Showing 90001 words to 93000 words out of 107295 words

Chapter 31 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1260

modern ake yi.

A sanyaye ta amsa da "Na gode Baba Mariya"

"Allah ya miki albarka dan Allah a ringa hattara"

Shigewa tayi tana yatsina fuska dai-dai zata shiga ta lura da Ummi tsaye a qofar gidan da alama ta dade da tsayuwar.

"Me kuke zantawa da Baba Mariya?" Gaban tane ya fad'i amma ta dake wai nasiha ta tsaya min tare da bani dogon tarihi akan Abban mu, halin shi me k'yau ne muyi koyi dashi kaza-kaza ni jin ta kawai nake bana game me take fad'a na kwaso rana."

A nutse Ummi ta dube ta tana karantar tanayin ta.

"A zahiri kuma ta amsa da Allah sarki Baba Mariya kenan."


"Shege ni." Farouk ya fad'a tare da dukan siterin motan bayan ya sauke ta yabar anguwar.

"Lallai Zaiyad dole kamin Katanga kak'i sake min cikar nan, koda sau d'aya ne kak'i ka barni na lasa naji nima, kai kad'ai kake more wannan ni'imar dana hango, Wallahi dole ka ringa haske da fresh abokina. Dole nima na lasa kalar zumar nan." Haka yayi ta sambatu har ya isa gida



******* ******** ******

Ganin ta take kamar a mafarki, har ta ida shigowa d'akin tare da jingina jikin gadon fuskar ta dauke da murmushi "Barka da safiya Salma, yaya jikin Allah ubangiji ya baki lafiya. D'azu zan shigo bakin gate nayi karo da Abban Husna bayan mun gaisa shine yake sanar dani kece baki ji dad'i ba, Allah ya baki lafiya."

"Amin." ta amsa jikin ta a sanyaye

Runtsa ido tayi wasu zafafan hawaye suka fara sauka tana tuno maganganun Habiba wanda data saurare ta da tabbas tasan da bata cikin wannan matsalar amma tayi fatali da ita da dukkan zancen ta. "Na rik'e Jameela ta zama siteri na sai yanda ta juya ni nake bi akan gida na." Zancen zucin da take kenan.





~_From The Everlasting Golden Pen ๐Ÿ–Š of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



ยฉ *2020*



_~We Love U All~_โค
[4/13, 8:50 PM] Sumayya Sumy B: ๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคท


*_MENENE RIBA TA โ“_*

๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†


ยฉ *2020*


๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*


*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ โ„ข _Golden Pen Writers Association_


