Showing 102001 words to 105000 words out of 110329 words
Chapter 35 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
suna kanana. Salma ta gyara zama ta tsurawa Iman ido tana sauraranta cike da mamaki.
Iman ta ci gaba da cewa "Yanzu ma na zo ne mu gaisa tunda na zo garin. Salma ta ce "Ko zaki min dalla-dalla don in gane ki sosai? Iman ta ce "Maganar gaskiya nice na ajiye muku Muhammad, amma nasan nayi muku laifi ku yafe min, babu yadda zanyi a lokacin. Salma ta zabura ta tashi tsaye ta dafe kirji ta ce "Ke ce? Iman ta nisa ta ce "Labarine mai tsawo. Salma ta ce "To bari na taso mai gidana Ibrahim, yana bacci a daki wannan lamarin babba ne. Ta shiga daki bayan *yan mintina suka fito tare, a zabure ya fito.
Iman ta gaishe shi sai taga ya na mata kallon tara saura kwata ya amsa da kyar. Ta nisa ta ce "Dan Allah idan baza ku damu ba zan iya shigowa da mijina shima ayi maganar a gabansa? Matar ta ce "Kwarai kuwa ya shigo. Ibrahim ya ce "Bari na aika a kira su Malam Shehu tunda suna nan aka tsinci yaron duk a hadu aji labarin. Tunda sune shaidu. Iman da mijinta, haka ga Salma ga mijinta Ibrahim sannan ga Malam Shehu da sauran Jama'ar da suke nan ranar da aka tsinci dan. Aka cika falon ana sauraran Iman. Ta fara basu labari tun daga farkon yadda Harriet ta haifi yaron har ranar data yarda shi. Babu shakka duk yadda ta kwatanto yadda ta yar da dan haka ne babu karya. Sai suka tambayeta yanzu meke tafe da ita, da kuma dalilin zuwanta yanzu. Iman ta ce ta zo ta ganshi ne ta tabbatar da inda yake sannan ta nemi izini su yarde masa ta dinga zuwa ganinsa. Sai tausayinta ya rufe marikan yaron da sun dauka cewa zata yi zata dauke shi.
Iman taci gaba da cewa idan da hali tana son ta sami wasu su rakata a je wajen Mahaifin yaron a Baucji yaga Babansa saboda watarana. Suka amsa mata da "Haka ne gaskiya ne. Duk ba abun damuwa bane. Yata *yan makaranta sun taso sai surutunsu ake ji kafin su karaso. Iman ta baza idanuwanta gaba daya tana duban kofar shigowa tana so taga Muhammad dinta. Suka shigo kofar sai suka durkusa suka gaishe su dukkansu. Daga gani babu tambaya, babu wanda ya nuna mata shi ta gane shi. Kamar kaki Micheal yayi, kamarsu daya da Ubansa. Ya girma sosai gashi da tsaho kamar ubansa. Iman ta fashe da kuka, ta ce ya je wajenta su gaisa. Ya tsaya yana kallonta bai santa ba. Sai da Mamarsa Salma ta ce masa "Muhammad jeka ku gaisa da Aunty. Sanna ya je wajen Iman, ta rungume shi tana kuka. Iman ta tambaye shi da turanci ajinsa nawa a makarantar boko? Ya amsa mata ya ce "Primary 2. Ta tambaye shi shekarunsa nawa ya ce bakwai. Tayi masa larabci ta ce Islamiyya fa ajinsa nawa? Ya ce uku. Ta ce kur'ani izunsa nawa? Ya ce izufi biyar. Iman tayi dariya ta fada da Fulatanci "Kai Muhammad har ka yi izufi biyar? Malamin ajinsu yana wajen ya ce "Ai ma har ya rage yanzu a izufi goma yake. Muhammad yaro ne mai hazaka har tsallaken aji ake yi masa saboda kokarinsa. Kafin ya gama primary zai iya sauke Alkur'ani. Iman taji dadi ya rufeta.
