Showing 60001 words to 63000 words out of 107295 words
Chapter 21 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
sallama, amma ina Salma nacan na masifa bata ma san abinda take yi ba.
Sai da duk tayi musu duka sannan ta saka su suka cire kayan dake jikin su ta ɗeba ta watsar.
Tana fitowa taga Habiba ƙara haɗe rai tayi tace; "ke kuma baƙar munafika meya kawo ki gidan nan?", Habiba cikin sanyin murya tace; "ai kya bari na zauna sai kiji meya kawo ni ko?".
"zama? Ai babu wajen zaman munafikai a cikin gidan nan ki tattara ki bar mini gida tunkan na saka ayi miki rashin mutunci, banza mara zuciya".
Habiba tace; "tunda haka kika ce zan fita sannan ina miki fatan shiriya Allah ya shirya ki yasa ki gane gaskiya, dama kaya ne aka samu kalar naku masu shegen kyau shiyasa nace bari in kawo miki".
"nace bana so ko ana ciniki dole ne? Mtseww aikin banza aikin wofi kun girma amma baku san kun girma ba, kin kasa riƙe girman ki wallahi anji kunya", jiki babu ƙwari Habiba tace; "Allah ya baki haƙuri zan fita amma ki sani banyi zuciya ba ni jinki nake kamar ƙanwa ta ko nace ƴar dana haifa dan haka duk ranar da kike buƙatar taimako na kina da numberta ki kira ni", tana gama faɗin haka ta fice daga gidan.
Tana juyo yadda Salma ke lailayo mata zagi, haka ta fice daga gidan tana kuma ƙara ɗaura ɗamarar taimakon ta dan daga gani rayuwar ta a da ba haka take ba.
Im madai Aljanu inma kuma wani ke zuga ta wannan shine tunanin ta.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) said:
'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'"
[Bukhari (also by Muslim).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ .
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 19*~
Yau Ƙanin mahaifin Abdul da kuma abokin shi suka je maganar saka rana, babu ɓata lokaci suka tsaida wata ɗaya wato kwana talatin kenan.
Salma tana zaune Abdul ɗin ya shigo ko samin arziƙin kallon shi yau bata yi ba domin kuwa wani littafi daya ɗauke mata hankali tsabar batsa ce da maɗigo kawai a ciki.
Abdul ya dube ta yadda ta maida hankali akan wayar sai ka ɗauka hanyar shigar ta aljanna ne a ciki.
Ya zauna a saman kujera sannan ya dube ta yace; "haba Salma yanzu abin naki ya wuce min sharri ya kai mahalaka, mijin ki ya dawo ace ko kallo be ishe ki ba".
Ta ɗan ɗago ta kalle shi cikin yanayin ko in kula sannan tace; "to me kake so nace maka kuma?", ya girgiza kai yana miƙewa tsaye sannan yace; "Allah ya taimake ki ya baki sa'a".
Ɗakin su Husna ya shiga abin ban haushi yadda ɗakin yake kaca-kaca komai yana yadda yake tsayin lokaci yana tunanin tun ranar sati daya share ɗakin be kuma ganin shara ba.
Ya kalli Husna dake zaune yayin da Musaddiq ke kwance daka gansu ka san yunwa na ɗawainiya dasu, da hannu yayi musu nuni akan su zo, da gudu suka nufo shi ba tare da yace komai ba ya jasu suka fice.
Yana tafe yana tunanin halin rayuwar daya faɗa shida yaran shi, lallai duniya abin tsoro ce haka mace bata da tabbas kamar wutar nepa, zata gatan taka yadda sai kaji cewa kai ɗin sarki ne da babu kamar shi ranar data botsare maka a ranar zaka tabbatar da almajirin dake bara a gefen tasha ya fika galihu.
A ƙofar gidan yayi parking inda ya buɗe musu suka fice, su kansu yaran sunyi farin ciki domin sun san Auntyn tasu tana kula dasu sosai.
Ya ɗan jima a tsaye kafin ta fito daga gidan, yauma dai wankan doguwar riga tayi baƙa tayi wacce taji stones a gaban rigar da hannun rigar, gyale fari tayi rolling dashi wanda ya ƙara ƙawata kwalliyar tata.
Tunda ta fito yake kallon ta, a rayuwar shi yana ƙaunar yaga mace tayi wannan shiga, ya sauke ajiyar zuciya a lokacin da muryar ta, ta ratsa dodon kunnen shi yayin yi mishi sallama.
