Showing 36001 words to 39000 words out of 107295 words
Chapter 13 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
dena turowa, haka ma video's ɗin. Saboda idan aka gani a cikin wayarki, cewa zakiyi ni na tura maki, kinga kin tona man asiri kenan"
Tana wannan masifar har ta isa gida. Tura wayarta tayi cikin riga, sannan ta shige.
Kaman kullum daiUmmin zaune take da baƙin ta, wai Fans ne suka kawo mata ziyara, daga cikinsu ma harda shatara ta arzuƙi, wai suna jin daɗin labarin ta, tana koya masu salo salo na kwanciya da ogannin nasu. (Hmm Fans kenan)
Ko kallonsu Saha batayi ba, ta nemi shigewa ɗakin nasu
Da sauri wata daga cikinsu ta buɗa baki tana cewa "Wannan fa Aunty Hibba? Ƴarki ce?".
Kai Ummi ta gyaɗa masu, tana mai ɗaga murya ta kwala ma Saha kira.
"Sahabat!!. Sahabat!!"
"Na'am" ciki ciki ta amsa tana mai fitowa daga ɗakin nasu.
"Ki gaida ƙawaye na mana, ko baki gansu ba?" cewar Ummin.
Tana Zumɓura baki tana komai ta gaishe su, wata daga ciki ce tayi saurin cewa "Aiko kaman na taɓa ganin photon wannan a Dp ɗin wata cikin group ɗinki Aunty, kai ita ma ce wallahi"
Gaban Sahabat ne ya buga damm!! Cikin in ina ta ƙarƙaro yaƙen dole tana mai cewa "a,, 'a aunty baani ba... Ce. Ni. Bana ma da wayaa"
Da mamaki matar ta maida kallon ta kan fuskar Ummi. Gyaɗa mata kai tayi cikin son tabbatar mata
"Kwarai ma kuwa Maman Aisar, ai bama barinta da waya yanzu, bata ma taɓa riƙe waya ba, kinsan ai sharrin zamanin nan na yanzu, saboda haka sai tayi aure, cen mijin ta ya siya mata. Gaskiya ba ita bace, ƙila dai kama ce ko?"
Gyaɗa kai Saha keyi kaman ƙadangaruwa, tana tsaye sai kyarmar ƙafafu take yi. Ita kuwa matar sai ta haɗiye wani irin miyau, tana mai murmusawa itama tace to" ƙila kamar ce, Amman tabbas dai na taɓa gani wallahi"
Da sauri Sahabat ta shige ɗaki, tana mai dafe baki da ƙirji, "Waih! Allah ya soni ni Sahabat, wannan shegiyar matar, ai data tona man asiri, ni me ya kaini ma sanya pic ɗina? Koda yake ai na cire tun ma ranar, ashe har ta gani, mayya kawai, to ta Allah ba taki ba, munafukan banza, ai wallahi duk sai kun shiga wuta, kuna karantawa kuna zuga ko? Harda wani kwaso ƙafafu wai kun taho godiya? Sai kace wani wa'azi ko hadisai take faɗa maku, ga masu rubutun Allah da Annabi cen, wanda ba zaka taɓa jin kalmomn batsa ba, bakwa son karantawa, amman idan aka fito ana maganganu kunfi kowa nuna ku na Allah ne, daga ku har Ummin Allah zai kama ku"
Har matan nan suka bar gidan, wadda aka kira da Maman Aisar tana al'ajabi. Sai bayan fitar su ne suka hau gulmar Ummin, wai wayau zatayi ma Allah, ita tana nufin ta kimlace tata, Amman tana ɓata na wasu, Allah dai ya shirya mana, amman yanda matar nan ke tsula tsiya a labaranta akace yarinyar ta na karantawa ai data sha kunya.
(Nace ai kuma kuna da laifi, da bakwa karantawa da basu rubuta ba, Allah ya kiyashe mu da kai kanmu wuta")
**********
Ita kuwa Hunayda da Allah shi kyauta tabi Saha, lamarin Saha na bata tsoro, ina duk tarbiyyr da Umminta ke iƙirarin tana yi mata? Ina duk kullen na Ummin tata?.
Da haka ta shige kitchen ɗin, zuciyar ta ba daɗi da irin yanda ta ɓata ma Sahar rai, ba da niyya tayi ba, saidai ba zata taɓa bari Sahar ta koya mata yima Ammin tata rashin kunya ba.
