Showing 12001 words to 15000 words out of 107295 words

Chapter 5 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1313

yayi mishi kwatancen gidan su Salma domin yaje ya nemar mishi auran ta. Shi ma mahaifin dan zumuɗi bai bari lokacin tashi yayi ba ya fito, yana zuwa gidan yasa akayi mishi Sallama da Haruna sai aka ce baya nan, yace anjima zai dawo.

Bai koma gida ba sai da ya haɗu da Haruna, dukkan su sun yabawa juna ta ko'ina, musamman Haruna, dan irin mijin da yake son Salma ta samu kenan.

Haruna bai ɓoye mishi komai ba akan ba shi ya haife Salma ba, har abinda yasa ta zo gurin shi, da matakin karutun ta, duk ya fada mishi, amma ya tabbatar mishi mahaifin ta bashi da matsala ko kaɗan, ya bashi izini ya fara zuwa idan suka amincewa juna sai a sanar da mahaifin nata.


Har cikin gidan Abdul ke shiga suyi hira, ranar da Salma ta fara ganin shi zuciyarta ta kamo da son shi,nan da nan muguwar soyayya ta shiga tsanin su,kullum kwanan duniya sai sun haɗu,duk ranar da basu ga juna ba cikin su ba wanda zai iya barci.

A SS two Abdul ya biya mata kuɗi ta zana jarabawar kammala candy, daman ya biya mata tayi jamb, dan shi kanshi yana son karatu, gashi Salma karutu shi ne abincin ranta, a lokacin ta haddace al-qur'ani gaba ɗaya, ita ta zo na ɗaya a musabaƙa, kyaututtuka kuwa tasha kuɗi sama da biliyan dan ko mahaifin Abdul rabin miliyan ya bata. Mahaifin ta Ɗahiru kuwa ranar sai da yayi kuka dan murna, ga labarin Salma ta samu miji, shi da kanshi yace a sa sati biyu, tabar makarantar haka tayi ta cika mishi burin shi Abdul ya nuna yana son idan sunyi aure yana son ta cigaba ta karatun ta, ba wanda ya hanashi.

Anan aka shiga shagalin biki, ranar ɗaurin aure aka yi walima da wa'azi, tun ƙarfe biyar aka kai ta gidan mijin ta, daman ita ba ƙawaye gareta ba.


Zaman so da ƙauna suke yi, Salma tana mutunta shi da girmama shi fiye da kowa a rayuwarta, haka shi ma, Salma ta samu gurbin karatu a KASU (Kaduna state university). Shekarata ɗaya da fara zuwa ta samu cikin Husna, Abdul yayi murna sosai dan shi mai son yara ne.

Bayan Salma ta haifi Husna ta cigaba da karatun ta, Husna na da shekara biyu ta haifi Mussadiq, yana cika shekara ɗaya ta kammala karatun ta inda tayi short service.

Taso yin aiki ya hana ta ta kuwa hanu domin bata musu da shi akan duk abinda ya ce mata, har lokacin suna zaman su cike da kulawa da kyautatawa, ganin zaman na mata yawa tunda ba makaranta, yara idan su ka fita makaranta tun bakwai basu dawowa sai shidda na yamma, yasa ta fara karatun littafin hausa, wannan shi ne dalilin sauyawar Salma lokaci daya, ganin mazan novel yanda suke yin dogon zango yayin mu'amalansu ta auratayya da matan su. A tunanin ta cutan ta kawai yake domin duk wani abu da zai iya shigan tsakanin su bai wuce awa d'aya a yayin da take ji a novel miji yakan kai sama da awanni 4-5 suna mu'amala da matan shi



~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 Of Golden Pen Writers Association Team Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~✍



_~We Love U All~_❤



🙆🏻🤷🏻‍♀ *_MENENE RIBA TA ❓_* 🤷🏻‍♀🙆🏻


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀



*~ ✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽~*

*~We are bearier's of so golden pen~*🖊

*~We write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/




*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say:*

*"The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path [un-trodden] in which You like money to be spent without spending in it for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but do so that it might be said [of you]: 'He is open-handed.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire."*

