Showing 63001 words to 66000 words out of 107295 words
Chapter 22 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
da rashin mutunci da silar lalata yara, hakan yasa idan kaga fuskar ta sai ka ɗauka albishir akayi mata da kujerar hajji kyauta.
Tana fitowa lungu ta haɗu dashi, ɗan dattijo ne dan ya fara tsufa ya ɗan rankwafa ƙasa kaɗan sannan ya gaishe da ita domin kuwa ta kan yi musu ihsani shida ƴan majalisar shi.
"Mal Mukhtar ya iyali?", ya amsa da; "lafiya lau Hajiya fatan an fito lafiya?", tayi murmushi tace; "lafiya lau ya akayi ne?".
Sai da ya ɗan ƙara gyara tsayuwa sannan yace; "dama wani abu ne naga yana faruwa da ƴar ki shine nace bari na faɗa miki domin kuwa yaran yanzu sai Allah".
Ummi ta ɗan ɓata rai sannan tace; "me kenan Mukhtar", ganin ta bashi dama yasa ya ƙara gyara tsayuwa yace; "akan Sahabat ne kusan kullum wani me mota ke zuwa ya ɗauke ta, sannan kuma ya kan dawo da ita kuma ko yau ma ƙannen kawai ta tura makaranta suna tafiya yazo da mota ya ɗauke.........".
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet (peace and blessings of Allah be upon him), who said:
"Allah (mighty and sublime be He) said:
'Spend (on charity), O son of Adam, and I shall spend on you.'"
[Bukhari (also by Muslim).]
عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: قَالَ اللَّهُ: أَنْفِقْ يَا ابْنَ آدَمَ، أُنْفِقْ عَلَيْكَ .
~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍
♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*
♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
♣ _Scene Five_
~*Page 20*~
Ummi cikin sauri ta ɗaga mishi hannu, cikin masifa tace; "yanzu Malam Mukhtar har yawpn gulmar ka ya tsallake kan mutane ya kawo kan ƴata?, to wallahi ka sani ba zan ɗauka ba domin kuwa ni ban haifi ƴar iska ba ya za'ayi kullum ina ƙoƙarin kyautata muku amma ku kuna ƙoƙarin bin jinina da ƙazafi, to bari kaji idan har hakan ya kuma faruwa sai na ɗauki tsattsauran mataki akan ka", shi dai Malam Mukhtar babu abinda yake yi sai ƙoƙarin bata haƙuri domin ya san ya ɓata damar shi.
Ummi ta ja dogon tsaki ta wuce shi tana faɗin; "mutanen yanzu basu tsoron Allah kwata-kwata, wai kai kana da naka laifin amma ka danne na wani kake son hangowa kuma wai ma har da sharri".
Haka har ta ƙarasa bakin titi ta tare Napep ta nufi Hall da suke taron, Allah-Allah take yi taje ko zata sami sauƙin abinda ke damun ta.
Me keke Napep na sauke ta, ta fara jiyo hayaniyar mutane inda ake shige da fice na jama'a, cikin zumuɗi ta nufi ciki da sauri me Napep ɗin ya fito yabi bayan ta yana kiran ta.
Sai da ta ja tsaki sannan ta juyo, yace; "Hajiya kuɗi na", ta kuma jan wani tsakin sannan ta ciro dubu ɗaya ta miƙa mishi ya ciro canjin ta ya miƙa mata sannan ya juya ya tafi yana mamakin me ake a ciki da har ya ɗauke mata hankali, ya ɗaga kafaɗa yana faɗin; "Ina ruwa na mane 🤷".
ita kuwa Ummi cikin sauri ta nuna pass get sannan ta shige ciki, waje ne Babba domin babban ɗakin taro ne da ake ji dashi a garin kaduna.
An ƙawata wajen sosai ga kujeru nan a jere ga kuma mutane ana ta hada-hada, babu abinda Ummi take banda wurga idanu ta ina zata hango ƙawarta amma sam bata hango ta ba hakan yasa ta fara takawa zuwa ciki.
Abinda ya bata mamaki shine jin me riƙe da speaker ɗin tana sanar da isowar ta, inda take cewa; "ga ɗaya daga cikin manyan marubutan da ƙungiyar *Muna wuta* take ji dasu wanda rubutun su har yanzu yana zagaya duniyar internet wato *Hibba* marubuciyar *Ni da shi*", aifa sai ga waje ya ɗauki ihu da tafi.
