Showing 63001 words to 66000 words out of 110329 words
Chapter 22 - YARENA ADDININA Book By Jamila Umar Tanko JUT.txt
janta suke yi. Nan da nan manyan Malamai suka bude Alkur'ani suka fara karatu. Ba su kadai ba jama'a da yawa suka ruga gida suka dauko Alkur'ani cikinsu harda Najib ya kwaso Kur'anan gidab gaba daya. Suhaif ma ya karba aka zagaye Iman ana tayi mata karatu. Ta dora hannu akai, ta nutsa kanta cikin gwiwowinta kamar zata nitse cikin kasa, saboda tsabar tsananin zafin addu'ar da take kona matsafan da suke jikinta. Ta mika hannu da kyar ta kamo bishiyar dake kusa da ita ta kankame bishiyar da karfi tana yare wanda babu wanda yake jin yaren. Haka kuma bai hanasu daina ragargazarsu da ayar Allah ba. "Mu muna sonta tun kafin ta rungumi addininku. Ta fada cikin wata kakkausar murya wacce ko kusa bata yi kama da muryar mace ba, cikin harshen Hausa take magana yanzu. Wani Malami ya ce "Karya kuke makiya Allah yau sai munga bayanku azzalumai. Kamar yadda kuka kashe sai an kasheku. Ana ta karatu an zagaye bishiyar da ta rike ta rasa inda zata sa kanta, idonta yayi jajawur sai zufa take keto mata tamkar ana ruwan sama ta jike hagaf. Ta sake cewa "Kuna kona mu kuna kashe mana *ya*yanmu da jama'armu fa. Sai su kuwa masu karatun suka sake daga murya suna karatun da karfi. Ukuba tayi ukuba, zafin kuna yayi zafi, sai Iman ta fadi kasa numfashi sama-sama. Baisa sun daina karatu ba, ana ta jan ayoyi masu karfi. Matsafan ji suke kamar ana musu ruwan wuta. Yau sunga ta kansu sun gamu da gamunsu, a yau suka yi nadamar haduwa da Iman, sun yi dana sanin nacin da suka yi shekara dashekaru. Tuba suke, hakuri suke bayarwa daga yau zasu rabu da ita. Ko hanyar da tabi ma sun daina bi, amma tuba da nadamarsu yau baza tayi amfani ba. Babu mai sauraronsu, babu mai tausayinsu, babu mai shirin sassauta musu. Tun ana jin abinda Iman take fada har ta fara magana a hankali yadda ba'a fahimtar ta har tayi shiru bata ce wa komai ta rufe ido kamar mai bacci. Ba'a tsagaita da karatun ba yi ake tayi. Can Iman tayi magana wannan karon muryarta ce. Ta ce "Gaba dayansu gasu nan sun mutu, sun kone kurmus da wuta. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya fada a baiyane "Alhamdulillahi. Ana ta karatun ba a daina ba har saida Iman ta tashi zaune daram tana kallon kowannensu daya bayan daya cike da mamaki. Sai ta tambayesu "Me yake faruwa? Suka tsaya da karatun itama suka tambayeta meya faru tsakaninta da matsafan? Ta yi shiru tana tunowa can ta ce "Na gansu suna ihu suna kamawa da wuta daga karshe suka fadi suka mutu, sun kone kurmus gaba daya garinsu ya kone kayan tsafinsu ma ya kone. Sai gaba daya *yan wajen suka yi kabbara. Malami daya daga cikin Malaman ya ce "Muna miki albishir kuma muna taya ki murna daga yau kin sami lafiya, kin rabu dasu har abada da izinin Ubangiji. Wannan wutar da kika gani tana konasu karatun da muka taru muka yi miki ne don haka mun konesu kurmus da ayar Allah.
Iman taji dadin da tunda uwarta ta haifeta bata taba ji ba. Sai ta rushe da kuka tana godiya ga Allah. Wani Malami ya ce "To ai shikenan sai ta dauki kayanta ta koma gidan su Suhaif ta ci gaba da rayuwarta, ku kuma jama'ar gari kunji da kunnuwanku ba laifinta bane don haka banda tsangwama da kananan maganganu. Samun mutum irin Iman sai an tona a wannan zamanin. Ta sadaukar da rayuwarta, ta sallama rayuwar jin dadin duniya saboda ta shiga Musulunci. Sai kowa yayi kabbara.