Ko da suka haɗu Islamiyya, tana gani Sahar tana galla ma malam Suhayl harara, sai duk taji ba daɗi, tayi niyyar bata haƙuri. Hakan yasa da aka tashi ta tsaida Sahar domin ɓata haƙuri, Amman sai ta sake yaɓa mata wasu maganganun, harma tana ce mata "Sannu shekiya uztaziya, ai dole ki nuna man Allah, kiyi mun wa'azi, tunda zaki auri alhuda huda, ai yanzu zaki ma iya cewa musulunci na ma bai cika ba". Tana gama faɗar hakan ta sanya kai tayi wucewarta, a gaba idanun ta Zaiyad ya faka da mota ta shige, dayake Surayya yau da Na'eef basu zo islamiyyar ba, bata san me ya hana su ba, ko ina suka nufa kuma oho, abun na Saha ya fara tsanani, ta kai ma ko Kunyar jama'a bata ji, wajen shiga motar wanda har yanzu ya gagara turawa gidan su, gashi kuma in sun keɓe ɗin ta sani abunda ba daidai ba suke aikatawa.
Da haka ta isa gida, zuciyar ta ba daɗi, saidai koda ta isa gidan, Ummin ta ke shaida mata cewa ta shirya tunda su Hajna sun samu hutu, zasu je Katsina gidan ƙawarta Hajiya Gambo, daganan zata kakkaisu sauran gidajen ƙawayen nata domin su gaida su.
Sai taji zuciyar ta tayi sanyi, ko ba komai zata ɗan huta da darun Saha, wata ƙila ma kafin ta dawo Sahar ta huce, da wannan zummar ta taka tana mai isa ɗakin nasu ta cigaba da har haɗa masu kayayyakin da tasan zasu buƙata...
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
♣ _Scene Four_
~*Page 12*~
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) says:
'Fasting is Mine and it is I Who give reward for it. [A man] gives up his sexual passion, his food and his drink for My sake.' Fasting is like a shield, and he who fasts has two joys: a joy when he breaks his fast and a joy when he meets his Lord. The change in the breath of the mouth of him who fasts is better in Allah's estimation than the smell of musk."
[Bukhari (also by Muslim, Malik, at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، عَنْ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَجَلَّ: الصَّوْمُ لِي، وَأَنَا أَجْزِي بِهِ، يَدَعُ شَهْوَتَهُ وَأَكْلَهُ وَشُرْبَهُ مِنْ أَجْلِي، وَالصَّوْمُ جُنَّةٌ، وَلِلصَّائِمِ فَرْحَتَانِ: فَرْحَةٌ حِينَ يُفْطِرُ، وَفَرْحَةٌ حِينَ يَلْقَى رَبَّهُ، وَلَخُلُوفُ فَمِ الصَّائِمِ أَطْيَبُ عِنْدَ اللَّهِ مِنْ رِيحِ الْمِسْكِ. رواه البخاري (وكذلك مسلم ومالك والترمذي النسائي وابن ماجه)
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Four_
~*Page 12*~
Hunayda kuwa taso ace kafin wucewarsu zuwa Katsinan sun haɗu da Saha, saidai hakan bai yuwu ba. Da misalin ƙarfe taran safe duk sukayi sallama da Ammin tasu, inda Abban su ne ya bada mota a kaisu. Saida Ammin taja masu kunne sosai, kafin ta damƙa amanar kula da Surayya hannun Hunaydan.
Tafiya ce da zamu iya kiran ta a nutse, domin Ammi tace ma Driver bata yarda yayi mata gudu da yaranta ba, ba sauri ake ba, balle aje ayi gaugawa.
Suna cikin motar ne Hunaydan ta danna ma Sahar tata kira.
Tana zaune gidan ƙunshi ana zana mata jan lalle, wanda Zaiyad ɗin yace mata yana so, kuma shine ma ya bada kuɗin, wai a cewar shi yana matuƙar son ƙamshin lallen.wayarta ce tayi tsuwwa alamun kira ya shigo.
Kallon ta ta kai kan wayar, lokaci guda tana mai janye idanun ta, gami da jan tsoki kaɗan.
"Kinji dashi ai, ki gama gaya man magana kuma ki nemeni yanzu? Me zan maki?" ta faɗa a hankali, iya kan laɓɓan nata.
"Me kika ce?" cewar matar dake zana mata lallen. Ba tare da Sahar ta kalleta ba tace "Ba dake nake ba". Sauke kanta ƙasa tayi taci gaba da zana mata lallen.
Hajna dake zaune gefe ce ta cigaba da girgiza kai a hankali.
Halin Yayar tata gabaki ɗaya yana bata tsoro, ko a gida fa ba'a san tana da waya ba, gashi taja mata kunnen akan idan ta sake ta faɗa, wallahi sai ta ɓaɓɓalla ta, gashi ita kuma abunda Sahar keyi yanzu ya fara bata mamaki, a kan idonta take waya da samari a cikin ɗaki, ko kuma ta shige bayi tayi ta waya, ko tayi ta karance karance marasa amfani.
Har ta buɗe baki da niyyar yima Sahar magana, sai wayar Sahar ta sake ɗaukar tsuwwa.
A hasale ta juya tana kallon Hajnar.
