Showing 78001 words to 81000 words out of 110329 words

Chapter 27 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt

22 Feb 2025

7479

yayi dariya ya ce "Ai ni zuwa Abuja zai yi min wuya, kasan yanayin aikina. Amma nan da wata guda zan dauki hutun bankina, a gidan zamu zo muyi honey moon ni da amaryata.
Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Kaji Sarkin makaryata, karya kake yi kana cewa ka samu mata har yau babu wanda ka taba nunawa ita. Najib ya ce "Wallahi da gaske nake, yau kuwa zaku gaisa da ita da bakinta zata fada maka sunanta. Suhaif yaji muryar mace ta karbi waya a hannun Najib ta gaishe da Suhaif, suhaif ya amsa cike da tunanin kamar ya san mai muryar. Sai ya ce "Amarya yaya sunanki? Ta ce "Sunana Naja'at, Suhaif ya zabura ya tashi tsaye ya ce "Wacce Naja'at? Babu tantama har muryar Naja'at kanwarsa ce. Ta bawa Najib wayar, ta zura daki da gudu itama sai yanzu ta gane Suhaif ne, dan Najib bai fada mata ko waye ba. Najib ya karba yana dariya ya ce "Ita ce matata, wallahi ita zan aura insha Allah. Mamaki ya rufe Suhaif ko kadan babu wanda yasan Najib da Naja'at suna soyayya. Bayan wata guda Suhaif ya zo Kano aka sha bikin Zubaida da Muslim, Najib da Naja'at. Suhaif yayi musu hidima da dukiyarsa abunsa, mutane suka yi ta mamaki duk wanda ya zo bikin ya kunshi goma ta arziki.


Gidan Amare ya kawata da gadaje da kujeru, show glass da kayan kicin duk na Italy ne Dubai da London. Baba na Kano ya sayi wasu, Suhaif kuma ya sayi sauran. Bayan ansha shagalin biki Suhaif ya koma Abuja, cike da damuwa kan damuwa. Yasan yanzu idon kowa ya dawo kansa dole za'a dame shi da zancen aure a dangi. Hankalinsa a tashe duk ya bi ya sukurkuce yana cikin tashin hahkali. Tunda ya kasa zabar wata ya aura wacce yake so, yake jira kuma shiru ba ita babu labarinta. Suhaif ya dubi sama da kasa a gidansa babu abinda ya nema ya rasa na rayuwar jin dadin duniya. Ya jawo wata brief case ya bude babu abinda ke cikin ta sai Dallers, ya wurgar da akwatin, kudin da ke ciki ya watse a tsakiyar dakin, ya buga kai a jikin gadon da yake zaune. Ya ce "Babu abinda na nema na rasa a duniyar nan amma bana jin dadin rayuwata saboda na rasa Iman, na rasa farin cikina.


