Showing 84001 words to 87000 words out of 107295 words
Chapter 29 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
๐๐๐
ยฉ *2020*
๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ๐คฆ๐ปโโ
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~โ๐ฝโ๐ฝGOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONโ๐ฝโ๐ฝ~*
*~We are bearer's of so golden pen๐~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden penโ,behold our words.~*
*~A product of our pen๐,savour our words, for it will cause you no pain.~*
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say:
"The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire."
[Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)]
ุนููู ุฃูุจูู ููุฑูููุฑูุฉู ุฑูุถููู ุงูููููู ุนูููููุ ููุงูู: ุณูู
ูุนูุชู ุฑูุณูููู ุงูููููู ุตููููู ุงูููููู ุนููููููู ููุณููููู
ู ููููููู: ุฅูููู ุฃูููููู ุงููููุงุณู ููููุถูู ููููู
ู ุงููููููุงู
ูุฉู ุนููููููู ุฑูุฌููู ุงุณูุชูุดูููุฏูุ ููุฃูุชููู ุจููู ููุนูุฑูููููู ููุนูู
ููู ููุนูุฑูููููุงุ ููุงูู: ููู
ูุง ุนูู
ูููุชู ูููููุงุ ููุงูู ููุงุชูููุชู ููููู ุญูุชููู ุงุณูุชูุดูููุฏูุชูุ ููุงูู: ููุฐูุจูุชูุ ููููููููููู ููุงุชูููุชู ููุฃููู ููููุงูู: ุฌูุฑููุกูุ ููููุฏู ูููููุ ุซูู
ูู ุฃูู
ูุฑู ุจููู ููุณูุญูุจู ุนูููู ููุฌููููู ุญูุชููู ุฃููููููู ููู ุงููููุงุฑู. ููุฑูุฌููู ุชูุนููููู
ู ุงููุนูููู
ู ููุนููููู
ููู ููููุฑูุฃู ุงููููุฑูุขููุ ููุฃูุชููู ุจูููุ ููุนูุฑูููููู ููุนูู
ููู ููุนูุฑูููููุงุ ููุงูู: ููู
ูุง ุนูู
ูููุชู ูููููุงุ ููุงูู: ุชูุนููููู
ูุชู ุงููุนูููู
ู ููุนููููู
ูุชูููุ ููููุฑูุฃูุชู ููููู ุงููููุฑูุขููุ ููุงูู: ููุฐูุจูุชูุ ููููููููููู ุชูุนููููู
ูุชู ุงููุนูููู
ู ููููููุงูู: ุนูุงููู
ูุ ููููุฑูุฃูุชู ุงููููุฑูุขูู ููููููุงูู: ูููู ููุงุฑูุฆูุ ููููุฏู ูููููุ ุซูู
ูู ุฃูู
ูุฑู ุจูููุ ููุณูุญูุจู ุนูููู ููุฌููููู ุญูุชููู ุฃููููููู ููู ุงููููุงุฑู. ููุฑูุฌููู ููุณููุนู ุงูููููู ุนูููููููุ ููุฃูุนูุทูุงูู ู
ููู ุฃูุตูููุงูู ุงููู
ูุงูู ูููููููุ ููุฃูุชููู ุจูููุ ููุนูุฑูููููู ููุนูู
ููู ููุนูุฑูููููุงุ ููุงูู: ููู
ูุง ุนูู
ูููุชู ูููููุงุ ููุงูู: ู
ูุง ุชูุฑูููุชู ู
ููู ุณูุจูููู ุชูุญูุจูู ุฃููู ูููููููู ูููููุง ุฅููููุง ุฃูููููููุชู ูููููุง ููููุ ููุงูู: ููุฐูุจูุชูุ ููููููููููู ููุนูููุชู ููููููุงูู: ูููู ุฌูููุงุฏูุ ููููุฏู ูููููุ ุซูู
ูู ุฃูู
ูุฑู ุจููู ููุณูุญูุจู ุนูููู ููุฌูููููุ ุซูู
ูู ุฃููููููู ููู ุงููููุงุฑู. ุฑูุงู ู
ุณูู
(ููุฐูู ุงูุชุฑู
ุฐู ูุงููุณุงุฆู)
~*WRITTEN BY*~ โข _Golden Pen Writers Association_
~*DAGA ALQALUMAN*~๐๐ป.....โ
โฆ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*
โฆ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*
โฆ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*
โฆ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ฦAREENATEEY.*
โฆ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*
โฆ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*
~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_
~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*
โฃ _Scene Five_
~*Page 24*~
Cikin fushi Salma ta ฦaraso kusa da Jameela ta fincikota, tace; "wallahi baki isa ba dole ki bar mini miji na, na baki amana shine zaki ha'ince ni?".