*Yan garin Doko gaba daya suka ji suna son Iman, saboda karfin Imaninta. Da gaske Iman take tana son Musulunci da *yan uwanta Musulmai. Yarinya mai kunya da ladabi, ko a hanya taga mutane zata yi musu sallama ta duka har kasa ta gaishesu. Haka jama'a suka gauraye wajen da yabonta. Suhaif yaji dadi sosai har kamar zaiyi tsalle don murna. Ya dauko jakar kayanta ya dauko mata takalmanta ya ce "Iman saka takalmanki ki zo mu tafi gida kiyi wanka, kici abinci ki huta kinji. Ta sharbe hawaye ta yi murmushin karfin hali ta ce "Na gode Suhaif Allah Ya saka muku da alheri kai da Iyayenka, *yan uwanka da mutanen Doko gaba daya. Ba zan kara ko kwana daya a garin nan ba, yanzu lokaci ne da zan koma gida wajen Iyayena in ga halin da suke ciki. Alhamdulillah abunda na zo nema na samu, na samu ilimin addinina. Zan iya kare addinina in kuma bada hujjoji masu karfi da za'a yarda abunda nake bautawa shine gaskiya. Hakika zan sami Iyayena in musu wa'azin da zai ratsa su, su karkato zuwa ga addinina musamman Mahaifiyata nafi ji, ta Mahaifina mai sauki ne domin yasan gaskiya karfinsa aka fi kawai. Ga Mama Tabita mai kaunata zan so ta kasance Musulma ba mushirika ba. Zuwana Kano da Doko na karu sosai, kuma a sanadiyyar haka na samu lafiyar ciwon da ya dade yana addabata.
Malamai su ka ce "Ai haka ya yi gara ki koma garinku ko hankalin Iyayenki zai kwanta, kin bar gida shekaru biyu kenan. Wannan hukuncin bai yiwa Suhaif dadi ba ransa ya baci, jikinsa yayi sanyi, ya shiga damuwa. Baya son Iman ta tafi ta barshi. *Yan sanda suka ce to ta shiga motarsu, su kaita Kano sai su sakata a motar garinsu. Suhaif ya yi caraf ya ce "A'a ku barta gobe zan kaita Kano in sakata a motar garinsu. Babansa yayi wuf ya katse shi ya ce "A'a ka bari tunda ga masu tafiya ka bari a kaita yau mana. Kafin Suhaif ya sake magana Iman har ta shiga mota, dan sanda daya ya karbi kayan Iman a hannun Suhaif ya saka a mota. Malamai suka shiga motocinsu, *yan sanda ma suka shiga, kafin aja motar *yan garin suka baibaye jikin wundon da Iman take zaune suna tayi mata sallama da fatan alheri. Iman tana hawaye tana mika musu hannu suna musabaha da bankwana ko rai kanga rai. Zubaida da Naja'atu suka zo wajen Iman, sai kuka ya kece musu su duka ukun. Zubaida tayi karfin hali ta ce "Iman ki yafe mana abubuwan da muka yi miki, baki taba yin fushi ba, baki taba kai kararmu wajen wani ba, bakya gaba damu. Cikin kuka Iman ta ce "Na yafe muku tuntuni Zubaida ku yafe mun nima.
Suhaif da Najib suka karaso jikin wundon Iman, sai kuka ya sake barkewa Iman ganin hawaye daga idanuwan Suhaif. Suhaif yayi karfin hali ya ce "Iman tafiyarki zata iya haddasamun abubuwa guda biyu, na daya zan iya rasa jin dadi a rayuwata har abada, na biyu zan iya kamuwa da ciwon rashinki har ya ja in iya rasa raina saboda damuwa. Iman karki tafi ki barni. Ta ce "Suhaif karka damu, kada rashina ya haddasa maka ciwo, Allah ne ya hada mu, kuma shine zai raba mu a yau. Shine kuma idan Ya so da izinin Sa zamu sake haduwa. Zai yi wuya in manta da kauna da halaccin da kayi mun a rayuwata, babu wani mahalukin daya taba sadaukar da rayuwarsa a kaina irinka. Ka soni a lokacin dana zama abar tsana, abar tsoro, abar gudu. Ina sonka nima bazan daina ba ko zai zamanto bazan sake ganinka ba har karshen rayuwata...... Ba ta karasa maganarta ba aka ja motar suka tafi. Tana hangen Suhaif yana ta bin motar da gudu yana ce wa "A tsaya! A tsaya!! Kuka mai zafi ya rufto musu ita dashi. *Yan gari suna ta dagawa Iman hannu har saida suka daina hango motar. Gwaggo da *yan matanta kuka suke tukuru na rabuwa da Iman. Haka jama'a da yawa basu shirya yin kuka ba, amma sai suka ji hawaye ya kece musu saboda bakin cikin tafiyar Iman. Sabo turken wawa, Iman ta shiga ransu sun saba da ita, ta saba dasu.
