Showing 1 words to 3000 words out of 110329 words

Chapter 1 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7489

+++++++ YARENA ADDININA +++++++
FARKON LABARI


Garin Doko gari ne mai yalwar jama'a masu sana'u daban-daban wasu Manoma, wasu *yan kasuwa suna yawan zuwa cin kasuwanni a garuruwa daban-daban. *Yan garin yaren Hausa suke yi saboda haka Hausawa ne yawancinsu, sai wasu kadan Fulani a garin. Garin yana karkashin karamar hukumar Garki dake Jihar Jigawa.
Yau daren goma sha hudu don haka garin ya gauraye da hasken farin wata, ko kwandalarka ce ta fadi a kasa zaka iya ganinta saboda hasken farin wata. Matasan Samari da *yan mata wadanda shekarunsu basu wuce goma zuwa goma sha biyar ba sune suke shawagi suna tsalle-tsalle suna wasanni kala-kala da alama suna jin dadin yanayin garin a yau. Ga hasken wata tar ga wata iska mai sanyi na kadawa.
Suhaif saurayin da babu mai iliminsa, kyau, nutsuwa, hankali da tsantsar iya kwalliya da gayu, yana fitowa daga gidan Kakarsa sai ya tsinci kansa da samun wani dan dakali a kofar gidan ya zauna yana kallon yaran da suke wasanni kala-kala yana murmushi shi kadai. Yana tuna baya lokacin da suke kamar haka suma sunyi duk irin wannan. *Yan maza suna wasan langa, wasu na wasan *yar buya. *Yan mata kuma gada suke yi. Wata zabiyar yarinya ce mai zazzakar murya ta ware murya ta fara rero waken gada ta ce.
"Uwar miji ta zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Uban miji ya zagen na durkusa ina ta neman gafara.
Da kishiya ta zagen na lillisata na kaita Ofishin *yan sanda sun lillisata sun juyata sun kaita lahira sai gata a duniya.
Iyaraye nanaye aiye raye iye nanaye *yan mata.


Dariya ta kubcewa Suhaif ya fada a bayyane ya ce "Kai mata, mace bata son kishiya. Sai ga dandazon mata *yan kai amarya sunzo wucewa za'a kai amarya gidan mijinta. Mata dauke da kwallayen alkaki da nakiya na gara. Wata guda daya daga cikinsu ta goya amarya a baya, sai rera waka kawayen amarya suke yi. Suhaif ya bisu da kallo har suka wuce. Gefensa kuma wata kanwarsa ce (cousin) dinsa mai suna *Yar Hajja tana zaune da fitila a gabanta tana sayar da kwai ana *yar fashe, duk wanda aka fasa nasa an cinye shi sai ya bawa wanda ya fasa kwan ya cinye. *Yar Hajja ta ware murya ta rada tallar gyada da karfi ta ce
"Ta soyu da manda rangadau.
Tayi arewa da filin dakata amaro,
Sai ta sake rerowa,
"Goro goriye goro daushe, goro dan Kano dan Kaduna wanda bai ci ba yaci sabo.