Cikin sanyin murya ya amsa, nan suka gaisa cike da mutunta juna, "iyaye na sunzo ɗazu kuma mahaifin ki ya tsaida lokaci nan da wata ɗaya", zoben dake hannun ta take wasa dashi fuskar ta kuma ɗauke da murmushi.
"au kunya ta kike ji ne?, lallai ma", da sauri ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta, tana me sakin dariya, hakan ba ƙaramin birge shi tayi ba wanda har yasa shi yin dariyar shima.
Jameela kuwa ta langwaɓar da kai, idanun ta a ƙasa sannan tace: "na san dai ba lallai kaci abinci ba dan haka yanzu ka shigo sai kaci tukunna ka tafi", yayi jim yana tunani ya san idan yace yaci abinci a gida yayiwa kanshi ƙarya gaskiya idan kuma yace beci ba ai abin kunya ne ace yana da mata amma kuma beci abinci ba har zuwa wannan lokacin kuma hakan zai zubar da ƙimar matar shi a idanun Jameelar.
Jameela tace; "yau dai ina neman alfarmar cin abincin ka anan gidan dan Allah kada kace mini kaci a gida", ya kalle ta bashi take kallo ba amma kuma yadda tayi da fuskar ta sai ta bashi tausayi dan haka yace; "shikenan muje".
Ɗakin dake zauren gidan wanda ƙannen Jameelar suke kwana nan ta kaishi dama tuntuni ta shiryawa hakan dan haka ta share ɗakin tass harda ƙamshin turare dake tashi.
Tunda ya shiga yaji wani irin farin ciki ya ziyarci ran shi domin kuwa Allah yayi shi da son ƙamshi amma ta dole yanzu ya haƙura domin dai Salma ta dena sa turare a gidan.
Kan darduma wacce Jameelar ta shimfiɗa ya zauna, gaban shi ta jere da kololi wanda suke shaƙe da abinci.
Daba dan kada yaga zaƙewar ta ba da da kanta zata zuba mishi amma ina bata so tayi abinda zai fahimci cewa kunyar ta ragaggiya ce dan haka dole ta miƙe ta fice daga ɗakin a ranta tana faɗin; "me nake ci na baka na zuba saurin me nake, ai inda jirgin sama yaje kunkuru ma zai je, za'a zo wajen ne idan na sawa kaina haƙuri".
Abdul kuwa tana fita ya buɗe kololin wainar shinkafa ce me kyau gashi da zafin ta, ɗayar kular kuwa miya ce ta alayyyaho wacce taji ƙashi ga wani irin ƙamshi da take yi, ɗayar kuma danbun nama ne haɗaɗɗe yaji kayan ƙamshi sosai, sai filet ɗin da aka yanka su abarba da lemo da kankana da dai sauran su, sai jug guda biyu wanda ɗaya ke ɗauke da lafiyayyen kunun aya yaji madara da kayan ƙamshi ɗayan kuma zoɓo ne shima me kyau da ƙamshi, sai gorar swan water guda biyu.
Abdul cikin jin daɗi ya buɗe ciki ya kwashi gara, inajin yama manta gidan surukai yake, gani a gefe ko ɗan san mini beyi ba😏.
ya gama ci kenan Jameela tayi sallama ta shigo, ya miƙe cikin basarwa yana faɗin; "bari nazo na koma wajen aiki", Jameela tayi murmushi tace; "nagode sosai", be amsa ba ya nufi hanyar fita itama tabi bayan shi.
Har ƙofar gida ta raka shi, yasa hannu cikin aljihu ya ciro kuɗi ƴan ɗari biyar-biyar ya miƙa mata yace; "ga kuɗin lallen nan", ta amsa tana faɗin; "na gode sosai",haka suka yi sallama sannan ta koma gida.
Husna da musaddiq idan ka gansu ba zaka ce wai ba gidan su bane har sunfi sakewa a nan sama da can gidan nasu.
Sai da Jameela ta ƙara shiryawa sannan tace da husna; "Yauwa Husna zo mu tafi ko?", yarinyar wacce ke sanye da doguwar riga ta nufo wajen ta ta kama hannun ta nan suka yiwa Mama sallama suka tafi.
Koda suka isa shagon, wajen babba ne sosai don waje ne na manyan mutane da hamshaƙai da suke garin na Kaduna.