Aisha da Abubakar sun girma ga kannensa nan kanana da aka haifa dukka maza. Iman ta dinga tunawa su Aisha tana cewa "Yanzu kun manta ni Mamar Muhammad da ku kace in ajiye muku shi kuna son kani. Aisha ta tuno amma Abubakar bai tuna ba saboda bashi da wayo a lokacin. Daga karshe Iman ta dauko musu kayan da ta kawo musu, alawa da biskit kala-kala na kasa shen waje da ta dawo. Suka hadu aka tsayar da shawarar gobe da sassafe su zasu zo su dauki Ibrahim, Malam shehu da shi Muhammad dina a tafi Bauchi wajen Micheal.
Washe gari da sassafe Iman da Suhaif suka shirya suka fito tafiya Bauchi. Suka biyo daukar su Muhammad. Iman na shiga gidan ta tarar an shirya su kawai suke jira. Suka dungumo suka fito wajen mota. Salma tayi musu rakiya duk jikinta yayi sanyi, hankalinta ya tashi gani take idan Mahaifin Muhammad ya ganshi zai dauke shi ya hana a dawo da shi. Iman ta lura da halin da Salma ke ciki sai ta shiga kwantar mata da hankali cewar babu matsala yadda suka dauki Muhammad yanzu haka in anjima zasu dawo mata da danta Insha-Allah. Sannan Salma ta saki ranta tayi murmushi ta ce "Allah Ya kiyaye hanya.
Suhaif ne yake tukawa, Iman a gaba. Ibrahim da Malam Shehu a baya Muhammad a tsakiyarsu a kujerun baya. Suka tafi, Salma da *ya*yanta suna daga musu hannu har suka yi nisa. Babu in da suka tsaya tunda suka fara tafiya sai a garin Bauchi. Bauchin Yakubu! Inji masu kirari. Iman ta shiga tunani ina zata fara neman Micheal a cikin garin nan, shi me gidaje kala-kala. Sai ta ce su fara zuwa gidansa na G.R.A kusa da gidan Gwamna. Tana nunawa Suhaif hanya har bakin get din gidan.
Iman ta fito daga mota tace su jira bari ta tambaya. Ta kwankwasa get, mai gadi ya fito da sauri ta karamar kofa dan yaga ko waye. Iman tayi murmushi ta gaishe shi ta ce "Dan Allah maigidan yana ciki? Ya ce "A'a ya tafi kasar waje da sabuwar amaryarsa yawon shakatawa, uwar gidansa ce kawai a ciki ita kuwa bama iya tunkararta saboda yanzu tana tsakiyar kishi sai ta huce a kanka. Kamar zata mare mu haka take mana, sai kace mu muka sa Alhaji yayi mata amarya. Iman ta ce Alhaji? Yaya sunan Alhajin ya ce "Alhaji Musa! Waye a garin nan baisan shi ba, ko dai batan kai kika yi? Iman ta ce "Ina mai ainihin gidan Micheal? Ya ce "Oh Micheal wannan tantirin yaron? Ai tuni ya tashi, ya sayar da gidan ko ince hukuma ta kwace gidan daya dunguma wani fashi aka kwace kadarorinsa. Iman ya ce "Yanzu a ina kake ganin zan iya ganinsa? Ya ce "Ke kuwa Hajiya ina kike neman kungurmin dan fashi, kina Musulma nai mutunci ko wani abu ya dunguma muku? Koda yake ba ruwana. Gaskiya idan na ce ga inda zaki ganshi nayi karya, don nima labarinsa nake ji ban sanshi ba. Iman tayi godiya ta shiga mota. Ta ce da Suhaif su tafi daya gidan nasa baya nan. Suna tafiya Iman tana hawaye idan ta waiga ta kalli dansa Muhammad, sai hawaye yayi ta zuba daga idanuwanta saboda tausayinsa. Suhaif yana kallonta ya rasa kalmar da zai fada mata da zata daina kuka. Yasan tausayin yaron take ji idan ta tuna da yadda aka same shi amma haka Allah Ya rubuto, uban wani baya haihuwar dan wani.
Duk in da Iman tasan gidan Micheal ne ta je sai su tarar an sayar da gidan wasu ne a ciki. Sun je gidajen abokansa gaba daya, suma ba sune a ciki ba. Daga karshe ta ce suje zaranda Hotel ko har yanzu yana zaman Hotel. Suka je, ma'aikatan Hotel suka duba sunayen Jama'ar dake ciki da lamabar dakunan da suke babu mai suna Micheal.