~*DAGA ALQALUMAN*~๐Ÿ‘‡๐Ÿป.....โœ

โ™ฆ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

โ™ฆ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

โ™ฆ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

โ™ฆ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ฦ˜AREENATEEY.*

โ™ฆ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

โ™ฆ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._


ุนูŽู†ู’ ู…ูŽุณู’ุฑููˆู‚*ู . ู‚ูŽุงู„ูŽ : ุณูŽุฃูŽู„ู’ู†ูŽุง ู€ ุฃูŽูˆู’ ุณูŽุฃูŽู„ู’ุชู ุนูŽุจู’ุฏูŽุงู„ู„ู‡ู (ุฃูŽูŠู’ ุงุจู’ู†ูŽ ู…ูŽุณู’ุนููˆุฏู ) ุนูŽู†ู’ ู‡ูŽุฐูู‡ู ุงู„ุงูŠุฉู : : ูˆู„ูŽุง ุชูŽุญู’ุณูŽุจูŽู†ู‘ูŽ ุงู„ู‘ูŽุฐููŠู†ูŽ ู‚ูุชูู„ููˆุง ููŠ ุณูŽุจููŠู„ู ุงู„ู„ู‡ู ุฃูŽู…ู’ูˆุงุชุงู‹ ุจูŽู„ู’ ุฃูŽุญู’ูŠุงุกู ุนูู†ู’ุฏูŽ ุฑูŽุจู‘ูู‡ูู…ู’ ูŠูุฑู’ุฒูŽู‚ููˆู†ูŽ )) ู€ ู‚ูŽุงู„ูŽ : ุฃูŽู…ูŽุง ุฅูู†ู‘ูŽุง ู‚ูŽุฏู’ ุณูŽุฃูŽู„ู’ู†ูŽุง ุนูŽู†ู’ ุฐูŽู„ููƒูŽ ุŒ ููŽู‚ูŽุงู„ูŽ)) ุฃูŽุฑู’ูˆุงุญูู‡ูู…ู’ ููŠ ุฌูŽูˆู’ูู ุทูŽูŠู’ุฑู ุฎูุถู’ุฑู ุŒ ู„ูŽู‡ูŽุง ู‚ูŽู†ูŽุงุฏููŠู„ู ู…ูุนูŽู„ู‘ูŽู‚ูŽุฉูŒ ุจูุงู„ุนูŽุฑู’ุดู ุŒ ุชูŽุณู’ุฑูŽุญู ู…ูู†ูŽ ุงู„ุฌูŽู†ู‘ูŽุฉู ุญูŽูŠู’ุซู ุดูŽุงุกูŽุชู’ ุŒ ุซูู…ู‘ูŽ ูŽ ุชูŽุฃู’ูˆููŠ ุฅูู„ูŠ ุชูู„ู’ูƒูŽ ุงู„ู‚ูŽู†ูŽุงุฏููŠู„ู ุŒ ููŽุฃูŽุทู‘ูŽู„ูŽุนูŽ ุฅูู„ูŽูŠู’ู‡ูู…ู’ ุฑูŽุจู‘ูู‡ูู…ู’ ุงุทู‘ูู„ูŽุงุนูŽุฉู‹ ููŽู‚ูŽุงู„ูŽ : ู‡ูŽู„ู’ ุชูŽุดู’ุชูŽู‡ููˆู†ูŽ ุดูŽูŠู’ุฆุงู‹ ุŸ ู‚ูŽุงู„ููˆุง : ุฃูŽูŠู‘ูŽ ุดูŽูŠู’ุกู ู†ูŽุดู’ุชูŽู‡ููŠ ุŒ ูˆูŽ ู†ูŽุญู’ู†ู ู†ูŽุณู’ุฑูŽุญู ู…ูู†ูŽ ุงู„ุฌูŽู†ู‘ูŽุฉู ุญูŽูŠู’ุซู ุดูุฆู’ู†ุง ุŸ ููŽููŽุนูŽู„ูŽ ุฐูŽู„ููƒูŽ ุจูู‡ูู…ู’ ุซูŽู„ูŽุงุซูŽูŽ ู…ูŽุฑู‘ูŽุงุชู ุŒ ููŽู„ูŽู…ู‘ูŽุง ุฑูŽุฃูŽูˆู’ุง ุฃูŽู†ู‘ูŽู‡ูู…ู’ ู„ูŽู†ู’ ูŠูุชู’ุฑูŽูƒููˆุง ู…ูู†ู’ ุฃูŽู†ู’ ูŠูุณู’ุฃูŽู„ููˆุง ุŒ ู‚ูŽุงู„ููˆุง : ูŠูŽุง ุฑูŽุจู‘ู ุŒ ู†ูุฑููŠู’ุฏู ุฃูŽู†ู’ ุชูŽุฑูุฏู‘ูŽ ุฃูŽุฑู’ูˆูŽุงุญูŽู†ูŽุง ููŠ ุฃูŽุฌู’ุณูŽุงุฏูู†ูŽุง ุ› ุญูŽุชู‘ูŽู‰ ู†ูู‚ู’ุชูŽู„ูŽ ููŠ ุณูŽุจููŠู„ููƒูŽ ู…ูŽุฑู‘ูŽุฉู‹ ุฃูุฎู’ุฑูŽูŠ . ููŽู„ูŽู…ู‘ูŽุง ุฑูŽุฃูŽู‰ ุฃูŽู†ู’ ู„ูŽูŠู’ุณูŽ ู„ูŽู‡ูู…ู’ ุญูŽุงุฌูŽุฉูŒ ุชูุฑููƒููˆุง . (ุฑูˆุงู‡ู ู…ุณู„ู… (ูˆูƒุฐู„ูƒ ุงู„ุชุฑู…ุฐูŠ ูˆุงู„ู†ุณุงุฆูŠ ูˆุงุจู† ู…ุงุฌู‡*