Zaku tausayawa Suhaif idan ku kaga halin da yake ciki, a cikin kasa ya zauna turmus yana damkar sawun tayar motar da Iman take ciki. Najib ya dade yana bashi baki amma kamar zugashi yake. Kowa ya watse ya barsu shi da Najib a wajen. Suhaif yaki tashi su tafi shi kuma ya kasa tafiya ya barshi, Suhaif sai rokon Najib yake Allah Annabi yake, ya tafi ya kyale shi anan shi ba zai koma gida ba, Najib yaki tafiya. Baba ya fito sallah Masallaci ya hangosu a zaune sunyi jugum-jugum ya zo ya same su, ya tambayesu me suke yi. Najib ya fada masa abunda yake faruwa. Ya shiga bawa Suhaif baki akan yayi hakuri ya manta da Iman Allah zai iya bashi wacce tafi ta. Suhaif yana dagewa shi fa Iman yake so gashi bai karbi adireshinta na garinsu ba, babu inda zai ganta. Haka Baba da Najib su kayi ta lallashin Suhaif da kyar Suhaif ya tashi suka nufi gida.
Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka.
Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin.
Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode.
Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake?
Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx
*************** YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Dole in damu saboda nasan meye sanadin mutuwar tasu. Shi yasa nake kaffa-kaffa ko da Malamina ko a kawayena *yan ajinmu nake gudun hatsaniya ta hadamu, da zarar sun harzuka sai inyi ta basu hakuri, amma suki hakura lallai sai sun daga murya asan muna fada, rashin sani sai su zazzageni. Zasu kwanta da daddare lafiya zanyi mafarki an kashesu da safe za ace min sun mutu. Da naga anyi haka sau daya, sau biyu, kafin ayi na uku sai na hada kayana cikin dare zan gudu in bar garin. Niyyata kuwa inkaura dokar daji inyi rayuwa da namun daji in sun gaji dani su cinyeni. In shirya kayana in fito inyi ta tafiya, sai naji hankalina ya dauke in fadi in yi ta barci, sai in yi mafarkin matsafan sun daukoni aka sun dawo dani har dakina kan shinfidata. Ina farkawa daga barcin a shinfidata zan ganni, inyi ta mamaki. Mun yi haka dasu yafi a kirga. Da ga karshe dole na hakura na zauna. Amma basu dai na hadani fada da jama'a ba suna kashesu cikin dare. Allah cikin ikonSa jama'a basu gane ba har sai da Maimuna *yar garinmu tazo ta tona min asiri. Ta fadi gaskiya bata yi karya ba, ta sanni sosai duk da ba kawarta ba ce kawar kannen Hamma Huzaifa ce su Bilkisu Islamiyyarsu daya.
Bayan na sha kuka da takaicin tona asirin data yi min, sai bacci da ciwon kai ya kamani. Hakika gangar jikina ce a kwance ruhina ya tafi wajansu, ranar raina a bace ina ta zaginsu akan su rabu dani, su rabu da jama'ata. Nayi-nayi inyi addu'a Allah bai bani ikon yi ba, ina ji ina gani suka kashe Maimuna. Su Baba, su Goggo a kaina suna tashina ban farka ba sai da kurwata ta dawo, na farka daman ba bacci bane. Ina tashi kuwa na samu labarin Maimuna ta mutu, daman ko basu koreni ba dole in kori kaina.
