Showing 87001 words to 90000 words out of 107295 words

Chapter 30 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1255

itama kuma Salmar take kallo tana murmushi.

Salma ta zaro idanu, idan bata manta ba Habiba ce wacce ta taɓa kawo mata tallan kayan mata har tayi mata wa'azi akan irin yadda take tafiyar da gidan ta da ƴaƴan ta ta zauna ta wanke matar tas batare data duba shekarun ta ba.



************ **************

Ummi tace; "Saha wai wane sabon al'amari kika shigo mini dashi cikin gida ne?", Saha ta saukar da kanta ƙasa tace; "babu komai Ummi kawai yanayin zafin garin ne", Ummi tayi jimm tana kallon ta sannan tace; "shikenan".

Saha ta sauke ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan ta wuce ɗakin su bayan ta ajiye bokitin, cikin sauri ta maida ƙofar ta kulle sannan ta faɗa saman katifar tasu.

Lallai Ummi tana daf da gano ta, dole ta canza taku gudun kada Ummin ta fara zargin ta, wata zuciyar tace mata; "ba Ummin ke janyo miki ba".

Ta maida idanu ta rufe tana tuno page ɗin jiya na littafin *MACE DA MACE* wanda wata marubuciya *Shukra* take rubutawa jiya aka fara turo shi group ɗin *MATAN HARKA* wanda Sahar take basaja a cikin shi kuma shine group ɗin da duk wata marubuciya me batsa da lesbian da kuma makarantan su suke ciki, Sahar ma da ƙyar aka saka ta a ciki sai da ta biya 5k sannan.

Saha ta sake juyi tana me kallon ƴar uwar ta dake kwance a saman gadon, ita lesbian ba wani damunta yayi ba amma yadda marubuciyar ta tsara shi da yadda ake yabon abin dan jiya firar da suka yi kenan a group din sai taji tana sha'awar aikatawa ko yaya ne dan taji ya ake ji a cikin shi.

Ta tashi zaune tana son taɓa Suraiya dake barci tana kuma tsoron abinda zai je ya dawo, ta ɗan ja tsaki tana faɗin; "dole ne nima na ɗan ji me akeji a ciki, amma bata haka zan biyo ba to yanzu ma waye zai koya mini yadda ake yin lesbian ɗin?", ta ƙarasa tana buga uban tagumi.

Ganin bata da mafita dole ta kwanta domin dai tana jin tsoron taɓa ƴar uwar tata gudun farkawa kuma ta tona mata asiri sai dai dole zata canza taku inda zata janyo ƴar uwar tata da kuɗi da kuma kayan ƙwalama.

Sai dai dole tana buƙatar me ɗorata akan hanya don haka ta yanke shawarar tuntuɓar wata yarinya wai ita *fici* ganin yadda jiya ta zaƙalƙale a group ɗin ya tabbatar mata da cewa ƴar hannu ce, da wannan shawarar barci ya kwashe ta.

Koda safe bata farka da wuri ba dan haka Suraiya ce ta ɗora abin kari ta gama ta maida ruwan wanka sai da yayi zafi ta juye tayi sannan tazo ta hau tashin ƴar uwar ta.

Saha tayi miƙa sannan ta miƙe, idanun ta ya sauka kan ƙanwarta ɗaure da towel nan da nan sheɗan ya fara ƙawata mata ƙanwartan.

Suraiya kuwa ganin yadda yayarta ke kallon ta tace; "Aunty Saha ki tashi kiyi wanka kizo mu karya Ummi zata aike mu fa".

Cikin sauri Sahabat ɗin ta dawo hayyacinta, sai taji muryar yarinyar kamar ana ƙara mishi zaƙi ne, ta saki munafikin murmushi sannan ta miƙe ta fice, ko wajen wankan surar ƙanwarta kawai take tunawa bata taɓa jin sha'awar mace ƴar uwar ta ba sai jiya zuwa yau kuma abin ban haushi wai ƴar uwar ta.