*On the authority of Masruq (may Allah be pleased with him), who said:*

*We asked Abdullah (i.e. Ibn Masud) about this verse: "And do not regard those who have been killed in the cause of Allah as dead, rather are they alive with their Lord, being provided for (Qur'an Chapter 3 Verse 169)." He said: "We asked about that and the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him) said: 'Their souls are in the insides of green birds having lanterns suspended from the Throne, roaming freely in Paradise where they please, then taking shelter in those lanterns. So their Lord cast a glance at them (1) and said: 'Do you wish for anything?' They said: 'What shall we wish for when we roam freely in Paradise where we please?' And thus did He do to them three times. When they say that they would not be spared from being asked [again], they said: 'O Lord, we would like for You to put back our souls into our bodies so that we might fight for Your sake once again. And when He saw that they were not in need of anything they were let be.'"*

*(1) i.e. at those who had been killed in the cause of Allah.*

_[Narrated; Muslim also by at-Tirmidhi, an-Nasa'i and Ibn Majah.]_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



โ™ฃ _Scene Six_

~*Page 26*~

"Kiyi hakuri Salma nasan kina cikin qunci da b'acin rai wanda banason in qara zama silar qara miki wani b'acin rai kamar yanda kika fad'a baki son ganina a inda kike, baki son inzo inda kike, na ma kaina alqawarin nisantar ki har zuwa lokacin daza ki gane gaskiya nasan ko baki sake ganina ba zaki tuna dani watarana Allah shi ya jarabce ni da jin ki a zuciya ta wanda shi yasan hikimar hakan. Dan haka ina mai baki hakuri kan shiga rayuwar ki da nayi na takura miki, yanzu ma da ba rashin lafiya naji an anbata ba bazan rab'a inda kike ba. Ina miki fatan samun lafiya mai daurewa tare da miki fatan samun nasara a rayuwar ki. Na barki lafiya"

Bata jira cewar ta ba tayi ficewar ta a d'akin.

D'akin ne taji yana juyawa da ita, duk da ak'wance take runtsa idon ta tayi wasu hawaye na bin k'uncin ta.

****** ****** *****

Misalin qarfe 2:00 na rana Abdul-Kareem ya dawo inda ya tadda Jameela zaune bakin inuwa tana yan latse-latse a wayar ta, bata san da isowar shi ba yasa hanun ya qarb'e wayar yace; " Allah yasa kema ba wai irin karance-karancen litatttafan ku na hausar nan ba kike?"

Fari tayi da ido tare da saisaita muryar ta cikin sigan daukar hankali tace; " Abinda ban tab'a ba ma kenan Haske na, gaba d'aya littattafan Hausa mussamman na yanzu da aka maidashi online ba abinda yake sai b'ata tarbiya domin batsa suke zubawa kawai a cikin ta."

Tohfa yau ga inda ake yi, Jameelar dake sa har dubu ta sai littafi guda, mussamman idan ak'wai harka, fin haka ma zata iya biya domin ko ba komai yana rage mata zafi.

Ganin ta harbo logon shi yasa ta dad'a narkar da muryar. " Haske na ai ko ina karantawa idan har baka so dole na ajiye saboda farin cikin ka shine nawa, dole in bi duk abinda kake so, sab'a maka kai tsaye kamar ina sab'awa mahallaci nane. Idan kuma so kake in fara karantawa toh."


Maganganun ta sun mutuqar tafiya da hankalin shi, ji yayi ya rungume ta amma gilmawar da mutane suke yasa shi dai-dai ta kanshi tare da kama hanun ta yace "Allah ya miki albarka, na gode da dukkanin halaccin ki gareni."

