Showing 84001 words to 87000 words out of 110329 words

Chapter 29 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7484

naga Suhaif yana cikin damuwa sai naji na damu. Kaga kamar lokacin da zai tafi bautar kasa ya ce baya so yaje kudu, Baba ya ce sai ya je damuwar da yayi tasa na rasa abunda yake min dadi. Zan tafi da damuwa a sanadiyyar damuwar da na bar Yaya Suhaif a ciki. A tunanina, na dauka dan zanyi aure ne ya sa shi damuwa, amma kace bashi ne damuwarsa ba. Yaya Suhaif mai fara'a, ga son wasa, ga shi da bayar da labari. Yanzu fa? Dubi halin da yake ciki, kace min kuma babu komai.
Huzaifa dauke da Invitation card din bikinsa da Iman ya sako kansa cikin falon abun da kunnensa ya jiye masa shine Najib yaji yana cewa. "Iman kamar yadda kika sani Suhaif yana tsananin sonki tun kafin ku rabu, to ko bayan rabuwarku Suhaif ya kasance yana matukar kaunarki, kaunarki tasa ranar da za'a tantancesu a wajen daya sami aiki ya ki zuwa ya tafi garinku nemanki. Satin Suhaif guda a Jalingo yana nemanki bai ganki ba, ya dawo a lokacin angama daukan ma'aikata. Duk tsawon shekarun nan Suhaif ya kasa daure zuciyarsa ya auri wata, a koda yaushe yana fadin Iman yake jira, saboda na kasa son kowacce *ya sai Iman. Mun bashi shawara ya hakura ya barwa Allah idan ke rabonsa ce ko bayan yayi aure sai ku hadu kuma ya aure ki. Ya ce duk *yan matan da yake haduwa dasu basu da hali irin naki don haka idan bake ya aura ba ya hakura da aure a duniya. Ya mallaki komai na rayuwa, wannan gidan da muke ciki nasa ne amma shi kadai yake rayuwa a cikinsa saboda rashinki. A koda yaushe yana addu'a Allah Yasa ya ganki, haka makasudin zuwanmu Makka yanzu takanas don yayi addu'a Allah Yasa ya ganki. Allah Ya amsa addu'arsa ya ganki, amma a kurarran lokaci. Ma'ana a satin bikinki don haka ya shiga damuwa fiye da ta da kafin ya ganki. Iman ta runtse ido sai hawaye sharr-sharr yake zuba daga idanuwanta. Najib ya dubeta yayin da hawaye ya surnano masa ya ce "Ba kuka za kiyi masa ba addu'a da nasiha za kiyi masa a matsayinki na Malama ki nuna masa kaddarace da jarabawa daga Allah, a matsayinsa na Musulmi dole ya yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau amma ni kaina ina tsoron halinda Suhaif zai shiga nan gaba, in dai ba Allah bane Ya saka masa dangana.
Iman ta hau karkarwa jikinta da bakinta da kyar maganarta take fita ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hakika na tausayawa Suhaif kuma bani da abunda zan bashi ko in fada masa yaji damuwar da yake ciki ta gushe. Illa nayi alkawari zan dauwama har karshen rayuwata, ina mai yi masa addu'a Allah Ubangiji Ya yaye masa ya kuma bashi macen da zai so fiye da ni. Bayan rabuwata da Suhaif sannan na sake gaskatawa na tabbatar Suhaif mai sona ne, so na hakika kuma tsakani da Allah. Ya soni a lokacin da kowa ya ki ni, Suhaif ya tsaya a lokacin da kowa yake guduna. Suhaif ya lallasheni lokacin da kowa yake hantarata. Suhaif ya kirani da masoyiya a lokacin da kowa yake kirana makiyiya. Suhaif ya kira ni da Iman lokacin da kowa yake kirana da Mayya. Sannan Suhaif ne ya fara fahimtata, yayi kokarin fahimtar da jama'a har saida suka fahimta ba laifina bane. Yana kuka da hawayensa lokacin da yaga ina kuka. Haka yana dariya lokacin da nake dariya. Ya hana kansa abu ni ya wadatar dani don kawai kada in banbanta da kawayena. Ya ki yadda in yi kukan maraici a lokacin dabani da Uwa ko Uba, babu dangin Uwa babu na Uba. Allah ne kadai gatana sai Suhaif. Sai kuka ya ci karfinta ta kasa magana. Najib ma hawaye ne yake kwarara daga idanuwansa. Hankalin Huzaifa ya tashi yayi shiru ya kasa motsi tamkar daskararriyar kankara ya zama a wajen da yake labe. Yayin da ledar dake hannunsa mai dauke da invitation card din bikinsa da Iman ta rikito ta fado kasa saboda ciwon rashin laka da ya kama shi yanzu-yanzu.