Koda ta fito nan ta fara lissafin watannin da ya rage su Ummin su tafi taron ƙungiyar tasu, saura wata uku da ƴan kwanaki dan haka tana saka ran kan wannan lokacin xata shawo kan ƙanwarta inda zasu more kan Ummin ta dawo duk da dai bata da tabbas ɗin akwai daɗi ko babu.

Ummi kuwa tana komawa ɗaki ta watsar da tunanin Sahar ta fara tunanin yadda zata tsara page ɗin gobe yafi na yau daɗi don jiya tasha comments ta kuma sami ƙuɗi sosai da sosai.

Shukra har jinjina sai da tayi mata, Ummi kam ta karanta littafin Shukrar jiya dan haka itama yana ɗaya daga cikin abinda ya fara ɗaga hankalin ta.

Sai dai ita bata da burin yin wannan harkar dan haka ta watsar dashi, safiya nayi kuwa ta baje saman kujera ta fara aikin nata wato typing.

Saha data gama shiryawa cikin doguwar riga ta atamfa me ruwan shuɗi tayi kyau sosai gashi ɗinkin ya zauna a jikin ta dan ada ɗin kin yayi mata yawa amma ƙara buɗewar da tayi sai ɗinkin ya dawo ya zauna a jikin ta sosai kuma ya kamata.

Suraiya kuwa riga da wando na pakistan ta saka me kalar pink da ratsin milk, itama tayi kyau dan yanzu ta fara girma sai dai ita tsayi gare ta saɓanin Saha da take da jiki yanzu.

Ummi ta kalle su ta washe baki sannan tace; "ah lallai ƴan mata na sun yi kyau", Surayya ta rufe idanu tana murmushi, Ummi ta miƙawa Saha kuɗin tace; "gashi Hajiya Kareema ta aiko miki dashi jiya tace ki siya abinda kike so, na san dai akan kayan kwalliya zasu ƙare", Saha ta saka hannu ta amshi kuɗin.

"ku siyo abinda ya kamata, kema ga naki sai ki taimaka mata ta siyo ɗan kayan ƙaleƙalen dan itama yanzu naga ta fara girma", Ummin ta faɗa cikin salon tsokanar Suraiyyar.

Sahar ta haɗa duka ta amsa tana faɗin; "an gode sosai, insha Allahu zamu siyo kamar yadda kike bukata", itama Suraiya tayi godiya.

Ummi tayi murmushi tace; "kada ku damu, ku dai ku tabbata kun dawo gida da wuri sannan banda shashashanci da kule-kulen maza a hanya", Saha tace; "to", tana jan hannun Surayyar suka fice.






~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



© *2020*



_~We Love U All~_❤

[4/13, 8:49 PM] Sumayya Sumy B: 🤷‍♀🤷‍♀🤷


*_MENENE RIBA TA ❓_*

🙆🙆🙆


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


~*WRITTEN BY*~ ™ _Golden Pen Writers Association_


~*DAGA ALQALUMAN*~👇🏻.....✍

♦ *Ummee Yusuf* ::--Maman Yusuf, marubuciyar *UMMU SALMA.*

♦ *Aminatu Hassan* ::-- *0um-Deedat*, marubuciyar *BAN FI KARFIN TA BA.*

♦ *SUMAIYYA BABAYO ABDULAHI* ::-- *SUMIEE B.*, marubuciyar *AMINTA.*

♦ *KHADIJA MUHAMMAD* ::-- *0ne luv*, marubuciyar *ƘAREENATEEY.*

♦ *FATIMA UMAR MODIBBO* ::-- *FATIMA BATULA*, marubuciyar *SAIF KO MALEEK.*

♦ *BINTU AHMED* ::-- *CYNOSURE* marubuciyar *SHABIHATY (ME KAMA DA Ni).*

~*DEDICATED*~ _To All Victims That Are Related To The Story_

~*WARNING*~ _K'irk'irarren labari ne ba'ayi dancin zarafin wani ko wata ba. Sunayen da suke ciki kama daga na mutane zuwa na gari an k'irk'ire su ne domin fad'akar,ilimintar game da nishad'antar dame karatu, dan haka ba'a yarda wani ko wata ta juya wannan labarin ta kowace siga ba._


عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَال*َ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: إِنَّ اللَّهَ إِذَا أَحَبَّ عَبْدًا دَعَا جِبْرِيلَ، فَقَالَ: إِنِّي أُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبَّهُ، قَالَ: فَيُحِبُّهُ جِبْرِيلُ، ثُمَّ يُنَادِي فِي السَّمَاءِ فَيَقُولُ: إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ فُلَانًا فَأَحِبُّوهُ، فَيُحِبُّهُ أَهْلُ السَّمَاءِ، قَالَ: ثُمَّ يُوضَعُ لَهُ الْقَبُولُ فِي الْأَرْضِ. وَإِذَا اللَّهُ أَبْغَضَ عَبْدًا، دَعَا جِبْرِيلَ فَيَقُولُ: إِنِّي أُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضْهُ، فَيُبْغِضُهُ جِبْرِيلُ ثُمَّ يُنَادِي فِي أَهْلِ السَّمَاءِ: إِنَّ اللَّهَ يُبْغِضُ فُلَانًا فَأَبْغِضُوهُ، قَالَ: فَيُبْغِضُونَهُ، ثُمَّ تُوضَعُ لَهُ الْبَغْضَاءُ فِي الْأَرْضِ. رواه مسلم (وكذلك البخاري ومالك والترمذي)*





*On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:*

*"If Allah has loved a servant [of His], He calls Gabriel (on whom be peace) and says: 'I love So-and-so, therefore love him.'" He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "So Gabriel loves him. Then he (Gabriel) calls out in heaven, saying: 'Allah loves So-and-so, therefore love him.' And the inhabitants of heaven love him." He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "Then acceptance is established for him on earth. And if Allah has abhorred a servant [of His], He calls Gabriel and says: 'I abhor So-and-so, therefore abhor him.' So Gabriel abhors him. Then Gabriel calls out to the inhabitants of heaven: 'Allah abhors So-and-so, therefore abhor him.'" He (the Prophet - peace and blessings of Allah be upon him) said: "So they abhor him, and abhorrence is established for him on earth."*

_[ Narrated; Muslim also by al-Bukhari, Malik, and at-Tirmidhi).]_



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM!*



♣ _Scene Six_

~*Page 25*~

Taku kad'an suka yi bayan fitowar su daga gida suka yi nasarar samun mai adaidaita sahu. Kai tsaye kasuwar Central ya sauke su inda Sahabat take rik'e da hanun Surayya tana d'an murza su a hankali wani bak'on yanayi take ji a jikin ta a lokaci d'aya kuma zuciyar ta na k'wadaito mata son aikata abinda ta karanta a littafin *MACE DA MACE.* Surayya kanta tayi mamakin yanda take ta haba-haba da ita, bata karaya ba sai da suka isa wani tafkeken shagon Cosmetics, Mayuka masu tsadan gaske dasu Powder, turare, da sauran kayan makeup ta zage ta ringa ibar mata abin tsoro ya koma bata bayan sun kammala taga kud'in data fidda ta biya duka kayayyakin wanda tun a nan sun cinye kudin da Ummi tasu ta basu.

Bayan sun gama da nan shagon suka nufi shagon kayan ciye-ciye da kwalamulashe ta nufa da ita, inda nan ma ta zage ta ibar mata su chocolate, sweet, biscuit da sauran su, Surayya kamar mutum mutumi ta zama domin gaba daya abin gani take kamar shirin film domin duk abinda ta dauko zata kalle ta da murmushi ta mik'a mata tare da fad'in. "My Sister wannan test d'inki ne" a haka har suka qarqare suka doshi wani Boutique inda ta siya mata Riga da skirt na English Wears masu tsada da k'yau guda biyu. Fitowa suka yi tare da nufan bakin hanya domin hawa adaidaita sahu ya sada su da gida. har a lokacin tana rik'e da hanun Surayya.

"Assalamu Alaikum, Ranki shi dade, barka da da wannan lokacin"

Abinda kunnuwar ta suka jiyo mata kenan da wani murya mai kama da busar sarewa, a tare suka juyo da Surayya tare da zuba mishi ido.