Cikin tsokana Suhaif ya ce da ita "Ke zabiya rufe bakin kar sauro ya fada miki. *Yar Hajja uwar son kudi bayan tallar Koko da kike da safe, kiyi ta dan wake da rana da daddare ma sai kin sayar da goro da Kwai da gyada amaro. Bari inzo inci alakoro. Ya taso ya zo gaban farantin *Yar Hajja ya tsaya. "Yar Hajja ta ce "A'a bana bayar da alakoro sai dai ka saya, wallahi Babangida ka cika son kudi duk kudin da kake jidowa idan kaje Kano kace baza ka saya ba sai dai alakoro kai ko tausayina baka ji. Suhaif ya kyalkyale da dariya ya ce "Kaji ta wai kudin da nake jidowa a Kano kamar wani barawo, kudin ma jido shi ake yi a Kano? Ai kin fini son kudi, lashe money sunanki fa. Ya kai hannu zai dauki kwai daya sai *Yar Hajja ta janye farantin ta ce "Wannan Kwan nawa ne na kashin kaina amma gyada da goro na Hajja ne kakata kuma kakarka ce babu abin da zata ce maka. Ya ce "Ni ai ba tsoho bane bana cin goro. Bana cin gyada kuma tunda ni ba mayunwaci ba ne kwai ni zanci. *Yar Hajja ta dauko kwai daya ta mika masa, ya karba ya mikawa wani yaro a kusa dashi. Sai ya fisgo kwan gaba daya farantin ya ce da yaran dake wajen "Ku shirya yanzu zan rarraba muku kwai ku ci kyauta sai kuyi mata wakar yayi kwantai. *Yar Hajja ta fashe da kuka ta tashi da gudu zata shiga gida taje ta fadawa kakarsu cewar ga Suhaif nan zai rabar mata da kwanta. Suhaif ya kwalla mata kira ya ce tazo ta karbi kudin kwanta zai siye ya bata kudinta. Ta dawo tasha kunu ta rike kugu. Ya zaro *yan dari-dari guda uku sababbi fil ya mika mata ya ce "Kudin kwan nawa ne? Nasan baifi dari biyu ba ga dari uku nan ki rike, uwar son kudi. Ta kyalkyale da dariya ta rafsa buda tana murna ya saye kwan duka harma ya kara mata kudin. Suhaif ya dinga rabawa *yan mata da yaran dake zazzaune a zagaye da fitilar *Yar Hajja kowacce ya mika mata sai farinciki ya rufeta daya bayan daya yake binsu. Daga karshe sai ya hango wata budurwar yarinya a can gefe a zaune da jakar kayanta a gabanta. Ya ce "Waccan kuma wacece ta tafi gefe ta zauna ita kadai? *Yar Hajja ta ce "Mu ma bamu santa ba, bamu taba ganinta a garin nan ba, tun dazu tazo ta sauna tana kallon mu. Munyi mata magana tayi shiru. Suhaif ya karasa gareta, ya mika mata sauran kwan dake hannunsa guda biyu. Tasa hannu ta karba. *Yar Hajja ta dauko fitila da sauri ta zo tana haska wannan baiwar Allah, sai taja mayafinta ta rufe fuskarta, Suhaif ya yiwa *Yar Hajja tsawa ya ce ta daina haskata sannan ta tafi da fitilar. Suhaif ya durkusa a gabanta ya ce "Yan mata ya sunanki ne? Ta yi shiru bata amsa ba. Ya sake cewa bamu sanki a garin nan ba, haka baki yi kama da *yan garin nan ba. Daga wanne gari kika zo? Tayi shiru bata amsa ba. Yana shirin jeho mata tambaya ta uku sai yaji ta rushe da kuka mai tsanani. Yaji hankalinsa ya tashi ya hau lallashinta yana cewa "Daina kuka Allah Ya baki hakuri na daina tambayar ki. Can da kukan ya tsagaita sai ta dago da wasu dara-daran idanuwanta farare sol ta dube shi cikin wata sanyayyiyar murya ta ce "Ina so insha ruwa ko zaka taimake ni da ruwa? Ya ce "Zan taimake ki da ruwan sha *yar uwata. Ya tsura mata ido yana kallonta yana mata murmushi, sai ta sunkuyar da kai kasa. Ya kwallawa *Yar Hajja kira ya ce taje cikin gida ta dauko kwanan shan ruwan Hajja Kakarsu sabo, ta kawo masa ruwan sha mai sanyi na tulu. *Yar Hajja ta tashi ta nufi gida don dauko ruwan sha.
