Showing 48001 words to 51000 words out of 107295 words
Chapter 17 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt
saɓanin da da ko wanene ya kira shi a gabanta yake amsawa, saboda tsabar soyayyar shi gareta da kuma yarda da junan da sukayi ma kansu.
Abun sai kuma ya dawo yana ɗan bata tsoro, hankalin ta ya fara tashi, me Abdul ke shiryawa, masalan da taga fafa ya fara tada ginin shi, na filin dake jikin gidan, sai ya fasa bangon tsakar gidan ya haɗe su, duk abunda yake yi, iyakar shi da ita kallo sai kuma amsa mata gaisuwa idan tayi mashi. Ta yaran shi kawai yake yi.
So take ta gyara komai, tsoron ta guda ace Abdul ɗin wani salon ya ɓullo mata dashi, bata iya jure wannan halin da suke ciki. Saboda haka ne ta miƙa kokenta a group ɗin masu, tare da naiman shawara.
Nan fa aka shiga bata shawarwari, Jameela ce mai zaƙal ɗin cewa ta cigaba da share shi, da kanshi zai nemeta, yayin da wasu suke ce mata kada tayi haka, ta nemi mijin nata su sasanta.
Dayake ta ɗauki dukkan yardar ta taba Jameelar, sai take ganin kaman Jameelar ce kaɗai mai ƙaunar ta.
Nema tayi da Jameelar tazo gidan ta su tattauna, Amman sai Jameelar take faɗa mata wai bata lafiya, duk da haka bata haƙura ba, sai tace ma Jameelar tayi mata kwatance zata je gidan nasu, daganan sai su gaisa da mama ta kuma duba jikin Jameelar.
Ba musu ko shayin komai Jameelar tayi mata kwatance.
Koda taje, sun jima suna fira, tare da gaisawa da maman tata.
Suna taren ne kiran wayar Abdul ya shigo wayar Jameelar. Saurin ɗauka tayi, tana mai ficewa daga ɗakin. Saida ta kammala wayar ne ta koma ɗakin.
Da murmushi Salmar ke bin Jameelar.
"Ya dai? Kodai Ogan ne ake ɓoye man?" ta faɗa da murmushi.
Itama Jameelar ɗan yaƙe tayi tana mai cewa "Laa kuji mata da sharri, meye na ɓoyo kuma? Sha kuruminki, har gida zan kai maki shi ai" tafawa sukayi, suna masu ci gaba da tattaunawar su.
Duk yanda Jameelar zatayi wajen ganin Salmar ta ƙara dagula lissafinta tsakanin ta da Abdul tayi. Ta kuwa ci nasara. Domin Salma dai sai abunda yaci gaba.
Yanzu maganganu take yaɓa ma Abdul, tana biye ma dokin zuciyar ta ne, tare da zuga da shawarwarin ƴan social media irin su Jameelar.
Shi dai Abdul wani lokaci ya kan ce "Allah ya kyauta" sannan yabar gidan. Ƙarin aure a gareshi dole ne, koda kuwa Jameelar bata kawo mashi kanta ba.
Duk da Salma take ganin ƙarin buɗi tattare da Abdul ɗin, domin yanzu ya kai wani matsayi a ma'aikatar tasu, hakan baisa ta kwantar da kai ga Abdul ɗin ba.
Gani take kullum ya gaza, har ƙarar shi ta kai gidan su, wai ya dena mata komai, kuma ko a shimfiɗa ya dena kula ta,bata ko ji kunyar faɗin hakan ba, tunda tana amfani ne da cewar su Jameelar, gani take kaman shawarwarin nasu sune mafitar ta.
Mahaifiyar ta da kanta ta ɗauko mayafi zuwa gidan Salmar, saidai saɓanin abunda Salmar ta faɗa ne ta tagani. Tunda da kanta ta shiga kitchen da store ɗin gidan.
Ai bata san sadda ta kaima Salmar duka ba, idan ba rashin godiyar Allah ba, me ta nema ta rasa? Akwatinta cike suke da kaya sababbin da ko ɗinka su batayi ba, haka store ɗin nata, cike yake da kayan masarufi daidai da magi ƙwaya ɗaya ba zata siya ba a waje.
Ai sai ta sanya waya ta kira Abdul ɗin, koda yazo bai shaida ma Mahaifiyar tata abunda yake tsakani da, kawai dai yace a ƙara yi mata faɗa, tana biye ma ƙawaye ne a waje.