"Amin." ta fad'a tana kashe shi da wani murmushi,

"Yaya mai jikin ya tambaya?"

"Jiki Alhamdulillah! Doctor yana son ganin ka, yana Office d'in shi bayan mata gwaje-gwaje an cigaba da mata qarin ruwa a halin yanzu dai tana barci."

"Alhamdulillah!" Ya fad'a

"Muje Office d'in nashi", langwab'e kafad'a tayi, sannan tace:

"A'a kaje kawai zan jira ka a nan idan ka fito sai mu shiga gurin nata."

Jim ya d'an yi, ba haka yaso ba. "Shikenan yanda kike so haka za'ayi amarya."


Kai tsaye office din likita ya nufa bayan ya nemi izinin shiga, ya mishi iso da nashi gurin zama, gaisawa suka yi inda ya gabatar mishi da kansa.

Binciken File d'in ta yayi game da fara kora mishi bayanai kan abinda yake damun ta.

"Bayan gwaje-gwaje da aka gabatar mata, sakamakon ya fito inda aka same ta da matsanacin gwambon ciki (Chronic Stomach Ulcer) sai Malaria da shima an same ta dashi amma ba yawa. Jinin ta ya hau sosai wanda tun maraice shi muke ta qoqarin ganin ya daidaita abin yaci tura, amma da yardar Allah yanzu munyi qoqarin yi mata allura dazai sa tayi barci tare da hutawa sosai bayan magungunan da aka bata da drip muna fatan za'a samu progress idan ta farka. Sai dai ak'wai buk'atan kiyaye duk wani abubuwa da dama saboda samun lafiyar ta mai dorewa mussamman kiyaye abinda zai ringa b'ata mata rai."

"Shikenan Doctor Insha Allahu za'a kiyaye na gode sosai, za a iya ganin ta?"

"Eh, zaka iya shiga sai dai ayi a hankali kar a tashe ta."

"OK, na gode" ya tashi ya fito jiki a sanyaye tare da jin tausayin ta mutuqa "Ke kika siya ma kanki damuwa Salma, kin je kin dauko halaiya da d'abi'un da ba taki ba kin yafa. Ya za ayi ki zauna lafiya?" Maganar da yake a zuciyar shi kenan har ya iso inda Jameela take.



******** ******** ********



Hunayda ce k'wance kan d'an madaidaicin gadon ta daya sha zanin gado mai taushi kalar fari da pink sai daukan ido yake, ta gyara shi gwanin ban sha'awa littafin *NAJWA* na Fhareedaty ta kammala karantawa wanda Aunty Sumiee ta ke musu posting littattafan yan qungiyar nasu mai cike da hikima basira da hikima wanda a iya rayuwar ta bata tab'a haduwa da littatafai masu cike da d'unbin basira kamar ire-iren su ba ta tun daga kan littafin *AMINTA* zuciyar ta ya kamu da son ta har ranta, wanda baza ta iya fasalta qaunar data ke mata ba a rayuwar ta mussaman irin muhimmin rawar data taka a rayuwar ta wajen ceto ta daga fad'awa tarkon Sahabat, Dan haka koda wasa ba ta bari littattafan da duk ta turo ya wuce ta ta qaru tare da daukan darasi daban daban wanda littattafai ne da suke tafiya da zamani masu cike da soyayya, fad'akarwa game da nishad'antarwa tabbas ba abinda za ta iya biyan wayanan bayin Allah sai godiya game da aduar gamawar su da duniya lafiya a hankali ta runtsa ido iskar fankar dake sama yana ratsa ta, ta fara lisafo sunan su a hankali *"UMMU SALMA na Ummu Yusuf, KAREENATY ( Khadija One love), HURU'AINI (Shamsiyya Yar Musa), RAYUWAR ALEESHA (Maryam A Shahada), JINNUL ASHQUE (Harira Aliyu/ Yar fillo), YAN UKU (Queen Indo) WANDA YACE TUKUNYAR WANI....( Ummity Yusuf), BANFI K'ARFIN TA BA. (Oum Deedat), SHABIHATY (Bintu Ahmad), A GIDAN MU( Shatu) KAICO NA (Nasbat Gaa...."