*[Muslim (also by at-Tirmidhi and an-Nasa'i)]*



*عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ، قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: إِنَّ أَوَّلَ النَّاسِ يُقْضَى يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَلَيْهِ رَجُلٌ اسْتُشْهِدَ، فَأُتِيَ بِهِ فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ قَاتَلْتُ فِيكَ حَتَّى اسْتُشْهِدْتُ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ قَاتَلْتَ لِأَنْ يُقَالَ: جَرِيءٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ تَعَلَّمَ الْعِلْمَ وَعَلَّمَهُ وَقَرَأَ الْقُرْآنَ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: تَعَلَّمْتُ الْعِلْمَ وَعَلَّمْتُهُ، وَقَرَأْتُ فِيكَ الْقُرْآنَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ تَعَلَّمْتَ الْعِلْمَ لِيُقَالَ: عَالِمٌ، وَقَرَأْتَ الْقُرْآنَ لِيُقَالَ: هُوَ قَارِئٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ، فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ حَتَّى أُلْقِيَ فِي النَّارِ. وَرَجُلٌ وَسَّعَ اللَّهُ عَلَيْهِ، وَأَعْطَاهُ مِنْ أَصْنَافِ الْمَالِ كُلِّهِ، فَأُتِيَ بِهِ، فَعَرَّفَهُ نِعَمَهُ فَعَرَفَهَا، قَالَ: فَمَا عَمِلْتَ فِيهَا؟ قَالَ: مَا تَرَكْتُ مِنْ سَبِيلٍ تُحِبُّ أَنْ يُنْفَقَ فِيهَا إِلَّا أَنْفَقْتُ فِيهَا لَكَ، قَالَ: كَذَبْتَ، وَلَكِنَّكَ فَعَلْتَ لِيُقَالَ: هُوَ جَوَادٌ، فَقَدْ قِيلَ، ثُمَّ أُمِرَ بِهِ فَسُحِبَ عَلَى وَجْهِهِ، ثُمَّ أُلْقِيَ فِي النَّارِ. رواه مسلم (وكذلك الترمذي والنسائي)*

~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_


~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da sauke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowoce siga ba._


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



♣ _Scene One_

*Page 6*



Har Sahabat ta gama dafa abinci Ummi na zaune a guri ɗaya tana abu ɗaya, takaici ya kama Saha, ko magana bata mata ba, ta zubawa Surayya da Na'eef itama ta zuba.


"Sahabat! ki zubo min abincin ki kawo min nan, na fara jin yunwa".

Saha, wacce lokacin har ta fara cin abincin ta ja tsaki, "Oh Allah! wai ni Ummi in dai ina gidan nan bata taɓa bari na na huta ba? Abin na ta yayi yawa, komai Sahabat! Bata iya taɓuka komai sai zaman danna waya!".

"Saha kina ji na?".

"Gani nan", ta tashi ta fita cike da jin haushi, abincin ta zubo mata.

"Yawwa Saha Allah ya miki albarka".

"Amin".


Kamar yadda ta saba bayan ta gama abinda zata yi, tayiwa Ummi sallama ta kulle ɗakin, kasancewar ita kaɗai ke kwana a ɗakin.

Wayarta ta fito da shi ta kunna, tana kunnawa ta buɗe data ta shiga WhatsApp, saƙon Zaiyad ta fara dubawa.


_"Kin dawo gida lafiya sweet?"_

_"Kewar ta dame ni, pls mu ƙara haɗuwa gobe kinji."_

Murmushi tayi tana ƙoƙarin yin reply wani saƙon ya shigo.

_"Yau baki zo da wuri ba, ina ta jira har hankali na ya fara tashi"_

_"Srry sweet ban gama aiki da wuri ba ne, amma yanzun ga ni, any latest?"_

_"Sonki ya fara min yawa, tamkar na zauce, mu haɗu gobe, idan ban ganki ba zuciyata ciwo zata min"_

_"Ini sonka fiye da komai a duniya Zaiyad, ka turo gidan mu ayi magana."_

_"Na turo! waiyo daɗi, kash! yanzun matsalar Dady baya gari, amma ki ban nan da wata ɗaya, lokacin ya dawo."_

_"To Allah ya dawo da shi lafiya."_

_"Kina so na kamar yadda nake son ki kuwa.?"_

_"I love u! how many times kake son na faɗa u are my life."_

_"Den prove it! ke da ko kiss baki taɓa min ba"_


_"Idan kana so a shirye nake da aikata duk abinda kake so, wanda zai saka cikin farin ciki."_

_"Komai?"_

_"Uhm"_

_"To yanzun zamu haɗu goben ne?"_


_"Ba lallai ba, dan ba makaranta gobe, Ummi ba zata barni na fita ba, amma zanyi try insha allahu"._

_"Yawwa my love kiyi ƙoƙari tabarki dan ina matsanaicin son ganin ki, tamkar nayi tsuntsuwa na zo."_

_"Nima ina son ganin ka, ka san bana gajiya da kallon ka."_

_"Yanzun dai turomin photon ki masu kyau."_

_"Okkk my love."_


Tana fita ta buɗe saƙon Hunayda.

