tana bata shawara akan Zaiyad, na ta rabu dashi ba mutumen kirki bane, inda itama Sahar ke bata shawara ta rabu da Malam Suhayl, wai tafi ƙarfin shi.
"Ya isa hakanan Saha, ki bar kuka, ko me kenan gobe ki shigo mu tattauna" cewar Hunaydan. Tana mai ɗan kallon sashen da Surayya ke kwance.
Da kyar ta lallaɓa ta tayi shiru, akan cewa gobe zata je gidan su Hunaydan suka rabu. Kashe wayar Hunayda tayi tana mai girgiza kai. "Allah shi kyauta" Abunda ta faɗa kenan a fili. Tana mai addu'ar Allah yasa Sahar ba kanta ta miƙawa Zaiyad ba.
*********
Cikin sabuwar motar daya cenza ƙirar 406 ya goga parking ƙofar ɗan madaidaicin gidan.
Da kallo yake bin gidan. Gida ne daidai misali na masu rufin asiri. Saidai ko ina daga gaban gidan tsaf yake, share kwal. Ya yaba da tsaftar mutanen gidan, shi mutum ne mai son tsafta a rayuwar shi.
Janye idanunshi yayi, yana mai ɗora su bisa fuskar wayar tashi daya zaro.
_"Ina waje"_ Abunda ya rubuta kenan yana mai tura mata.
_"You are welcome Abban Musaddiq. Ka ƙaraso daga ciki mana"_
Abunda ta rubuto mashi kenan.
Saurin maida mata yayi da _"Noo ina sauri ne"_
Shi da yaje katse alaƙa, meye nashi na shiga cikin gida?
Ko minti biyu ba'a yi ba, sai gata ta bayyana, tana ta faman kyalli da ɗaukar idanu.
Daga ciki ya sanya hannu, yana mai buɗe mata murfin motar.
Zama tayi a hankali, bakin nata ɗauke da bismilla. Lokaci guda kuma tana mai haske shi da wani irin murmushi.
Ɗan kauda kanshi yayi gefe kaman bai gani ba. Salma yake tunawa, wane irin sone Salma batayi mashi ba? Wane irin so ne Salma bata nuna mashi ba? Wace irin kulawa ce Salma bata bashi ba..?
Katse mashi ɗan guntun tunanin tayi, ta hanyar cewa "yau gaka a gidan su Jameela, saidai baƙo a tsaitsaye, kaƙi shiga ko Mama ce ka gaida, koda yake nasan watarana zaka shiga ne" ta faɗa, tana mai ɗan murza yatsun ta, fuskar ta ƙasa, idanun ta na bisa hannun nata da ya sha ƙunshi ja.
Ɗan murmushi yai, yana mai cewa "Mu hanzarta fa, Salma na jira na"
"Aunty na zaka ce" tayi saurin tarar numfashin shi.
Ɗan jinjina kai yayi gefe.
"Humm namiji kenan, wai shi nan ƙoƙari yaje in gane Salma na kula dashi, baisan kaf labarin gidan nashi a tafin hannu na yake ba" ta faɗa a cikin ranta. A zahiri kuma, sai ta sake dakin murmushi a karo na biyu.
Sake gaishe shi tayi, cikin wani irin ladabin da bata dashi tun cen baya.
Dayake bai sani ba, sai yaga abun wani iri. Irin yanda take ta bashi kulawa, shi yaja hankalin shi, sai ga Abdul da ɗan biye ma Jameelar sama sama suka taɓa fira. Inda tayi ta ƙoƙarin cusa mashi kanta.
Ba laifi, ba kaman yanda ta zata ba, ya ɗan bata kulawa, duk da akai akai yake kallon agogo.
Kayan ciye ciyen data haɗa mashi ta kwaso mashi, wai ya kai ma yara. Bai musanta ba ya amsa, gami da yi mata godiya, ai ko ba komai kaso mai son naka, kuma yana ganin kaman kulawar da su Husnan suka gaza samu wajen Salma, jamilar zata iya kulawa dasu.
Sai gashi kafin yabar ƙofar gidan, saida ya sake mata sosai, ta hanyar abubuwa da kalaman da Salmar ta faɗa mata yana so tayi amfani.
Cewa yayi zai kira ta, dazaran ya natsu. Gaban idanun ta yaja motar shi, tana ɗaga mashi hannu har ya ɓace ma ganin ta.
Juyawa tayi zuwa cikin gidan, hankalin ta kwance, fuskar ta ɗauke da murmushi, tana rayawa a ranta cewa muddin ta shiga gidan nan, kashin Salma ya gama bushewa...
