Showing 81001 words to 84000 words out of 110329 words
Chapter 28 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
komai ba dazu, kadan ka caccakula amma baka ci ba. Suhaif ya ce "Ban ci ba kuma bazan ci ba. Najib ya wuce kan tebur yana cin abincinsa, ya dauko waya ya dannan lambar abar kaunarsa Naja'at. Ya kashe murya ya kirata da sunan da ya saba kiranta "My life, ta amsa da "Na'am my heart. Suka rincabe da hirar soyayya kowannensu yana bayyana halin da yake ciki saboda rashin ganin dan uwansa. Suhaif ya tashi zaune yana sauraran Najib dake kan dinning area yana waya babu abinda ya fado masa sai dama shine da Iman.
Washe gari kamar yadda suka saba tunda la'asar suna Harami har bayan sallar isha'i, sannan suka fito suka nufi masaukinsu. Sun sha mamaki kafin su hau lift ta kaisu dakinsu sai suka iske Iman a reseption. Ba su gane ta ba sai da ta yaye bakin nikaf din da ta rufe fuskarta. Ta na murmushi ta ce "Sannunku da zuwa, na dan dade da zuwa, ince a can cikin Masallacin ku ke shi yasa baku fito da wuri ba ko? Najib ya ce "Wallahi muna can kusa da Liman shi yasa fitowa tayi mana wuya. Suhaif wanda ya zama tamkar wani gunki yana tsaye yana kallon Iman, idan zata kalleshi sai yayi sauri ya kawar da idonsa. Najib ya sami kujera ya zauna a gefen Iman. Suhaif kuwa sai ya wuce ya hau lift ya haye sama. Yana shiga dakin sai ya nufi gadonsa ya kwanta zuciyarsa cike da damuwa. Wato duk begen Iman da yake da bata nan, ashe wannan ba komai bane sai yanzu da ya ganta. Sonta ya karu a kokon zuciyarsa, haka bugun da zuciyarsa take abun ya kazanta. Hakika halin da Suhaif yake ciki abun a tausaya masa ne, kuma abun a tsorata masa halin da zai shiga nan gaba idan ya rasa Iman har abada.
Najib bai shigo daki ba sai bayan awa guda, tunani ya ishi Suhaif da mamakin wai shin ina Najib ya zauna haka? Ko ya bi Iman gidansu ne? To ita Iman din me ya kawota Hotel din da suke? Najib na shigowa dakin, Suhaif yayi zunbur ya mike tsaye ya tari Najib yana tambayarsa "A ina ka tsaya ka dade? Ina Iman din take? Najib ya samu abinda yake so, so yake Suhaif ya dinga tambayarsa, yana ta binsa ya bashi labarin yadda suka yi da Iman, shi kuma yana sharewa yana basarwa yana ja masa rai. Lallai badan labarin Iman za'a bawa Suhaif ba da har abada ba zai sake tambayar Najib ba. Najib ya shiga wanka ya fito ya dauki waya ya buga kicin ya fadi irin abincin da za'ayi musu odar. Sannan ya juya ya kalli Suhaif wanda ya na zaune yayi tsuru yana kallon Najib. Tausayinsa ya rufe Najib ganin yadda ya zaku yana jira a bashi labarin Iman. Da Najib zai cewa Suhaif sai ya bashi guzirinsa gaba daya, ko tantama babu Suhaif zai bayar da duk abinda yake da shi don a bashi labarin Iman.