Hankalin Iman ya tashi kwarai, ita dama ace ta sami wanda ya sanshi ma ya bata labarin idan mutuwa yayi hankalinta zai fi kwanciya. Idan yaron ya girma a shaida masa Uwarsa da Ubansa sun mutu yafi sauki. Suna shiga mota zasu fita daga Hotel din sai ga wani wanda ta sani abokin Micheal ne sunansa Mansir. Yana tafe yana kallon Iman harda tuntube yana yi mata kallon sani. Iman ta fito daga mota da sauri ta kira sunansa. Nan da nan ya dawo wajen da take tsaye jikin mota. Ta ce "Mansir ne ko? Cike da mamaki ya ce "Ni ne kamar preety ce ko? Iman tayi murmushi ta ce "Ni ce. Sai ya girgiza kai yayi shiru hawaye yana zuba daga idanuwansa. Ya ce "Preety kinga yadda rayuwa ta zamar mana ko? Wato duk abokan mu da kika sani an harbesu. *Yan matanmu su Janet duk sun mutu. Irina da ba'a kamamu ba, mun tuba da fashi mun zama abun tausayi. Yanzu haka sana'ata haka rijiya da yasar masai ko kwata. Iman ta tambaye shi cike da fargaba ta ce "An kashe Micheal ma? Ya ce "Micheal ba'a kashe shi ba, amma wadanda aka kashe sun fishi kwanciyar hankali duk da ban san halinda suke ciki a can ba amma duk karshen mutum mutuwa kowa sai ya mutu. Gara ni dinnan da kika ganni da tsumma akan Micheal. Ni ina haka ana biyana shi ba zai iya ba saboda ya nakashe, ga shi ya tsiyace komai nasa ya kare. Kin sanshi mafadacine shine ya je Lagos ya yo tsokanar wasu gungun *yan fashi ko kudin da suka yi fashi ne ya kwashe ya hanasu? Ban dai sani ba shine suka biyo shi Bauchi zasu kashe shi basu same shi ba suka je suka kashe Mahaifiyarsa. Da yaga haka shima ya je yayi musu barna shine suka biyo shi suka sare masa kafa.
Ba na da lafiya ne kun ga labarin kadan yau, ina bukatar addu'ar ku.
Reedwan
===============YARENA ADDININA
CI GABAN LABARI
Iman ta runtse ido sai hawaye ya zubo ta ce "Yanzu ina Micheal din yake? Ya ce "Yana gidan Mahaifiyarsa, nan ne ba nisa cikin G.R.A nan yake. Ya zama tamkar tababbe babu shiga gidan, yanzu sai ya farfasa maka kwalba a kai, abincinsa giya da taba. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Mansir ka rakani, shi na zo nema garin. Mamaki marar misaltuwa a fuskar Mansir ya kalleta ya kalli *yan cikin motar da alama dai mai tukawar mijinta ne *yan bayan kuma Babanta da wanta. Me za su je wajen Micheal suyi? Mansir ke tambayar zuciyarsa. Ya ce "Ba matsala muje in kaiku. Ibrahim ya dora Muhammad akan cinyarsa suka matsawa Mansir ya shiga suka tafi yana nuna hanya har kofar gidan Mahaifiyar Micheal. Mansur ya ce "Ga gidan ni zan koma, shawarar da zan baku kuyi a hankali domin farfasa kai yake da kwalbar giya, ni bazan shiga ba.