_"ke fah ba mutunci gareki ba, mutum yai miki magani ki wani share, kuma kina gani sannan kin san dan ke nake tsayawa har wannan lokacin ban sauka ba."_

_"Sorry! Sahiba kin san idan muna chat da Zaiyad ne bana raba hankali na biyu."_

_"Kina da matsala Saha, ki rage wannan son fa, irin shi ne ake samun matsala."_

_"Ba wata matsala, kuma da kike cewa haka dan baki san irin son da yake min ba ne, ke kamar baki san so ba, ko da yake baki taɓa haɗuwa da wanda ya iya soyayya ba ne shi yasa."_

_"Hm! kinji ki, ba haka ba ne, yadda kowa yake ɗaukar abu ne, Zaiyad ɗin shi autan maza ne ko me? koma duk iyawar shi wani ya fi shi, ke ni dai yanzun turomin littafai masu daɗi."_


_"Naki wasa ne, bari wata rana zan haɗa ku dai ki ganshi, kina ganin shi zaki tabbatar," littafin Ni da shi da ƙauna ce ta tura mata._

_"Zaki iya karantawa kuwa?"_

_"Me zai hana.?"_

_"Littafan sun haɗu ne a ba dai daɗi ba."_

_"Shine bazan iya ba, sauran dana iya karantawa fa."_

_"Su daban ne, amma ki karanta, bari naje gurin love idan kin tafi to saida safe, raguwa kawai baza ki iya kai ɗaya kina chat ba."_


Photo nan ta tura mishi," Ga su my love."

Saida ya gama ƙura ma hotunan ido yana jin wani abu a ranshi mai wuyar misaltuwa, lasar laɓen shi yayi, sanan ya ce;

_"Wow! Sweet, kyawunki yana tsorata ni, Allah yayi halitta gaskiya, ke ko cikin su mata kinyi fice, kinga dirin ki kuwa! duk namijin da ya same ki yayi sa'a, za'ai dai mu kira shi ɗan baiyawa."_

_"Mijin na kuma, ai kai ne mijin nawa."_

_"Na gode sweet!"_

_"Na me?"_

_"Da kika ƙara tabbatar min da ni kike son na zama mijinki, ɗazun ban yarda da kika ce na turo ba, amma yanzun na yarda kuma na amince tabbas kina so na, kamar yadda nake son ki, ke ce muradi na."_


_"Sweet zaka fasa min kai da kalaman ka, wani irin so zan ma wanda bazan so ka zama uban ƴaƴanah ba..."_


Sai gurin uku da wani abu sannan ya barta ta kwanta.



*Wacece Sahabat??*

Zuwaira shine ainihin sunan Ummi, ƴar asalin jihar Kaduna ce, unguwar Rafin Gusa, su biyu ne gurin iyayen ta, ita ce babba sai ƙanin ta Zakari, kasancewar su biyu ne gurin iyayen su yasa tarbiyyar su da ilimin su bai wahalar da iyayen ba, dan suna da rufin asiri dai-dai bakin gwargwado, mahaifin ta ƙaramin ma'akaci ne na gwamnati, mahaifiyarta koyarwa take yi faramari.


Zuwaira(Ummi)tayi karatu har gaba da sakandiri, ita da ƙaninta zakari.

Isma'il Ridwan sunan mahaifin Sahabat, shi ma ɗan Kaduna ne, mahaifan shi duk sun rasu shi kaɗai yake gurin babban yayan mahaifin shi yake, wanda suke zaune a Abakwa, mutum ne kamili wanda ya san darajar mutane, kuma ya iya zama da su, rayuwa mai sauƙi yake yi, yana karatu kuma yana gyaran motor, domin rufawa kan shi asiri da wanda yake gurin shi.


Bayan ya kammala karatun shi ya samu aikin gomnati, shekarar shi biyu da samun aiki ya haɗu da Zuwaira, taje bikin wani abokin shi, nan da nan suka amince wa juna, soyayya da shaƙuwa ta shiga tsakanin su.


Ya turo magabatanshi aka yi maganar aure, lokaci nayi aka ɗaura auran Zuwaira da Isma'il.


A Kurmin Mashi suka zauna, unguwar su Hunayda tazara kaɗan ne a tsanin gidajen su.


Zaman lafiya da soyayya Zuwaira da Isma'il suke yi, suna nuna wa juna soyayya da kulawa, bayan shekara ɗaya da rabi da yin auran su aka haifi Sahabat, cikin so da ƙauna Sahabat ta taso gurin iyayenta.Sahabat na da shekara uku da rabi aka haifi Suraiyya, soyayya da shaƙuwa irin da wa da ƙani ke tsanin Sahabat da Suraiyya.