Nan kuwa uwar tata ta rufa a kanta, faɗa, zagi da wulaƙanci iri iri babu wanda Salma bata gani ba. Ai sai ta ƙullaci Abdul, sai abun ya ƙara tsamari, shi ba dakai ƙara ba, shi da amsar hukunci.
Wannan duk bai dame shi ba, kawai ya ɗauki hakan a matsayin wata Jarabawa ce a rayuwa data same shi, kuma yana ƙoƙarin ganin yaci jarabawar. Babu wanda ya taɓa faɗa ma halin da yake ciki a waje, dama hasalima shi ba mai abokai bane da yawa, kasancewr irin aikin nashi, da har dare yana kaiwa wani lokaci.
Koda yaje da zance ƙarin aure gidan nasu, babu wanda yayi yunƙurin hana shi, duba da yanayin shi, ba sai ya fito ya faɗa ba, ko ramar dake jikin shi kaɗan ya isa ya shaida ma mutum halin da yake ciki. Addu'a iyayen nashi suka bishi da ita, tare da fatan nasara, domin ya zuwa yanzu dai Abdul ɗin ya fara zama wani abu, riƙe mata biyu ba zai yi mashi wahala ba.
Ranar da komai ya ƙara rincaɓewa ita ce; ranar da Abdul ya kawo ma su Husna chocolate da biscuit da yawa yake shaida masu inji Auntyn su, watau amaryar da zaiyi kwana kusa.
Nan fa Salma ta ruɗe, kuka take tayi, tare da aibace aibace. Kalmar daya faɗa mata cewa "Abunda ka raina shi wani ke so, kuma inda wani yaƙi da yini, nan wani keso da kwana"
Tashin hankalin da Salmar ta shiga bai ƙilguwa, ko bayan daya fice, Jameelar ta kira tana kuka, saidai Jameelar tace ta kwantar da hankalinta, ƙila barazana ce yake yi mata domin ta gyara, saidai ko alama, ta tada mashi hankali, har sai yace ya zanye maganar auren.
Haka akayi, kwana biyu ba kwanciyar hankali a gidan. Husna da Musaddiq ma ya kwashe su, ya kaisu cen gidan su.
Abaya kawai ta zara tayi gidan su, wai tayi yaji, aikuwa dawa Allah ya haɗa maman tata ba da ita ba. Ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Sannan tace tayi gaugawar komawa ɗakin ta ma, tun kafin mahaifin nata ya dawo ya same ta. Lallai ta yarda Salmar bata da hankali, ta yarda duk ta watsar da tarbiyyr da sukayi mata a gida. Dama a haka Abdul ɗin ke zama da ita, Amman bai taɓa kai ƙarar ta ba? Lallai Abdul ya cika suruki, wanda ko wacce uwa zata so ace ya auri ɗiyar ta.
Saboda haka ne ta sanya waya tana mai kiran shi, haƙuri ta dinga bashi harma yaji kunya, yace ba komai dan Allah suma suyi haƙuri in ransu ya ɓaci.
Ba ariziƙi ta koma gidan, tare da gargaɗin cewa daya dawo ta tabbatar ta bashi haƙuri, ba'a aure ita aka aure ta?
Sai take ganin kowa ya juya mata baya ne, ita ba'a kula da lalurar ta, ba'a kula da damuwar ta, saboda tana mace komai sai ace ita ce ƙasa? Ita za'a taka? Wallahi kuwa indai haka ne, Abdul bai zaɓa ma kanshi zaman lafiya ba.
Hidimar biki ta kankama. An kammala ginin gudan sashen amaryar, inda har yanzu bata kwantar da hankalinta ba, balle ma tasan wacece amaryar. Kuma dama ko a shimfiɗa ta dena neman shi, shima idan yaje haka take kulle ido ta gaigaya mashi maganganu marasa daɗi, Shiyasa ma yanzu ya dena neman ta. Sai ya sanya mata idanu, aure ne dai babu fashi, saidai duk abunda take jin zatayi tayi.
