Showing 75001 words to 78000 words out of 107295 words

Chapter 26 - MENENE RIBATA BOOK Complete By Ummee Yusuf.txt

18 Nov 2025

1256

bata isa ba suka ɓata gaba ɗaya, nan ta hana shi shiga ɗakin babu arziƙi ya tattara ya koma ɗakin amarya.

Allah yasa ma sai gobe zasu zo danki, daga gobe kuma dole ya canza wajen kwana haka ya kwanta yana me janyo wayar shi ya hau fira da abar ƙaunar shi.

Washe gari aka zo aka yi danki, inda nan ma sai da Salma ta nuna halin ta dan sai da suka tafi da ita a baki.

Ita kuwa babu abinda ya dame ta, ji take wannan shine dai-dai kuma har yanzu ta yarda da maganar Jameela akan Abdulkareem ɗin zai iya tsorata yace ya fasa.

Dangin amarya kuwa sai da suka kulle ɗakin tsaf sannan suka tafi da makullin gudun abinda zata iya aikatawa bayan sun tafi.

Abdulkareem ranar sai cikin motar shi ya kwana, washe gari kuwa ko idanun shi Salma bata gani ba yana dai jiyo hayaniyar ta a ciki nan ya wuce can gidan su dama tuntuni ya kai su Husna can acan ya karya sannan yayi wanka ya canza kaya.

Sai dare sannan ya koma nashi gidan, abin mamaki yau tsabar masifa ma Salma ko wayar bata danna ba dan wani irin zafi zuciyar ta yake yi mata.

Kamar ba zai shiga inda take ba sai kuma ya shiga, hannun shi ɗauke da leda, yayi sallama ko kallon shi bata yi ba ta dai amsa sallamar.

Ya saba da halin ta yanzu dan haka yace; "ga kayan ki nan na fitar biki tunda baki amshi akwatin ba, na kaiwa su Husna nasu, dan Allah Salma ki dena abinda kik........".

Cikin fushi ta shaƙi wuyan shi sannan cikin ihu tace; "ka fita ka bani waje Abdulkareem!!!", sosai abin ya bashi mamaki dan be taɓa jin sunan nashi a bakin ta ba.

Ganin yadda ta koma kamar mahaukaciya yasa ya bamɓare hannun ta daga jikin shi ya juya zai fice, ta ɗauki ledar da jefa mishi a jiki ya juyo da sauri, cikin sanyin murya kuma tace; "dan Allah ka ɗauke bana so", ta ƙarasa muryar ta na rawa.

Sosai ta bashi tausayi, a wajen ta zauna ta fara kuka, ance soyayya daban take dole Abdulkareem yaji wani abu ya caki zuciyar shi ya san da cewa Salma itace macer da yaso so na gaskiya.

Da sauri ya ƙaraso inda take ya ɗago ta, Salma da kamar ma bata hayyacin ta abu ɗaya take ambata shine; "ka tafi ka bani waje kawai", be saurare ta ba haka ya ɗauke ta ya kaita har saman gadon ta ya kwantar.

A hankali yake shafa gashin kanta tana sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya yace; "Salma kiyi haƙuri duk abinda ya faru kece kika janyo mana, ki ɗauki aure na a matsayin hukunci daga ubangiji ki sassautawa kanki haka mana, na san da cewa kina sona har yanzu dan auren soyayya muka yi dake amma meyasa kika canza mini lokaci ɗaya?".

Bata ce komai ba sai dai har lokacin hawaye na zuba daga idanun ta, haka ya dinga kwantar mata da hankali cikin dabara kuma cikin taimakon Allah taji ta ɗan sami sauƙi.

Ranar dai tsakanin Abdul da Salma sunyi kwanan farin ciki duk da babu abinda ya shiga tsakanin su, asuba suka tashi inda yace; "ki tashi yanzu kiyi sallah", babu musu ta tashi tayi.

Yana dawowa haka suka kuma shan barcin su cike da ƙaunar juna, Abdul yayi ƙoƙari wajen kaudar da damuwar da Salma take ciki.

Sai takwas suka tashi, nan suka shiga kitchen tare suka samawa cikin su abinda zasu ci, sai da suka gama sannan yace; "yanzu ki tashi muje mu gyara gidan nan kinji", fuskar ta cike da damuwa dan ta tuna ko jiya sai da Auntyn ta ta kira ta akan zasu zo su taya ta gyara tace bata so suyi zaman su.

Abdul ya riko hannun ta yace; "kada ki damu Matata ki muje muyi aikin mu", tayi murmushin da be kai zuciya ba sannan ta miƙe.

