Showing 3001 words to 6000 words out of 110329 words
Chapter 2 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
irin wannan gangancin? Da daddaren nan ka tsinci yarinya ka dauke ta ka kaita gidan tsohuwa kace ta kwana, ba ka kaita gidan me gari ba shima idan yaga bazai iya riketa ba a kaita wajen hukuma su riketa. Bakasan duniya ta lalace ba, ka taimaki mutum shi kuma ya cuceka. Yanzu idan ka bibiya ma yarinyar karya take yi. Ko aure aka yi mata bata san mijin ta gudo. Suhaif ya ce "Baba ba haka bane duk wannan tambayoyin Hajja tayi mata nima nayi mata ta rantse ba auren dole aka yi mata ba. Kuma yarinyar kintsattsiyar yarinya ce Baba, ko daga maganarta zaka san yaran Hausa bai ishetaba, Baba Musulma ce tana neman taimako mu taimaketa mana. Yanzu idan muka kyaleta tayi gaba zata iya fadawa wani hannu a cuceta a matsayinta na mace budurwa akwai hatsari. Daga jin Hausarta zaka san ba girman nan ba ce. Alh. Hayat yayi shiru can ya nisa ya ce "Suhaif tunda kace haka na amince kaje ka taho da yarinyar nan gidan yanzu, don ba za'a bar tsohuwa ta kwana da wacce ba'a san asalinta ba, duniyar nan a bar tsoro ce. Ni kuma zan shiga gida in sanarwa Mahaifiyarka da kannanka kafin ku karaso.
Suhaif har zaiyi magana ya ce a bari sai gobe, sai yayi shiru ya amsawa mahaifinsa da "To madalla Allah Ya kara arziki da wadata. Ya tashi ya nufi gidan kakarsa, Babansa kuma ya shiga cikin gida.
Suhaif yayi sallama a gidan Hajja ya tarar da Iman ta gama cin tuwo tana wanke hannu, Hajja kuwa tana kishingide akan shinfidarta. Tana jin muryar Suhaif sai tayi zunbur ta tashi zaune ta ce "Muryar wa nake ji kamar Babangida, daman baka tafi ba ko dawowa kayi baka gama tsokanar daka saba bane? Suhaif yayi dariya yazo ya zauna a kusa da ita ya fara koro mata bayanai kamar yadda suka yi da Babansa a hankali suke maganar ba tare da sun bari Iman taji ba. "Zancen banza yarinya mai hankali da nutsuwa har na fara jin dadin zama da ita shine kake so ka dauke mun ita? Gata wayayyiya tafi *yar Hajja wayo ko talla suka je ba zata ajiye kayan tallar ba ta hau wasa da kawaye kamar yadda *yar Hajja take yimin. Suhaif ya kwashe da dariya ya ce "Ai ba'a yayin dorawa *yan mata talla yanzu Hajja, yayin karatun boko ake yi. Kinga Iman bata yi kama da *yan talla ba da mai ilimi take kama. Anyi-anyi kibar dorawa *yar hajja talla kinki, taci makarantar kwana anan Garki babu nisa kinki yarda a kaita ai lokaci zan samu inzo in sace ta in kaita makarantar dole ta zauna tayi karatu. Takaici ya hana Hajja yin magana saita gyara filo ta kwanta. Suhaif ya juya dubi ya dubi Iman wacce ta takure a gefe kan tabarmar da tayi sallah tana jan carbinta yayi murmushi ya ce "Iman ki dauko kayanki kizo mu tafi can giddanmu su Baba suna so su ganki ku gaisa. "Bata kara ko sakon daya ba ta tashi cikin ladabi gami da amsa masa ta nufi dakin da ta ajiye jakar kayanta ta fito. Suhaif ya mike tsaye yana yiwa Kakarsa sallama, kamar yadda ya sani daman baza ta amsa ba saboda tana jin haushin dauke Iman kuma yayi mata maganar makarantar *yar Hajja wacce da zarar yayi mata in ranta yayi dubu sai ya baci. Iman ma tazo ta durkusa a gaban Hajja tayi mata sallama gami da yin godiya, Hajja ta amsa dakyar. Suhaif fuskarsa cike da murmushi ya shige gaba Iman na biye da shi suka fice. Sun danyi nisa Suhaif ya juya ya kalli Iman ya ce "Af kawo jakar kayan in taya ki rikewa. Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Ka barshi nagode zan rike babu komai. Suhaif ya sake mika hannu ya ce ta bashi ya rike mata. Sannan ta mika masa jakar suka ci gaba da tafiya.
