Showing 42001 words to 45000 words out of 107295 words
Chapter 15 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
a rana. Jameela Jameel"_
Ɗan murmushi yayi, mata a wannan zamanin sun fita daban, ace wai ana zamanin da mace zata kai kanta wajen namiji, har rana roƙon shi daya taimaka ya kula ta. Wannan wace irin rayuwa ce? Kuma bayan tasan yana da aure, da mata harda yara biyu.
Ɗan tsoki yayi yana mai kashe wayar ma baki ɗaya, mata kenan, gashi da ɗaya ma wace Allah cika, balle ya jawo ma kanshi jaye jaye.
Kusan zamu iya cewa cikin kwana biyun nan, babu ranar da Jameela bata kiran Abdul, tun yana share wa, har ta kai ga yana ɗan biye suyi fira, chatting ne kawai baya yi da ita. Amman ɗan fira haka, kaman na minti biyu sukan yi.
Idan ya dawo gidan ya kan tadda yaran shi da kayan wasanni ko kuma kayan ciye ciye, suna ce mashi aunty Jameela ce ta kawo. Saidai yayi murmushi kawai. Domin ya zuwa yanzu ya fahimci Jameelar Ƙawar Salma ce, shine take neman ta ƙwace mata miji smman dayake Salmar sa karya ce, sai gashi bata ko kula ba.
Wannan kaɗai ya samu abun riƙewa, koda Salimar zata kula ta hankalta kuma.
Wani lokaci Salmar kan bada kai bori ya hau, Amman da an kammala sai kuma mita, da gunguni, baya biye mata, in da sabo ya saba, sai gashi bata tsinana mashi komai a cikin gidan, amman ta iya tayi shaye shayen magungunan ta, ta kuma kai kanta ko kunya bata ji. Duk yana kula da abubuwan da yake yi Amman ya share ta. Shi dai kawai abunda ya sani, ba zai kashe kanshi ba, tunda haka ta zaɓa sai a cigaba a yanda take so ɗin.
*************
Kaman kada su tafi haka suke ji su duka. Cikin week end Hajiya Gambo ta zuba su duka cikin mota, harda Sulaym, da yanzu ta zama aminiya wajen Hunayda. Sai Kaduna garin gwamna.
Hunayda ta ƙara kyau, clean da kuma gogewa tarayyar ta da Sulaymin. Ga abubuwa data koyo zaman ta a gidan Hajiya Gambon. Sannan tarayyar ta da Sumie B. Abun gwanin ban sha'awa. Duk Abunda taga bata gane ba, ta kan tambayi Aunty Sumie ɗin. Har ta kai da ta kan ce mata Aunty na, ita kuma Sumiee tace mata Ƙanwata.
Ammi taji matuƙar daɗin ganin yaran tana, sai godiya take zuba ma Ƙawar tata, nan fa suka buɗe babin sabuwar fira, inda Hunaydan taja Sulaym zuwa ɗakin nasu. Labarin malam Suhayl ta shiga bata, har ta kira mata shi a waya suka gaisa. Sulaym taji matuƙar daɗi, ganin duk wasu halaye da taga Hunayda dasu, ta idasa kakkaɓe mata su. Ta yaba da Malam Suhayl ɗin, inda ta sake ba Hunaydan shawara akan ta kula da Malam Suhayl ɗin, domin daga ji shi mutum ne mai daraja, masalan ma kasancewar shi malamin Islamiyya mai ɗinbin sani. Sai Hunaydan taji ta ƙara son Sulaym ɗin, masalan ma da take bata shawarwari nagari, saɓanin Sahabat da kullum ita tunanin ta, tayaya zasuji daɗi, suyi enjoying rayuwar su, sai yanzu ne take gane Sam rayuwar tata batayi kamanceceniya da Sahabat ba. Tasha alwashn kulle duk wata ƙofa da Sahabat ɗin zata ɓullo mata, wajen ganin ta sake tunzura ta ga aikata abunda ubangijn ta zai yi fushi da ita.
Sun ci abinci sun huta, kafin Hajiya Gambon tace zasu koma. Aiko nan Ammi ta cika su da shatara ta arziƙi itama, duk da tayi ma su Hunaydan soyayya mai yawa suma a A.A Moda, da kuma Umar Store.
Sun rabu suna masu kewar juna. Tun daga ranar Ammi taga cenji a cikin halayen Hunayda. Komai ba sai tace ta tashi tayi ba take yi, hatta da maida hankali kan waya kullum da take yi, yanzu duk ta rage sosai, girki mai daɗi, tsafta da komai Hunaydan yanzu ba baya ba. Idan Malam Suhayl yazo, rabi fira rabi karatu ita da Surayya. Tare suke zuwa cen wajen nashi suyi ta yarintar su. Abunda kan ƙara ma Malam Suhayl ƙwarin guiwar mallakar Hunaydan.
