Showing 108001 words to 110329 words out of 110329 words

Chapter 37 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7471

kan wajen Iman. Ta saka shi a makaranta mai kyau mai tsada wacce *ya*yan manyan Nigeria suke yi. Yaro mai hazaka da son karatu, a bangaren karatun addini kuwa Iman ta daukar masa Malamai masu koya masa. Amma ba shi da Malamin da ya wuce Iman, Iman ta tsaya tsayin daka tana koya masa ilimin kur'ani da hadisai. Dai-dai Lokacin da Muhammad ya gama primary yana shirin shiga Secondry a lokacin ya sauke alkur'ani, babu inda za'a bude masa ya kasa karantawa.
Iman ta ga ya dace ta hada masa kayatacciyar walima yadda *yan Uwa da abokan arziki gaba daya za'a hadu dan a kara dankon zumunci. Ta buga kati masu yawa ta rarrabawa dinbin kawayenta da abokan arziki da suke mutunci a Abuja. Ta tashi Rashida mai aikinta da direba mai zuwa Kano da Doko ta kai musu nasu katin. Sannan ya aikawa *yan Jalingo nasu, na gidan Iyayenta, Iyayen Huzaifa, Kawayenta Mumuyawa da gidan Ibrahim da Salma marikan Muhammad. Iman ta jajjadawa Salma lallai-lallai a taho da Aisha, Abubakar, Aliyu da Usman in ji Mohd. Alhamdulillahi! Duk wanda Iman ta gayyata babu wanda bai zo na harma da wadanda bata gayyata ba suma sunzo dan su ganewa idanuwansu.
Da misalin karfe hudu na yamma za'a fara gudanar da shagalin walimar saukar karatun Muhammad a katafariyar farfajiyar gidan Suhaif da Iman na Abuja. Dan haka tun misalin karfe uku mutane suka fara hallara. Wadanda suka zo daga nesa kamar *yan Jalingo tun jiya suka karaso suka kwana a gidan, amma *yan Kano da *yan Doko a ranar suka kamo hanyar Abuja, karfe biyun rana tayi musu a Abuja. Ma'aikata na musamman mata da maza sune suke rarraba riguna ga duk wanda zai shigo cikin get din gidan, maza a basu farar riga fara sol mai dogon hannu, hirami ja da bakin kokoro irin na Larabawa da suke dorawa akan hirami. Mata kuwa doguwar riga ake basu baka mai dan kwali (open) wacce ko wanne irin kaya kika saka zaki iya dorawa aka. Kusan dole ne duk wanda zai shiga wajen walimar ya saka wannan riga.


