Showing 39001 words to 42000 words out of 107295 words

Chapter 14 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1267

dakata ne daga waje, saboda ganin baƙin takalma a ƙofar shiga falon.

Har yanzu hankalin su baikai kanshi ba, da yake nufar hanyar shiga bedroom nasu.

"Oyoyo Dady you are welcome" cewar Husna dake wasa da teddy a ƙasan falon ita da musaddiq.

Wurgar da teddy ɗin tayi, tana mai miƙewa da gudu ta nufi ɓangaren da Abdul ɗin yake

Cak ya tsaya, yana mai juyowa a hankali ya kai kallon shi kan Husnar dake tsaye kusa dashi, ta kama ƙafafun shi ta maƙalƙale.

A hankali ya zuƙunna, yana mai ɗango Husnar, ya shiga ɗan juyi da ita, yayin da yarinyar keta faman kyalkyala dariya. Shima Musaddiq ɗin ganin haka, sai ya dunguro a hankali yana mai ɗaga ma Dadyn nashi hannu, alamun shima ya ɗaga shin.

Ajiye Husnar yayi ƙasa, sannan ya ɗaga Musaddiq ɗin kaman yanda yayi ma Husna. Saida yaji kaman kanshi ya fara juyawa, sannan ya direshi, yana mai rungumo yaran nashi zuwa cikin ƙirjin nashi, cike da soyayya da ƙaunar yaran nashi.


"Ya gida my kids? Kunci abinci? Wasa kuke?" duk ya jero masu tambaya, kaman wasu manya, cikin salon muryar shi ta cikakken namiji.

Husnar ce ta fahimci me yake nufi, saboda haka ne ta shiga girgiza mashi kai "A'a Dady, Momy bata bamu abinci ba, tace sai ka dawo zaka siyo mana" yarinyar ta faɗa kai tsaye, ba tare da shayin komai ba.

A hankali ya juyar da kanshi zuwa ga ɓangaren da Salmar ke zaune, ita da baƙuwar da har yanzu bai shaida fuskar ta ba, saboda ko sau ɗaya bai kalli inda suke ba.

Idon shi cikin bata, abunda yasa tayi saurin janye idon nata kenan, tasan tana son Abdul, kuma Abdul ɗin irin namijin da kowacce mace keda nuradin kasancewa dashi kenan, saidai Sam baya da cikakken quality a bisa gado.

Maida kallon shi yayi bisa fuskar yaran nashi. Yana mai sakar masu ɗan murmushi, saboda Sam baya so yaran su fahimci kaman akwai wani abu tsakanin shi da Momyn ɗin tasu, masalan ma Husnar da take da bala'in wayau

"Kuje ku zauna ko? Zan cenza kaya sai inzo in dafa maku indomie" ya faɗa yana mai raba jikinshi dana yaran.

Ai dagudu suka koma tsakar falo suna tsallen murna, masalan Husnar da ta ɗan fahimci me Dadyn nata yace.

Shi kuwa daga haka, kai tsaye ɗakin ya shige, yana mai jin wata irin ƙaunar yaran nashi a cikin ranshi.

Da kallo Jamilar tabi Salma tana mai jinjina kai a hankali. Kallon farko da tayi ma Abdul ta gano tsantsar wautar da Salmanke tafkawa, kai tun ma tako ƙafar ta a karon farko cikin gidan, ai Abdul ɗin ba da irin su ake saka ci ba. Amman sai ta kalli Salmar gami da cewa "Wannan shine mijin naki?"

Ɗan taɓe baki Salmar tayi "Shine ko kin sanshi ne?"

Girgiza kai Jamilar tayi, "Ban sanshi ba, amman sai naga ai baya da kamannin Raggon da kike faɗa a kanshi"

"Humm! Haka dai kika ce Jamila, dandai ba ke bace a gadon, da zaki faɗi haka, Amman ki bari duk lokacin da hakan ta kasance dake zaki gane ne"

Salimar ta faɗa itama cikin I dont care tone.
"Zakuwa ta kasance, kuma zan bi dashi kaman yanda yake so" Jamilar ta faɗa a cikin ranta
Gyaɗa kai Jamilar tayi, tana mai ɗan ɗaga idanun ta a hankali tabi ƙayataccen madaidaicin falon daya sha kayan alatu da kallo.

Komai yayi, komai yaji, gidan da mai gidan, komai ya mata yanda ake so. Abubuwa da yawa take rayawa a cikin ranta.