K'warjinin da ya mata yasa bata san lokacin da bakin ta ya bud'e har ta amsa mishi sallamar da

"Amin wa'alaikas salam"

"Wow yanda komai yaji, haka Voice dinta yake nasan ciki kuma sai tafi haka" a zuciyar shi yake wannan zancen a zahiri kuwa wani lallausar yaudararriyar murmushin shi ya sake da har sai da gefen kumatun shi ya lotsa tare da mik'a hanun shi mai d'auke da zaran-zaran yatsu da nufin karb'ar ledar dake hanun ta cikin salon muryar shi ya ce; "Gimbiya wannan ba girmar ki bane rik'e shi, sai mu bayin ki"

Qamshin turaren shi ya mutuk'ar birge ta kuma ya mata kamaceceniya dana abin k'aunar nata *Zaiyad*. Shigar shi ta mutuqar birge ta shiga ce ta qananan kaya daya dace da siffan jikin shi, Fari ne dogo, hancin shi d'an matsakaici, Sajen daya zagaye fuskar shi, ya qara ma fuskar k'yau da haiba wandaya sha gyara ya kwanta lub yana ta zuba shek'i. Dimple ne ya qara qawata fuskar tashi domin duk sanda yayi magana sai ya lotsa.

"Na gode" ta fad'a ba tare da ta sakar mishi ledar ba.

Kallon shi ya maida kan Surayya, " Sister na kawo in taya ki tunda Auntyn mu tak'i kawo nata." ya fad'a cikin narkar da muryar irin ta shagwab'ab'u.

Kallon ta Surayya tayi inda taga bata ma kallon inda suke hankalin ta naga kan hanya.

Ba tare da ta mik'a mishi ba yasa hanun ya karb'i babbar ledar dake hanun hagun ta. Sakar mishi tayi inda ya dube ta yace "Bismillah ranki shi dade, idan baza ki damu ba in sauke ki, domin bai kamata rana ya ringa samun rabon shi a jikin wannan lallausar fatar fatar ba."

Ji tayi wani yamm kalamun shi suna fasa mata kai tare da jin kanta na qara girma.

"A'a ka bar shi kawai na gode"

"Haba gimbiya bai kamata ki hana bawar ki yi miki hidima ba a daidai lokacin daya dace ba tare da wani dalili ba instead ki bada Umarni kawai."

Lumshe ido tayi tare da kai duban ta gun Surayya, "Sis muje."

Ta fad'a a tak'aice tare da bin bayan shi har gurin da yayi parking d'in dalleliyar motar shi, gidan gaba ya bud'e mata ta shiga sannan ya bud'ewa Surayya baya ta zauna zagawa yayi ya tadda motar suka d'au hanya inda yake tambayar ta anguwar su ta fad'a mishi a tak'aice.

"Abinda bata tab'a ba shi yau tayi domin har qofar gida sai daya sada ta wanda bata san lokacin da suka iso ba saboda irin kalaman dayake tsara mata wanda kuma suke tasiri a zuciyar ta, tana kuma mamaki dama ak'wai namijin daya iya jere kalamai kamar Zaiyad d'inta? Kalaman shi sun shagalar da ita sosai da sosai kunnuwar ta kuma basu gaji da sauraron su ba, wannan yasa sun so su wuce ma Surayya ce ta ankarar dasu inda yayi baya tare da goga parking a daidai qofar gidan.

Bayan musayar namba waya da suka yi, sabbin rafa yan d'ari biyar ya dauka tare da mik'a mata na 20k a sanyaye ta qarb'a tare da yin godiya, bud'e murfin motar tayi ta fito wanda Surayya tuni ta riga tayi shigewar ta cikin gida, yana tsayawa ta balle murfin motar tayu shigewar ta domin irin yanda taji yana sakar magana kai tsaye gaba daya sai taji ta a takure.