Najib ya ce "Ai na dauka baka son labarin Iman saboda wulakancin da kayi mata kamar baka son ka kara ganinta a rayuwarka. Ka haye sama ko magana baka amsa mata ba. Ban ji dadi ba nima balle kuma ita, har kuka tayi. Ta shaidamun saboda kai ta zo amma ta fuskanci yanzu baka son ganinta, Suhaif ya zabura ya ce "Saboda ni ta zo, da gaske haka ta ce? Najib ya ce "Of course, da saboda ni ta zo? Suhaif ya yi ajiyar zuciyar zuciya ya ce "Me ta ce? Najib ya ce "Ta zo kawai mu gaisa ne, sai kuma ta tambayeni da gaske har yanzu baka yi aure ba kuma saboda me baka yi aure ba har yanzu? Shine nace mata lokaci ne baiyi ba. Suhaif ya zabura ya mike tsaye ya rufe Najib da fada yana cewa dan me yasa bai fada mata cewar ita yake jiraba dalilin da yasa bai auri wata ba? Najib ya ce "Naga kamar za'a fasa mata kai, kai kasan mata. Ko kanta zai ragargaje karewar fashewa ka fada mata haka, tasan ina sonta dan haka ba abun kunya bane dan Iman tasan banyi aure ba saboda jiranta. Najib ya ce "To sai hakuri, ni dai boye mata nayi, duk tambayar da ta yi min sai ince ba haka bane ban nuna mata kana sonta ba har yanzu. Suhaif ya dakawa Najib tsawa ya ce "Malam ka rufemin baki kawai ka cuceni, idan gani kake ka karamin aji, to zubar min da aji kayi, najib ya mike ya nufi darning table daman har ma'aikata sun jera musu abinci, najib ya ce "Kasan zanyi maka shirme dan me yasa baka tsaya kai da ita kunyi magana ba? Ita ai kai take so kuyi magana a rashinka ne ta fada min abunda take so taji. Ni kuma gani nayi an gama maganar aurenta da Huzaifa babu makawa auren za'ayi tun da gashi nan zasu dunguma suje ayi biki, na ga babu fa'ida da zan zubar maka da aji, ince sonta ne ya hana ka aure har yanzu, tunda da tana sonka yadda kake sonta da bata amsawa wani ba, ko da yake Huzaifa ma ba wani bane shima yayi mata halacci a rayuwarta. Yanzu dai ka zo mu ci abinci sai in rakaka gidan da take ko kuma ga nunbar wayarta mu kirata mu gyara bayani. Suhaif yayi dogon tsaki ya ce "Na ce ka rabu dani bana son bayaninka, da wata banzar shawararka wacce ba zata amfane ni ba yanzu. Najib ya dauko waya ya bugawa matarsa Naja'at yayin da ya make murya ya ce "My life ya kika yini yau? Suhaif ya zo a fusace ya fusge wayar ya kashe ya ce "Ba zaka yi wayar ba kaji idan da dadi. Dariya ta kubucewa Najib ya girgiza kai yace "Allah Yasa Iman matarka ce ko muma ma huta.
Suhaif da dan Uwansa Najib basu fasa nafilfili ba da dawafi suna addu'ar Allah Ya zaba abunda yafi alheri tsakanin Suhaif da Iman. Har ranar da su Huzaifa suka zo suka dauke su zuwa filin jirgi. Tun bayan da Suhaif ya gaishe da Huzaifa da El-Sadik, Iman ma da matar Huzaifa suka gaishe shi, Suhaif bai sake cewa komai ba har suka shiga jirgi. Ya tafi can nesa ya samu kusa da wani ya zauna. Najib da Huzaifa ne suka zauna kujera daya, Iman da matar Huzaifa a bayansu sai Fatima da Huzaifa *ya*yan Huzaifa suma an balla musu belt din kujeru suna zaune a bayan kujerun su Iman. Har zuka iso Abuja Suhaif bai ce uffan ba haka ko kallon abincin da ake rabawa a jirgi baiyi ba. Zuciyarsa ta nausa ta tafi uwa duniya tana tunanin Iman. Haka Iman ta kasance bata magana sosai saboda damuwar da ta shiga ganin yadda taga Suhaif yana damuwa, ta rasa abun da yake damunsa ga Najib ya ce ba damuwar rashin aurenta ba ya shiga. Tasan Suhaif, tasan halinsa ba haka yake ba ada.