************
"Sahabat! Sahabat! Sahabat! Wai ke lafiyar ki ƙlau kuwa? Kwana biyun nan fa na gaza gane maki Saha, kullum yini kike a banɗaki, wani lokaci ma sai inji kina ta maganganu ke ɗaya, kodai aljanu ne suka kama ki?" Cewar Ummin tasu, tana maganar tana bubbuga kyauren toilet ɗin ɗakin nasu Sahar.
Saurin cusa wayar ta tayi cikin ɗan ƙaramin wandon dake ƙasan doguwar rigar tata, dama takan sanya shine idan tana son ɓoye wyarta, nan ne aljihun da take tura wayar, bayan ta maida ta silent.
Da sauri ta fito tana mai fiƙi fiƙi da idanu, alamun rashin gaskiya.
"Ummi ban lafiya, kwanan nan atini nake fama dashi sosai wallahi" ta faɗa itama tana mai sosai kai.
"Atini fa kika ce? Tun yaushe kika fara?" Ummin ta maida mata da amsa.
"An kwana biyu Ummi" itama ta mayar mata, har yanzu jikin ta ɓari yake, ta kula yanzu Ummin tata ta sanya mata idanu, kaman ma bata yarda da ita ba, to kodai Hajna munafukai taje ta faɗa ma Ummin wani abu ne?
"Maganar da nake ji kina yi cikin bayan gidan fa?" Ummin ta faɗa, tana mai ƙureta da idanu.
"A..a'..a Ummi nishi ne nake, shine sai in dinga cewa way... Yyo, saboda akwai zaf.. I" ta faɗa cikin in'ina daga ji bata da cikakkar gaskiya.
"Shine sai ki dinga magana a toilet dan kina sakarya? Ba zaki iya zuwa ki faɗa man ba, in baki kuɗi ki amso magani?"
Ummin ta faɗa, tana mai juyawa ta nufi nata ɗakin.
A baya Sahar ta bita, tana mai yi mata gwalo da ƙunƙuni, faɗi take cikin ranta, duk bake bace ke rubuta abunda zai sanya mutum cikin wani hali? Yanzu ma ai update ɗinki nake karantawa ne, Shiyasa kika ji ina ta surutai, ai dole ne ma in nemi Sweet heart, domin bana jin zan iya bacci yau da wannan Bomb ɗin da kika haɗa man.
Kuɗi Ummin ta bata, tana mai cewa tayi maza taje asibiti, a duba ta, kada ta daɗe, su Hajna sun kusa tasowa daga makaranta.
Da to tabi Ummin. Tana mai juyawa ta fice.
Murna take da jin daɗi, ko ba komai ta samu mafakar fita.
Sauri sauri tayi ta shirya, tana mai cema Ummin sai ta dawo. Da a dawo lafiya ta bita, tana mai ƙara jan kunnen ta akan ta kula.
Kaman yanda yake al'adar shi, yau ma da mota ya tsaya ɗan nesa da gidan su Sahar, da an sha kwana sai gidan su Sahar. Tunda ta kira shi yake ihun murna, ya ɗan kwana biyu bai haɗu da ita ba, acewarta wai Ummi ta sanya mata ido, tare da sabunta dokoki ta.
Motar ta faɗa kai tsaye, motar yaja yana mai kamo hannun ta cikin nashi. Ba kunya ta matsa sosai zuwa jikin nashi, dayake glassan motar tint ne, sai babu wanda zai iya hango abunda suke yi cikin motar.
Ajiyar zuciya mutumin ya sauke, ba wannan ne karo na farko ba, da yake ganin yarinyar na shiga motar, wadda ba zai iya shaida wanene a ciki ba. Ya san yarinyar marainiya ce, kuma ba zaiba uwar ta wata shaidar banza ba, sannan yasan tana iya ƙoƙari ta wajen kula da yaran, toh saidai zamani fa ya cenza, zamani ne da yaran suke ganin kaman sunfi iyayen wayau. Sai gashi ana zuwa da mota ana ɗaukar yarinyar.
..............
"Sweet heart ki barni hakanan, tun kafin ki sanya motar nan ta ƙwace man" cewar Zaiyad ɗin da yake tuƙin motar da hannu guda, gudan hannun kuma yana tallafe da ƙugun Sahar.