Kwanci tashi shekarar auren su Najib uku. Su Naja'at har sun gama bautar kasa. Zubaida ta haifi *yan biyu mace da namiji aka saka musu suna Hauwa da Adam. Amma Naja'at da Najib Allah bai basu haihuwa ba, suna neman haihuwa ido rufe.
Suhaif da Najib suka je Umara a watan Maulud. Ba su cika zama a katafaren Hotel din da suka sauka ba, koda yaushe suna Harami. Babu abin da suke sai ibada, babbar matsalar Najib shine Allah Ya basu haihuwa shi da matarsa Naja'at, sai kuma Allah Yasa a kara masa girma a wajen aiki. Suhaif kuwa bayan ya nemawa kansa da Iyayensa gafara, sai addu'ar Allah Ya hada shi da Iman kuma ya aureta. Domin ya kasa aure har yanzu bayan duk abokansa da kannansa sun yi aure sun hayayyafa. Dawafi suke tayi, Suhaif ya daga hannu yana addu'a fadi yake "Allah Ka jeho min Iman ina zuwa Nigeria, Allah Ka sa in auri Iman. Allah Kai ka halicceni ka halicci Iman Allah Kasa Iman ce matata. Allah Kai ka hadani da Iman Ka rabamu Allah Ka sake hada mu alfarmar Annabinka Muhammad (S.A.W). Najib dake kusa dashi ya karasa salatin. Suhaif ya juya ya kalli Najib ya ce "Daman kana jin abunda nake cewa? Najib ya ce "Wanda yake nesa da kai ma zai ji balle ni da nake kusa dakai, ai a fili kake fada baro-baro. Ina jinka wannan shine zagayenmu na shidda amma abu daya kake roko Iman! Iman!! Iman!!! Kawai kake ambato. Ba gara ka dinga sirkawa da idan ba ita ba wata da ta fita. Wani tsoho Bahaushe a bayansu ya ce "Ai ina bayanku duk zagayen nan da kuke yi Iman kawai kake kira. Wasu mata larabawa guda biyu a gabansu kawaye ko kuma ya da kanwa suma tare suke zagayen sai suka waiwayo suna kallon Suhaif kamar sun san su ko kuma suna jin abunda suke cewa. Duk da dai bakaken kayane a jikin matan tun daga sama har kasa babu abinda zaka gani sai farin tafin hannunsu. Sun rufe fuskarsu da nikaf. Hawaye ya kwararo daga idanuwan Suhaif ganin ya fara zautuwa har ya zama abin kallo saboda ambaton Iman. Son ta ya zame masa tamkar numfashinsa, yadda dole zaiyi numfashi haka dole Iman tana ransa.
Da suka kewayo na bakwai kenan, sai suka yi kokarin fitowa daga wajen dawafin zuwa bayan mukami Ibrahim dan suyi sallar Nafila raka'a biyu wacce ake yi idan an gama dawafi. Tare suka fito da Bahaushe tsohon nan na bayansu da matan larabawan nan guda biyu na gabansu suma sun yi zagaye bakwai. Suka yi nafila a waje daya. Dai-dai lokacin aka kira sallar magruba. Suka jira aka yi sallar Isha'ai. Suhaif yana addu'a, sai Najib ya ce da Suhaif "Muna jinka fa har yanzu. A zuciyarsa yake addu'a amma baya sanin sanda addu'ar take fitowa, Iman dai yake kira. Tsohon nan ya ce da Suhaif "Yaro wacece Iman? Najib ya ce "Wacce yake so ya aura amma bai san inda take ba, kuma ya kasa daina sonta. Tsohon ya ce "Allah Sarki sannu yaro, Allah mai amsa addu'a ne zai bayyana maka ita kaji ko Insha Allah. Suhaif ya kasa magana amma a zuciyarsa yace amin.
Daya daga cikin larabawan nan biyu ta matso tayi musu sallama, su duka ukun suka amsa. Tayi magana da larabci, su duka ukun basu gane abunda take cewa ba. Sai suka ji tayi Hausa ta ce "Allah mai karbar addu'a ya hadaka da Iman. Sai suka zazzare idanu suna kallon-kallo, su kalli junansu su kalleta babu wanda ya iya bata amsa ko kuma ya tambayeta me take nufi. Babban abun mamaki Balarabiyar Saudia da ta iya Hausa radau. Bayan wannan ma ya akayi tasan sunan Suhaif. Tasa hannayenta farare tas ta bude nikafin dake fuskarta sai ga fuskar Iman. Iman ce Allah ya hada Suhaif da ita inda bai taba tsammani ba. Su duka ukun suka hada baki suka ce "ALLAHU AKBAR!