Najib da Huzaifa kuwa hira ce ta rincabe a tsakaninsu suna yi suna kyalkyala dariya suna tafawa kamar da can sun san juna. Har mutanen jirgin duk suka yi shiru sai su kadai suke magana. Ko gyangyadi basu yi ba suna labari har aka iso Abuja. Bayan doguwar mota ta debe su daga bakin jirgi zuwa arrival. Huzaifa yana kokarin saka layinsa na Nigeria ya kira kanwarsa Bilkisu zata aiko da direba ya zo ya daukesu. Sai Najib ya hana shi ya ce ya bari sunyi waya tun kafin su taso, za'a zo da motoci a daukesu tun da tsakar dare ne sai su kwana a gidansu washe gari sai a kaisu inda zasu je. Huzaifa yaje ya sanarwa Iman abunda Najib ya ce, tayi murmushi ta ce ba komai su je su kwana gobe sai su je gidan Bilkisu kanwarsa din.
Motoci guda hudu na alfarma ne suka biyo layi suka zo taryar uban gidansu Suhaif. Tun daga nan Iman da Huzaifa suka fara mamaki kafin suga gidan da za'a kaisu. Sun sha matukar mamaki a lokacin da suka gansu a cikin katafaren gidan Suhaif wanda kirarsa da zubinsa irin na turawane tamkar a America. Amma ba su tantance gidan na Suhaif ne ko na Najib ne. Najib ya kai Huzaifa wani bangare a gidan masaukinsa, ya dawo ya kai Iman da matar Huzaifa da yaran bangaransu. A cikin gidan suke su duka amma wani ba zai ga wani ba saboda girman gidan. Kowanne bangaren yana dauke da tafka-tafkan falo mai dauke da maka-makan bandakuna na alfarma. Lallai gidan Suhaif gida ne kayataccen gaske, ko daga wacce kasa kake sai ka dubeshi ka sake duba, kuma da wuya idan baka ga abunda baka taba gani ba. Iman ta kwana tana tunani ko wannan gidan waye a cikinsu amma bashi ya fi damunta ba irin halin damuwa da Suhaif yake ciki har yaki ya kulata balle ya dubi inda take har yayi mata magana.
Washegari da safe Najib yaje bangaren Huzaifa ya kwankwasa kofa, bayan ya bude sai ya shiga suka gaisa ya ce idan ya kintsa ya fito babban falo zasu karya kumallo. Najib ya fito ya nufi bangaren su Iman, nan ma Iman ce ta leko bayan sun gaisa ya ce suna jiransu a babban falo idan sun kintsa su zo suci abinci, ta amsa da "To gamu nan zuwa. Najib ya wuce bangaren maigida Suhaif dan shima a bangare daban ya kwana. Najib ya shiga ya iske shi a zaune a falo yana kallo da alama ya dade da tashi daga bacci. Bayan Najib yayi masa sallama, Suhaif ya amsa. Ya mika masa hannu suka gaisa sai ya sanar da shi ya fito falo za'a hadu a ci abinci. Suhaif ya dan yatsine fuska ya ce "Bana jin zan iya cin komai yau. Najib ya zauna a kan kujerar dake fuskantar Suhaif ya ce "Gaskiya Suhaif bai dace irin wannan basarwar da shariya da kake yiwa wadannan bayin Allah ba, idan kayi musu haka a Makka amma nan gidanka suka zo. Ba su san maye a ranka ba, basu yi maka laifi ba, to meyasa ba zaka daure zuciyarka ba don karsu dauki wani abu a ransu. Ko baka ci dole ka zauna ayi wasa da dariya, kuma lallai-lallai dole muje Jalingo bikinsu, ka dauki kaddara matar mutum kabarinsa. Hakika abun da Najib ya fada gaskiya ne amma fa bugun da zuciyata take yi, tsananin bakin cikin daya addabeni ba zai bari in zauna a tsakiyar Huzaifa da Iman ina kallonsu ba. Suhaif yake tunani a zuciyarsa. Najib ya katse shi ya ci gaba da cewa "Zancen wasa ya wuce ina gaya maka gaskiya da gaskiya nasan yadda kake ji, duk wani masoyinka zai jiye maka, amma ikon Allah Ya wuce haka, duk yadda Allah Ya so haka ya keyi da bayinsa, ka zubawa Sarautar Allah ido kaga irin matar da zai sauya maka a madadin Iman. Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya mike tsaye ya dafa kafadar Najib ya ce "Na ji abun da ka fada, mu je falon ba komai.