Suna isa gidan a tsakar gida suka iske Baban Suhaif da Babarsa. Bayan sunyi sallama sun amsa musu sai suka shigo Suhaif ya dubi Babansa ya ce "Ga Iman din na taho da ita. Iman tazo ta durkusa a gabansu ta gaishesu suka amsa dukkansu. Mahaifiyar Suhaif ta ce da Iman ta dawo gefen tabarma tazo ta zauna. Iman tayi godiya cikin ladabi ta zo ta zauna a kusa da mahaifiyar Suhaif. Suhaif ma ya sami waje ya zauna. Alh. Hayat yayi gyaran murya ya dubi Iman ya ce "Yarinta ki fada mana gaskiyar dalilin da yasa kika bar garinku, karki boye mana idan kina so ki zauna damu anan baza mu kore ki ba sai mu zauna tare. Kuka ne amsar tambayar da yayi mata, tayi kuka har ta godewa Allah, su duka lallashinta suke yi, dakyar ta tsagaita da kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce "Duk abunda na fadawa Suhaif shine gaskiyata ban boye muku ba, ina neman alfarma ku yi min sutura ku taimake ni in zauna daku babu inda na sani, babu wanda na sani. Tausayinta ya rufe su Goggo mahaifiyar Suhaif har hawaye take yi ta ce "Iman yi shiru daina kuka zamu rike ki tamkar *yarmu ta cikinmu. Goggo ta kwallawa Naja'atu da Zubaida kira suka fito daga dakinsu suka zo suka sami waje suka zauna. Alh. Hayat ya shaida musu ga *yar uwa kuma kawa tazo zata zauna dasu, ya shaida musu marainiya ce tana neman taimako don haka kada su wareta su riketa tamkar *yar uwarsu jinin su domin haramun ne cusgunawa maraya. Sun dauki alkawarin cewa zasu zauna da Iman lafiya tamkar *yar uwarsu. Daga karshe Goggo ta ce su dauki jakar kayanta su tafi da ita dakinsu suyi mata shimfida kusa da shimfidarsu. Farin ciki mara misaltuwa ya rufe Iman ta sake durkusawa ta yiwa su Alh. Hayat godiya. Naja'atu ce ta dauki jakar kayan Iman na biye dasu har cikin daki suka yi mata shimfida ta kwanta. Daga karshe Suhaif ya yiwa Mahaifansa sai da safe ya tashi ya nufi shagonsa dake zauren kofar gidan. Bayan Alh. Hayat da Goggo sun taba hira suma suka shiga dakinsu suka kwana.
Mahaifin Suhaif Alh. Hayat dan garin Doko ne haka ma Mahaifiyarsa Raliya. Raliya ita ce matar Alh. Hayat ta farko kuma tun daga kanta bai sake aure ba. Hayatu yana son Raliya sosai don sunyi soyayya mai wahala dakyar iyayensu suka yarda suka daura musu aure, kasancewar Raliya kyakkyawa ce duk garin babu mai kyanta a waccan zamanin, samari da dattijan garin masu kudi da masu sarauta sun fito neman aurenta. Ita kuwa ta ji bata son kowa sai saurayinta Hayatu shi kuma a lokacin maraya ne ba uwa ba uba sai kakansa ne yake rike dashi amma yana da sana'ar yi, da gonar gadonsa makekiya yana nomawa kuma yana da tumakan da yake kiwatawa. Yana da ilimin boko daidai Junior secondry school ya kuma sauke kur'ani yafi a kirga. Ba karamar gwagwarmaya aka sha ba wajen neman auren nan. Kakar Suhaif Hajja ita ta haifi Raliya Mahaifiyarsa. Ta kekashe idanuwanta ta ce ita fa *yar ta ba zata auri dan yaku bayi ba sai mai kudi. Mahaifin Raliya lokacin bai rasu ba shine ya takura Hajja ya canja mata wannan tsattsuaran ra'ayi nata ya ce dole a aurawa Raliya saurayin da take so tunda bai sabawa shari'a ba. Shi musulmi ne kuma yana da sana'ar yi. Dole bada son ran mahaifiyar Raliya ba aka daura musu aure da Hayatu.