**********
Koda Sahabat taje gidan su Hunayda basu kwashe da daɗi ba, duk shawarwarin da Hunaydan taba Sahar, babu wanda take jin zata iya ɗauka a cikinsu. "Ki rabu dashi kawai Saha, dama ba sonki yake ba, kin tabbata har ga Allah babu wata alaƙa data shiga tsakanin ku? Saha kin ba Zaiyad kanki ne? Kin amince mashi?" kalaman da Hunaydan tayi ta nanata ma Sahar kenan da suka ƙara tunzura ta. Gani take tama raina ta, wannan ma ai cin fuska ne. Ya tazo mata da matsala, zata sanya ta gaba tana mata tambayoyin banza da wofi? Kenan ita ga wadda zata auri malami ko? Wannan ce ta sanya ta itama yayyaɓa ma Hunaydan magana. Na cewa ko ta bashi, miye ruwanta? Ai wlh data tsaya kula irin su Malam Suhayl sau ɗaya, gara ta kula irin su Zaiyad so dubu, duk da yake ɗan iskan, ai dai shi da kuɗin shi, da kuma gatan shi,kuma da tasan abunda zata faɗa mata kenan, da batayi gigin sake ɗauko ƙafar ta ta tako gidan su Hunaydan ba.
Saidai Hunaydan ta bita da murmushi da Addu'a. Yanzu Hunayda ta fara gane kanta, tarayyar ta da malam Suhayl, Sulaym da kuma Aunty Sumiee B. Ya ƙara taimakawa wajen daidaituwur rayuwar tata, a bisa siraɗi madaidaici.
Ko karance karance yanzu ta dena yi, inba littafin Aunt Sumie ba, sai kuma girke girke da ake yi masu turorial, da kuma litattafan addini da malam Suhayl kan tura mata cikin wayar tata.
A take ta danna ma Sahar blocking, bayan fitar ta gidan nasu. Inda har saida Ammi ta leƙo, wai me tayi ma Sahabat ta fita tana ta fushi? Murmushi kawai tayi ma Ammin, tana mai cewa "Ammi ba komai fa, ƙyale ta kawai gaskiya kawai na faɗa mata, shine taji haushi ta tafi"
Girgiza kai ammin tayi, tana mai cewa "Gaskiyar me? Bana son haka fa Hunayda, da tana da waya, da kin kira ta kin bata haƙuri, ni bana son faɗan nan wallahi, kuna yara bakwa iya kai zuciya nesa"
Da kallo ta bi Ammin, tana mai raya ma ranta cewa "Ammi da zaki san halin da Sahabat ta jefa rayuwar ta, da baki sake barinta ta tako ƙafar ta gidan nan ba, koma menene ni bazan tona mata asiri ba, taje, ai duniya ce ta fi bagaruwa iya jima ai"
Saha tasha matuƙar wahala kafin Zaiyad ya yarda ya sauko, shima saida ya kafa mata sharaɗin cewa da kanta zata kai mashi kanta, sannan tayi mashi alƙawarin cewa duk abunda ya nema zai samu. Dayake so ya rufe mata idanuwa, kuma huɗubar shaiɗan na tasiri kanta, shaiɗan na kaɗa mata ganga bisa tsakiyar kai. Cikin sauri ta bada kai bori ya hau, ta hanyar ce mashi yayi mata kwatancen inda zata iske shi. Aiko ba daɗewa sai ga Address ɗin gidan ya bayyana a saman secrean na wayar tata.
Ƙudurcewa tayi a ranta cewa, gobe duk wayo, da ƙaffa kaffan Ummin tata, sai tasan yadda akayi ta ɓalle taje ga Zaiyad farin cikin rayuwar tan.....
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) says:
'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk."
[Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه)
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Four_
~*Page 15*~
Ba ƙaramin yaƙi yayi da zuciyar shi ba, wajen ganin bai ba Jameela dama akan shi ba, saidai inaaa! ya riga ya makaro, ita zuciya a kullum mai kyautata mata take so.
Ita kanta Salmar ta kula da yanayin Abdul ɗin ya cenza, yanzu fushin da take yi dashi ma, gani take kaman bai damuwa, sai ya zauna yana yima yaran shi wasa amman ko inda take baya kallo. Har firarraki zata ji yana yi masu, ko ya kwashe su su fita, ko ya kaisu cen gidan nasu.
Butsu Butsu sai taji wayar shi tayi ƙara, bai ɗagawa a gabanta, sai ya tashi ya ficewarshi waje ya amsa wayar,