"Zo ki duba man, kibi a hankali kar ki ɓata mun waya". Shiru Hajnar tayi mata tana mai ɗauke kanta gefe, gami da turo baki gaba.
"Waike dan ubanki ba dake nake magana bane? Ki kiyaye ni fa Hajna, naga kaman kin fara raina man wayau"
Sake tura baki tayi gaba. "Wayar ma da Ummi bata san kina da ita ba? Wallahi ba dan ina jin tsoron ki dena ƙara man kuɗin tara ba, ai da sai na tona ki"
Ta faɗa itama ciki ciki.
"Me kike cewa? Ba dai zagina kike yi ba ko? Ah ke! wallahi sai in ɓaɓɓalla yarinya yanzun nan"
Bata ko kula ta ba, ta miƙe tana mai isa kusa da Sahar, dama ita ba'a sanya mata ƙunshin ba, tace ba zatayi ba, a makaranta an sanya masu dokar yin lalle, saboda haka ne ma har ya fita ranta. Amman duk da hakanan Ummin bata bari Sahar ta taho ita kaɗai ba.
Saƙon Hunayda ne tana shaida mata kada ta jita kwana biyu shiru, sunyi tafiya ne zuwa Katsina, Amman zasu dinga waya, ta kira ta bata kusa.
Taɓe baki tayi tana mai cewa "Umma ta gaida assha"
Duk da Hajnar na mamakin me ya shiga tsakanin Sahabat ɗin da Hunayda, Amman tsoro ya hana ta tambaya, kuma ko ba komai yanzu ta samu Sahar na ƙara mata kuɗin break akan wanda Ummi ke bata, Amman taja mata kunne akan idan ta faɗa ma Ummin aka gane tana da kuɗi, ba zata sake bata ba,dukda itama tana mamakin inda Sahar ke samun kuɗaɗe masu yawa har haka.
Saida aka kammala ma Sahar ƙunshin, harma ta wanke kafin suka bar gidan,
Ita kanta matar dake ƙunshin mamakin Sahar take yi, yarinya tana abu kaman wata matar aure? Ko kafin su bar gidan ƙunshin tayi waya da saurayin ta ya kai sau biyar, kuma shagwaɓar take zuba mashi son ranta, harma tana cewa sai ya ƙara kuɗi akan wanda ya bada. Da addu'ar shiriya ta bita, domin dai tasan irin zafi da tsananin Ummin tasu, Amman ace ƴar yarinya kaman wannan tana fira da maza irin haka.
*********
Sun samu tarba fiye da zaton su, babban gida ne daya amsa sunan shi gida, babu ce kawai babu ciki.
Nan danan matar ta shiga hidima dasu, sannan ta kira ɗiyar ta mai suna Sulaym ta haɗa su. Dayake Sulaym yarinya ce mai natsuwa, saidai akwai wayewa a tattare da ita, itama bata da hayaniya sosai, saidai tana da walwala da saurin sabo da mutane. Dan danan ta saki jiki dasu Hunaydan. Saida suka ci abinci suka huta, kafin Driver ɗin ya juya, a cewar Hajiya Gambon idan zasu koma da kanta zata je har gida ta maida su.
Saida ta cika Driver ɗin da abun arzuƙi, Hajiya Gambo ba dai kirki ba.
Zaman gidan yayi ma su Hunayda daɗi, domin rayuwa ce ake cikin gidan ba takura, ga wuraren shaƙatawa a cikin gidan, idan kuma sun so su fita, Hajiya Gambon ce ke kwasar su da kanta tana kaisu duk inda zasu masalan ma Katsina da take cike da mutane masu mara da kunya da karamci,
Hunayda da Sulaym sun ɗinke, kusan zamu ce sun zama ƙawaye, hatta makaranta da Sulaymin ke tafiya wani lokaci tare da Hunayda suke zuwa, komai a tare suke yi. Gashi Abunda ke birge ta, idan kitchen Hajiya Gambo zata shiga tare suke shiga, domin ita tace tana da ƴan mata ba abunda zai sanya ta ajiye mai aiki.
Komai na tafiya kaman yanda Hajiya Gambo ta tsara. Daga zuwan su Hunayda gidan ko sati biyu ba'a rufa ba, sai gashi hannun Hunayda ya goggoge da yin wasu abubuwan, sannan ta ƙara sani akan abubuwan kitchen, wanda suke amfani da wuta.
Zamu iya cewa Hunayda har ta manta da batun Sahabat, al'amurransu suke yi cikin kwanciyar hankali. Kullum sai sunyi waya da Ammin su, tana daɗa ja masu kunne akan yin biyayya da iya zama da mutane.