"Amman please Salma kije kiji ya ya dawo, ba zanji daɗi ba in kika ƙi zuwa dan Allah"

Girgiza kai Salma tayi, alamun ba zata ba. Nan fa Jamilar tayi ta roƙon ta, har dai lokacin data ajiye wayar tata bisa kujera tana mai ce mata "inazuwa"

Tana ganin ta shige ɗakin, tayi saurin ɗaukar wayar Salmar, gami da yin minimixing ta shiga contact.

Bata sha wahala ba, wajen ɗaukar number ɗin Abdul ɗin, bayan ta tabbatar ita ce mallakin mijin Salmar.

Bata daɗe da ajiye wayar ba Salmar ta fito.

Zama tayi tana mai faɗin "ki share shi kawai ƙawata, ai yama shiga toilet, yanzu dai idasa faɗa man yanda zanyi amfani da magungunan nan"

Ƙasa ƙasa Jamilar ta shiga yi mata bayani, ba wasu magunguna bane masu kyau, hasali ma da kanta ta haɗa su a gida, Amman sai ta dage tana ta kambama ma Salmar magungunan, harma ce mata take sunansu *tazarce*

Suna zaune ɗin dai Abdul ya sake fitowa daga ɗakin, yayi wanka ya cenza kaya. Yayi matuƙar kyau, sumar shi ta kwanta luf-luf gwanin ban sha'awa.

Da ɗan kallo Jamilar ta bishi, tana mai yaba kyau da haiba irin ta Abdul ɗin. Ita a hakan yayi mata, kuma duk ƙulla ƙullar da zatayi domin ganin ta kwaci Abdul ɗin a hannun Salmar zatayi, balle ta fahimci ga yanda al'amurran suke.


Indomie da kwai ya dafa ma yaran, da kanshi ya zaunar dasu a bisa dining yana ba Husnar, yayin da Musaddiq ɗin yake zaune bisa tashi cinyar.

Jamila dai taƙi tafiya, sai ɗibar Salma da fira take, har kai lokacin data kula Abdul ɗin ya kammala komai yana ƙoƙarin ficewa, sannan nayi maza tayi ma Salimar sallama ta fice, gami da yi mata alƙawarn zasuyi magana online. Cikin jin daɗi Salimar ta amsa mata, har tana raka ta bakin gate ɗin gidan, gami da sake yi mata godiya, na ƙoƙarin gyara mata zamantakewar auren nata da take ƙoƙarin yi.


Tun daga nesa ya hango kaman ana tsayar dashi. Saboda haka ne ya goga parking daga gefen titin, yana mai ƙare ma fuskar tata kallo.

Bai shaida ta ba, saboda bai kalli inda take ba ko a cikin gidan.

Kanta ta sunkuya dashi daidai saitin inda yake. "Dan Allah malam ko zaka taimaka ka fidda ni hanya? Tun ɗazu nake takawa ban samu abun hawa ba" ta furta cikin wata irin murya mai taushi, lokaci guda tana ɗan farfara idanu gami da ɗan yamutsa fuska alamun gajiya.

Ɗan jim yayi, baya son irin hakan, Amman taimako wani abu ne, beside ma ba cewa tayi ya kaita gida ba, iyaka hanya ne zai kaita. Saboda haka ya gyaɗa mata kai alamun ta zagaya ta shiga, sannan ya sanya hannu daga ciki yana mai ɓalle mata murfin gaban motar.

"Come in" ya furta cikin wani irin cool voice.
Daidaita zamanta tayi a gaban motar, tana jin wani irin daɗi, da alfaharin gashi daga haɗuwa dashi yau zata fara yaɗa manufarta, wannan jin daɗin da Salma ke iƙirarin tana samu, tabbas itama zata samu irin shi, koma muce wanda ya fishi, domin dukkan abubuwan da Abdul ɗin keso, Salmar ta riga ta faɗa mata from A to Z.

Saboda a haka ne, ta murmusa cike da ƙwarin guiwa, daidai lokacin da Abdul ɗin ya yima motar key yana mai daidaita tafiyar tashi bisa titin...








~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



© *2020*



_~We Love U All~_❤
🤷‍♀🤷‍♀🤷


*_MENENE RIBA TA ❓_*

🙆🙆🙆


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_


~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍

♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*

♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



♣ _Scene Four_

~*Page 13*~



Kwarjini yayi mata sosai, masalan da take ta satar binshi da kallo, ganin yanda yake sarrafa stearyn motar hankalin shi kwance.