Sauka tayi tana mai komawa kujerar ta.
"Ni ɗince yau full my Dear. Naji bama iya bacci sai na ganka"
Ta furta tana mai maida numfashi, lokaci guda tana mai zame hijab ɗin dake jikin ta.
"Shine aka zo kaman za'a gama dani?" ya maida mata shima, yana mai sakin wani irin Killer smile.
"Huh! Ka bari kawai, wani littafi ne na karanta mai zafi, idan munyi aure zamu dinga yin irin yanda suke yi dear" ta faɗa itama kai tsaye, ba tare da wata kunya ba.
"Ki bari dan Allah? Me zai hana mu kwatanta yau to? Ko sauri kike yi kaman kullum?"
Gyaɗa mashi kai tayi. "Ba yanzu ba dear, ai su aure sukayi.." "Muma ai auren zamuyi, so ina ganin gara mu koya tun yanzu" yayi hanzarin katse mata maganar da take yi.
Har gidan shi suka shiga, ba yanda baiyi ba juyin duniya Sahabat ta ƙiya, saidai abunda ba'a rasa ba, saida su dukan su suka samu abunda suke so, sannan ya ɗaga mata ƙafa, duk da har yanzu Sahabat bata bari Zaiyad ya kusance ta ba, Amman babu abunda basa aikatawa. Ya zuwa yanzu Sahar ta mugun sakin jiki da Zaiyad ɗin, a ƙarairayin da yake shirga mata kullum. Bata jin Kunyar ya gantaba ko sutura, zuciyar ta kullum ƙara ƙeƙashewa take yi. Har ta kai yanzu ta kan yi aiki da yatsunta, domin biya ma kanta buƙata, idan kuma sun haɗu haka Zaiyad ɗin keyi nata.
(Duk acikin irin busar sarewa ta shaiɗan da yake yi masu, tare da ragamar Rubutun litattafan banza da Ummin ta take yi, wanda shine silar faruwar komai, ba tare da ankarewar ta ba)
Saida suka gama abunda zasuyi, sannan suka baro gidan cikin jin daɗi. Chemist ya kaita, aka rubuta mata magani, tare da bata ya biya kuɗin, sannan ya ƙara mata wani, wai tukuicin rowa da batayi bashi, duk da yasan tabbacin tana sonshi ɗin kenan. Kafin ya maida ta kusa da gidan ya dire ta.
A gaban mutumen da take zaune bisa ƴar tsohuwar tabarmar shi ta sake gittawa ta shige gidan. Yayi da shima Zaiyad ɗin ya ja motar shi yana mai barin wurin, tare da raya ma zuciyar shi cewa yana daf da cimma buƙatar tashi akan Sahar.
Girgiza kai mutumen yayi, ya zama dole wajibi ya sanar ma mahaifiyar wannan yarinyar, ko hakan zai sa ta ɗauki mataki, idna kuma ɗan uwanta ne, ya kamata dai ace an sani. Ƴar butar shi dake ajiye gefenshi ya ɗauka, gami da fara ɗaura alwalar sallar la'asar.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) says:
'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk."
[Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه)
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Four_
~*Page 14*~
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
*******
"Assalamu alaikum wa rahmatullah"
Karo na biyu kenan da daɗaɗɗar sautin nata na shiga kunnen shi.
Shi kanshi baisan dalilin shi na amsa kiran nata ba, ba wannan ne karo na farko da take kiran nashi ba, saidai ganin baya da wata alaƙa da ita ne, ya sanya yake kauda kai, da kuma sharewa. Baya son yanda take shisshige mashi, sai yake ganin wannan ai kaman cin amana ne, tunda ta kasance ƙawar Salmar shi.
"Yayana ka amsa man sallamar mana please"
"Wa'alaikumus-salam". Shima ya amsa mata a taƙaice.
Shiru ne ya biyo baya, na tsawon ƴan second. Sai cen ne tayi ƙarfin halin cewa; "Ya iyali ya su Musaddiq?"
"Duk suna lafiya, ya naku mutanen gidan?"
Cikin wani irin farin ciki ta amsa, zuciyar tata ɗauke da addu'a. Bata so ya watsa mata ƙasa a ido, so take ta samu gurbi a cikin zuciyar tashi, saidai taga hakan ba mai yuwuwa bane. Ta ƙagara ta ganta a cikin gidan nashi, a matsayin matar shi. Bata jin idan zata iya bari wani dalili ya hana ta kai ga cin nasara.