Nima dai sai da na ziyarta.... Lolxx


Reedwan Suraj Isma'il




===============YARENA ADDININA
KARSHEN LABARI


Aziza ta dubi mai gidanta Ashraf tayi ajiyar zuciya ta jujjuya rigar da aka bata. Ta ce "Dadina da zuwa gidan Iman kenan, kullum sai ta wahalar da mutum dole sai ya canja kaya, idan karamin gyale na sa dole sai ta bani hijabi na saka kafin na fito daga gidanta, yau kuma da doguwar riga mai dankwali ta hadamu. Saboda bana son kaya mai nauyi ne fa na saka material ban sako atamfa ba ko leshi. Ashraf ya yi dariya ya ce "Ai ni Iman tayi min daidai hakan da take miki shi yasa duk kawayenki nafi sonku tare kamar yadda kawarki Hanna Haisam take koya miki hakurin zama da mutane. Bai rufe bakinsa ba sai ga Hanna da Haisam sun fito daga motarsu, kai tsaye suka tunkaro inda Aziza da Asharaf suke tsaye, suka gaisa kowannensu cike da farin ciki. Suka ma'aikatan masu raba riguna suka dubi yanayin jikinsu suka dauko musu size dinsu. Kowannansu ya zura goguwar riga suka dunguma cikin farfajiyar gidan. Iman da Suhaif suna tarar baki suma suna sanye da dogayen riguna irin wadanda ake rabawa. Iman da sauri ta zo ta tari kawayenta Aziza da Hanna, bayan sun yiwa juna sallama su kayi musabaha sai suka rungume juna. Suhaif ya gaishe da Ashraf da Haisam game da nuna musu wajen zaman maza, suka je suka zauna. Iman ma ta kai su Aziza bangaren da aka warewa mata suka zauna.
Aziza ta yamutse fuska ta dubi Iman da Hanna ta ce "Gaskiya na takura da aka raba min wajen zama da mai gidana Ashraf. Mu fa bamu rabuwa, duk inda zamu je ga kafata ga tasa, ga hakarkarina ga nasa. Bama iya rabuwa ta secon ashirin da hudu, ko awa ashirin da hudu balle ace KWANA ASHIRIN DA HUDU rasuwa kawai zamu yi. Dukkansu suka yi dariya. Iman ta ce "Yau dai kuyi hakuri, idan ku ka zauna tare sauran mutane fa? Wata matar wani ce, wani kuma mijin wata ne babu dadi a gauraya mata da maza ba maharraman juna ba, kunsan ina kishin YARENA ADDININA. Aziza ta ce "Wa'azi dai kullum, daman nasan yanzu zaki fara wa'azi da an zauna a kusa dake zaki fara yiwa mutane wa'azi. Hanna tayi dariya ta cewa Iman "Kinsan halin iyayin Aziza, ki daina kulata kina mata bayani. Ta tashi ta je kar ta zauna a kusa damu din, ta je wajen mijin nata. In ba iyayi ba zaman awanni sai ta ce ba zata iya ba sai a kusa da mijinta dadi miji. Dukkanmu nan muna tsananin son zama a kusa da mazanmu amma muka hakura, don GANGAR JIKINA ce kadai anan zuciyata na wajen Haisam. Iman ta ce "Ai shine, ni naga Hanna da Haisam wadanda soyayya ta kusa hallakasu. Aziza ta ce "A'a dakata Hanna, karma a hada soyayyarmu da ta ki, ke fa ba ke kadai ba ce. Yau idan ya kwana biyu a wajenki, gobe kwana biyu zai yi a wajen Ramla, ni kuwa fa kullum muna tare.
Iman taga surutun kawayenta ya ki ya kare ga baki sai duddukowa suke yi, ta tafi wajen jama'a suna ta gaggaisawa. Micheal da amaryarsa suma sun karaso. Sai ga Huzaifa da matarsa Zainab suma sun shigo. Iman da Suhaif sun yi mamakin ganin Huzaifa domin ko da wasa Huzaifa bai ce musu zai zo ba, sun dai sanar masa a waya ya taya su murna. Dinbun jama'a mata gaba daya kayansu iri daya yaransu da manyansu bakar riga doguwa mai dan kwali. Maza kuma yaransu da manyansu farar riga doguwa da hirami a kansu. Idan ka kalli mutanen wajen tamkar a kasar Saudia kake, babu abinda yake tashi sai sallama kowa na yiwa na kusa dashi sallama. Masu daukar hotuna da masu daukar bidiyo suna daukarsu.
Muhammad wanda ake taron dominsa ya caba ado da farar doguwar riga, farin harami, da farin takalmi da bakar alkebba tsadaddun gaske. Ya fito dauke da katon hoto lamination hoton Harriet Mahaifiyarsa. Hoton Iman ta dauko a ranar da Harriet ta haifeshi ta mutu. Babu dan kwali akanta a hoton amma Iman tasa an yafa mata mayafi a computer tamkar da mayafinta tayi hoton. Aka yi katon enlargement. Mohd ya dafa hoton aka dauke shi a hoto. Iman ta ce ya je wajen Babansa Micheal a daukesu a hoton tare da hoton Harriet. Cikin sanyin jiki da nadama Micheal ya tsugunna, Muhammad yana tsaye duk sun daddafa hoton Khadija (Harriet) aka dauka Micheal ya kurawa hoton Harriet ido cike da tausayi da nadama, ya juyo ya dubi Iman yayi dan murmushi yayin da hawaye ya sirnano daga idanuwan sa ya ce "Allah Ya jikan Harriet. Ku yafe min a madadinta ke da danta, kiyi hakuri karki fadawa danta abubuwan da suka faru idan ya girma. Iman tayi murmushin karfin hali yayin da ta zubo da hawayen daya cika mata ido ta ce "Harriet ko Khadija? Ai Khadija sunanta, domin itama ta musulunta kafin ta rasu, ta zabi suna Khadija da kanta. Kar ka damu a kullum kuma a koda yaushe ina cusawa danka Muhammad ya so ka kaine Mahaifinsa. Na yi alkawari duk hutu zan yi kokarin in dinga kawo shi wajenka hutu yadda zai shaku ya saba da kai. Micheal ya gyada kai ya ce "Na gode Pretty, na godewa Allah da Ya hada ni dake.
Micheal ya je gaban Mahaifi da Mahaifiyar Iman ya durkusa ya gaishe su. Kamar yadda Iman ta basu labarin Micheal hakika gaskiya ne Micheal ya canja ba kamar da ba, sanda yake saka dan kunne, sarka da kaftara-kaftaran zobuna a yatsu. Ya zama nutsattse, mai kunya da ladabi da biyayya. Su ka amsa masa cike da fara'a, ya kira matarsa itama ta zo ta gaishe su.