Maganar Ammi da taji ne ya dakatar da ita.

Cike da murmushi Ammi ta qarasa shiga cikin d'akin tare da zama a bakin gadon tace, "Wannan lisafe-lisafen danaji kinayi na sunayen mutane fa?"

Murmushi tayi game da mik'ewa ta gyara zaman ta tare da cire ear piece d'in dake kunnen ta wanda take sauraron cool music d'in Abdul D one wanda yanzu shine mawaqin da yake birge ta mutuqa, saboda waqoqin shi gaba d'aya na soyayya ne kuma cike suke da nutsuwa ba hayaniya.

"Ammi Sunayen haziqan marubutan qungiyar *Golden Pen Writers Association ne da littattafan* su dana karanta wanda nake qoqari a koda yaushe in haddace sunayen su tare da littafin su, saboda babu wacce ban dauki darasi ba a cikin labarin ta abin da yake bani mamaki Ammi shine, wasu daga cikin marubutan nan fa Yan Mata ne amma kuma idan suna baka darasi kan zamantakewar aure, maqota da tsakanin ka da dangin miji zaka ce sun shekara hamsin cikin gidan aure. Lallai na yarda wannan baiwa ce da Allah yake bama wanda yaso kuma a lokacin daya so, wallahi Ammi babu batsa babu rashin kunyar na wasu marubutan mussaman wasu daga cikin marubutan online da suke kiga sun fito da komai baro baro ba sakayewa."

Cikin jin dadin bayanan yar nata ta sake fad'ad'a murmushin ta tare da dafa kafad'ar ta, "Nayi farin cikin jin haka daga gare ki Hunayda, irin nunin da nake miki kenan a can baya. Alhamdulillah na godewa Allah daya amsa min rok'o na na kuma godewa wayannan bayin Allah da suka d'ora daga tarbiyar min dake, babu abinda zance sai hamdala da godiya gare su tare da musu aduar ganin farin ciki a rayuwar su ta nan duniya zuwa har cikin aljanna ya kare musu zuri'ar su daga gurb'atattun mutane da abokai ya daukaka darajar su. Ke kuma a koda yaushe kiyi qoqari kiyi amfani da abinda yake dai-dai cikin duk abinda kika karanta domin d'an Adam tara yake bai cika goma ba sannan ki nemi littafi ki ringa rubuta duk littafin da kika karanta sunan shi dana marubuciyar shekarar da aka rubuta da darasin da littafin yake dauke dashi, kinga sai ki adanawa yaran ki ki kuma basu labarin wayannan marubuta kamar yanda na baki nawa, domin kinga zamanin ku online ce tafi yawa bamusan me gaba zata haifar ba kuma idan muna raye."

"Allahumma Amin Ammi, lallai na gode da shawarar nan kuma insha Allahu yanzu zan ma fara ba sai anjima ba, amma abinda yake dad'a qara ma wayannan marubuta qima da daraja ido na shine wannan rubutun da suke ficika basa karb'a wallahi, rubutu suke fisabilillah da dukkanin qarfin su, tunanin su zuwa aljihunsu wasu daga cikin su ma datar watarana gagarar su take, amma wasu daga cikin Fans sai kiga da an k'wana biyu ba ayi posting ba zasu fara qorafi ba tare da la'akarin wani abu makamanci wannan ba domin wasu daga ciki ma cajin waya sai sun biya kud'i an musu, idan basu da wuta mussaman matsalar qasar nan da ko yaushe cikin matsalar wutar lantarki ake."

"Kinsan harka da jama'a sai a hankali, kowa da kalar fahimtan shi da kuma hangen nesa, amma magana ta gaskiya ku masu karatun ya kamata ku ringa k'yautata musu, domin kaman maluman ku suke idan kuka k'yautata musu Allah sai ya albarkaci abinda kuka karanta daga gare su."