Cab! Allah Ya kiyaye,,,, gaskiya soyayya wata wahala ce babba, hmm *
Reedwan Suraj Isma'il
::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Sun isa falon da yake dauke da tafkeken dining area me kunshe da zungureren table da kujerunsa. Huzaifa kawai suka iske ya iso, Suhaif cikin fara'a ya mika masa hannu suka gaisa. Suhaif ya ce "Jiya ina jinku a jirgi kuna ta hira ciwon kai ya hanani magana. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Ayya! Allah Ya sawake, wallahi ban sani ba, kuma Najib bai fadamin ba da nayi maka sannu. Yaya ciwon kan yanzu? Suhaif ya ce "A'a yanzu na warke da nayi bacci. Huzaifa ya ce "Alhamdulillahi Allah Ya sawake. Shigowar su Iman ce ta katsesu sai dukkansu hankalinsu ya koma ga duban bakin kofa suga masu shigowa. Iman da matar Huzaifa dukkansu suna sunke a cikin burgujejiyar bakar riga daga sama har kasa amma yau basu saka nikaf ba fuskokinsu a bude. Fatima da Huzaifa suma fes dasu Iman tayi musu wanka ta caba musu ado da wandon jeans da riga shirt iri daya banbancin kawai ta Fatima anyi adon irin na mata a jiki na Huzaifa kuwa anyi ado irin na maza. Yaran kyawawan larabawa ne babu abu daya da zaka gani a halittarsu kace sun hada jini da bakar fata, duk da dai namijin kamarsu daya da Mahaifinsa amma gashinsa da fatar duk na larabawa ne.
Suhaif ya fara dimaucewa yana kokarin rikicewa irin wacce ya saba yi idan suka hadu da Iman. Yayi yaki da zuciyarsa ya daure ya saki ransa kamar baya jin komai. Iman ta dubi angonta Huzaifa wanda tun shigowarsu ya zuba mata ido, ta gaishe shi da larabci, matarsa taje ta rungumeshi sannan ta sumbaci kumatunsa yaransa ba irin gaisuwar da suka yi masa kenan. Ya yiwa yaran magana da fulatanci ya ce su je su gaishe da su Suhaif. Fatima da Huzaifa suka je suka yi musu sallama suka mika musu hannu suka gaisa. Matar Huzaifa ma ta dubi su Suhaif tayi murmushi tayi musu sallama, suka amsa cikin fara'a. Iman ta karasa kusa da Najib ta gaishe shi tana mai fargabar gaishe da Suhaif tana gudun kada yaki amsawa. Suhaif ya katse kokonta ya ce mata "Amarya Iman ina kwana. Sai abun ya basu mamaki da dariya ita da Najib. Ta ce "Amarya Iman ka saka min? Huzaifa ya ce "Ai kuwa sunan yayi dadi daga yanzu ma Amarya Iman zan dinga kiranki. Wai shin ina kika samo suna Iman ne? Sunan yayi min dadi tun ran nan nake tambayarki baki fada min ba. Iman ta dubi Najib ta juya ta dubi Suhaif, yayin da su duka suka zuba mata ido tayi murmushi ta ce da Huzaifa "Tambayi Yaya Suhaif ko Yaya Najib. Sai su duka suka kyalkyale da dariya suka dunguma kan teburin cin abinci. Irin kayan alatun da aka jera yafi karfin cikin mutane shida, mutane ashirin zasu iya ci su koshi su rage, babu abin da babu kai har da dumamen tuwo miyar kuka duk an hado musu sai wanda kake so zaka zaba. A waya Suhaif ya zanowa Kukunsa abubuwan da zasu daddafa tun jiya da daddare suke aiki har wayewar garin yau. Lallai kuwa wannan kayataccen Breakfast ya burge wadanda aka yi dominsu.