Iman ta ce "Mansur ba zaka tafi ba ka dai tsaya tukunna. Zan baka linkin kudin da kake samu a rana idan kayi hakuri, ina so ka taimake ni kai ka san gidan nan da halin da Micheal ya ke ciki, yanzu yaya zamu yi mu ganshi? Mansir ya ce "Ba ki nayi ba Pretty amma me yasa kike so lallai-lallai sai kin ganshi mutumin daya zama haka? Iman ta nuna masa Muhammad ta ce "Kalli yaron sosai. Mansur ya zurawa Muhammad ido ya ce "Kai! Ai kamar su daya da Micheal sak. Iman ta ce "To dan sa ne. Cikin mamaki Mansur ya ce "Tare kuka haifa? Iman ta girgiza kai ta ce "Tare da Harriet suka Haifa amma ta mutu garin haihuwarsa ni na dauke shi, shine na zo in nunawa yaron Ubansa. Mansur ya ce "Kwanaki a garin nan naga Harrit din ai. Ko ba wannan kawar taki ba? Iman ta zabura ta dafa kirji ta ce "Kaga Harriet a ina? Kai Harriet ta mutu ba dai ita ka gani ba mai kama da ita dai. Ya ce "A'a ita ce. Ba ita ce bakatsiniyar nan ba yarinyar Gabriel da nake gidansa? Iman ta ce "Okey! Fadila zaka ce min. A ina ka ganta? Ya ce "Tayi aure harda *ya*yanta, naje gidan nayi musu haka, itama ita ta fara gane ni. Iman ta ce "Allah Sarki dan Allah ka kaini in ga Fadila idan mun gama da nan.
Suhaif, Ibrahim da Malam Shehu suna zaune a mota suna kallon Iman da Mansur suna sauraran abunda suke fada. Sai yanzu Suhaif yayi magana ya ce "Wai ku fada min yadda zamu shiga gidan mai fasa kai da kwalba. Iman ta ce "Yaya Suhaif ni da Mansur zamu shiga, ku jira mu anan. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Bana so ki shiga ki barmu mu maza mu shiga. Malam Shehu ya ce "Mu shiga kawai da ayar Allah ba zai iya daga kwalbar ba balle ya rotsawa wani kai.
Suka fito daga mota su duka suka dunguma cikin gidan. Mansur da Suhaif ne a gaba. Iman rike da hannun Muhammad a tsakiya. Malam Shehu da Ibrahim a baya kowa yana karanto addu'ar dake bakinsa. Suna tafe suna kalle-kalle, gida kamar babu bil'adama a ciki bayan dogayen ciyayin da suka rufe farfajiyar gidan, kofar shiga cikin gidan ma da kyar mutum zai samu ya shiga ciyayi sun yi tsawo kamar bishiyoyi. Suna shiga falon kuwa kujeru ne kowacce ta kalli kabilarta. Talabijin a kife a kasa T.B stand an rabata biyu. Yi suke suna waiwaye-waiwaye kada ya diro musu ta inda basu zata ba. Suka yi ta magana shiru, wannan ya ce Hello, wancan ya ce Hi, wannan ya ce ka fito kayi baki. Babu motsin kowa a gidan kamar ma babu mutum a gidan. Sai suka shiga bubbude kofofin dake falon suna lellekawa, dakuna ne da bandakai babu kowa a ciki sai yana da kura.
Mansur ya shiga kicin ya bude kofar store din kicin babu komai sai duhu ko tafin hannunka ba zaka iya gani ba. Su Suhaif a falo sai suka ji Mansir ya kwalla kara a lokacin da yaji an cafke shi. Suhaif Ibrahim da Malam Shehu suka kutsa cikin store da gudu sai suka ga Micheal ya shake Mansir a jikin bango yana shirin kwakwale masa makogaro. Nan dai maza suka saki karfi suna jan Micheal amma gamgam sun kasa fusge hannunsa daga wuyan Mansur. Kokari yake ma ya wawuro daya daga cikinsu ya hada ya matse.
Iman na falo rungume da Muhammad kam suka shige wani lungu sai sharbar kuka take. Taji shiru har yanzu ba su fito ba sai kakarin Mansir take ji kamar mai shirin tafiya lahira. Su Suhaif na cewa ja shi ta nan, rike hannun, a'a kafar za'a ja, sun kasa fisge Mansur daga hannun Micheal. Iman ta ce da Muhammad ya zauna a lungun kada ya fito, tana zuwa. Tun daga cikin store suka fito kicin ana ta dambe. Cikin rudani da tashin hankali Iman ta kuga da karfi ta ce "Micheal! Sake shi mana karka kashe shi. Micheal ya waiwayo da sauri ya dubi mai wannan muryar wacce tayi masa kama da muryar abar begensa Pretty. Sai kuwa yaga Pretty ce. Mansur da kansa ta fusge hannun Micheal daga wuyansa saboda Micheal yana ganin Iman sai jikinsa yayi sanyi. Sannan su Suhaif suka sake shi shima. Ya dade yana kallon Iman can ya ce "Pretty! Pretty!! Are you Pretty!!! Iman ta gyada kai ta ce "Yes I am. Micheal ya sulale ya zauna ya rike kai da alama tunani yake mai tsawo kansa ya daure. Mansur dai ido yayi masa jawur ya fita bakin baranda yana shan iska. Suhaif da Ibarahim suna tsaye suna kallon Ikon Allah. Malam Shehu kuwa yana jan carbi yana ta tofa addu'a kusurwa-kusurwar gidan.