"Haka ne Ammi, Allah ya bamu ikon k'yautata musu."

"Amin" ta amsa

Amma Ammi abinda ke daure min kai shine littattafan batsar nan da ake rubutawa naga k'wanaki ana ta yawo a social media wai suna taron qungiyar marubutan irin tasu wanda suka yi a nan Kaduna suna masu alfahari da kasancewar su masu rubutun *ADABIN BARIKI* shin Ammi dama ak'wai wani sigan rubutu ne haka? Ni ban tab'a ji ba duk kuwa da dad'ewar da nayi ina d'aukar darasi a Hausa."

"*ADABIN BARIKI KUMA?" Ammi ta tambaya da mamaki

"Eh! Adabin bariki! Domin yanzu abin dad'a gaba-gaba yake duk da matakin da wasu daga cikin qungiyoyin online writers d'in suke dauka na hana turo irin wayannan littattafan cikin groups din su, an samu saukin abin kam sosai da sosai ba kaman can baya ba daza ka ringa cin karo da pages din su ta ko ina. "

"Lallai kice yanzu duniyar online yazo da wani salon mai wuyar fassaruwa ga marubuta, zuwa masu karatu. Gaskiya banda masaniya akan haka amma kinsan ilimi kogi ne kuma na dade rabona da karatun littafi sama da shekara goma sha biyar. Amma zanyi qoqari in fara sannan dan kuma bincika wannan adabin barikin ta inda aka samo shi ."

"Tohm Ammi, amma dana fi kowa farin ciki idan kika fara bibiyar littafin nan kinga Ammi da *Banfi k'arfin Ta Ba* zaki fara kiga yanda rayuwar Suhan, da Yaya Ameen kiga son zuciya da cuta gurin Mom zjwa su Maree wanda Mom ta gada gurin iyayen ta da kakan ta sannan kiga mai zuciyar yan Aljanna irin su Ummah Allah sarki, tsatsan hakuri, da daukan qaddara." Ta qarasa maganar kamar zatayi kuka

"Dariya sosai Ammi tayi lallai ko zan karanta ni gashi ai har kin lasa min Zuma a baki naji na k'wadaita. Amma yanzu tashi kizo ki shirya na aike ki gidan Mariya ki karb'o min d'inki na jiya tace zata kammala amma naji ta shiru kar ta min halin teloli."

Dariya tayi sannan ta mik'e tare da fara qoqarin kintsawa. "Shikenan Ammi bazan je Hajna bata tashi a barci ba?"

"Bata tashi ba, kije karki zauna, ki dawo yanzu ga sauran kud'in nan ki bata. Ki gaishe ta kuma"















~_From The Everlasting Golden Pen ๐Ÿ–Š of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



ยฉ *2020*



_~We Love U All~_โค
๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคทโ€โ™€๐Ÿคท

ย  ย 
ย  ย  ย  *_MENENE RIBA TA โ“_*ย ย 
ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย ย 
ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ย  ๐Ÿ™†๐Ÿ™†๐Ÿ™†

ย  ย  ย  ย  ย  ย ย  ยฉ *2020*

๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*~โœ๐Ÿฝโœ๐ŸฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโœ๐Ÿฝโœ๐Ÿฝ~*

*~We are bearer's of so golden pen๐Ÿ–Š~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโœ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐Ÿ–Š,savour our words, for it will cause you no pain.~*

~*WRITTEN BY*~ย  โ„ข _Golden Pen Writers Association_

~*DAGA ALQALUMAN*~๐Ÿ‘‡๐Ÿป.....โœ

โ™ฆ *Ummee Yusuf*ย  ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

โ™ฆ *Aminatu Hassan*ย  ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

โ™ฆ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI*ย ย  ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

โ™ฆ *KHADIJA MUHAMMAD*ย  ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ฦ˜AREENATEEY.*

โ™ฆ *FATIMA UMAR MODIBBO*ย  ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIFย 

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login