Nan fa Ummi taji wani abu yana flying saman kanta, ji tayi har tafiyar ta sai da ta canza taku.
Manya-manyan cikin su haka suka dinga gaisawa da Ummi sannan aka bata wajen zama a saman high table inda daman aka tsara cewa nan ne wajen zaman manyan ƙwarin ƙanana kuma suna ƙasa.
Ta kalli gefen ta, sannan tayi dariya tace; "ai ina ta neman ki Afra amma ban ganki ba ashe kina nan sama", matar wacce zasu yi sa'a da Ummin tayi murmushi sannan suka sake gaisawa.
Wata ƴar figigiyar mace ita aka kira ta hau saman domin yin jawabi, nan fa ta shiga godiya sannan ta fara sakin zance kamar a club su kuwa sauran babu abinda suke sai dariya da tafa mata.
Figigiyar macer tace; "ai mu abin alfaharin mu ne duk wanda zai zage mu sai dai ya karawa kanshi zunubi kuma koyar da yadda ake harka yanzu muka fara, ni nan Asmy ina nan zan rubuta littafi a wannan watan wanda ko miji na ya karanta idan bana kusa sai ya afkawa ƴata 😥".
Nan fa waje ya ɗauki sowa ana faman ihu da murna, ta cigaba da cewa; "Kuma ina nan zan rubuta ɗin wa'inda suka fasa zagin nawa ba ƴan halas bane", nan ta ringa kutuntumo ashar su kuma suna jin cewa ai ta kai ƙarshe kawai.
Bayan ta gama nata jawabin haka wata wacce daga gani ita ko auren farin ma bata yi ba amma kana jin magan-ganun ta ka san sun wuce shekarun ta.
Koda aka zo kan Ummi itama tayi nata jawaban cike da batsa da rashin tarbiya sannan ta ɗora da yi musu albishir ɗin tana gama *Ƙasan Cibiya* zata fara wani sabo wanda yafi wannan kawo wuta.
A ƙarshe aka naɗa sababbin shuwagabanni wa'inda zasu wakilci ƙungiyar a nan kaduna inda aka bawa Ummi treasurer.
Shugabar da aka naɗa musu me suna Bihal ta miƙe tayi godiya sannan tayi fatan komawar su gida daga nan aka sami zabiya inda take badawa suna amsa mata.
*Muna Wutaaa.......*.
*Suna binmu da fetur*.
*kowa yace bamu ba*.
*ɗan hassada ne*.
*meye a cikin duniyar?*.
*Banda a hole*.
*daga duniya sai kaduna*.
*in tayi ƙamari Abuja*.
*kusa shagalin ku duniya ce*.
*Muna wuta suna bin mu da fetur*
Haka take faɗa su kuma suna mata amsa mata, sai da suka gama sannan aka ɗauki tafi kafin kuma a fara kacaniyar cin abinci me rai da lafiya ana yi kuma ana gaisawa cike da farin ciki ga waƙa irin ta batsa dake tashi a hankali a hankali gefe masu rawa da shafe-shafen jiki suna ta yi kowa na ƙoƙarin ya gwada iya rashin tashi tarbiyar da kuma ƙwarewar shi a fitsara.
Ni dai abin ya ishe ni haka kada na ɗauko abinda yafi ƙarfin kunne na hakan yasa na kwashi slippers ɗina a hannu na sannan na fice amma sai da na ɗauki take away ɗaya na ɓoye a baya na kada su gani su ƙwace😏.
A waje na haɗu dasu Aunty Umme inda suke zaman jira na don mu wuce gidan Abdul na Salma da Jameela baban Husna da Mussadiq😂.
******** **********
Salma tayi tsalle ta dire sannan ta kwasa tayi waje da gudu, Abdul na ganin ta fita ya zauna yana dafe kanshi yana kuma faɗin; "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un".
Ya jima a zaune gaba ɗaya duniyar yaji tana juya mishi, gani yake gaba ɗaya matan yanzu tsoro suke bashi har Salma ce yanzu zata iya fira a gaban shi irin wannan with confidence🤔 Ina ilimin nata?".