Karar faduwar ledar ita ta ja hankalinsu su dukka suka dubi bakin kofa amma sai basu ga kowa ya shigo ba. Najib ya tashi ya leka baranda sai ya ga Huzaifa a tsugune yana kwashe katinan da suka watse a kasa. Najib yayi sauri ya goge idanuwansa don kada ya gane halin da yake ciki, ya karasa da sauri inda yake tsugune, ya ce "Ranka ya dade bari kayi ne? Huzaifa yayi karfin hali ya saki ransa yana murmushi ya ce "Zan hawo barandar nan kawai ledar ta subuce ta fadi. Najib ya harhada masa yana zubawa a leda. Bayan sun tsince suka shigo falon tare. Iman wacce tuni ta goge fuskarta ta hau murmushi tamkar ba itace mai kuka yanzu ba, ta fake da matsa remote ita a dole kallo take. Ta dubi Huzaifa fuskarta cike da annashuwa cikin harshen Hausa ta ce "Sannu da zuwa, ina fatan baka sha wuya ba wajen gano gidan ko? Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ko a Bahrain ba za'a batar dani ba balle a kasata Nigeria. Najib ya ce "Sai a kasa batar da kai a Bahrain amma a batar da kai a Nigeria, kai Nigeria fa da yawa. Huzaifa ya ce "A'a Najib ba dai ni ba, ai duk inda zan shiga saina fito. Nan dai suka dinga musu Iman na taya su, tana bayan Najib cewar gaskiya za'a iya batar da Huzaifa don dai iyakacin yawonsa bai wuce Jalingo, Yola, Kaduna ba.
Suhaif wanda ya shiga lambu cikin fulawoyi ya buyar da kansa don takaici sai yanzu ya fito. Yana shigowa falon ya dubi Huzaifa yayi murmushi ya ce "Ah ango yaushe ka dawo ne? Ina fatan baka bata ba? Su duka suka kwashe da dariya. Huzaifa ya ce "Au kaima zancen batan zaka yi min? Nima fa dan Nigeria ne, dan kunga na dade a Madina, na kaura Baharain daga can? Ai yanzu Najib suke min musu wai zasu iya batar dani a Nigeria. Suhaif ya samu kujera ya zauna. Najib ya ce "Sai da Suhaif ya ce ango na tuna kamar katin aurenku na gani a cikin ladar nan ko? Huzaifa ya ce "Af kaga na shagala na manta ban nuna muku ba. Najib ya ce "Baka nuna mana ba ko baka bamu namu ba? Muma da *yan gayyarmu fa. Zuciyar Suhaif ta hau dukan uku-uku, wata zufa ta gangamo masa, yayin da huhunsa suka yi ta dauki ba dadi da numfashinsa yana kokarin ficewa gaba daya saboda tashin hankali.
Katinan bikin sun kawata matuka, an yi su irin na zamani, irin na masu hannu da shuni saboda ita kanta ambulan din da katin yake ciki abar kallo ce. An buga katinan da yare kala-kala anyi da Hausa, Turanci, Fulatanci da Larabci. Huzaifa ya ce "Gashi nan kowa ya dauki yadda zai yi masa da kuma yaren da yake ji. Najib ya debi guda shida na turanci biyu, na Hausa guda biyu, na Larabci daya na Fulatanci. Ya dauki adadin haka ya mikawa Suhaif. Suhaif wanda tuni karfin jikinsa ya kare, da Najib ya miko masa sai ya ajiye a gefensa yayi shiru. Ta ido Najib yayi masa sigina sai ya fahimci abun da Najib yake nufi. Wato ya daure ya bude katin ya karanta, sannan ya taya su murna kar su gane halin da yake ciki.