Jameela ta taษe baki tace; "wannan kuma matsalar ki ne, ke in banda hauka kalar taki taya zaki sami miji kamar wannan amma ki zauna wasa", Salma kuwa babu abinda take banda jijjiga Jameela tana kuka.
Abdulkareem kuwa da yaga abin ba zai ฦare ba, da kanshi ya hau raba su, da ฦyar ya fincike Jameelar a hannun Salma.
Salma kuwa lokaci guda ta fita hayyacin ta, babu abinda take yi sai kuka idanun ta sam sun rufe faษi take; "macuciya Allah ya isa tsakani na dake".
Abdulkareem dai jan hannun Jameela yayi suka fice daga ษakin, Fatima da Firdausi wanda hayaniyar su Salmar ya tayar dasu, Fatima ta riฦo Salma wacce ke kwance saman tiles tana kuka tace; "Aunty kiyi haฦuri".
Salma tace; "Fatima ku tafi ku bani waje, mutane gaba ษaya macuta ne basu da amana, Fatima kije nace", dole haka Fatima ta tafi ta barta.
Salma bata tashi daga wajen ba har aka yi kiran sallar asuba, haka ta miฦe jikinta babu ฦarfi ta shiga bayi tayi alwala ta hau darduma ta fara sallah.
Sai da ta idar sannan ta tashi su firdausi domin suma suyi sallah, kan kujera ta koma ta kwanta tana tariyo rayuwar su ta baya ita da Abdulkareem ษin.
Har gari yayi haske sannan su Firdausi suka fito suka shiga kitchen domin haษa abiษ kari, Salma na kwance tana jinsu amma saboda yadda zuciyar ta da jikinta babu daษi yasa ko ษago kai bata yi ta kalle su ba.
Sai da suka gama sannan Fatima tazo ta tsugunna kusa da ita tace; "Aunty Salma mun gama, zamu kawo miki naki ne nan?", Salma tace; "kuci kawai idan zanci zan muku magana", Fatima ta ษan yi jimm sannan tace; "shikenan".
Fiddausi ta jera abincin saman tray sannan ta nufi part ษin amarya dashi, sai dai me tana zuwa ta samu a kulle dan haka ta bubbuga.
ฦangaren Amarya da Ango kuwa suna zuwa ษaki Jameela ta mantar dashi wata Salma haka suka sha love ษin su a matsayin su na sababbin amare.
A lokacin da Firdausi ta buga ฦofar suna bayi suna wanka tare, Jameela cikin salon ษaukar hankali tace; "Annurin zuciyata bari na duba naga ko waye", da gayya ta saka ฦaramin towel ta fito a haka kai a jiฦe don ta san Salma ce kuma tana so ta baฦantawa Salmar rai.
Sai dai kash! Tana buษewa taga Fiddausi dan haka ta haษe rai, Fiddausi kuwa ta ฦaฦalo murmushi tace; "barka da safiya Amarya dama Aunty ce tace na kawo muku abin kari".
Jameela ta harare ta sannan tace; "kije kice mata bama buฦatar abincin ta domin iya abinda na bashi da daddare jiya da wanda ya bani ya ishe mu yinin yau", tana gama fadar haka ta maida ฦofar ta rufe.
Fiddausi ta kama baki tana mamakin halin Amaryar, haka ta maida kayan zuwa ษakin Salma wacce bama ta san anyi ba, Fatima tana karyawa taga Fiddausi ta tulin abinci ta dawo.
"meya faru kuma?", Fiddausi ta faษawa Fatima duka abinda ya faru, Salma tana jinsu sai dai bata da ishashshiyar lafiyar da zata amsa musu.
Haka suka dinga didimar su har sai da Maman su tayi kiran su akan su koma gida sannan suka tattara kayan su suka tafi.
ฦangaren amarya da ango kuwa bayan ta koma tace; "matar ka ce tazo yi mini gargaษi wai kona bar gidan nan ko ta kashe ni", yayi murmushi me ciwo cikin ษacin rai yace; "da kuwa na ษauki mummunan mataki akanta".
Jameela tayi munafikin murmushi, sai da suka taimakawa juna suka shirya sannan Jameela ta shafa cikin ta tace; "Haskena yunwa nake ji fa".
Yayi ษan jim sannan yace; "bari naje na amso a wajen Maman Husna idan ta girka", ba tare da tace komai ba ya juya ya fice.
Da sallama ya shiga ษakin, komai a gyare yake fes dashi, Salma tunda ta ษago ta kalle shi ta maida kanta tana rufe idanu, zuciyarta kamar ta tsago ฦirjin ta, ta fito haka take ji dama ace zata iya ษaukar wuฦa ta soka mishi ya mutu kawai kowa ya huta.