Bayan haihuwar Suraiyyah da shekara uku da rabi aka haifi Na'eef.

Yara sun fara tasowa cikin tarbiya ta kulawar iyayen su, rana ɗaya kwasam Isma'il yayi haɗarin motor Allah ya amshi abinshi, lokacin Na'eef na da shekara shidda, lokacin ita kuma Sahabat na da shekara goma sha huɗu tana aji uku na secondry.

Sun yi kuka iya iyawar su, Saha da Suraiyya su na da wayo, Na'eef ne bashi da waiyo a lokacin.

Rayuwa ta sauya musu, gonmati na biyan su kuɗi duk wata, shi yasa basu samun wata matsala ɓangaran amfanin kuɗi, sannan Zakari yana taimaka musu, haka iyayen ta, basu da wani matsala ta bangaran kuɗi sai dai kewa.

Tun daga wannan lokacin Ummi ta fara rubutu na littafan hausa ta online, bata da kunyar rubuta batsa a littafin ta ko kaɗan, bata tunanin abinda hakan zai haifar mata a gaba, ɓaro-ɓaro take baiyana komai na rayuwar ma'aurata.

Tunda ta fara rubutun nan rayuwarta ta sauya gaba ɗaya, bata kula da komai sai wannan rubutun, gaba ɗaya hankalin ta da natsuwarta duk ta ba rubutu.

Ummi tana mugun son Saha a rayuwarta, shi yasa duk yadda rubutu ya shagalartar da ita bata manta da kula da kiyayewa akan Saha ba, bata barin ta da wata ƙawa sai Hunayda, bata barin ta fita idan ba makaranta ba, sai gidan su Hunayda, shi ma ba kasafai ba,Tsoron kar ruɗin Zamani yaja Saha yasa Ummi ta hana ta riƙe waya.


Sahabat; kyakyyawa ce dai-dai iya kyau tana da shi, tana da idanu wanda shi ya ƙara mata kyau, ita ba baƙa ita ba fara ba, amma tafi Hunayda haske kaɗan, da tsawo shi ma idan ba a jere ka gansu ba baza ce ta fi ta ba, tana da ƴar qibarta dai-dai ba can ba, dan ta wuce a kira ta siririya, kuma bata kai a kira ta mai qiba ba, tana da zati dai-dai bakin gwargwado.

Sahabat Yarinya ce mai son ado da shigar yayi, tana da tarbiyya da girmama mutane, amma tana da tsiwa da rashin haƙuri da juriya, wannan halin ne yasa ba zaka ce tana da tarbiyya ba, ga surutu kuma bata son raini, tana da son girma, ban-bancin su da Hunayda kenan, dan ita Hunayda tana da tsoro kuma tana da hakuri da kau da kai.

Wannan halin yasa Saha idan ta ya buɗe na rashin tsoro, takan aikata duk abinda taji ranta yana son aikatawa.Ƴar soyayya ce, bi ma'ana tana son soyayya tun kafin ta fara soyayyah, film ɗin soyayyah yake birgeta, raguwar zuciya gareta, ma'ana mai saurin yadda da amincewa akan duk wani shafa larabi shuni, shi yasa Zaiyad yai saurin kama ta da maganganun shi, ko na ce shafa larabi.

Wata rana Ummi ta aike ta unguwar su, akan hanyarta na dawowa ta haɗu da Zaiyad a mator shi, ya ɗauko ta, tun kafin Zaiyad ya ce yana son ta,ya shiga ranta, dan a tsarin Saha tana son namiji ɗan gaye wanda ya iya wanka kuma mai kyau, shi kuwa zaiyad duk ya haɗa su.

Tun kafin ya sauke ta ta sake mishi fuska, ko da ya tambaye ta zai samu damar zuwa gidan su idan dare yayi, ta ce mishi ba'a barin ta fita, ta gaya mishi inda zasu haɗu gobe, zata fito idan zata makaranta sai su haɗu.

Bayan ta amince mishi, suka fara zuba soyayya, Saha na son Zaiyad sosai a rayuwarta, shi ne first love ɗin ta, daga nan ya sai mata waya a ɓoye, suna fita yawo irin wanda masoya ke yi, duk wanan abun Ummi bata sani ba.

Tun asuli Saha tana da sha'awa amma tana haƙuri da juriya, wayar da Zaiyad ya siyan mata ne ta fara WhatsApp, a inda ta fara karanta littafan hausa, sai abun ya tsanan ta, akan littafin *Ni da shi*, wanda mahaifiyar ta, Ummi ta rubuta, wanda yanzun takan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login