Kafin Suhaif ya ce komai sai da ya tashi yayi sallar nafila raka a biyu ya idar sannan ya ce "Iman! Iman!! Kece? Ta yi dariya nan tata mai kayatar da mai kallonta. Ta ce "Yaya Suhaif ni ce. Cike da fargaba yana in-ina ya tambayeta ya ce "Iman kin yi aure? Kafin ta bashi amsa na kusa dashi zai iya jiyo bugun zuciyarsa saboda fargabar irin amsa da zata bashi, ba Suhaif kadai ba har da Najib da tsohon nan zuciyarsu bugawa take uku-uku Allah ya sa amsar ita ce bata yi aure ba. Iman tayi murmushi gami da rufe ido don kunya, can ta dago taga sun zubo mata ido suna jiran abunda zai fito daga bakinta. Ta ce "Banyi aure ba, Najib kai fa kayi aure? Najib ya ce "Eh nayi aure amma Suhaif baiyi ba, su duka suka yi dariya. Najib ya ce "Ai nasan Suhaif kike so ki tambaya ko yayi aure ko baiyi ba, to baiyi ba. Shi kuwa gogan sai murmushi yake kawai dadi zai kashe shi. Najib ya zunguri Suhaif ya ce "Ta shi ka sake yin nafila raka'a biyu bata da aure. Suhaif ya tashi ya tayar da ikama, ita kuma Iman sai dariya take yi musu kawai.
Kamar yadda su Najib suka saba idan suka idar da sallar Isha'i sai su koma Hotel su ci abinci, su yi wanka, sannan su kwanta ba tare da sunyi shafa'i da wutiri ba. Su tashi karfe biyun dare su dawo masallaci suyi ta nafifili har sai kusan asubah sai suyi shafa'i da wutiri, suyi sallar asubah tare da Liman. Bayan an idar sai suyi ta dawafi har gari ya waye. Sannan su koma gida suci abincin safe sai su sake kwanciya suyi barci har sai da azahar suke tashi suyi wanka suci abinci sannan su koma Harami ayi sallar azahar dasu.
Suhaif, Najib, Baba tsoho, Iman da kawarta suka fito daga Masallaci zuwa bakin titi. Iman ta ce "Ya kamata mu je ku ga gidan da nake zaune, Najib ya ce "Tare da *yan garinku ki ka zo? Iman ta ce "A'a ni ai yanzu shekara ta hudu kenan a kasar nan ina karatu a jami'ar koyar da ilimin addini. Na kammala karatun waccan watan muka gama, akwai gidan da nake zama, anan kurkusa babu nisa, mu je ku ga gidan. Suhaif yayi sauri ya amsa mata da "To muje.
Baba tsoho ya mikawa Suhaif da Najib hannu suka gaisa ya ce "To na barku lafiya zan tafi masaukina naga hanyar ba daya ba ce. Suhaif yasa hannu a aljihu ya dauko Riyad da yawa ya bawa tsohon. Mamakin kudin nan mai yawa ya rufe tsoho sai godiya da addu'a yake yiwa Suhaif Allah Yasa Iman rabonsa ce. Suhaif yaji dadin adu'ar baba tsoho. Ya sake ciko hannu da Riyad ya sake bawa tsoho. Tsoho ya sake rike baki yana mamaki. Suhaif ya dauko katin da yake dauke da adreshinsa da nambar waya ya bawa tsohon ya ce idan sun koma Nigeria ya nemeshi zai yi masa alheri. Najib cewa yake "Ai kai dan tsoho Allah Ya hadaka da arzikinka tunda Allah Yasa a gabanka Suhaif yaga Iman. Iman da kawarta suna gefe sai murmushi Iman take kawai.
Suna tafiya a hanya Najib yake cewa "Af ban tambayi sunan kawar taki ba ko gaisawa ba muyi ba. Iman ta ce "Sunanta Zainab ai bata jin Hausa kuma bata jin turanci Balarabiyar baharain ce. Da kyar Iman ta yarda suka jera da su Suhaif saboda girmamawa sai take tsayawa a bayansu. Saida Suhaif ya roketa sannan ta yarda suka jera. Farin ciki ya hana Suhaif magana sosai, Najib da Iman ne suke hira. Idan za'a auna yawan farin cikin Suhaif da Iman ban san na wanda zai rinjayi na wani ba.


Yo aini bakin ciki ne ya rufe ni, na san ba na da wani abin katabus da na shiga takara, tunda har yanzu Hamma Huzaifa ya na sonta,,,, uhmmm wayyoni Masoyiyata!!!