Har kai lokacin daya gangara gefen titin, yana mai ɗora hannun shi kan murfin ƙofar motar, yatsun shi na bisa fuskar shi.

Idanun shi a ɗan kulle ya juya yana mai kallon ta. "Ina ganin anan zaki iya samun abun hawa ko?" ya faɗa a hankali, saboda baya buƙatar ɗaga murya, tunda suna kusa ne da juna.

Sai ta samu kanta da gyaɗa mashi kai a hankali, ji take bata son rabuwa Sam dashi, ƙamshin daɗaɗɗen turaren shi na dokar mata hanci.

Ɓalle murfin motar tayi a hankali, tana mai cewa dashi "Nagode Allah ya saka da alkhairi, ba zan taɓa manta alkhairinka a gareni ba"

"Ba damuwa" ya maida mata amsa, yana mai janye idanun nashi daga ɗan kallon da yake mata.

Saida ya tabbatar ta sauka ta rufo ƙofar, kafin yaja motar tashi yana mai barin wajen.

Kai tsaye wajen aikinshi ya koma. Aikin nashi aiki ne mai wahala, yana buƙatar natsuwa, yana buƙatar mai kwantar mashi da hankali, Amman sai gashi ita Salmar tashi Sam ba abunda ke gabanta ba kenan. Yanzu ta kai ga har ta fara wulaƙanta shi gaban ƙawayen ta.

A hankali ya sauke ajiyar zuciya, yana mai dire biron dake hannun nashi. Lamarin Salma ya fara bashi tsoro, gashi har mutanen da yake tare dasu sun fara fahimtar halin da yake ciki, kowa cewa yake rashin natsuwar da yake ciki, ƙila daga gida ne, gashi akai akai ya kan fita yaje ya duba yaran nashi.

Gaskiya ya kamata ya zauna da Salma, gara ya sani, idan har ta gaji da zama dashi ne, ba zai takura mata ba, ba zai tilasta mata ba, gara su san abun yi daga shi har ita. Duk yanda yake sonta, muddin akaci gaba da tafiya a haka, dole ne zai gaza.

Ƙarar wayar shi ce ta katse mashi dogon tunanin da yake yi.

Saƙo ne ya shigo wayar, ganin baisan number ɗin ba, har zai ajiye wayar hankalin shi ya kai kan kwantaccen tsararren rubutun dake jiki.

_"Assalamu Alaikum Wa Rahmatullai Ta'ala Wa Barakatuhu Ya Ma'abocin Karamci Da kuma tausayi. Haƙiƙa naji daɗin ƙaramcin ka gareni, wannan ce ta sanya ni samun number ɗinka domin sake yi maka godiya, nagode kwarai Allah ya saka da mafifucin Alkhairin sa, ya kuma raya maka zuri'a Husna da Musaddiq. Ina fatan zaka huta lafiya, ka kuma kasance cikin farin ciki da annashuwa"_

Sake bin saƙon yayi da idanu, haƙiƙa ba gizo idanun nashi suke yi mashi ba.

Wacece wannan? Hada sunan yaran shi fa ta ambata.

Shaf ya manta daya rage ma wata hanya jiya. Saboda haka ne ya sanya shi saurin dialling number ɗin.

Saida ta gyara murya sosai kafin ta amsa, tana mai wani narkewa bisa gado.

Sautin amsa sallamar tata ya daki dodon kunnen shi sosai.

"Zan iya sanin ko wacece please?"

Ya furta, bayan ya gama amsa mata sallamar tata.

"Ba lallai ka gane ba, amman kasan ance yaba kyauta tukuici"

Ɗan murmushi ya saki.

"Naji kin ambaci sunan yara na ne, dalilin kiran kenan, ko ba komai na tabbata kin sanni, shine nake so inji ke wacece, kuma alkhairin me na aikata maki?"

Sake narkewa tayi, tana mai sakin wani irin ƙayataccen murmushi,wanda har saida ya jishi a kunnen nashi.

"Hakan shi zai daɗa tabbatar mani da cewa alkhairi a jinin jikinka yake, kai ma'abocin shine. Gashi kai kayi, Amman har ka manta, saboda dan Allah kayi."

Ɗan muskutawa yayi, bai gane inda zantukan nata suke dosa ba, hakan ce ta sanya shi saurin cewa

"Kinga aiki nake kika katse mani, kada ki riƙeni da yawa please"

Maganar tashi tayi mata daɗi, a yanda ta ganshi jiya sai tayi tunanin zai wahalar shawo kai, Amman daga fara maganar dashi ta tabbata ma kanta yana da sauƙin kai. A karo na biyu da ta ayyano irin wautar Salma. Allah ya baki miji irin wannan, amman kina wasa da damarki.