Saukar ta yayi dai-dai da fitowar Baba Mariya daga gida zata anguwa, da mamaki ta dube ta tare da bin bayan motan da kallo hanun ta rik'e da bakin ta lallai abinda jama'a suke fad'a a kan Sahabat dama da gaske ne ashe? Tunda gashi ta gani da idon ta. An sauke ta ga siyayya ga kuma maqudan kud'ad'e a hanun ta Yooo wannan zamani da ake ciki idan ba fasiqanci za ai dake ba wani namiji ne da bai ko tura gidan ku ya nemi izini ba zai ringa miki irin wannan hidimar?

Gaisuwar Sahabat d'inne ya katse mata tunani. Inda ta amsa da "Lafiya Saha"

Har ta ratsa ta zata wuce tayi saurin tsaida da ta.

"Uhumm nace ba Saha."

Cak ta tsaya tare da d'an yin baya a daidai lokacin kuma da take qoqarin saka kud'in cikin Purse d'in dake hanun ta.

"Kiyi hakuri, zan shiga abinda ba ruwa na amma ina ganin wannan shine zaman tare saboda hakkin maqotaka ya wuce wasa sannan irin zaman amanan da akayi da mahaifin ki mutumin kirki Allah ya qara masa rahma, ya gafarta masa zunuban sa."

"Amin" ta amsa jikin ta a sanyaye domin tana mutuk'ar ganin girmar Baba Mariya, tana da kamala da kamun kai sosai sannan kome na anguwa tana tashi tsaye abinda ya shafi zamantakewa da mak'wafta da sauran su duk wani abinda zai taso sune a gaba-gaba.

Cigaba tayi da magana "Saha maganganun dana ke ji a kanki sam bana jin dad'in su duk da bangani ba a zahiri amma masu fad'ar na tabbatar da baza su mik'a qage ba ko sharri, sannan yanzu kuma na ga saukar ki a mota da kuma yanayin dakika sauka.".

Ta fad'a tare da nuna hanun ta, "Saha dan Allah kiyi hakuri ki rik'e maraicin ki, ki duba girmar Allah. Ki sani duk abinda kika yi na alkhairi ko akasin sa sai an isarwa mahaifin ki. Mahaifin ki mutumin kirki ne mai qoqarin ganin ya k'yautatawa duk wanda ya rab'e shi, baida abokin fad'a ko gaba tsawon zamana dashi a anguwar nan tun kafin yayi aure ban tab'a ganin wani abun asha dayayi ba. Samarin zamanin nan ba abinda yake gunsu sai rud'u da yaudara ki yi tunani, har yau banji ance ga garon tambayar ki ba, amma koda yaushe sai dai ace ga shinan an dauke ki mota an sauke ki nan aikin kenan abubuwa marasa dad'i bazan b'oye miki ba naso zuwa in samu mahaifiyar ki kan zancen amma kuma wai-wai nake ji amma kinga yanzu da ido na ya gane min ban bari ki wuce ba na tsaida ki.
Dan Allah Sahabat ki kula ki kame kanki, ki tsare mutunci ki na ya mace Dana iyayen ki, ki kare martabar ki domin duk namijin da yake miki soyayya ta gaskiya tsakani da Allah bazai fara tsaida ki hanya ba yana hure miki kunne da kalamun shi na yaudara face ya dangana da gidan ku ko ya nemi wani naki domin neman izinin hakan. Wannan shine kuma addinin, da al'adar mu suke tafiya akai, kuma yin hakan shi ne siya ma kanki daraja a idon duniya da kuma shi kanshi namjin idan Allah yayi mijin ki ne, saboda maza ba tabbas suke dashi ba. Sun aure ka tare sun same ka a mutunci ma sun wulaqanta ka idan ba'ayi sa'a ba ballantana."

Sahabat da tunda ta fara maganar kanta yake qasa da farko maganganun sun b'ata mata rai, suka koma bata mamaki sako zancar mahaifin ta kuma ya sanyaya mata jiki. Tabbas duk maganganunnta haka ne amma kuma fa Baba Mariya baza ta gane ba domin wani al'adar neman aure etc duk wannan a zamanin su ne yanzu ana Digital life ne komai is

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login