Allah Ya albarkace su da *ya*ya mata har uku sai dai kash, da sun fara dan wayo sai su rasu, daga baya ne suka haifi Suhaif. Raliya tayi ta addu'a tayi kuka, tayi fargaba akan tana tsoron ko shima Suhaif mutuwa zaiyi kafin ya girma amma Allah mai komai mai kowa sai Ya raya musu shi har sai da ya shekara shida, sannan akayi masa kanwa mai suna Nadiya ana yaye Nadiya itama ta rasu. Bayan nan ta kara haifar *yan biyu suna rarrafe suka rasu. Hakika wannan rasuwar yara guda shida ba karamin tayar da hankalin Raliya da Hayatu yayi ba suka dukufa da yin addu'a suka rungumi dansu kwaya daya Suhaif, tamkar su hadiyeshi don kauna.
Alh. Hayatu su uku ne a wajen iyayensu akwai Furera itace Babba tana Garki tana aure. Sai Alh. Hayatu sannan kaninsa Usman. Allah ya yiwa Usman arziki don haka yana da katafaren gida a Kano a Unguwar *Yankaba da matarsa Usaina ana kiranta Usai ita *yar Gumel ce suna da *ya*ya uku. Babban dansu sunansa Najib, sai na biyun Sagir sai *yar autarsu Zubaida. Don haka Alh. Hayatu yayi shawarar gara ya dauki dansa kwaya daya jal ya kaishi Kano wajen kaninsa Usman ya hadasu da Najib dansa a saka si a makarantar boko me kyau yadda zaiyi ilimi sosai. Haka kuwa akayi tun daga Nursiry har suka shiga primary tare ajinsu daya Suhaif da Najib kuma daman kamarsu daya tunda iyayensu kamarsu daya kamar an tsaga kara suma kuma kowa da mahaifinsa yayi kama sai dai Suhayf ya dauko farar fatar Mahaifiyarsa da gwarzagwarzan idanuwanta. Suhaif yana firamare aka yi masa kanwa Naja'atu Raliya bata ma dora rai akan Naja'atu ba don taji a jikinta ba rayuwa zata yi ba ita ma. Amma babu wanda yasan gaibu sai Allah Ya raya Naja'atu har ta girma.
Naja'atu Hayatu da Zubaida Usman suma sa'anni ne duk da Naja'atu a garin su Doko tayi karatun firamare sai daga baya ta koma Kano aka hadata da Zubaida a makarantar Sakandire daya wato F.G.C Kano nan suka gama shima Suhaif da Najib F.G.C Azare suka gama suna fita daga sakandire suka wuce Bayero University Kano inda Suhaif ya karanci Enginearing, Najib kuma ya karanci Physic. Sun gama cikin wannan shekarar sakamakonsu ya fito, bautar kasa zasu wuce.
Raliya kuwa su biyu mahaifinsu suka haifa ita da kaninta Nasiru shima ya haifi *ya*yansa da yawa duk suna mutuwa sai Rabi ce kawai tayi saura wato *yar Hajja tana karama mahaifinta ya rasu Hajja ta dauketa shine yanzu take rike da ita.
Naja'at Hayat da Zubaida Usman sun shaku bayan *yan uwantaka ta jini ga kawance, don ko a makaranta ba sa rabuwa har *yan biyu ake kiransu daman kuma kamarsu daya suma sai dai Zubaida ita kuma ta danfi Naja'atu haske. Yanzu ma haka basu fi watanni biyu da kammala karatun sakandiren su ba shine kuma suka dungumo Doko suka zauna har suka shiga makarantar Islamiyya. Kullum da safe daga karfe tara zuwa sha biyun rana, ranar alhamis da juma'a ne kawai basa zuwa makaranta. Sai su zauna a gida suyi ta hira da mahaifiyarsu Raliya wacce suke kira da Goggo tamkar wasu kawayenta. Suyi labari suyi dariya su tafa haka suhaif ma yake zama da mahaifiyarsa yayi ta hira, wasa da dariya, sai dai son girmansa yayi yawa bai cika zama da kannensa Naja'at da Zubaida yayi hira dasu ba. Wani lokaci idan *yan fara'ar basa kusa ko kallansu yayi sai su hau makyarkyata suyi wuf su shige daki. Amma wasu lokutan yakan yi hira dasu, amma yana taka musu birki idan yaji hirar tasu ta fara shiga raini. Yafi yin wasa da *yar Hajja saboda dariya take bashi, bayan kauyancin daya addabi halinta gata rikon Kaka ce, saboda haka tabargazarta tayi yawa.