Suhaif ya dauki katin ya bude amma tsabar rudewa, da daman kawai ba karantawa yake yi ba, bai san upside-down ya juya katin ba sai da Huzaifa ya kula ya karba ya gyara masa gami da cewa "Malam Suhaif yaya dai ciwon kanne yake damun ka, ka juya katin Upside-down kana karantawa? Suhaif yayi ajiyar zuciya har guda uku a jere ya kirkiro wani bushasshen murmushi ya ce "Kamar ka sani kaina ne yake ciwo. Najib wanda ya kurawa Suhaif ido yana masa nuni akan ya daure ya sake daurewa ya cije kada a gane shi.
Suhaif bai san Najib ya fadawa Iman halin da yake ciki ba, don baisan ta sani ba, haka su duka basu san Huzaifa yaji ba. Sai kowa yake dannewa yana nunawa babu komai a ransa. Kallo daya Suhaif ya yiwa katin yaga an rubuta Huzaifa Ahamed Jalingo weeds Fatima Lamin Jalingo sai yaga ganinsa ya raunana ya koma hatsa-hatsa tamkar yanar ido ce ta tsuro a idonsa yanzu-yanzu. Sai yayi sauri ya mikawa Iman kati ya ce "Ke amarya baki karanta ba. Iman ta karbi katin ta kasa budewa sai ta ajiye kan tebur ta rufe fuska. Huzaifa ya dubeta ya ce "Waike har yanzu kunyar fulanin ce bata sake ki ba? Kunsan da fa ana fara zancen auran take tashi tabar wajen. Wai nan dagewa tayi ta zauna a wajen da ake rabon katin bikinta. Najib da Suhaif suka yi dariya.


Ina tunanin sai jibine zan ci gaba idan Allah Ya kaimu


Reedwan Suraj Isma'il




>>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI


Huzaifa yayi gyaran murya ya ce "To Alhamdulillahi! Mun gode Allah, mun gode muku akan matukar kokarin da kuka yi wajen dawainiya da ni da bataliyata, ga Uwa Uba wahalar da zan baku ta gayyatarku da nayi zuwa wajen daurin aurenmu tun daga Abuja har Jalingo Allah Ya saka da alherinSa. Najib ya yi sauri ya katse shi ya ce "Haba mai gida meye abun wannan doguwar godiya? Mu da ku ai mun kulla zumunci har abada kuma duk kasar da kuke zamu kai muku ziyara balle daga nan zuwa Jalingo ai babu nisa. Suhaif ya yi gyaran murya ya ce "Iman *yar gidanmu ce, kanwarmu ce, tamkar jinin jikina take. Idan a bangon duniya za'ayi daurin aurenta zamu je. Kai kuma mai gidanta kun zama daya, mun zama daya da ku. Huzaifa yayi murmushi ya ce "To mun gode mun ji dadi muma zamu rike ku kamar yadda ku ka dauke mu *yan Uwa, jinin jikinku kuma dan Allah ku cika alkawari, kamar yadda ku kayi alkawari, nasan zaku cika alkawari ku zo daurin auren nan kada a samu matsala wani daga cikin ku yaki zuwa. Najib ya ce "Haba Huzaifa ai mu da Iyayenmu mata da maza da kannan mu duk zamu zo insha Allah. Huzaifa ya ce "Lallai kuwa zan zamo mai farin ciki. Yanzu zamu kama hanya zuwa Jalingo ina ga zai fi kyau mu tafi Yola ta jirgi. Nan ma zamu raba kati, sai mu wuce Jalingo. Iman ta ce "Ba da Bilkisu zamu tafi ba, ko ita ba yau ba? Huzaifa ya ce "Duk zancen nan da muke baki gane ba? Nafisa ta tafi Lagos tun karfe bakwai na zafe zata sayo ankon da za suyi kuma zata karbo dinkunanki, dukka lefen naki can takai a dinka miki. Tace sai wajen jibi zata je Jalingo shine ta bawa direbanta katinan daurin auren ya kawo min, ta