Reedwan Suraj Isma'il




:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI


Sun isa katafaren gida mai kyawun gaske. Iman ta ce su shigo ciki babu damuwa. A katafaren wurin cin abinci suka iske mutanen gidan an shake teburi cike da abinci kala-kala da abun sha iri-iri. Abunda zai fi daukar idon mai kallon teburin bankararrun dakwalan kajin da suka yi bake-bake akan plates. Teburin mai daukar kujeru goma sha biyu ne don haka akwai sauran kujeru birjik.
Su Suhaif suna tsaye, Iman ta karasa wajen wadanda suke zaune tayi musu wata magana. Maza ne guda biyu, daya balarabe daya kuma bakar fata ne amma shima sai kayi masa kallan kurilla zaka san ba balarabe bane, hancinsa, farar fatar, laushin gashin, dogon gemun duk irin na larabawa ne. Sannan da wata mata balarabiya itama tana zaune. Maza biyu suka taso suka rungume su Suhaif irin gaisuwar larabawa. Bakar fatar yayi musu Hausa ya ce su zauna su ci abinci. Najib da Suhaif suka zauna kusa da daya matar, suka hadu su bakwai kenan suna cin abinci.
Balaraben nan mai fara'a yana so suyi hira da su Suhaif toshi ba turanci, su babu larabci, haka sauran matan ma larabawa ne ba turanci. Su Iman sun bude fuskokinsu sun daga nikaf din sama don haka Suhaif yana ta satar kallonta, ya ga ta kara kyau da fari har tana kokarin fin larabawan kyau. Wayyo dadi kan dadi yau zuciyar Suhaif sumul sai farin ciki.
Iman ta katse tunanin Suhaif ta ce "Af na manta ban gabatar muku dasu ba ko? Ta dubi Suhaif ta nuna bakar fatan nan ta ce "Wannan shine hamma Huzaifa dana baku labarinsa. Hamma Huzaifa? Suhaif da Najib suka maimaita. Numfashin Suhaif ya dauke cak saboda tashin hankali domin yasan akwai tsohuwar soyayya tsakanin Hamma Huzaifa da Iman.
"To koma dai har ya aureta ne ta boye musu? Suhaif yake tunani a ransa. "Babau tantama mijinta ne dan haka ma Iman ta kauro Saudia, idan ba haka ba ta yaya zata dawo Saudia da zama haka kawai? Iman ta nuna kawarta Zainab ta ce "Zainab kuma matar Huzaifa ce. Sannan numfashin Suhaif ya diro zuwa kahon zuciyarsa don saboda kwanciyar hankalin daya samu.
Iman taci gaba da cewa "Yanzu Hamma Huzaifa yana koyarwa a wata Jami'a a kasar Baharain, a can ya hadu da Zainab ya aureta, Allah Ya albarkace su da *ya*ya biyu mace da namiji. Macen aka sa mata sunana Fatima, namijin kuwa aka saka masa suna shima Huzaifa. Suhaif ya nanata sunan a ransa Fatima! Lallai har yanzu Huzaifa na son Iman kenan? Amma kwalelensa matata ce. Iman ta nuna balaraben ta ce "Shi kuma sunansa El-Sadik, dayar kuma matarsa ce, sunanta Na'ima. El-sadik abokin Hamma Huzaifa ne tare suka gama karatu a Madina, shi kuma anan kasar yake koyarwa, nan ne gidansa, Allah bai basu haihuwa ba. Suhaif da Hamma Huzaifa suka sake yin hannu suka gaisa. Iman ta ce da Huzaifa. Kamar yadda na fada maka na taba zama a gidansu, Huzaifa ya ce "A Kano suke kenan? Iman ta ce "A wani gari sunan garin Doko. Najib da Suhaif sunyi mamakin yadda aka yi Iman bata bawa Huzaifa labarin rayuwarta ba, bayan rabuwarsu saboda shakuwar da su kayi tun tana yarinya. Amma daga baya sai suka daina mamaki da suka tuna Iman ba ta da surutu, suma dalili ne yayi dalili yasa ta basu labarin Huzaifa. Domin tunda ta zo bata taba labarinsa ba saida ta kwabe gaba daya.