Sai da suka fara wucewa wajen masu wanke kai aka wanke musu sannan fa suka dawo suka fara bin layin ƴan ƙunshi da kitso, babu jimawa sosai aka zo kansu domin kuwa mutane ne da yawa suke aiki a wajen.
Wasu suka kama kan Husna wasu na Jameela, masu lalle ma suka kama nasu aikin cikin ƙanƙanin lokaci aka gama yi musu.
Me wajen Hajiya Fatima Batula matar senator na kaduna north, kasancewar akwai sanayya tsakanin ta da Jameelar tace; "yau babu gyaran jiki kenan?".
Jameela tayi murmushi tace; "wallahi naso na yi to kuma bana so na daɗe a nan ne domin ina so mu biya kasuwa daga nan sannan zan koma gida nayi girki, amma biki na idan ya matso zan zo ayi mini gyaran jiki na musamman".
Hajiya Batula tace; "an saka lokaci kenan?", Jameela tace; "nan da wata ɗaya insha Allahu", Hajiya Batula cike da farin ciki tace; "ah lallai idan ya matso ki kirani ni kuma zan baro Abuja nazo nayi miki gyara na musamman irin wanda nayiwa Her Excellency Hajiya Amina Hassan minister of health".
Jameela ta kama baki tace; "wai! Wace ni ina naga kuɗin da zan biya ki har kiyi mini kalar wannan a'a kawai kiyi mini dai-dai kuɗi na".
Hajiya Batula tayi dariya tace; "ke dai kada ki damu daya matso kamar saura sati biyu ki kira ni a waya kawai", Jameela tace; "shikenan an gama ranki shi daɗe", zuwa lokacin ya bushe dan akwai sanyin Ac a wajen, wata me aiki a wajen tazo ta wanke musu sannan aka shafa musu muhallabiya nan fa yayi raɗau dashi.
Jameela ta kalli Hajiya Batula tace; "gaskiya ina son aikin ma'aikatan ki domin sun ƙware sosai", Hajiya Batula tayi dariya yayin da take zaro ƴan dubu-dubu daga jakar ta ta miƙawa Husna sannan tace; "gashi kya sai Chocolates ko kinzo na shagon ya ƙare gaba ɗaya".
Jameela tace; "ai kuwa mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi, sai na kira ɗin na gode", nan suka yi sallama cikin mutunci da girmamawa don Hajiya Batula bata da ɗaukar kai, hakan yasa mutane ke son mu'amala da ita.
Sai da suka biya ta kasuwa Jameela tayi siyayyar ta sannan suka wuce gida a lokacin har magrib ta matso.
Suna isa gida kayan kawai ta ajiye sannan ta shiga kitchen domin kamawa mahaifiyar tata girkin daren, kowa ya yaba da ƙunshin nasu nan kuwa Jameela ta dinga washe baki tana basu labarin Hajiya Batula.
Sai da suka yi sallar Magrib sannan suka zauna cin abinci, suna cikin cin abincin Abdul ya kira ta akan gashi yazo ɗaukar yaran.
Jameelar ta fara fita, nan cikin lallami da lallashi ta roƙe shi akan ya shigo yaci abinci tukunna, "kaga daga nan ma sai ka gaishe da Mama", duk yadda yaso kaucewa abu ya gagara hakan yasa ya amince kawai.
Yanzu kam Tuwon shinkafa da miyar kuɓewa ɗanya 😋 taji man shanu ga nama zuƙu-zuƙu.
Nan fa ya ƙara kwasar garar shi ko kallo na beyi ba😭.
Sai da yaci yayi nak ya godewa ubangiji don rabon shi da abinci irin wannan har ya manta, nan Jameela tayi mishi jagora zuwa ciki ya gaishe da Maman.
Ya ajiyewa Maman ƴan kuɗaɗe sannan suka fito, Jameela na riƙe da hannun Husna Abdul kuma na riƙe da hannun Musaddiq.
Ta buɗewa Husna baya ta shiga sannan ta saka mata ledar dake hannun ta, yana daga cikin mota ita kuma ta tsaya a bakin motar.
"na gode sosai na kuma ji daɗi Allah ya kaimu lokacin da zan mallakeki ki zama taqa gaba ɗaya", Jameela tasa hannu ta rufe fuskar ta, tana dariya.