****************
"Kiyi haƙuri Hunayda, nima ba'a son raina ba zan tafi in barki, saidai hakan ya zame man wajibi je, karatu zan tafi yi ba wani abu ba, kuma zamu dinga yin waya, sannan insha Allahu zan dawo in iske ki kaman yanda na barki, zuwa lokacin shekarunki sun rufa ma yanda Abban ki ya ɗibar mana, kinga zuwa lokacin zamu iya auren mu cikin kwanciyar hankali, na samu aiki, zan iya riƙe ki da duk wasu buƙatun ki" Suhayl ɗin ya faɗa cikin shigar lallashi.
Share hawayen fuskar ta tayi, sai take ji kaman idan ya tafi shikenan ba zai dawo ba, ta saba dashi, ta fara koya ma kanta sonshi, kwatsam rana guda yazo mata da maganar zai tafi wata ƙasa ƙara karatu?
"ki dena kuka, dariya ya kamata kiyi My Nayda, farin ciki shi ya kamace mu, shekara biyu kawai zanyi, insha Allahu da na kammala zan kawo takardun, ƙanen Babana yayi mani alƙawarin aiki mai tsoka, wanda insha Allahu har wani ma sai mun taimaka"
Gyaɗa kanta ta shiga yi cikin gamsuwa, a hankali ta shiga kwararo mashi addu'a, har yanzu fuskar tata babu walwala sam a tattare da ita. Saidai bata da yanda Zatayi, kaman yanda ya faɗa ɗinne. Hakan ba ƙaramin ci gabansu bane. Saidai idan ya tafi dawa zata dinga fira? Wa zai dinga ƙara mata karatu?.
Kaman yasan tunanin da take yi, yayi saurin cewa "Saidai ina roƙon wata alfarma guda ɗaya My Nayda, dan Allah ki zam mai kula, ki riƙe man alƙawari na, banda biye ma ƙawayen banza, banda yada karatun ki, wanda kin sani dashi ne zaki bama yaran da zamu haifa tarbiyya, ki man alƙawari My Nayda zan dawo in iske ki, natsattsa, kamammiya kaman yanda na tafi na barki". Ya ƙarashe shima yana mai karya kai, zuciyar shi tayi rauni, masalan da yaga wasu siraran hawaye na kuma biyo fuskar tata, daga cikin idanun nata.
Ji yake kaman ya kamata ya rungume, kaman ya share mata hawayen, kaman ya ɗora bakin shi saman goshin nata. Saidai inaaa, ba zai iya ba, yasan hakan haramun ne a gareshi, yasan hakan ba da cewa bane, koda ba'a haramta ba, baya jin zai iya, tarbiyyarshi bata bashi haka ba, balle yasan wutar Allah mai zafi ce, wadda ɗan adam ba zai iya daure mata ba.
Cikin tabbatar da alƙawarin nata take gyaɗa mashi kai. Ba zata taɓa guje nashi ba, kaman yanda itama bata fatan ya guje matan.
"Kaima kayi man alƙawarin ba za ka kula kowa ba acen, ba zaka barni ba, ba zaka yi man kishiya ba, ba zaka taɓa haɗa son wata da nawa ba, idan kayi man hakan insha Allahu, nayi alƙawarin kamewa da tsare maka komai nawa, har sai ka dawo munyi aure" ta samu kanta da faɗa
Shima cikin son maida hawayen daya taho mashi yake gyaɗa mata kai. HUNAYDA daban ce, komai nata a nutse take yinshi, kalaman ta masu taushi, yana mai jinjina ma Amminta, irin tarbiyyr data bata, tare da ƙoƙarin kiyaye yaran nata daga faɗawa halaka da ruɗin zamani.
Cikin wani irin yanayi sukayi Sallama, ita dai Hunayda kuka take marar sauti, yayin da Suhayl ke tafiya yana waiwayen ta. Ba dan tafiyar tazo mashi a bazata ba, babu abunda zai hana shi tsayawa tsawon yini yana lallashin ta.
A haka masoyan biyu suka rabu suna masu marmarin juna, sai ɗaga mata hannu ya ke, yayin da ita kuma ko kallon shi ta gaza yi. Har ya ɓace daga cikin layin nasu. Sannan ta tashi ta faɗa cikin gidan nasu tana mai rusa kuka.
Ita kanta Ammin tayi mamaki da Hunaydan ke faɗa mata yanda sukayi da Suhayl. Ashe ɗiyar tata soyayya take har haka? Har tayi zurfin da zata dinga rusa kuka irin haka, saboda tafiyar saurayi. Da Addu'a da shawarwari tabi Hunaydan, har saida taga ta ɗan dayaye, sannan ta umurceta akan ta shiga ɗaki ta kwanta ta huta.