Fargabar Suhaif da Mahaifansa daya, ita ce a zaman Iman da su Naja'at sun san dole sai Iman ta fuskanci wariyar launin fata don sai sun hade mata kai su biyu sun wareta duk da sa'anni ne su duka ukun. Ba sau daya ba, ba biyu ba Naja'at da Zubaida sun sha yiwa kawayensu halin ko in kula baku damemu ba, kanmu kawai muka sani, bamu san ku ba. Duk kawar data rabesu sukan shareta har ta gaji ta kama gabanta kansu a hade yake su biyu basa son su sami ta uku. Haka kuwa aka yi suka ware Iman suna wani kaf-kaf da junansu ita kuma tana binsu, idan suna hirarsu tazo ta zauna ta tsoma musu baki. Idan aiki suke yi tazo ta sa hannu suyi tare. Suhaif yasa ido sosai yana kula da yanayin zamansu, ya gane abinda ke faruwa. Bai wata-wata ba ya kira Naja'atu da Zubaida dakinsa ya ja musu kunne sosai yayi musu fada, yaci layar muddin basu canja halinsu ba, sunja Iman jikinsu tamkar *yar uwarsu, kawarsu to lallai su guji hukuncin da zai yanke a kansu. Ko tantama basu yi a zuciyarsu ba sunsan zai aikata abunda yace zaiyi musu in har suka kuskure gargadinsa. Suna daurewa suna jan Iman a jikinsu badan sun saba da ita ba, sai don dolen da Yaya Suhaif yayi musu. Ko da suka fara zama da Iman sai suka ji sun fara sonta har cikin zuciyarsu, saboda Iman mutum ce mai tsananin dadin zama. Mai hakuri, mai fara'a tasan me take fada, mai son aiki ga tsananin ladabi da biyayya bayan tsantsar ibada ta rike addininta.
Gason Reedwan da ta ke .....lolx =))
*yaudara* ni na ma mance ko wacece Matawata,,,, na daina sonta ga daidai dani Iman...............reed1
Ehem to gwauraye a huta anan sai kuma gobe da yardar Allah.
Reedwan Suraj Isma'il
INA KWANAN KU?
_____________________ YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN
Ba su Naja'at kadai ba har su Goggo da Babansu nan da nan suka ji Iman ta shiga ransu saboda wadannan kyawawan dabi'unta. Inda tafi burge Babansu shine tunda Iman tazo gidan nan ya huta da bugun kofar dakin su Naja'at da asuba, kafin yazo ya tashesu sai ya tarar Iman ta tashesu tuntuni har sunyi sallah. Haka kuma take zama ta bude alkur'ani tayi ta kwarara karatun alkur'ani da kira'arta da muryarta mai dadi har garin Allah Ya waye. Dole su Naja'at suka fara koyi da ita. Goggo kuwa Iman ta kara shiga ranta saboda rashin son jikinta akwai aiki ko an hanata bata hanuwa. Kafin su ankara ta gama aikin gidan kakaf, har aikin da basa yi kullum Iman ta kirkiro shi kamar cire yana, da wankin bandaki kullum. Su Naja'at masu son jiki sunyi farin ciki da zuwan Iman gidan nan saboda hutawarsu kawai suke yi. Ko Goggo ta korosu ta ce su zo su taya Iman aiki sai ita Iman ta hana su ta ce su bari kawai zata yi. Ko kuma idan tana gudun kada Goggo tayi musu fada sai ta ce su sami waje su zauna su dinga yi mata hira tana aikin. Nan da nan suka ji sun shaku da Iman. Matsalar daya ce wacce take kawo musu illa wajen kara shakuwa da juna ita ce Hausa bata ishi Iman ba. Tana so ta fadi wani abu da yawa da yaren Hausa bata sanshi ba, haka idan suka fada bata cika ganewa ba. Harshenta yafi kama da na Fulani, wani lokacin kaji kamar Larabci ne yafi yawa a bakinta, Hausa dai kadan-kadan take yi. To inda Allah Ya tarfawa wannan matsalar tasu ta bambamcin yare ruwan sanyi shine da ga baya sai Iman ta fuskanci Goggo tanajin fulatanci, itama ashe fulatanci ne yarenta sai suka fara yarawa. Sannan sai suke turanci tsakaninta da Zubaida da Naja'atu da Suhaif. Babansu kuma daya fuskanci tana jin larabci sai shima suke yarawa, duk da bazai iya doguwar hira da ita ba sosai da Larabci bai kware ba. To fa yare ake zubawa a gidan nan kala-kala.