Wayar shi ya kunna torch yana faɗin; "Lah haka dama lallen yayi kyau amma baki faɗa mini ba", tayi murmushi tana saukar da kai ƙasa.
Oh jameela green snake🤸
Haka yayi sallama da ita cike da nishaɗi da jin daɗi domin kuwa Jameelar tana ƙoƙari wajen ganin ta kyautata mishi tare da yin abinda yake so domin kawai ta sake kama shi a hannun ta, kuma tabbas tana ganin cigaba tunda gashi har yana yaba mata sannan ita kanta ta san ta samu matsayi me girma a zuciyar shi.
koda ya isa gida Salma bata falon hakan ya tabbatar mishi da tana ɗakin su kenan, shi da kanshi ya shirya su Husna suka kwanta barci sannan ya musu addu'a ya rufo ɗakin.
Da sallama ya shiga ɗakin, tana kwance saman gado tana ɓaɓɓaka dariya sannan kuma tana sauraren Voice wanda ake turo mata.
Ko sallamar bata amsa ba shima hakan be wani dame shi ba domin yanzu ya saba da halin matar tashi dan haka dressing mirror kawai ya nufa ya ajiye wayoyin shi da makullan shi sannan ya nufi bayi.
Sai da ya gama duk abinda zai yi sannan ya fito, raka'a biyu yayi wato shafa'i kafin yayi shirin kwanciya har lokacin kuma Salmar na kwance tana faman dariya da tura voice da kuma saurara.
"ai wallahi yau yanda nake ji na idan Salim be kwana a kaina ba to sai mun raba dare dan yau babu ɗaga ƙafa", maganar da yaji kenan wata tana faɗa wacce har sai da ya ɗan dakata.
Salma kuwa bata wani damu ba sai ma fara recording tayi inda take cewa; "ai wallahi shine dai-dai kada ki saurara mishi yayi miki cin da Fu'aid yayiwa Sukainah a *Ni da shi*, ni mkaina dan nasan ba zan samu bane shiyasa sai dai raina kawai ya ɓace amma page ɗin yau yayi wuta wallahi".
Abdul sai da dardumar hannun shi ta faɗi tsabar mamaki da al'ajabi cikin fushi da ɓaci rai ya nufi inda take.
Salma duk rashin kunyar ta, tana tsoron Abdul dan haka ganin yadda ya nufo ta yasa ta miƙe cikin sauri.
Me zai faru? Sai kun cigaba da biyomu kawai domin jin yadda zata wakana tsakanin ma'auratan nan masu son junan su a baya da kula da tattali kafin a samu akasi😥.
*** ****** ******
Ummi ke ƙoƙarin kulle gida domin yau suna da taron su na *MUNA WUTA* na Kaduna state wanda ɗumbin marubutan batsa ne kawai a ciki kai harda na maɗigo duka shine suka haɗa ƙungiya wanda ainihin ƙungiyar ta samo asali ne daga jahar Gombe sai Kano, Abuja yanzu kuma ta shigo Kaduna, asalin ta Gombe sun buɗe tane saboda nasiha da kuma jan kunne da akasarin mutane masu karatu, malamai da kuma sauran marubuta suke yi musu akan su ji tsoron Allah su dena, to ganin hakan dan su ƙara bawa mutane haushi shine suka kafa ƙungiya inda duk bayan wata uku sukan samu waje su haɗu, dalilin sa mata sunan *MUNA WUTA* kuwa shine masoyan su dakan fasa musu kai, suke zuzuta su alhalin basu san cewa masoyan nasu suke komawa su zage su ba da yake mahaukata ne su kawai sai suka ɗauka suka ɗorawa kai suna ganin cewa ai hakan shine dai-dai sannan sai kayi haka za'a sanka a duniyar marubuta na Online, wannan shine dalilin samuwar sunan a yayin da ma gani suke wa'inda keyi musu magana hassada ce da baƙin ciki, to wa'innan dalilan sune dalilin saka wannan suna a matsayin sunan ƙungiyar.
Wannan shine taro na farko da za'a yi a jahar Kaduna inda kowacce jaha daga cikin sauran jahohin ta turo da wakilanta, Gombe, Kano da Abuja duka.
Ummi kam ai ɗauki kwalliya ta gani ta faɗa dan ta jima rabon ta da irin wannan kwaliyyar murna fal ranta domin zata shiga cikin wa'inda suka ɗarata a rashin kunya