"Ba zan riƙe ka ba Abban Musaddiq, saidai zanso ace na samu lokacinka mai yawa, duk da na lura da cewa tsada ne gareshi"

Itama ta sake furta wa cikin wani irin salo.

Ya fara gajiya da maganar, gashi dama kanshi cikin zafi yake.

Sai yayi saurin ce mata.

"Idan ba zaki faɗa ba, zan iya kashe kiran, saboda na faɗa maki ina da ayyukan yi a gabana"

Jin hakan da tayi ne ya sanya ta saurin tashi zaune, to ya haka kuma? Ita da take ganin abubuwa sun fara tafiya daidai? Sai kuma ya rikiɗe mata?

Saurin cewa tayi "Yi haƙuri Abban yarana, nice wadda ka rage ma hanya jiya, Naji daɗin hakan ne, Shiyasa na nemeka domin in sake maka godiya, jiya naga kaman kana sauri ne, ban samu damar yi maka ba"

"Ba damuwa, wannan ba komai bane ai" ya furta shima, bayan ya fahimci wadda yake maganar da ita, dama kuma ko a jiyan yana kula da yanda take satar kallon nashi. Duk sai taji ba daɗi.

"Nagode! Zan so ace na sake kira lokacin da kake free domin mu ɗan tattauna wani batu."

Ta furta a hankali, tana mai miƙewa ta fara takawa, duk sai taji ma ta kasa sukuni, kaman tana gabanshi ne.

"Na dai san kinsan ina da mata, kaman yanda naji kin ambata sunan yara na, saboda haka kinga bana da wani time, daga na bautar Allah, sai na aiki na da iyali na. So na gode, zanso ki bar maganar tattaunawar nan hakanan please"

Ya faɗa yana mai ƙoƙarin datse kiran, saboda shi bai ga alaƙar shi da ita ba, da har zata so ɗauke mashi hankali daga kan aikin nashi.

"Idan wani ya ƙi ka da yini, wani da kwana yake sonka, tunda Salma ta fara yi maka haka, me zai hana ka jaraba wata?" zuciyar shi ta shiga raya mashi. Girgiza kai ya fara yi a hankali, yana son Salma, baya jin idan zai iya haɗa ta da wata a rayuwar tashi, zai so ace Salmar ta hankalta ta gyara, da zaifi kowa jin daɗi, farin ciki da annashuwa.

Kasaƙe tayi da waya a hannu. Ya da haka kuma? Zuciyar tace ta shiga raya mata "ai dama irin waɗannan mazajen suna da wuyar samu, ki daure ki shawo kanshi tukunna, kada kiji haushi"

Gyaɗa kanta ta fara yi cikin gamsuwa da zancen zuciyar tata. Sake daddanna mashi saƙo tayi, tana mai turawa, sannan ta faɗa saman gadon nata, tana mai sauke ajiyar zuciya, gami da dafe ƙirji.

Koda yaga shigowar saƙon, bai kula tashi ba, haka ya cigaba da aikin shi, har ya kammala ya kama hanyar zuwa gidan nasu. Saida ya gaido iyayen nashi, kafin ya juya akalar motar zuwa gidan nashi, riƙe da ledar chips daya siyo wa yaran nashi.

Saida ya kammala komai na al'ada sannan ya kwanta, har yanzu babu wata alaƙa tsakanin shi da Salma, ita ala dole fushi take, shi kuma tunda baiga abunda yayi mata ba, ya kuma yi lallashn duniya akan ta bar fushin nan ta ƙiya, Shiyasa ya share ta shima, yana kallo ta, tsakanin shi da ita saidai kallo. Duk dai abun buƙata zai siyo ya ajiye, amman ko nairar shi ya dena bata. Ba don komai ba kuma, sai dan ta gane irin kuskuren da take neman tafkawa, sannan ta gane ba kwanciya ce kaɗai rayuwar zaman aure ba, kaman yanda tasha faɗa tana ji a litattafai.

Wayar ya ɗauko da niyar maida ta silent, idanun shi suka kai kan saƙon ɗazu.

"_Mai son tsuntsu shi yake binshi da jifa, ina maka fatan nasara da sa'a a duka rayuwar ka, sannan ina mai roƙon alfarmar a ɗan dinga kula ni, koda sau ɗaya ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login