Suhaif yayi-yayi Iman ta saki jiki dashi su saba su dinga hira abu ya faskara taki yarda su saba. Kunya ce da ita sosai, daga gaisuwa babu abinda take kara ce masa sai dai idan yayi mata tambaya ta amsa, ta mike ta shige daki. Saboda ita nema ya fara zama da kannensa yana hira idan yazo ya same su suna hira, amma dif zaiji Iman ta dauke wuta ta daina zuba labari ta hau gyara nayafi tana tura gashi cikin dankwali. Idan ta sunkuyar da kai kasa ba zata kara dagowa ta kalleshi ba, balle suyi hira.
Bayan zuwan Iman da wata guda ta nuna sha'awarta ta shiga makarantar Islamiyyar su Naja'at da Zubaida. Bayan sun shaidawa shugaban makarantar cewa zasu kawo sabuwar daliba ya ce su biya mata kudin wata sai ta fara zuwa. Iman da Zubaida da Naja'at suna tashi da sassafe suyi aikin gida suyi wanka duk da ba kayan makaranta (uniform) suke sawa ba sai su saka manyan hijabansu wani lokacin Iman takan saka katuwar (nikaf) ta rufe fuskarta, su dauki jakar littattafansu su tafi. Ajinsu daya kasancewar nan ne ajin manya wadanda suka yi nisa, sun sauke alkur'ani tuntuni hadda ake koya musu. Da aka gwada Iman don asan wanne aji za'a saka ta sai suka ga Iman harta wuce *yan manyan ajin saboda tayi nisa sosai a hadda. Haka a fannin hadisai da zauransu. Tunda babu aji na sama dana su Naja'at sai suka sakata a ajinsu. Iman bata wasa da karatunta akwai hazaka a gida da makaranta koda yaushe ka ganta da littafinta a hannu tana karantawa idan bata da aiki. Haka take kara koyowa Zubaida da Naja'at inda suka kakare. Goggo ma ba'a barta a baya ba, ta yarda da hankali da nutsuwar Iman don haka take zama da Iman tana koya mata karatun kur'ani.
Yau Alhamis babu makaranta bayan duk sun tashi da asuba sunyi salla, kamar yadda *yan makaranta suka saba sai kowacce ta zauna akan abin sallarta ta bude kur'aninta tana karantawa har saida gari ya washe. Naja'at da Zubaida suka gyara shinfida suka sake kwantawa suka bude wani sabon barcin da basa samu suyi saboda makaranta. Iman ta mike ta fito tsakar gida don ta gaishe da Baba da Goggo sai taji tsit babu kowa da alama dai sun koma barci. Ta juya zata koma dakinta sai taji karar bude kofa. Tana jiyowa sai taga Baba ne ya fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunsa. Ya yi wanka ya yi kwalliya yana ta kamshin turare. Tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaisheshi cikin harshen larabci. Ya amsa mata cike da fara'a ya shaida mata yau Kano zaije sai gobe zai dawo idan su Naja'at sun tashi ta fada musu ya wuce. Ta amsa masa da to, sannan tayi mas fatan Allah Ya kiyaye hanya. Ya fita ita kuma ta koma daki ta cire hijab da doguwar riga baka dake jikinta ta daura wani tsohon zaninta wanda ta mayar