Ni kuwa nace; "an rufe border dashi mana😎.
Kwata kwata barcin ma kasa yi yayi a daren gashi baya jin zai iya faɗawa wani sirrin gidan shi amma gaskiya yana neman mafita.
Wata zuciyar tace mishi; "mafitar kenan ka ƙara aure ko zata yi hankali", ganin hakan ba zai fishe shi ba yasa kawai ya tada kabbarar sallah.
Salma kuwa sai da ta jita a ɗakin yaran nata, ta jingi na da jikin ƙofar tasu tana me maida numfashi, lallai yau ta tsorata da mijin nata.
Ta jima tana saƙe-saƙe kafin kuma ta nufi kan gadon nasu ta kwanta, sai dai abin ban haushi tana kwanciya taji ƙasa a bayan ta.
Wani dogon tsaki taja kafin ta tashi zaune, yanzu dama Abban Husna be share ɗakin nan ba yau ya gyara?", abinda ta faɗa kenan.
Dole haka ta tashi ta ɗauko wani zanin ta shinfiɗa a saman sannan ta kwanta, sai a lokacin ta kalli kan yarinyar tata, kitso ta gani ƙanana-ƙanana masu kyau gwanin ban sha'awa ta kai hannu saman kan ta shafa, kitson ba ƙaramin birge ta yayi ba ta kai hancin ta taji yana wani irin ƙamshi me daɗi na mayukan daya sha, hannu tasa ta janyo hannun yarinyar lalle ne gashi nan a saman fatar yarinyar wanda ya tsaru yayi kyau haka ma ƙafar shi kanshi hannun ƙamshin muhallabiya yake yi, Salma ta taɓe baki tana me juyawa.
Idanun ta ya sauka kan ledar dake gefe wacce Jameela ta bawa Husnar da zasu taho, kamar ta kwanta sai kuma wata zuciyar tace duba kiga meye a ciki.
Da sauri ta tashi ta ɗauko ledar ta buɗe, dogayen riguna masu kyau guda biyu ƴan kanti ɗaya pink da milk ɗayar kuma ɓaki da ash sosai kayan suka yi kyau duka a cikin ledar su, sai riga da wando ƴan kanti guda biyu suma, sai t-shirt da wando jeans kala uku, agoguna guda biyu ƙanana sai babba ɗaya sai kuma takalma dai-dai Husnar ɗaya me ɗan tudu ɗaya flat, na maza kamar ƙafar Musaddiq suma guda biyu masu kyau ɗaya slippers ɗaya cover shoe, sai turare manya guda uku masu ɗan tsada da kuma tarkacen kayan kwalliya.
Salma cikin mamaki tace; "waye kuma ya basu wa'innan kayan, wannan dai rigunan da riga da wandon na Husna ne wannan kuma na musaddiq, wa'innan fa?", ta faɗa tana nuna turaruka guda uku da kuma agogo ɗaya.
"ABBAN HUSNA",amsar da zuciyar ta ta bata kenan dandanan kuwa taji gaban ta ya faɗi lallai ma wacece wannan kenan.
Kenan da gaske wai auren zai yi? Lallai akwai tashin hankali a gidan nan Allah ya kaimu gobe sai ya gaya mini wace tsinanniya ce ta bashi wannan kayan, haka tayi ta zuba surutun ta ita kaɗai.
Tayi can tayi nan ji take zuciyar ta na saƙa mata irin rashin mutuncin da zata yi mishi kasa haƙuri tayi dan haka tayi post a group ɗin su wai shi *Matan Manya* Nan fa suka dinga bata shawarwari wanda kusan duk akan kada ta yarda ne.
Wata har cewa tayi ta kwashi kayan kawai ta ƙona tun daren nan wata tace mata taje yanzu ta mishi rashin mutunci wata kuma tace ta bari sai da safe.
Ita kanta tafi aminta akan ta bari sai da safen kawai dan haka tayi godiya sannan ta kashe datar ta nemi waje ta zauna tana ƙara saƙa yarda zasu kwashe da safe.
Har akayi kiran Assalatu idanun ta biyu dan haka bayin su Husnar ta shiga ta ɗoro alwala sannan tazo tayi sallah.