Jiki a mace ta shige ɗakin, ji take kaman ta rabu da Suhayl kenan rabuwa ta har abada, gani take kaman Suhayl ɗin zaifi Ƙarfinta idan ya dawo. Da haka har bacci kaɗan ya sace ta, tana mai tunanin Suhayl da irin yanda rayuwar ta zata zama, idan akace ba Suhayl ɗin.
***********
Sanye take cikin kayan islamiyya. Hijabin ta har ƙasa, fuskar tata Sanye take da liƙaf baƙi. Cikin sauri take takawa har zuwa bakin titin inda zata tari Napep ɗin.
Tun bayan data samu ta gilla ma Ummin tata ƙaryar cewa an saka ta cikin masu musabaƙar karatun Alƙur'ani ta bana, dan haka cen zasu yini suna bita, abinci ma saidai suci ce, sai Ummin tata take ce mata, ta tafi idan su Hajna sun taso daga Lesson zata kai mata abincin. Saurin tarar Ummin tayi da cewa "A'a Ummi, ta dawo daga Lesson ta gaji, kada a takura mata, ki bani kuɗi kawai na siya cen inci. Insha Allahu ƙarfe shidda a gida Zatayi mana, alabasshi idan na dawo sai in ci mai yawa in ƙoshi Ummi"
Ummin bata kawo tunanin komai ba, ta ɗauko kuɗi a jikkarta, tana mai miƙa ma Sahar cikin jin daɗi, irin yanda take maida hankali kan karatu, duk da take mai nukura, Amman sai gashi yanzu harda ita wai cikin gasa, kai Allah na gode maka.
Da fatan alkhairi tabi Sahar, tana mai shige wa kitchen, domin yau kenan saidai ita Zatayi girki dole, Saha bata nan, haka ma Hajna, sai Na'eef kawai wanda ya rage a cikin gidan.
*"Malali Lowcost"* Sahar ta faɗa a hankali, tana mai ɗan waige waige, kada ace wani ya ganta.
Bata jira cewar mai a daidaita ɗin ba ta faɗa ciki kawai. Da kuɗin abincin da Ummi ta bata tayi amfani wajen biyan mai adaidaitan. Bayan ya sauke ta gaban wani madaidaicin gida.
Wayar ta ta zaro daga cikin riga, tana mai danna kiran sahibin nata.
Dama jira yake yi, saboda haka a kira na biyu ya ɗaga cikin wata irin annashuwa yake faɗin "Ya dai my Habat? Har kin iso kenan?"
"Eah na iso, gani ƙofar gidan" ta faɗa itama, tana mai ɗan waige waige.
Ƙarar buɗe ƙofa taji cikin seconds, kaman dama yana bakin ƙofar ne.
Da kallo yake binta sama da ƙasa, cikin wata irin dariya ta rainin wayau.
"Wow! Kunga malama ta fa, gashi tazo ɗaukar karatu" ya faɗa cike da rainin wayau, lokaci guda yana tafa hannu.
Mai makon Sahar taji ba daɗi, sai itama tayi dariyar, tana mai yaye hijabin dake sanar rigar tata.
Ƴar riga ce amless kalar ja, tsawon ta iya guiwa, duk tabi ilahirin surar jikinta ta shafe, komai na jikin ya bayyana, hatta da hannun brezier ɗinta da take kalar baƙa.
*"Woooh ko kefa My Habat, yanzu kinfi kyau, wow! Wannan shiga haka duk ni kaɗai akayi mawa, in more inta kallo?"*
Ya faɗa yana mai saƙalo hannun nata cikin nashi, zuwa cikin gidan, bayan ya maida gidan ya kulle.
Sai taji wani irin daɗi, Zaiyad ya cika namiji, ganin shi cikin farin ciki ba ƙaramin nishaɗantar da ita yayi ba.
Bisa kujera ya zaunar da ita, yana mai amsar hijab da ƴar jikkar tata ya wurga su bisa sofar.
Bai ƙyaleta hakanan ba, faɗa wa yayi bisa jikin nata, Amman bai sakar mata nauyin shi ba. Numfashin sune ya gauraya. Saurin ɗauke kanta gefe tayi, tana son Zaiyad ɗin, sai take jin kanta kaman ma gata cen ta shiga gidan nashi a matsayin matar shi.