Suhaif ya sake duban Yarinyar ya ce "Idan na taimake ki da ruwan sha, zaki taimakeni ki fada mun sunanki da kuma inda kika fito? Ta gyada kai kai tana jujjuya kwai biyun dake hannunta. Ya nisa ya ce "Kawo kwayayen in bare miki. Ta mika masa ba tare da ta kalleshi ba. Kafin ya gama barewa *Yar Hajja ta kawo ruwa a cikin kwanan sha, mai sanyi kuwa tamkar daga firij ya karba ya mika mata. Lallai ta kwaso kishirwa kusan kwanan shan duka ta shanye, kadan ta rage. Ya mika mata kwan sai yaga ta karba tana ci bayan kishirwar data kwaso da alama akwai jin yunwa ma a tare da ita. Suhaif ya ce "Gashi kuwa kwan ya kare dana suyo miki wani sai dai gyada da goro. Ta girgiza kai ta ce "Ya isa na gode. Har yanzu a durkushe yake a gabanta. Ya nisa ya ce "Ina jiran amsar tambayata. Tayi narai-narai da ido ta ce "Sunana Fatima ana cemin Iman. Daga tashar *Yankaba na hau motar Gumel, kudin motata bai cika ba shine masu motar suka saukeni anan garin suka ce anan kudina ya kare. Ya ce "Ke kuma Gumel kike so kije suka sauke ki anan Doko? Yanzu idan aka baki kudin motar zuwa Gumel shi kenan matsalarki? Iman ta rushe da kuka ta ce "Gumel din ma idan naje bansan inda zani ba, bansan kowa ba kuma. Suhaif ya gyara tsugunansa ya ce "Iman ban gane ba, baki san inda zaki ba kenan? Ta kara rushewa da kuka mai tsanani tana cewa "Ban san in da zani ba, ban san kowa ba a duniyar nan. Ya bude baki yana mamaki can ya ce "Iman yi shiru ki daina kuka in tambayeki. Ina Iyayenki? Cikin kuka ta ce "Ni a Makka a ka haife ni, uwata ta rasu kwanannan, ubana kuwa tun ana goyo na ya rasu. A Makka muke zaune, sune kadai suka rage min bansan danginsu ba. Shine askarawa masu kame a Makka suka kamoni. Suhaif ya girgiza kai cike da tausayi ya ce "Oh my God! Yi shiru Iman insha Allah zan taimakeki. To amma abunda ya daure mun kai shine daga jin Hausarki kun dade a Makka baku da takardar shaidar zama (igama)? Iman ta sharbe hawaye ta ce "Wahala da wulakanci nake sha tunda iyayena ba su bar min wata dukiya ba, aikin gidan larabawa suke yi kuma daman bamu da takardar zama, ina yawo askarawa suka kamani suka kawo mu kasar, bansan kowa ba a Nigeria. Kukan ya sake kece mata. Ya girgiza kai yayin da tausayinta ta sashi kwalla.
Ya nisa ya ce "Iyayenki *yan asalin wanne gari ne? Iman cikin shesshekar kuka ta ce "Sun ce su Fulanin Sokoto ne, Suhaif ya ce "Allah Sarki *yan Sokoto kuwa suna da kirki, zo in kaiki cikin gida wajen Kakata in shaida mata. Ya rike mata jakar kayanta tana biye dashi suka nufi cikin gidan. *Yar Hajja da kawayenta suka bi su Suhaif da kallo suna *yan gulmammakinsu. *Yar Hajja ta ce da kwayenta "Babangida zai kai mana wannan bakuwar gida karfa aljana ce ko mayya ta cinye mu cikin dare. Kwayenta suka ce "Wallahi, dan kuwa lokacin da kika haskata da fitila mun ganta kyakkyawa ce, kamar aljana don kyau. *Yar Hajja ta ce "Dalla, waye ya ce muku aljanu kyawawa ne? An ce har kaho garesu da kofato a kafarsu.