Abdulkareem kuwa mamaki yake yi da tunanin sauyin halin Salma wato ko gaisuwa ba zai samu ba, cikin haษe fuska yace; "ina abin karin mu".
"Lallai namiji munafiki ne", abinda Salma ta faษa kenan a ranta amma a fili tace; "bar girka daku ba", tana faษar haka ta juyar da kanta gefe.
"wai wannan wane kalar hali ne kika ษauko Salma kamar kwana biyu kin dena yanzu kuma mugun halin yana so ya dawo?, Salma ni kike wulaฦantawa ko, har Jameela zaki je ki yiwa kashedi akan ta bar miki gida idan ba haka ba zaki kashe ta ko? Yanzu ban isa dake ba ko to kiyi duk abinda kike ganin zaki yi sai dai ki sani yadda na ษauki wulaฦanci a da yanzu ba zan ษauka ba domin kuwa da da yanzu da bambamci", yana gama faษar haka ya fice daga ษakin.
Salma ta saki kuka wai ko zai sanyaya mata rai akan abinda Abdulkareem ษin ya aikata mata, lallai rayuwa kenan.
Yana fita ya koma ya cewa Jameela tayi haฦuri ta ษora musu abin kari, cikin kissa tace; "ayya Haskena kada ka damu ni da nazo neman aljanna", yaji daษi sosai a da ya san yaji kalan kalaman nan daga wajen Salma sai dai a yanzu da Jameela ta faษa sai ya tabbatar da cewa ya cutu na samun rashin kulawa daga matar shi.
Suna gama karyawa jama'a suka fara zarya domin ganin ษakin amarya hakan yasa Abdulkareem ficewa daga gidan gabaki ษaya.
Salma na kwance zazzaษi ya rufe ta kuma tana jiyo zuwan kowa har dangin su Abdulkareem ษin amma babu wanda ya leฦo yace ci kanki nan fa ta fara zubar da hawaye domin ta san cewa Jameela ta cuceta kuma ta kaita ta baro domin kuwa itace silar da ta dinga yiwa dangin Abdulkareem ษin rashin mutunci yanzu gashi sun dena ganin farinta yayin da Jameelar kuma ta sami damar shigewa ฦดan uwan mijin nasu.
Har dare Salma na kwance abinda yake tayar da ita sallah, su Husna ma an dawo dasu gidan amma abin mamaki babu wanda ya shigo inda take.
Haka Salma ta kwanta cikin baฦin ciki, domin kuwa yaran ta ma gudun ta suke yi, wannan ya ฦara tayar mata da hankali.
Ta kira yayyin nata tayi musu complain amma kowa cewa yake yi Allah ya ฦara ita ta jawa kanta.
Ranar ma dai Salma bata yi wani barcin kirki ba domin kuwa ga rashin lafiya ga kewar yaran nata da mijin ta haka ta kwana a wahalce.
Da safe kuwa da ฦyar take iya buษe idanu saboda yadda suka kumbura gashi sunyi jajur dasu, ga wani irin ciwo da kanta yake yi.
Abinda ke ฦara bata mamaki rashin shigowar mijin nata inda take tun jiya da safe da yazo ษakin nata karษar abinci be kuma takowa inda take ba.
Haka ranar ma ta wuni a kwance sai dai idan taji yunwa ta janyo flask ษin ruwan zafi ta zuba tasha sai kuma sallah.
Kuma yanzu abin ya fara bata tsoro domin kuwa yaran nata sai dai ta jiyo hayaniyar su ษangaren Amaryar haka duk wani wanda zai zo wajen ta.
Tana neman me bata shawara a rayuwar ta, duk da ta san meya kamata tayi amma tana buฦatar me ษora ta akai, Kuka kam da yana magani da yayiwa Salma har hawayen nata ma da ace suna ฦafewa da sun ฦafe kuwa tsabar kuka ta rasa inda zata saka rayuwar ta, kwana biyu kenan amma duk ta fige ta lalace.
Washe gari zata amshi girki a hannun Jameela duk da dai amarya ce kuma tun daren farko basu kuma haษuwa ba, ita Salma ko ฦofar ษakin ta bata fita komai a ษaki take yi dan tana da kitchen da bayi a ciki.
Har lokacin bata da wata cikakkiyar lafiya, dan haka babu abinda tayi na gyaran ษaki ko kuma girki ko dai wani abin.
A haka Abdul yazo ya same ta, ya baje hanci ya shaฦi ฦamshin da yanzu Jameela ta sabar mishi amma maimakon haka sai ฦari da yaji domin kuwa har amai yau Salma sai da ta kwara shi.
ya ja tsaki cike da jin haushi, ya kalli yadda ta kwanta can ฦuryar gado, ba dan Jameela ta koro shi ba babu abinda zai kawo shi wajen wannan matar wallahi.