Sunyi aiki sosai da sosai dan irin yadda gidan yayi datti, har wajen azahar basu gama ba gashi da an idar da azahar ɗin za'a ɗaura auren, har ma abokanan shi sun fara kiran shi.

Ya cire hannu daga wankin da suke yi ya kalle ta cikin damuwa yace; "bari nazo na shirya na tafi amma zan kira miki su Aunty Maryam kinji kada ki damu", tayi murmushin yaƙe tace; "to.

Ta bishi da kallo har ya shige ɗakin, kasa cigaba tayi da wankin ta tsaya kawai, ita ba tunani ba ita ba aikin ba.

Har yayi wanka ya shirya tana tsaye, ƙamshin da hancin ta ya fara kawo mata ne yasa ta ɗaga kai ta kalle shi, kamar ta ɗora hannu akai tayi ihu haka take ji.

don mijin ta data gani sanye da farar shadda ƙarr da ita wacce aka yiwa aiki da zare me ruwan ƙasa yayi kyau sosai wular kanshi da takalmin shi sau ciki duka ruwan ƙasa ne, ga wani irin ƙamshi dake tashi a jikin nashi wanda ya buɗe gidan.

Yayi mata murmushi sannan ya matso kusa da ita ya bata kiss a goshi yace; "zan tafi kada nayi latti azo ana jira na", ta ɗaga kai kawai.

Ya kwanto ta jikin shi sannan yace; "babu rako ma Sweet", ba dan taso ba ya riƙe hannun ta har zuwa bakin get ɗin gidan, ita dai binshi take kawai da kallo.

Shigowar ƴan uwan ta nan suka hau yi mishi tsiya yana dariya, Salma kuwa babu eh babu a'a, sai da suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka wuce suka barsu.

Yace; "zan tafi", ta ɗaga mishi kai ya langwaɓar da kai yace; "babu addu'a", tace; "Allah ya kiyaye hanya yasa a ɗaura lafiy....." bata ƙarasa ba hawaye suka fara zubowa daga idanun ta.

Ya ciro handkerchief ya hau goge mata sannan yace; "kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka Salma haba Uwargida ki zama jaruma mana, ki zauna kusa da wayar ki anjima zan kira ki", ta ɗaga kai kawai ya kaiwa lips ɗin ta kiss sannan ya sake ta ya fita.

Ta daɗe tsaye a wajen tana sharar hawaye, zuciyar ta kamar zata tsago ƙirjin ta ta fito haka take ji, ga wani iri da numfashin ta keyi yanzu shikenan zasu zama su biyu wajen mijin ta.

A sanyaye ta koma cikin gida inda ta tarar da ƴan uwan nata har sun gama wankin sun ɗora mata abinci.

Auntyn ta Aunty Maryam ta balla mata harara tace; "ji yadda kika maida kanki ko?", Salma ta sauke kanta ƙasa.

Aunty Jidda tace; "mijin ki na son ki amma kin bi kin sa duk ya juya miki baya ai wallahi da ba dan ya kira Abban Aarif ba da ba zan zo ba ki zauna kici haukar ki shashasha kawai".

Aunty Maryam tace; "barta Jidda wallahi ta cigaba da ɓata mishi rai ya sako ki, ki koma gida dama Abba yace ai ki bari mijin naki ya sako ki ki dawo gida sai kin gane baki da wayo".

Aunty Sameeha tazo ta riƙe hannun ta sannan tace; "kai Jidda da Maryam ku bar mini ƙanwa haka, kinji zo muje ciki kije kiyi wanka na tsantsara miki kwalliya kema kada amarya tazo ta raina ki".

Maryam da Jidda suka yi dariya suka ce; "Allah matar yaya Salman ce bata da hali kwata-kwata".

Nan dai Sameeha taja hannun Salman suka shiga ciki, da kanta ta haɗa mata ruwan wanka ta shiga tayi.

Tana fitowa wayar ta ta hau ƙara, ganin me kiran sai da gaban ta ya faɗi, amma haka ta daure ta ɗaga, a can ɓarin taji yace; "Uwargida an ɗaura", ba tare da tace komai ba ta katse wayar kawai ta saki kuka.

Aunty Sameeha ta hau rarrashin ta tare da yi mata nasiha, ita dai Salma yanzu gani take ma Sameehar ba son ta take yi ba.