Bayan na tafi samari suka bini zasu dake ni, to tun daga nan na rasa hankalina, suka turani tsohon ginin gidan Mahaukacin nan na shiga. Sun sami yadda suke so, Musulmai sun koreni, na zama ta su kenan. Na zamo a zaune kawai nake sun zagayeni babu ci babu sha, babu alwala bare salla, bana magana balle inyi addu'a. Gagarumar liyafa suka hada cikin dare a cikin gidan don murna, yau na zama tasu, yau sunci galaba kaina. Mutanen da nake so wato Musulmi sun kore ni daga cikinsu kwata-kwata. Ta kai ta kawo na ma daina ganinsu a mafarki ido biyu nake ganinsu. Suhaif ya ga jini an diddiga tun daga kofar gidan har cikin dakin dana ke, su suka disa akan takalmana, suka daura takalmi daya a akan saman rufin dakin yana diga, daya kuma yashe a tsakar gida da jini a jikinsa. Sunyi haka ne don Suhaif ya gani ya shaida ni mayya ce, suka daura min jajayen kyalle a jikina, sai daga baya na ciccire.
Suna fakon Suhaif sosai, sun kudiri niyyar sai sun kashe shi, saboda shine kadai ya rage mai takura musu da addu'a, shine bai tsane ni ba, bai rabu da zuwa inda nake ba. Babu makawa sun gama shirye-shiryen kashe shi tsaf a cikin daren dana ce masa ya kwana yana sallah yana addu'a kada yayi bacci. Da suka je zasu kashe shi suka kasa shiga inda yake balle su ganshi su kashe shi, sai suka kufula a daren kwana suka yi suna gana min azaba. Ban damu ba tun da mutuwa nake nema.
Babu wadanda suka jawo min wannan matsananciyar rayuwa sai Mahaifana, tun farko da na hadu da Matsafan da sun hadu sun taru sun rabani dasu da karfin addu'a da haka bata faru ba, duk da nasan kaddara ce. Amma kowannensu addininshi daban, wannan yana jin haushin wannan, idan ya kawo mai addu'arsa yana ganin kara min ciwo ake, kawai sai rigima ta harde su, daga karshe suka kyaleni da ciwo yana bibiyata har girmana. Duk lokacin da waninku ya hadu da dangina ku shaida musu abubuwan da suka faru dani har izuwa mutuwata. Nasihata zuwa ga Mahaifana itace su dawo su rungumi addinin Musulunci, suma su mutu a cikinsa kamar yadda nima zan mutu Musulma.
Iman ta rushe da kuka mai tsanani sai jama'a da dama a wajen tausayinta yasa su kuka suma. Cikin kuka ta dukar da kai kasa ta ce "Na gama labarina ku kasheni kamar yadda ku kayi alkawari, na gaji da rayuwar wulakanci da kyama da tsangwama a cikin *yan uwana. Kafin wani ya bude baki yayi magana, ganin Iman akayi ta daka tsalle ta fadi can gefe kamar wani ne yayi ball da ita. Sai ta tashi a gigice tana kallon wani gefe tana magana kamar a kwai wadanda take gani mutane basa gani. Cikin harshen Turanci take magana take cewa "Ku rabu dani, karku matso kusa dani, baku zaku kashe ni ba, ku bar *yan uwana Musulmai su kashe ni. Suhaif yana jin haka ya tashi da gudu ya fisgota ya kawota tsakiyar Malaman yana fassara musu abunda yaji tana fada da Hausa. Sai suka gane cewar matsafan sun zo su kasheta saboda ta tona musu asiri. Yanayin halin da suka lura Iman na ciki shine matsafan suna rike da ita suna shirin su kasheta.
A gigice Suhai yake janta yana so ya kwace ta daga hannun matsafan duk da baya ganinsu yasan janta suke yi. Nan da nan manyan Malamai suka bude Alkur'ani suka fara karatu. Ba su kadai ba jama'a da yawa suka ruga gida suka dauko Alkur'ani cikinsu harda Najib ya kwaso Kur'anan gidab gaba daya. Suhaif ma ya karba aka zagaye Iman ana tayi mata karatu. Ta dora hannu akai, ta nutsa kanta cikin gwiwowinta kamar zata nitse cikin kasa, saboda tsabar tsananin zafin addu'ar da take kona matsafan da suke jikinta. Ta mika hannu da kyar ta kamo bishiyar dake kusa da