Iman ta durkusa a gaban Micheal cikin harshen turanci ta fara yi masa nasiha da wa'azi mai ratsa jiki. Micheal ya kwalla kara ya daki wata dorowa ya ce "Ke rabu dani, bakya ganin yadda na zama? Zaki ce min in yi hakuri rayuwar duniya sai a hankali. Na saraki, na rasa dana, na zo na rasa Mahaifiyata. Bayan dukiyata da abokaina dana rasa na rasa kafa guda daya. Dan me zan dauki duniya a hankali? Yanzu na fara kisa, yanzu na fara datsewa jama'a kafa, kowa sai ya rasa kafa a garin nan. Iman ta ce "Micheal yi hakuri duniya a sannu a hankali ake bin ta kaga da ka dauketa da karfi shi yasa ta zo maka a haka. Idan kayi hakuri za ka ga rayuwarka ta gyaru ka dawo rayuwar farin ciki fiye da tada. Ya gallawa Iman wata uwar harara ya ce "Ki gaya min yadda rayuwar da zata dawomin? Ko kin fara dawo da matatattu duniya? Ko kina iya dawo min da kafata da aka gutsire aka yar? Ko zaki iya auran mahaukaci ki zauna da shi? Don ada da nake cikakken mutum ma kin kini balle yanzu. Wani dacin kishi ya darsu a zuciyar Suhaif.
Iman tayi murmushi ta ce "Duk wannan abubuwan da ka zano min amsar ita ce "A'a amma Allah Zai iya musanya maka da madadinsu gaba daya. Ya sake zabura ya fisgi kanannadadden gashin daya zama Dada saboda rashin aski ya ce "Da a ce wata ce bake ba, da yau sai na kasheta. Dan me zaki sani a gaba kina fada mun tatsuniya, dan kin daukeni mahaukaci ko? Kina so ki ce min zan iya samun wata uwar bayan uwata? Kina nufin zan sake samun wani sabon da bayan dana na wajenki daya mutu koma nace kika kashe min shi, daga baya na samu matsala likitoci sun ce bazan sake haihuwa ba. Na yi aure shekarun baya matar taga ba zata iya zama ba ta haihu ba ta gudu. Don haka karki sake kallona ki fada min wata maganar da hankali ba zai dauka ba, na san a bunda nake.
Iman ta fashe da kuka. Sai Micheal ya tsaya yana kallonta can ya tambayeta "Kuka kike yi? Me yasa kike kuka? Kina tausayina ne bayan kin ki ni da? Kin guje ni bakya sona, kece kika sakani a cikin wannan halin. Domin son da nake miki, dana aureki zaki iya canja ni. Pretty me kike so yanzu? Fadi meke tafe da ke? Kinzo kiga mahaukaci ne ki tafi? Ko wadannan mazan ne suka satoki yanzu in kashe su? Duk abunda kike so zan yi, fada min. Iman ta share hawaye ta ce "Gaba daya rayuwarka ce bana so kaci gaba da irinta. Ina so ka canja, ka dawo addinina, zaka ga yadda Allah zai canja maka rayuwarka. Micheal ya tuntsire da dariya ya ce "Addininki! Ni zaki fadawa addini? Kin manta Mahaifiyata shugaba ce a wajen bauta? Iman ta ce "Addinina ba addinin Mahaifiyarka ba. Micheal ya ce "Wannene addininki? Iman ta ce "Musulunci. Ya ce "Ke Musulma ce? Iman ta ce "Ni Musulma ce shi yasa kaga bana zina, bana shan giya, bana fashi saboda tsoron Allah. Addinin Musulunci ya haramta duk wannan. Micheal yayi shiru yana