Suhaif yana dan cin abinci duk da dakyar yake iya hadiyewa saboda kallon soyayyar daya fuskanci Huzaifa yana yiwa Iman. Ita kuwa kanta a sunkuye a kasa ta kasa kallon kowannensu. Suhaif ya fake da yiwa yara wasa da yake Babansu ya koya musu turanci da fulatanci don haka da turanci Suhaif yake musu magana. Najib da Huzaifa sun barke da hirar da suka saba yi tun jiya, hirar dai bata wuce halin wahala da talauci da masu mulkin kasashe suka jefa talakawansu ba. Iman da matar Huzaifa suma sun juya harshe suna ta larabci. Haka suka kasance suna cin abinci amma kowa da abokin hirarsa. Bayan sun gama sai suka dunguma zuwa kujerun falo inda suka zazzauna. Wayar Huzaifa tayi kara kanwarsa ce Bilkisu. Bayan ta gaishe shi cikin yarensu fulatanci ta shiga nuna bacin ranta da damuwa akan kin zuwansu jiya. Ta ce har sha biyun dare ta hana direbanta tafiya dan yaje ya daukosu idan sun karaso amma taji shiru. Yanzu ma kamar da wasa ta gwada lambar taji ta shiga, wato da bata kira ba ma baza su bugo suce mata sun karaso ba ko? Huzaifa sai dariya yake yi ya dannan speaker yadda Iman zaya ji. Ya ce da kanwarsa "To kin gama tutsiyeni? Ga Iman tana jinki ita zata baki amsa. Iman ta ce "Bilkisu kiyi hakuri, ba haka bane. Ai yanzu zamu zo. Bilkisu ya ce "Kuzo ina? Aini yanzu haka ma bana gida, gani nan har zamu shiga jirgi zan tafi Lagos. Huzaifa ya kashe speaker, ya tashi ya fito baranda suna magana da kanwarsa ta sirri. Matarsa ta bishi barandar bayan ya gama waya ya juyo ya dubeta ya kirata da sunan masoyiyarsa cikin harshen larabci ya tambayeta me yake damunta ne? Ta shakwakkwabe ta ce ta gaji duk jikinta ciwo yake, haka kirjinta yana mata ciwo. Yayi mata sannu yayin da ya jawota ya rungumeta. Ya jawo hannunta ya ce ta zo ya rakata daki ta kwanta ta huta yanzu zai fita zai sayo mata magani. Iman tayi-tayi da yaran su zo wajenta su zauna kada su dami Mahaifiyarsu, suka ki suka bi Mahaifiyarsu daki.
Bayan dan wani lokaci Huzaifa ya dawo ya ce da Najib "Bani mukullin mota zan je Gwarunfa yanzu zan dawo. Suhaif ya ce "Akwai direbobi a waje, mukullan motar na hannunsu ka zabi daya ya kaika. Huzaifa ya ce "Ba komai zan je da kaina, nima fa dan gari ne bazan bata ba. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Suhaif ya ce "Muje wajen motocin sai in karbar maka mukullin. Bayan Suhaif ya bawa Huzaifa mukullin motar, Huzaifa ya shiga suka yi sallama akan yanzu zai dawo ba dadewa zai yi ba sako kawai zai karbo.
Suhaif ya dade annan a tsaye ya rasa me yake yi masa dadi, hakika idan ya ci gaba da zama kusa da Iman zai iya kasa controlling kansa ya fadi abunda Huzaifa zai gane halin da yake ciki. Sai kawai ya yanke shawarar ba zai koma cikin gidan ba sai ya nufi katafaren lambun da yake bayan gidan, ya samu lungu ya zauna yana tunani. Najib da Iman ne kadai ke zaune a falo suna *yar hira. Iman ta ce "Ina Yaya Suhaif, ko ya bi Hamma Huzaifa ne? Najib ya ce "Anya, naga giftawar Huzaifa shi kadai ne a motar, bari in leka watakila ya tsaya da masu aiki ko direbobi suna lissafi. Najib ya leko farfajiyar gidan yaga babu kowa, sai ya dawo falo ya zauna. Ya dubi Iman ya ce "Baya area nan ban san inda ya kutsa ba, yayi wani bangaren. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Najib na tambayeka ka ki ka fadamin tsakani da Allah abunda yake damun Yaya Suhaif. Nasan dole akwai abunda yake damunsa, wallahi da kasan yadda na shiga damuwa da ka tausaya min. Ban san dalili ba tun ina Doko idan