Suhaif na shiga suka iske Hajja Kakarsa a tsakar gida yayi sallama ya shiga. *Yar tsohuwa ta amsa ta ce "Wa nake ji kamar Babangida, dawowa kayi, tsokanar da kayi mun dazu bata isheka ba? Ya yi dan murmushi ya ce "Daman ban tafi ba ina kofar gida, Hajja ga wata marainiya na tsinto a kofar gidanki tana zaune tana kuka bata san kowa ba bata san inda zata ba. Iman shigo ki zauna akan tabarma. Hajja ta ce "Marainiya ka tsinta a kofar gidana? Suhaif ya ce "Gata kuwa kina ganin mu tare. Iman ta zo ta zauna a gefen Hajja ta duka ta gaisheta. Hajja ta amsa gami da sa hannu ta shafa kan Iman ta ce "In shafa kan marainiya in samu lada. Allah Sarki daga ina kike? Iman ta rushe da kuka mai cike da tausayi. Sai Suhaif ya fara bawa Kakarsa labarin Iman kamar yadda ta fada masa. Hajja ta ce "Sokoto, wai akwai nisa da sai kaje ka nemo *yan uwanta su taimaka su rike yarinyar nan, tunda babu iyayen a raye marainiya ce, su riketa tunda sune jininta. Suhaif ya ce "Ai Hajja babu zancen akaita a roke su tunda bata taba zuwa Nigeria ba a can aka haifeta bata san su ba. Kuma ko da ace tasan inda suke, yanzu duniyar nan mutane basa abu sabi Allah komai na ganin ido suke yi, sunga babu ran iyayenta wulakantata za su yi, yanzu idan muka ki riketa yaya za'ayi taje garin? Allah Ya kiyaye ai barin yarinya budurwa kamar wannan hatsari ne sai ta fada hanyar banza a garin ta sami abunda zata dinga cin abinci. Kawai ta zauna anan garin Allah Ya rayata, mu bama wulakanta *yan uwanmu Musulmai, muna son Musulmi kuma ko yaya yake. Hajja ta yi murmushi ta ce "Babangida sarkin zuciya har ranka ya baci yanzu ka farajin haushin danginta kenan? Bi a hankali Babangida kasan yaran yanzu wai so nake a bincika ko auren dole aka yi mata ta gudo kasan yaran nan basa so su fadi gaskiya. Iman ta rushe da kuka ta hau rantse-rantse ita ba auren dole za'ayi mata ba. Ta sake shaida musu bata san *yan uwanta ba, da taje wajensu. Da man kuma ita kadai iyayenta suka haifa don haka yanzu da ta taho ma babu mai nemanta. Suhaif ya ce "Hajja kinji ko, kinji wannan abun tausayi to yanzu tayaya zamu dauki yarinyar nan mu kaita inda bata san kowa ba? Ga Hausarta nan ma bata fita, babu alamar karya a labarin Iman. Iman ki kwantar da hankalinki kinzo gida, kinzo wajen mutanen da suke sonki. Mune danginki, zamu taimake ki insha Allah. Ta dago ta dubi Suhaif ta ce "Nagode madalla. Suhaif ya nisa ya ce "Babu komai Iman yanzu zan tafi in barki anan gidan zaki kwanta, gobe da safe zan dawo, Hajja ki bata tuwo taci don ta kwaso yunwa. Hajja ta ce "Ai dole ne yanzu zan zuba mata tuwo. Iman ta ce "Na gode madalla, sai dai kafin in ci abincin ina son inyi salloli tukunna. Suhaif ya nuna mata buta da bandaki, yayi musu sallama ya tafi.


Reedwan Suraj Isma'il




YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN


Suhaif na isa gida ya iske mahaifinsa Alh. Hayatu suna kofar gida a zaune shida wani bako yazo neman na cefane. Bayan ya gaishe su sai ya sami waje ya zauna a gefensu. Baba yace da Suhaif ya shiga ya aunowa wannan bawan Allah gero kwano uku Suhaif ya je ya auno ya kawo. Mahaifinsa ya hadawa mutumin da kudi dari biyu ya bashi, Mutumin yana ta godiya ya dauka ya tafi. Alh. Hayatu ya dubi Suhaif ya ce "Yaya na ganka duk kayi sanyi kalau kamar marar lafiya? Suhaif yayi murmushi ya ce "Lafiyata kalau Baba, sai dai ina tausayin yadda nan gaba talakawa zasu ci gaba da rayuwa a kasar nan. Yanzu Allah ne kadai Yasan yawan magidantan da suke cikin halin rashi ga iyali da yawa haka suke kwana da yunwa sabo da babu, sun buga ko ina basu samowa iyali komai ba, su kuma ba musakai ba ballantana suyi bara. Taimakon irin wadannan yana lada tunda baza su iya yawon bara ba, su kuwa musakai zasu iya bara a basu.