Da sallama ya shigo ɗakin ganin ta a tsaye yasa ya juya kawai ba tare da ya ƙaraso ciki ba, ita kuma kuma taja tsaki sannan ta nemi waje ta zauna.
Sai da aka idar da sallah a masallatai sannan ta tashi su Husnar suka je suka yi sallah, wayar ta ta janyo ta hau online inda ta ƙara cin karo da shawarwarin ƙawayen nata.
Gari yana fara haske ta jiyo motsin mijin nata a kitchen wanda hakan ya tabbatar mata da ya tashi kenan, dan haka cike da ƙarfin gwiwa ta miƙe hannun ta riƙe da kayan ta fito.
Har ya fito da kayan karin a hannun shi, kallon kallo suka yi kafin ya ratse ta gaban ta ya wuce.
Wannan abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka cikin sauri ta dawo gaban shi sannan ta jefar da kayan a ƙasa cikin gadara tace; "waye ya baku wa'innan kayan?".
Ya kalle ta cike da mamaki kan yabi kayan da suka zubo daga cikin ledar da kallo, bece mata komai ba sai ajiye kayan karin da yayi ya nufi ɗakin yaran inda ya tarar har sun shirya ya riƙo hannun su suka fito falo nan ya zaunar dasu ya zuba musu abin karin.
Ganin yadda yayi banza da ita yasa ta ƙara fusata cikin jin haushi tace; "wai ba tambayar ka nake yi bane, nace waye ya baka wannan kayan?".
Be kula ta ba sai kofin da yake cike da kunun daya dama ya ɗauka da nufin kaiwa bakin shi, cikin ingizawar da zuciyar take mata tasa ƙafa ta bige kofin wanda kofin be sauka ko'ina ba sai fuskar Musaddiq kasancewar yana gefen Abdul ɗin ne, yaron ya tsandara ihu.
Abdul yayi kanshi da sauri, kunun ya ɓata fuskar yaron sosai ga kuma shi kunun da zafi ga kofin irin mug ɗin nan ne, wani irin abu ya haɗiya sannan ya kalli Husna yace; "jeki bayi ki wanke mishi, daga nan ki shiga ɗakin ku ki kwantar dashi sannan kema ki zauna a ɗakin", yarinyar ta amsa da "to Abba", ta ja hannun Musaddiq ɗin suka wuce.
Abdul yana ɗagowa ya kwashe Salma da mari dama da hagu, ta saka hannu ta dafe kuncin ta cikin masifa tace; "ni ka mara to wallahi sai na rama banza mugu azzalumi lusari kawai, wallahi sai na ram.....", bata rufe baki ba ya kuma ɗauke ta da wani marin.
Jijiyoyin kanshi sun fito ruɗu-ruɗu tsabar ɓacin rai, cikin haɗuwar numfashi yace; "shege ka fasa in kin fasa ramawa", aikuwa Salma na jin hakan tayi kukan kura tayi kanshi shi kuwa ya saka mata ƙafa ji kake timmm a ƙasa.
Ta bugu sosai hakan yasa ta miƙe da ƙyar, cike da gajiya da halinta Abdul yace; "wallahi idan baki bar wannan hanyar da kika ɗauko ba kina tattare da wahala,banza wacce bata san inda yake mata ciwo ba, kina so ki san inda muka je har aka bada kaya ne ko, to ba wani waje bane face wajen matar da zan aura nan da wata ɗaya ke kuma sai ki zauna ki cigaba da mugun halin da kika ɗauko", yana gama faɗin hakan ya shige ɗakin su Husna ya barta a tsaye kamar wacce aka shuka.
Cikin jin haushi tace; "au haka kace to wallahi sai na tada hankalin ka a gidan nan, sai dai kowa ya rasa nasa farin ciki, babu wacce ta isa ta shigo gidan za kuma ka gani".
Kamar mahaukaciya haka ta janyo wayar ta, number ɗin Jameela ta nemo ta danna kiran ta, koda ta ɗaga cikin kuka take sanar da ita abinda ya faru.
~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~
© *2020*
_~We Love U All~_❤
[3/9, 9:36 AM] GOLDEN PEN WRITERS ASSOCI: 🤷♀🤷♀🤷
*_MENENE RIBA TA ❓_*
🙆🙆🙆
© *2020*
🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀🤦🏻♀
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*
*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him) from the Prophet