bani lambarsa nayi masa kwatance, yanzu muka hadu a bakin titi ya bani, ta ce ko zamu fara rabawa kafin ta zo. Iman ta ce "Ai da ban gane ba, na dauka tana gidanta zan zamu je sai mu dunguma mu tafi. Huzaifa ya ce "Na rasa yadda zamuyi wannan tafiyar ina so in tsaya a Kano akwai abokaina da *yan Uwana da nake so in gayyata. Najib ya yi caraf ya ce "Muma Kanon zamu tafi dan *yan gida ba su san mun dawo jiya ba. Me zai hana mu dunguma a mota muje Kanon kayi rabon katinan, Iman ma ga kawayenta su Naja'at ta gayyacesu da bakinta. Ku kwana gobe da sassafe in saku a jirgin Yola ku isa Yola da wuri kuyi rabon a nutse sannan ku wuce Jalingo. Tun da yau bikin saura kwana shida babu lokacin da zaka je Yola ka dawo Kano kuma. Huzaifa ya ce "Gaskiya ne. Ya dubi Iman ya ce "Haka yayi miki? Ta gyada kai ta ce "Haka yayi Hamma Huzaifa. Suhaif dai yana zaune yana kallonsu tamkar ya rusa ihu dan tashin hankali. Ya rasa haushin wanda yake ji. Haushin Iman yake ji? Ko na Huzaifa? Ko kuwa haushin kansa da kansa yake ji oho?
Haka kuwa aka yi, mota daya direba da Huzaifa a gaba Iman da Zainab matarsa a baya. Daya motar direba da Najib a gaba, Suhaif da yaran Huzaifa a baya. Suka dunguma suka kama hanyar Kano. Tafiya suke a titi, tamkar a jirgin sama suke saboda dadin motar. Kujeru lausasa hade da sanyin A.C da kamshin turaren dake manne a kowacce kusurwar cikin motocin.
Huzaifa ya juyo ya dubi Iman cikin harshen fulatanci yace mata "Fatima bani labari, wanne labari Hamma Huzaifa? Labarin da kika taba bani can kwanaki na abubuwan da suka faru da rayuwarki bayan tafiyata. Kin fada min inda kika zami jariri da yadda ki kayi da jaririn. Kin tsaya a inda kikabi matar nan Masallacin B.U.K baki karasamin ba. Iman ta ce "Duk tsawon lokacin nan baka tambayeni ba sai yau? Huzaifa ya ce "Ai kin san komai kamawa yake yi, kinga yanzu da kin karasa mun labarin da nasan su Suhaif kafin ki gabatar mun dasu kamar yadda suka sanni kafi ki musu bayanina. Iman tayi murmushi ta ce "Haka ne amma kasan ban cika son yin hira da kai ba a gaban matarka ko? Babu dadi za taga kamar cin fuska ne kasan mata da kishi. Huzaifa ya ce "Ke kike ganin haka laifine ita tasan zan aureki yanzu haka ma katunan daurin auren duka suna wajenta saita hana mu hira? Bani labari bata jin fulatanci shima direba baya jin fulatanci.
Iman bata yiwa Huzaifa musu, duk abunda Huzaifa zaisata komai wahala zata yi masa balle labari ai ba zai zama matsala ba. Ta gyara zama ta fara rangadowa Huzaifa labarin duk abunda ya faru. Musamman da taga barci ya kwashe matarsa sai ta saki jiki tana ta zuba. Ta bashi labarin zamanta a gidan larabawa wato Mummy Naila, bata boye masa ba duk yadda suka yi da Matsafan akan Abdul-Malik dalilin da yasa ta bar Kano kenan ta nufi Doko garin su Suhaif. Tana hawaye tana fada masa halinda ta tsinci kanta da irin halaccin da Suhaif yayi mata. Amma har yanzu Huzaifa bai ji kalmar da yake son ji ba daga bakin Iman, bata kira kalmar so ba tsakaninta da Suhaif. Sai take kiran Suhaif da Yayanta.