Ya ษan matsa kusa da ita yace; "Maman Husna", Salma da tun shigowar shi tana kallon shi ta amsa da ฦyar yace; "ina abinci na".
Ta ษan yi jim sannan tace; "nifa babu abinda na dafa", ya ja dogon tsaki sannan ya fice, wajen Jameela ya koma ya marairaice mata inda ita kuma ta cika mishi ciki da abinci tana ฦara jan shi da fira sai da ya raba dare sannan ya baro ษakin nata.
Salma ta kalle shi sannan ta kalli agogo ษaya saura, ta koma ta kwanta domin kuwa amai ne ya tada ita, Abdulkareem kuwa cikin alamun rashin gaskiya yace; "tunda baki dafa kin bani ba ai dole ne naje inda za'a bani".
Salma tana jin shi amma ta kanta take yi dan haka bata tsaya bashi amsa ba, haka ya nemi waje ya kwanta.
Wajen ฦarfe uku na dare jikin Salma ya ฦara tashi sosai, haka ta miฦe cikin jiri amma kan ta kai bayi aman yazo dan haka anan ta tsugunna ta fara kwara shi.
Abdulkareem cikin barci yaji kakarin amai, dan haka ya sauko ganin Salma na amai a wahalce ya ษaga hankalin shi sosai ya tallabota har ta gama sannan ya ษaga ta ya nufi bayi da ita.
Shi ya taimaka mata ta gyara jikin ta sannan ya kaita saman gadon ya kwantar da ita shi kuma yazo ya gyara wajen da tayi aman.
Koda aka idar da Sallar asuba da wuri Abdulkareem ya dawo daga masallacin yazo ya ษauke ta domin tafiya asibiti.
ฦakin Jameela ya ฦwanฦwasa ta buษe ฦofa jikinta sanye da hijab wanda ke nuni da sallah ta idar.
"Maman Husna ba ta da lafiya zamu je asibiti", ya faษa mata, Jameela tace; "Innalillahi! Meya same ta? Bari na shirya mu kaita tare".
Abdulkareem ya lumshe idanu yana jin daษin yadda take nuna tsantsar ฦaunar ta ga shi da matar shi da ฦดaฦดan shi duk da ฦasan zuciyar shi yana gargaษin shi akan Salma ma haka ta nuna da farko.
Jameela data fito daga ษakin tayi saurin tallabo Salma tana faษin; "Haskena bari na riฦe ta", Salma taji wani abu ya caki zuciyar ta.
Haka Jameela ta taimaka mata har suka isa motar Abdulkareem ษin ya saka ta a ciki suka fice daga gidan.
Wani asibitin kuษi suka je wanda yake kusa, sun sami ฦดan aikin dare basu tafi ba dan haka su suka yi mata duk abinda ya dace.
Da yake asibitin kuษi ne kafin gari yayi haske har sun gama mata komai an ษaura mata drip ta sami barci ma.
Ganin ฦarfe shida da rabi yasa Jameela tace; "Haskena bari naje gida ka san yara na suna da makaranta yau idan na shirya su suka tafi na sama musu abinda zasu ci sai na dawo".
Yace; "muje na kaiki nima sai nayi shirin zuwa wajen aiki, tunda ta sami barci", haka suka miฦe suka fice daga ษakin.
Salma da duk taji abinda ke faruwa ta girgiza kai hawaye yana biyowa ta idanun ta, ga zafin ciwo ga kuma zafin kishi da kuma karayar zuciya data samu daga ฦawar tata kuma aminiyar ta.
Tayi tunanin zasu dawo tare amma koda ta farka Jameela ta samu a zaune, Jameelar tana ganin ta farka tace; "sannu, mun dawo kina barci shine Haskena yaga zai yi latti yace bari kawai ya tafi".
Salma bata ce komai ba banda kauda kai da tayi kawai, Jameela ta taษe baki tace; "da kin haฦura kin bini a sannu da nima zan sassauta miki sai dai ki sani duk iya ษaga hankalin ki da shige da ficen ki babu wanda zai yi tasiri a kaina dan haka ki kwantar da hankalin ki kawai, Abdulkareem yanzu sai Jameela haka Jameela sai Abdulkareem", tana gama faษar haka ta fice daga ษakin.
Salma taja dogon tsaki tana me dangwarar da kofin data ษauko domin haษa abin kari, lallai dama bahaushe yace mutum mugun ice.
Tana cikin wannan tunanin taga an turo ฦofa an shigo, ta ษaga kai tana kallon wacce ta shigo,