Haka tayi banza da ita, su Aunty Maryam ne suka shigo ganin yadda Salmar ke kuka Sameehar na lallashin ta abin ya basu haushi nan suka hau Salmar da faɗa babu arziƙi ta goge hawayen ta, Aunty Sameehar ta hau yi mata kwalliya.

Shaddace ruwan toka wacce taji aikin wuta da stones doguwar riga ce tayi kyau sosai, nan Aunty Sameehar ta kashe mata ɗauri me kyau, Aunty Maryam tace; "da kyawun ki da komai amma kin zauna kin ɓata wayon ki gashi mijin naki akwai ƙoƙari wajen siyo miki kayan kwalliya, nan dai suka ƙara yi mata nasiha sosai.

Sai lokacin Salma taji hankalin ta na ɗan kwantawa ga kuma jikin ta da yayi sanyi jin yadda ƴan uwan nata suke mata wanka me kamar jirwayi, ga wasu ayoyi a alƙur'ani da suka janyo mata su wanda Salma duka ta san ma'anar su dan ba jahila bace, basu ƙyale ta ba sai da suka tabbatar da ta fara dawowa hayyacin ta sannan suka ce ta tashi ta fita.

Babu musu ta miƙe ta fita inda tana fitowa mijin nata yana shigowa da abokanan shi, nan fa suka hau tsokanar ta wai ta zama tsohuwa ita dai murmushi kawai take yi domin bata da kuzari, gashi ta kira number din Jameela amma bata ɗaga ba.

Haka ta tura mata da text akan an ɗaura auren ta taya ta da addu'a, Jameela na ganin saƙon ta saki shewa tana dariya.

Sun yi barkwanci sosai tsakanin ango da abokanan shi kafin aka ɗauki hotuna har zuwa wani lokaci sannan suka fice daga gidan.

kamar yadda al'adar kaduna take, sai da aka gama dinner ƙarfe goma sannan aka nufo da amarya gidan ta, a lokacin kuwa Salma na saman dadduma dan tun wajen takwas ƴan uwan nata suka bar gidan inda aka bar mata ƙanwar ta Fiddausi da kuma Fatima, to su ɗin ma kowacce tana kan waya tana faman fira da saurayi.

Jin guɗa yasa gaban Salma faɗuwa dan bata je dinner ba saboda kunyar ƴan uwan Abdulkareem ɗin da take yi na ganin irin rashin mutuncin da tayi musu.

Sallama taji a falon ta wanda ya bata tabbacin an kawo mata amarya ne, ta kalli su Fatima sannan tace; "Fatima muje falo", dole suka ajiye wayoyin suka fito duka.

Nan aka gabatar da Amarya ga Uwargida aka kuma damƙa amanarta gare ta tare da ƴan nasihohi, Salma cikin sanyin murya tayi godiya tare da jaddada musu insha Allahu zata riƙe amana ƙarshe tayi addu'a sosai wanda hakan yasa ƴan uwan amaryar jin ta birge su, duk da sukar ta da ƴan jere suka kai amma yanzu ta wanke wancan Jameela kuwa ba haka ranta yaso ba amma babu yadda zata iya.

Haka suka tashi suka tafi suna yaba halin ta wasu na cewa ladaf tayi dan babu yadda zata yi wasu kuma suna cewa halin tane hakan.

Salma kam suna fita ta koma ciki kan daddumarta tana ƙara neman yafiyar Allah akan abinda ta aikata tare da neman taimakon Allah.

Anya kuwa tuban gaskiya kika yi Salma🤔.

Sai wajen sha ɗaya sannan ango ya shigo gidan, Salma na jiyo haniyar su har suka gama duk abinda zasu yi.na al'ada sannan aka yi addu'a aka watse.

Nan Ango yace; "amarya tashi kiyi alwala muyi sallah", kasancewar ba yarinyar bace ta san hakan babu musu ta tashi tayo alwala.

Sai da suka gabatar da sallah raka'a biyu nan yayi addu'ar da manzon Allah ya koyar sannan ya tambaye ta game da addinin ta babu laifi ta ɗan bashi amsa.

Yayi.murmushi yana me tuna lokacin da suke amare shida Salmar shi yadda ta amsa mishi tambayoyin cike da birgewa da kuma nutsuwa.

Ya riƙo hannun Jameelar yace; "zo muje wajen Auntyn ki", Jameelar kam haushi taji sosai amma ta dake tace; "to muje", ya ɗauko ɗaya daga cikin ledojin dake ajiye a saman center table kana suka fice.