Alh. Hayat ya girgiza kai don tausayi ya ce "Hakane Suhaif, kasar nan sai addu'a, talaka yana wahala Allah Ya canja mana wannan rayuwa. Suhaif ya ce "Amin Baba, amma kaga da za'a sami iri-irinka, masu hali su dinga taimakawa marasa hali da kan musulmai ya hadu, sun so junansu musulmai, da masu yin bara sun rage bara. Abu ne mai wahala kaga wanda wanda ba Musulmi ba yana bara duk yawancin masu bara Hausawa ne kuma Musulmi kaga bama kishin YARENMU DA ADDINIMU. Amma sai kaga mai kudi ya tara abincin da zai iya ciyar da iyalinsa har tsawon shekaru, makwabcinsa kuwa bashi da ko kwayar shinkafa. Alh. Hayat ya yi murmushi ya ce rufin asiri dai Alhamdulillahi tunda duk shekara ina samun amfanin gona wanda zai isheni in ciyar da iyalina har wata shekarar, amma nima wataran na cefane sai mun harhada da mahaifiyarka da kai kanka dan abinda ka samo a Kano. Daman mutum ba zai ga Allah yayi masa wata baiwa ba sai ya dubi wanda yafi, amma muddin yana duban na sama dashi wanda suka fishi ba zai godewa Allah ba. Yanzu me yasa na dage na hakikance na ce sai kayi digiri? Duk garin nan waye ya taba wani karatu me zurfi kamarka? Ai dan a sami ilimi a garin wanda wataran in Allah Yasa ka zama wani kusa a gwamnati ka tuna da *yan garinku ka zo ka taimakemu. Dan haka abunda nake so da kai shine kaga ka gama karatunka na digiri kuma ka fito da sakamako mai kyau (First class). Bautar kasa ya rage muku kuje kuyi shikenan ka samu aiki ka fara. Duk garin da aka kai ka bautar kasa kaje babu komai dan ina jiyo ka rannan kana hira da dan uwanka Najib kana cewa idan ba Kaduna ba ko Kano aka kai ka babu in da zaka je kai baza kaje Kudu ba. Suhaif yayi murmushi ya ce "Baba ba kudun ne bana so ba, saboda bana so in shiga cikin mutanen da Yarena, addinina ya bambanta da nasu, kaga ko a B.U.K bana zama dasu a daki daya saboda bana sonsu suma basa son Bahaushe Musulmi. Baba kawai ka taya ni da addu'a Allah Yasa a kaini arewa. Alh. Hayatu ya ce "Zan taya ka da addu'a amma fa kai ka fada mun cewar *yan Kudu arewa ake turosu, *yan arewa kuma a kai su kudu sai dai idan mutum yayi sa'a. Ni dai ina baka shawara karka dauki wannan sanadiyyar raunana karatunka kace baza ka je bautar kasa ba dan an tura ka kudu. Ina da kyakkyawan zato a kanka Suhaif ka rike karatunka ka nemi aiki ka taimaki al'ummar garin nan, naga kana son taimako kana kishin Yarenka da Addininka.
Suhaif ya gyara zama ya ce "Baba ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, abunda duk kaga ina yi a wajenka nake koyi kamar son taimakawa mabukata da kishin YARE da ADDINI. Alh, Hayat yayi dariya ya ce "Ai shi yasa ake son iyaye su zamana masu kyakkyawar dabi'a don duk abinda suke yi shi *ya*yansu suke kwaikwaya, Allah yayi maka albarka ya taimakemu baki daya. Suhaif ya ce "Amin Baba, yanzu ma daga gidan Hajja nake naje gaisheta. To ina fitowa kofar gidan sai naga *yar Hajja da kwayenta a kofar gida suna sayar da goro da kwai. Suka nuna min wata yarinya bakuwa ce bata san kowa a garin nan ba tana kuka tana neman taimako bata san inda zata je bama. Da nayi mata tambayoyi sai ta ce ita marainiya ce bata da uwa bata da uba ita kadai kuma suka haifa. Danginta kakaf bata sansu ba Nigeria ma bata taba zuwa ba, a Makka aka haifeta shine aka kamota don bata da takardar zaman kasar ba tare da tasan inda zata je ba. Baba idan kaga yarinyar sai kayi mata kuka abun tausayi, shine na kaita gidan Hajja na ce su bata abinci ta kwana gobe inji shawarar da zaku yanke. Alh. Hayat yai shiru can ya ce "Suhaif waye ya ce maka ana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login