Iman da jama'a sai hotuna ake dauka, ta dauka ita da danta Huzaifa, Muhammad da Suhaif. Iman ta dauka da Mahaifanta da kannenta, Muhammad rike da allon saukarsa a tsakiyarsu. Aka dauki Iman, Muhammad, Marikan Muhammad, wato Ibarahim da matarsa Salma da *ya*yansu Aisha, Abubakar, Usman da Aliyu. Aka dauki Iman da Muhammad da Iyayen Huzaifa. Aka dauki Iman, Suhaif da Hamma Huzaifa. Aka dauki Iman, Suhaif, Muhammad Baba na Doko, Baba na Kano, Mama da Goggo. Sannan aka daukesu su duka wato Iman, Suhaif, Muhammad, Micheal, Marikan Muhammad, Najib da Matarsa Naja'at da dan Jaririnta a hannunta, sai Baba na Doko, Goggo, Baba na Kano da matarsa, Zubaida da mijinta, Iyayen Iman da Iyayen Huzaifa, MATAWATA da Reedwan,, lollxxx. Laillai hoton nan zai yi matukar kyau, """GASKIYA YA DACE IN WANKARWA MAKARANTA LITTATTAFAINA DOMIN SUMA SU GANEWA IDANUWANSU WADANNAN MUTANEN DA NAKE BASU LABARINSU"""" inji tauraruwar marubutan Hausa wato "J.U.T".
Matan kayansu iri daya, maza ma yaransu da manyansu kayansu iri daya, shigar larabawa. Sai Iman tasa aka dauketa a hoto ita da Mama Tabita da Mijin Mama Tabita wanda shima a yanzu haka cikakken Musulmi ne. Iman taje tsakiyar kawayenta mata da maza Mumuyawa wadanda tuni suka rungumi Musulunci a hannun Iman. Wadanda suka yi sallama da jahilci, duhun kai da talauci a sanadiyyar Iman. Ta canja musu rayuwarsu gaba daya, ta basu izinin duk matsalar da ta taso su gaya mata, a shirye take ta taimaka musu.
Iman, Muhammad, Fadila, mijin Fadila, da *ya*yansu suma aka daukesu. Iman da masu aikinta mata da maza aka dauka gaba daya. Suhaif, Iman, Kakarsa Hajja da *yar Hajja da Iyayenta aka dauka. Iman, Suhaif, Aziza, Ashraf, Hanna da Haisama ma aka dake su. EH LALLAI DOLE IN WANKARWA MAKARANTANA WADANNAN HOTUNA. In ji "J.U.T". Cancadi! Sun zuba kyau ainun a hotunan nan. Iman tayi alkawari zata wanko hutanan nan masu dinbin yawa dan a rabawa masu son ganinta su ganta.
Muhammad aka kira aka bashi lasifika ya fara rangado karatu mai dadin saurara da kira'a mai dadi irin ta Iman. Jama'a duk suka zazzauna suna sauraren Muhammad. Ma'aikata suna ta raba abubuwan da aka buga da hotunan Muhammad kamar, kalandu, memo, jakunkuna, sallayu, atamfofi, hijabai kur'anai littafin rubutu masu kyau, tun daga wani kamfani a London suka sa aka buga musu ma musamman.
Abinci da abin sha kuwa babu wanda aka yiwa iyaka, kowa da kansa zai zuba abunda yake so yadda yake so. Komai akwai babu ce kawai babu, a jere akan zungureren teburan da aka cika da darukan abinci. Daga karshe Iman ta je ta zauna kan wata kujera Muhammad shima a kusa da ita akan tasa kujerar da teburi a gabansu wanda ke dauke da kur'anai akai. Iman ta dubi dunbin jama'ar da ta tara, gaba daya sun zagayeta suna sauraranta. Ta tuna mutane da dama wadanda a da ba Musulmai ba ne a yanzu kuwa sun Musulunta. Kukan dadi ya keto mata, sai ta share hawayenta tayi murmushi cikin harshen Hausa ta ce "Gaba dayanmu nan addinin mu daya, Allah daya muke bautawa mun yarda Annabi Muhammad (S.A.W) Manzonsa ne. Amma kuma yarenmu daban-daban. Shin da wanne yare zan yi magana yadda kowannen ku zai ji, zai fahimce ni? Idan na yi magana da turanci wasu basa ji, idan fulatanci ne da yawa basa jin fulatanci, balle in yi magana da Igbo, Tangalanci ko Mumuyanci wadanda suke ji a cikin ku kadan ne. Sai su duka suka dau dariya waje ya hargitse da hayaniya, kowa yana ambaton tayi magana da yarensa. Iman tayi dariya ta ce "Ina ganin kusan kowannen ku anan yana jin Hausa a ganina muyi amfani da yaren Hausa a matsayin yarenku kuma YARENA.
Iman tayi gyaran murya tayi bismillah sanan ta fara karanto Hadisai tana fassarawa da Hausa, ta dauko tarihin Manzon Allah (S.A.W) tun daga ranar da aka haifeshi har ranar da yayi wafati. Ta gangaro rayuwar Sahabbai har zuwa rayuwa irin tamu ta yanzu. Ta ce "Shin ba zamu yi koyi da rayuwa irin ta lokacin Annabi ba? Yanzu duk kan Musulmai sun rarraba, masu hali basa tausayin marasa hali. Masu mulki basa tausayin talakawansu. Talaka baya hakuri da talaucinsa, *ya*ya basa tausayin Iyayensu, Iyaye basa bawa *ya*yansu tarbiyya yadda ya kamata. Ba'a soyayya dan Allah sai dan wani hali. Musulmi ya kashe Musulmi saboda kudi ko neman mulki ko dan ya fadi gaskiya. An danne gaskiya an daukaki karya. An daukaki duniya tamkar ba za'a mutu ba. Sace-sace sunyi yawa. Gulmace-gulmace sunyi yawa, cuta, danfara, hassada ba babba ba yaro. Kowa baya tausayi, burinsa ya samu wani ya rasa. Iman tayi kira, tayi roko ga *yan Uwa Musulmai su gyara halayensu. Su ji tsoron Allah, su so junansu saboda Allah. Suyi aure saboda Allah.
Hawaye ne ke zuba daga idanuwan Iman da gaba daya masu sauraronta. Kowa yayi shiru, wasu sun doka uban tagumi suna sauraren Iman hawaye ne ke ta kwaranya daga idanuwansu. Hakika Iman ta hadu da ilimi, ta iya wa'azi mai ratsa zuciya kaji tunaninka da rayuwarka gaba daya sun kaura lahira. Mahaifiyar Iman sai kuka take tana duban irin baiwar da Allah Ya yiwa *yarta da ta haifa a cikinta. Ta godewa Allah daya bata *ya irin Iman har Allah Yasa ta Musulunta a sanadiyyarta.
Daga karshe Muhammad ne yake karanta kur'ani Iman tana fassarawa. Ayar da suka karanta ta karshe wacce daga ita za'a rufe taro da addu'a saboda magruba ta kawo kai, ita ce Suratul Kafirun:


Mohammad:- "Bismillahir-Rahmaanir-Rahiim
Iman:- "Da sunan Allah Mai rahma Mai jin kai.
Mohammad:- "Kul yaaa- ayyuhal KAAFIRUUN!
Iman:- "Ka ce, "Ya ku kafirai!
Mohammad:- "Laaa'a -budu maa ta - buduun.
Iman:- "Ba zan bauta wa abun da kuke bauta wa ba.
Mohammad:- "Walaaa'antum -aabiduuna maaa'a'a-bud.
Iman:- "Kuma ku, ba ku zama masu bauta wa abun da nake bauta wa ba.
Mohammad:- "Wa laaa 'ana 'aabidummaa 'a'maa abbattum,
Iman:- "Kuma ni ban zama mai bautawa wa abin da kuke bauta waa ba.
Mohammad: "Wa laaa antum 'aabiduuna maaa'a -abud.
Iman:- "Kuma ku, baku zama masu bauta wa abin da nake bauta wa ba.
Mohammad:- "Lakum Diinukum wa li-ya Diin.
Iman:- "Addininku na gareku, kuma ADDININA yana gareni.
Sai aka dauki kabbara gaba daya wajen. Aka rufe taro da addu'oi sannan aka tashi.
KARSHE!!!
ALHAMDULILLAH.


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki da ya sanya na kammala muku karshen littafinnan lafiya, na gode da bibiyata da kukai.


@ watsapp 08097365237
@2go............reedwan2021

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login