Wasu abubuwa ya fara mata, yana mai faɗin wasu kalamai na ƙauna a gareta., tana mai tashi tsaye, ta shiga gyara wuyan rigar tata.
"Toilet zan shiga My Love" Ɗan maida numfashi yake sama sama.
"Muje in raka ki kenan.?" Ya faɗa cikin wani irin salo, yana yi yana kashe ido guda.
Ɗan girgiza kanta tayi cikin kunya, tun da ta sako ƙafar ta gidan ta gaza yi mashi cikakken kallo. Duk da ba yau ta fara ganin namiji a tuɓe ba riga ba, amman kasancewr ita Kunyar soyayya daban take.
Wando ne short sosai iya cinya, jikin nashi babu riga, sai yalolon gashin da yake kwance luf, jikin ilahirin kyakkyawar farar fatar jikin nashi.
Zaiyad ɗin namiji ne cikakke, dayake yana yin jim sosai, sai ya kasance jikin nashi a murɗe yake, ga 6packs daya ajiye a bisa cikin nashi.
Juyawa tayi tana mai nufar bed room ɗin nashi. Ba yau ta fara shiga ba, Amman bata san dalili ba, wata irin faɗuwr gaba ce ta ziyarce ta.
Ita kanta tasan bata kyauta ba, tasan hakan ba daidai bane, saidai ta biye ma huɗubar shaiɗan ne, da yake raɗa mata cewa ai ba wani abu bane a wajen budurwa dan tazo wajen saurayi, haka taji Ummin ta ta faɗa cikin wani littafinta, har ta ƙara da cewa hakan shine wayewa da kuma nuna tsantsar ƙauna ga masoya, ya kasance koda yaushe suna jin ɗumin juna.
Ko bayan data fito daga toilet ɗin, bata koma falo ba, ta samu gefen gadon nashi ta zauna, tana mai fiddo wayar ta daga cikin rigar ta, wadda ta mayar tun kammala wayar da Zaiyad, dayake hakan ya zame mata al'ada.
Ta kusan minti talatin bata ji ɗuriyar shi ba. Sai cen ya shigo ɗauke da tray babba, a saman shi plate guda ɗaya na dafaffiyar indomie, wadda taji kayan haɗi da kwai, sai ƙamshi take yi.
Gudan plate ɗin kuma kayan marmari ne ya yayyanka. Sai cokulla da suke ajiye bisa babban tray ɗin, tare da Jog mai haɗe da kofuna, cikin shi lafiyayyen Banana and Milk shake ne.
"Here is your delicious yummy my Habat"
Ya faɗa a hankali, yana mai dire tray ɗin gefen gadon kusa da ita.
Sauke wayar tayi a hankali bisa cinyar ta, tana mai haske shi da ɗan murmushi. Sai suka zama kaman turawa, irin kular da mazajen turawa keba matayen su, a haka take hango kansu cikin ƙwayar idanun nata.
Shima murmushin yayi mata, yana mai ɗauke wayar tata zuwa bisa stool.
Gyara zama sukayi su duka. Sannan ya kalle ta,yana mai cewa "Feel free dear, and eat your food, here is your home, or u want me to feed you, uhmm.?" ya ƙarashe cikin salon da yana yana tafiyar da ita.
Idanunta na kan abincin take ɗan girgiza mashi kai, Amman duk da hakanan saida ya cida kanshi, sannan yake cida ta, da cin abinci yayi daɗi ma, jawo ta yayi zuwa bisa jikin nashi, yana bata yana ba kanshi, hannun shi guda ɗaya na bisa jikin nata yana mata abubuwa marasa daɗi, wanda take jin daɗin su, take kuma hararo yanda Ummin ta ke wassafa daɗin hakan.
Duk da haka Saha bata kula da kuskuren da take neman tafkawa ba. Ko bayan da suka gama cin abincin, kallo ya kunna masu a laptop ɗin tashi, yayin da suka gyara kwanciya bisa madaidaicin gadon nashi.
Bisa ƙirjinshi fa take kwance, yanzu har ƴar hular tata ya zame mata, kalamai na soyayya suke zuba ma junan su, tana jin daɗi idan yace wannan gidan gabaki ɗaya, da mallakin gidan nata ne. Sai take ji ko