Huzaifa ya tausayawa Iman matuka, kuma ya jinjinawa Suhaif da irin taimakon da yayi mata. Haka suka dinga hira har suka shiga Kano. Motar su Suhaif na gaban ta su Iman dan haka su suke bi a baya. Basu tsaya a ko ina ba sai a Hadeja Road unguwar Iyayen Najib. Suka shiga gidan suka iske Mama da Baba suna nan. Sai Baba ya dubi Suhaif da Najib ya ce "Wai yaran nan kun zama *yan Saudia ne, na ganku da larabawan mata har da *ya*yansu? Suka yi dariya dukkansu. Suhaif ya ce "Kwarai kuwa Baba muma mun zama *yan kasar Makka tunda gamu da *yan kasar mun taho muku dasu. Najib ya ce Baba wannan itace Iman *yar Jalingon nan da ta zauna a Doko. Sai Suhaif ya yi sauri ya ce "Ga kuma mijinta gobe zasu wuce Jalingo bikinsu. Kallo daya zaka yiwa Baba da Mama kasan sun shiga damuwa sabida tausayin Suhaif. Idan kasan Suhaif kasan shi da kaunar Iman. Huzaifa ya zaro kati ya mikawa Baba ya ce "Baba ya amsa da insha-Allah. Akayi-akayi a kawo musu abinci Najib ya ce a gidansa zasu ci abinci ya yiwa Naja'at waya ta hada musu abinci kala-kala.


Gidan Najib a Badawa Layout yake, suka dunguma sai gidan Najib. Naja'at tayi mamakin ganin Iman murna ta kamata suka rungume juna. Daga karshe Naja'at ta damu har taso a gane damuwarta da taji labarin Iman zata auri Hamma Huzaifa tana tausayawa dan Uwanta Suhaif tana tunanin halin da zai shiga. An jera musu abinci kala-kala sunci sun sha sun koshi. Bayan sunyi sallar la'asar sai Suhaif yayi musu sallama ya ce zai tafi Doko yanzu haka yana yi musu fatan alheri sai ya zo Jalingo daurin aure kenan. Najib, Naja'at Huzaifa da Iman suka raka shi har bakin mota ya shiga shi kadai zai tafi ba tare da direba ba. Ko kadan baya garajen duban gefen da Iman take ita kuwa babu abunda take sai satar kallonsa, ko tantama babu tana so tayi masa magana amma babu dama dan haka maganar da tayi masa ta karshe shine ya gaishe mata da Goggo, Baba, Hajja da *yar Hajja. Ta ce ya cewa Goggo dan Allah ko kowa bazai zo bikinta ba ita ta zo. Suhaif ya amsa mata da "To zan fada musu yaja mota ya tafi yayin da hawaye ya zubo a idanuwansa, Iman ma haka amma sai tayi sauri ta shige gida.
Misalin karfe biyar na yamma Najib da Huzaifa suka shirya fita gidajen *yan uwa da abokan Huzaifa. Iman da Naja'at suma suka ce zasu je NNDC quater sharada gidan Zubaida su kai mata nata katin. Don haka gidan ma rufeshi aka yi tunda babu kowa. Najib da Huzaifa a motar Suhaif wacce suka zo da ita suka fita. Naja'at, Zainab da Iman da yara su kuma suka fita a ta Najib tunda tafi girma. Naja'at ke tukawa suka nufi Sharada.
Sun iske Zubaida itama shigowarta kenan ko fitowa daga mota bata yi ba, daga gidansu take Hadeja Road. Daman tana da labarin Iman ta zo. Ta tare su da sauri cike da mamakin ganin Iman. Itama Iman tayi mamakin ganin Zubaida saboda yadda tayi uwar kiba haka. Iman ta rungumeta suka gaisa ta ce "Zubaida me kike ci kika yi kiba, nima in ci, ina mamakin kibar Naja'at ashe ita ba kiba tayi ba akan ki. Zubaida ta kyalkyale da dariya ta ce "Ke dai kina nan yadda kike Iman dama ni ce, kamar kara dawowa yarinya kika yi, kin zama *yar siririya kin dada fari da kyau, kiyi zamanki a haka ni ai bana son kiba. Oh! Iman sai naga katin aurenki da Hamma Huzaifa ya aka yi? Naja'at ta ce "To uwar tambaya ai sai ki kaimu cikin gidan mu zauna sai ayi labarin, ga bakuwa da yaranta suna tsaye. Sannan Zubaida ta ce "Lah ashe da wata ban kula ba, wannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login