*Sumayya Abdullahi Babayo* marubuciya ce data shahara a fannin rubutun hausa irin na zamani, sannan tayi fice wajen tsara labarai da kuma fiddo ma'anarsu a fili, sannan da bayyana kura kuran da abu mara kyau kan haifar. Wannan ne ya sanya ta samu lambobin yabo da dama, da kuma kambun girmamawa. Rubutu take mai cike da tsafta da tsari, ana alfahari da irin litattafan ta ko a social media ɗin, bata taɓa yin rubutun littafi ta wallafa ba, saidai tana yin rubutun tane online, ga duk mai sha'awar karantawa, ko ina ya nema zai samu. Wannan ne ya sanya hatta da BBC Hausa saida ta bata kambun girmamawa.
Ƙungiyar su ɗaya da Hajiya Gambo. Kusan ma zamu iya cewa, tana daga cikin wanda Hajiya Gambo ta tsaya tsayin daka wajen ganin al'amurranta sun tafi daidai, masalan ma da take mai biyayya, girmama wanda tasan sun fita, da kuma natsuwa da kula da iyalin ta, ba tare da ta bari harkar rubutunta ta taɓa lafiyar zaman auren nata ba.
Kaman yanda Ammi suka tsara da Hajiya Gambo, hakan ce ta faru, domin kuwa Hajiya Gambo sun zauna da Sumie a pc a tsanake sun tattauna, daga nan ne Sumie ta buƙaci da abata numb Hunaydan, gami da yin adding ɗinta a special group nata, da kuma inda take tuttura litattafai.
Daga ƙarfe takwas na dare, Sulaym kan zauna karatu, ita kuma Hunayda sai ta shiga group ɗin Sumiee B. Inda take ganin irin tattaunawa mai muhimmanci da akeyi, da kuma ƙara wayar da kai akan al'amurran duniya da suka shafi girki da kula da kai da tsaftar jiki.
Duk abunda su Hunayda keyi akan idon Hajiya Gambo ne, idan ta samu lokaci kuma ta kan zauna dasu taji damuwoyinsu, takan bincika wayar su sosai kuma akai akai, sannan ta sake basu wasu shawarwarin.
Sosai zaman Katsinan yayi ma Hunayda daɗi, ba dan gida gida bane, da sai tace tafi jin daɗin nan. Yanzu tana kallon Saha online tana turo mata litattan data saba turo mata, da kuma videos wanda tayi imanin Zaiyad ɗinne ke turo ma ita Sahan.
Wani lokaci ta kan biye mata su gaisa sama sama, har Sahar ke mata ƙorafin wai ta manta da ita. Amman har ga Allah yanzu ta samu natsuwa, duk karance karancen da takanyi, wanda suke jawo mata matsala taji har bata iya tsallake karantawar, ko domin ta samu gamsuwa, takan guje masu, domin ya zuwa yanzu ko Sahar ta turo mata gogewa take yi kawai, ko don ma kada Hajiya Gambon ta gani.
Sahar dai ya zuwa yanzu ta ɗan fahimci wani abu, hankalin Hunayda ya karkata wani waje, taso taja Hunaydan a hanya da take, tana so idanun Hunaydan su buɗe kaman yanda nata suka buɗe, tana so Hunaydan ta dinga jin daɗi kaman yanda takeji itama. Taso ace ma Hunaydan ta samu namiji kaman Zaiyad, ta yanda itama zata ji daɗi, ta more rayuwar ta kaman yanda take yi itama. saboda haka ne ta ɗauri aniyar sake juyo da karkato da hankalin Sahan ɗin zuwa gareta, sannan taci ɗammarar raba Hunayda da wannan malam Salim ɗin, da idanun shi kaman na Mayu.
Sahabat abu yaci gaba, ya zuwa yanzu ko Zaiyad bai nemeta ba, da kanta take neman shi, tayi imann cewa da Zaiyad kaɗai zata iya rayuwa. Babu inda bata mallaka ma Zaiyad a jikin ta ya taɓa, har gidan shi ya kan kai ta suji ɗumin juna, kaman yanda ya kan ce, ai wannan shine soyayyar.
Kullum dai maganar shi ɗaya Dady ɗinshi yake jira, har yanzu bai dawo ba, sannan ya ƙara da cewa baya so a gidan su asan da zaman shine, yafi so manya su fara shiga al'amarin, ta yanda zai sake samun karɓuwa kai tsaye.
Kullum Ammi tayi sabon post, idan tana karantawa Zaiyad kawai take assuming, ji take dama shine yake mata kwatankwacin abunda Ammin tata takan rubuta. Wannan ya ƙara taka muhimmiyar rawa, wajen ganin akalar Sahabat ɗin ta ƙara warwarewa. (Hibba baki san kanki kike cutar wa ba, Amman akwai ranar nadama)
**********
Ya kai kusan minti biyu yana kwaɗa sallama. Har saida ya gaji ya kutsa kanshi cikin falon. Dama ya