Suna cin abinci suna hira El-sadik kam yana so ayi hiran nan dashi ba Hausa, ba turanci sai Huzaifa ne yake fassara musu, sun ci sun koshi sosai. Iman, Zainab da Na'ima suka fara kwasar kwanuka suna kaiwa kicin. Huzaifa ya tambayi su Suhaif yaushe zasu koma Nigeria. Suhaif ya ce ranar lahadi suka yi bukking. Huzaifa ya yi dariya ya ce "Ku ce ma rana daya zamu tafi. A wanne jirgi? Suhaif ya ce "EGYPT. Hamma Huzaifa ya sake tuntsirewa da dariya ya ce "To ashe ma jirginmu daya, a Abuja zaku sauka ko? Suhaif ya ce "Eh a Abuja zamu sauka Hamma Huzaifa ya ce "Alhamdulillah! Tare zamu tafi kenan. Ina fatan za kuzo jalingo idan muka gayyace ku bikin mu ko? Najib ya ce "Insha Alla, mai zai hana zamu je. Suhaif ya gyara zama ya ce "Har da Iman zaku tafi? Huzaifa ya ce "Tare zamu tafi, daman itama shekara hudun nan data yi anan sau daya taje gida saboda karatu yanzu kuma ta gama. Ga matata ita ma sau daya na taba zuwa da ita Nigeria. Shine kuma yanzu daga Bahrain muka biyo mu dauki Fatima sai mu dunguma.
Iman ta zo ta kwashi plates ta nufi kicin, ita da Suhaif sai kallon-kallo suke. Suhaif ya bar sauraron hirar da Huzaifa da Najib suke yi yana kallon abar kaunarsa. Kamar aradu ce ta fado daga sama haka Suhaif yaji sautin maganar Hamma Huzaifa a kunnensa ya ce "Ai bikina da Fatima zamu je, za'yi nan da sati biyu. Iman ta fito daga kicin itama kunnenta ya jiyo mata, sai ta tsaya cak. Wai! Wai!! Wa yaga zare ido wajen Suhaif? Ya kurawa Iman ido kem yana mata kallon "Haka zaki min? Najib ya hau doguwar addu'a yana tofawa Suhaif a zuci saboda tsoron halin da dan uwansa zai shiga. Huzaifa bai san muzuran da ake yi ba shi dai yana ta zuba musu labari.
El-sadik ya fito daga cikin daki ya zo ya sami su Huzaifa cikin harshen larabci yayi masa magana. Huzaifa ya dubi su Suhaif ya ce "Ya kamata muje inga masaukinku kun ga ranar da zamu tafi sai mu biya mu daukeku. Najib ya yunkura ya tashi ya jawo hannun Suhaif domin yasan Suhaif baya fahimtar komai tunda tashin hankalin nan ya rufta masa.
Suka dunguma su hudu suka nufi wajen mota Iman na rakasu a baya jikinta yayi sanyi. Suhaif kallonta kawai yake wannan karon ba kallon kauna bane, amma kuma bana tsana bane tabbas yafi kama da harara. Ya kasa kwatanto halin da zai shiga a rayuwarsa nan gaba. Yasan tabbas ya gama samun sukuni har abada. Ga Iman baro-baro sun hadu amma ta subuce ya rasa ta har abada.
Suhaif, Najib, Huzaifa da El-Sadik suka shiga mota suka nufi katafaren Hotal din da su Suhaif suka sauka wato Darul Tauhid yana daf da Harami. Har dakin Huzaifa ya bisu domin yaga dakin saboda ranar lahadi su biyo su dauke su. Ga duk wanda yasan Suhaif kuma yasan halinsa kallo daya zai yi masa yasan yana cikin halin damuwa, dakyar yake iya bude baki yayi magana. Najib da Huzaifa ne kadai suke hira. Huzaifa bai dauki komai a ransa ba, saboda haka ya dauki Suhaif a matsayin irin mutanen nan ne wadanda halittarsu ce haka basa son suyi magana. Huzaifa da El-Sadik suka yi musu sallama suka tafi. Tunda Suhaif ya jawo filon dake kan gadonsa ya dora kansa ya kwanta kai ka ce bacci yake yi mai nauyi, nan kuwa idonsa biyu tunani ne yayi masa yawa harma yake jinsa tamkar ba'a wannan duniyar yake ba. Najib yayi waya kicin din Hotel ya fadi irin abincin da abin shan da za'ayi musu order, bayan ma'aikatan sun zo sun jera musu akan darning table. Najib ya dinga tashin Suhaif, Suhaif yayi shiru kamar baya jinsa. Najib yasa hannu yana girgiza shi Suhaif yaki tashi, Najib ya fisge filon ya ce "Malam ka tashi mana meyasa ka cika damuwa ne akan kaddara da Allah ya jarrabceka? Kaifa Musulmi ne kuma Malami. Suhaif ya tashi zaune a fusace ya ce "Dalla Malam rabu dani, bana son bayaninka ko lallashinka, ka rabu dani kawai. Najib yayi murmushi ya ce "Har abun ya kai haka, nifa dan uwanka ne kuma ciwon da namiji ai na namiji ne, Suhaif ya harare shi ya ja dogon tsaki ya ja filon ya dora akai yana ta juyi yana tunani. Najib ya ce "Abinci zamu ci fa kuma saboda kai nayi order naga baka ci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login