Da sallama suka shiga ɗakin, ganin haske a ciki ya tabbatar mishi da cewa idanun Salmar biyu, ya kalli Jameelar yace; "zauna anan bari na shiga na kira ta", Jameela ta taɓe baki sannan ta zauna yayin da shi kuma ya shiga don kiran Salmar.

A Zaune a saman gado ya same ta , ta zuba tagumi yayin da Fatima da Fiddausi ke fama barci abin su hankali kwance.

Yadda ya ganta ba ƙaramin tausayi ta bashi ba, yana yin sallama ta ɗago ta kalle shi sannan ta amsa.

"kizo falo ina son ganin ki", be jira cewar ta ba ya fito itama kuma bata ce komai ba ta miƙe ta biyo bayan shi gaban ta yana faɗuwa.

Koda ta fito kan amaryar yana sauke a ƙasa dan haka bata ganin ko fuskar wacece, Salma taje ta zauna saman one seater, Abdulkareem yayi addu'a sannan ya ɗora da yi musu nasiha akan su zauna lafiya ya kuma ce jameela itace ƙarama dan haka ta girmama Salma yayin da yace Salma ita kuma ta kama girmanta sannan ta su.riƙe juna amana babu wacce tafi wani a wajen shi duka so da ƙauna ne ya haɗa su kuma dukan su so iri ɗaya yake yi musu su zauna lafiya.

"sannan batun kwana ya kuke ganin za'a dinga yi", Salma tace; "ta zaɓa duk yadda ta zaɓa shikenan".

Abdul yace; "a'a kece babba dan haka ke ya kamata ki zaɓa", Salma tace; "shikenan bibbiyu ina ganin hakan yayi ai?".

Abdul yace; "to kamar yadda addini ya tanadar budurwa ana yi mata sati ɗaya ne bazawara kuma kwana uku, don haka zan yi mata kwana uku tukunna sai kuma a koma kwana bibbiyu, Amarya ke hakan yayi miki?".

Jameela tace; "eh yayi tunda haka ta zaɓa a barshi a hakan amma da sai nace kwana biyu gaskiya yayi.mini yawa dan ba zan iya jure rashin miji na a kusa dani ba har tsayin kwana biyu bayan na san can inda yake ba wai kula yake samu ba".

Dum gaban Salma ya faɗi, dan tabbas muryar Jameela take jiyowa idan har kunnen ta ba ƙarya yake yi mata, Abdul kuwa kasa cewa komai yayi fatan shi ɗaya kada Salma ta tanka dan baya so su fara hayaniya tun yanzu dan haka ƙoƙarin shi na kauda maganar yasa ya miƙe sannan yace; "taso muje".

Jameela har ta miƙe Salma tayi sauri ƙarasawa gaban ta, ta ɗaga mayafin data rufe fuskar ta dashi, cikin kiɗima da mamaki tare da ruɗewa tace; "Jameela!!!! Kece matar da miji na ya aura yau, Jameela kece kika aure mini miji??".

Jameela tayi wani munafikin murmushi tace; "nice mana Ƙawata Aminiya ta ya san ranki, ai dama nace miki zan zo.miki da abin mamaki ya kika gani?".




~_From The Everlasting Golden Pen 🖊 of Golden Pen Writers Association Team! Of MENENE RIBA TA & ALLAH GATAN MARAYA_~



© *2020*



_~We Love U All~_❤

[15/03, 09:08] Yaya Umar: 🤷‍♀🤷‍♀🤷


*_MENENE RIBA TA ❓_*

🙆🙆🙆


© *2020*


🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀🤦🏻‍♀

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/





*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*


*~We are bearer's of so golden pen🖊~*
*~we write assidiously perceive no pain~.*
*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*
*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*



On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said: I heard the Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) say:

"The first of people against whom judgment will be pronounced on the Day of Resurrection will be a man who died a martyr. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I fought for You until I died a martyr.' He will say: 'You have lied - you did but fight that it might be said [of you]: 'He is courageous.'' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man who has studied [religious] knowledge and has taught it and who used to recite the Qur'an. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I studied [religious] knowledge and I taught it and I recited the Qur'an for Your sake.' He will say: 'You have lied - you did but study [religious] knowledge that it might be said [of you]: 'He is learned.'' And you recited the Qur'an that it might be said [of you]: 'He is a reciter.' And so it was said. Then he will be ordered to be dragged along on his face until he is cast into Hell-fire. [Another] will be a man whom Allah had made rich and to whom He had given all kinds of wealth. He will be brought and Allah will make known to him His favours and he will recognize them. [The Almighty] will say: 'And what did you do about them?' He will say: 'I left no path

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login