"Yayana dan Allah kada kace na dameka, ni kaina bansan me ya shiga kaina ba akanka, bansan dalilin da ya sanya nake jin ka har cikin raina ba, kada Kaga laifi na, kasan shi so makaho ne, kuma baya shawara, dan Allah ka tausaya ma baiwar Allah, tun ranar da ka rage man hanya, nayi mantuwar zuciya ta tattare dakai, ka taimaka ka dawo man da ita dan Allah"
Ta ƙarshe cikin sanyin murya, kaman zata saki kuka, abun daga zuciyar ta ne yake fitowa.
Jin yayi shiru bai ce komai bane, ya sanya ta sakin wata irin wawuyar ajiyar zuciya.
"Nasan wata ƙila nayi laifi, saidai wannan ba magana ce daya kamata inyi a waya bace, Amman na gaza jurewa ne, idan ban faɗa ba, zan iya shiga wani halin, ka taimaka kada ka maido man ƙoƙon bara ta, nasan baka rasa komai ba wajen salma, amman dan Allah ka taimaka mu raba wannan kyautatawar da take maka. Insha Allahu nayi alƙawarn zama da duk wani wanda ya shafe ka lafiya"
A hankali ya sauke wayar daga kunnen shi, yana mai latse ta ya kashe ta baki ɗaya ma.
Maganganun nata sun ratsa mashi kwalwa, me hakan yake nufi? Yana hango natsuwa da kamala tattare da yarinyar, Amman me yasha kan shi? Duk da ga fuska bata kama da budurwa, amman kalaman nata, suna nuni da tsantsar ƙaunar ta gareshi.
Baiso kalaman nata suyi tasiri a cikin zuciyar shi, dalili daya sanya ya tattara komai nashi kenan ga zuwa gida.
Yanda ya bar falon, haka ya kuma dawowa ya tadda shi, su Husna da Musaddiq ma sun riga sunyi bacci.
Saboda haka ko inda take zaune bai kalla ba. A daƙile tayi mashi sannu da zuwa, baima zata ba, hakan ya sanya ya zauna a hankali bisa sofar dake kallon tata, yana mai ce mata "Yauwa Madam ya gida ya yara, ya kuma kaɗaici? Koda yake ai kince bakya jin kaɗaici in waya na riƙe a hannun ki"
Ɗan murmushi tayi iya fuska, har yanzu idanun ta na kan wayar.
Miƙewa yayi zuwa ɗakin, yau dama dama ta gyara gado, Amman ai da sai in ya dawo ne yake gyarawa, wani lokaci ma sai yace ta tashi ya gyara, sannan take tashi ta tsaya, yana gyarawa ta koma tayi kwanciyar ta.
Da kallo yake bin ɗakin. Kaman ba ɗakin mutane ba. Ko ina kaya, ga yana da ta fito duk ta kama POP ɗin dake ɗakin, abunda bai taɓa gani ba.
Kayan shi ya rage, daga shi sai ƴan ciki.
Zagewa yayi ya gyara ɗakin tsaf, sannan ya kwashe yaran daga falon ya maida su ɗaki, bai ƙasa a guiwa ba, ya gyara falon tsaf, duk tana zaune tana caccakar waya, sai dariya take yi ita kaɗai, tana buɗe audio na mutane tana shan dariya.
Nan ma bai kula ta ba, ya shige toilet ya wanke, sannan yayo wanka, yazo ya murza mai yana mai hayewa gado.
Saidai me, yana kai kafaɗar shi ƙasa, tunanin Jameela yayi mashi sallama. Sai a lokacin ya manta da wayar ma ashe ya kashe ta.
Yana kunnawa text ɗinta na shigowa.
_Ba dai zan gaji ba, kayi man lamuni gobe inzo Office ɗinka_
Ɗan murmushi ya saki. Mata kenan da ƙarfin hali suke. Baya so ya saki jiki da Jameela, daga baya kuma tazo mashi da tsurfa, kwatankwacin wadda Salma tazo mashi da ita yanzu.
A hankali ya lallatsa reply ya mayar mata.
_Your Address, Amman ba dai Office ba_
Cikin second sai ga reply ɗinta, da exact Address nata.
Gidan su Baida wuyar kwatance. Saboda haka yayi alƙawarin neman ta gobe. So yake gashi gata ya bata haƙuri, baya so alaƙar tasu tayi nisa, ko dan gudun Salma tace yaci amanar ta.
Shi kanshi ya sani, yana masifar son Salma, Amman Salma ta zaɓi hanya marar ɓullewa.
"Ok i'll meet u 2mrrw by 4pm"
Ya sake tura mata.
Ba jimawa sai ga reply nata.